Showing 27001 words to 30000 words out of 171161 words
Chapter 10 - MATAN AREWA BOOK TWO COMPLETE PDF .txt
da ƙirjina ya yi mini, haka Baba da Baba ƙarami ma suka ta kwantar mini da hankali ta sigar nasiha kafin suka tambaye ni abinda nake son sha ko ci na nuna musu babu abinda nake da sha'awa a wannan lokacin basu daddara ba suka ce zasu taho mini da gashashshen nama da madarar yogot suka fice har da yaya Majid da ya rufa musu baya.
Sannu a hankali raguwar mutanen ɗakin suka fara miƙewa suna fice tare da cillo mana harara ni da Umma a faƙaice. Umman Salma ce kawai ta kasa ɓoye nata maitar sai da ta bayyana shi a fili bayan ta tsirkan da wata tsaki mai dogon zango ta ɗaura da faɗin"ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta, ai ga fili ga mai doki wanda ya iya sarrafa linzami shi ke da nasara. Gaskiyar Halima da take faɗin kin mallake Abbansu ashe abin ba iya kansa ya tsaya har da mazajenmu. Da yake ɗiyarki ce ɗiyar so ƴar gwal ƴar riritawa in tana jinya duk hankulansu ya rikice su kasa zaune su kasa tsaye, muma da muke gida bamu huta ba sai an rakito mu zuwa asibitin da ba gaira ba dalili. Abin taƙaicin ma wai akan namiji ta faɗa wannan halin wanda bai san tana yi balle fahimtar halin da take ciki, Allah dai ya kyauta".
"Haba Umma haba Umma!, meyasa ne haka dan Allah?. Ki dubi halin da take ciki fa kwananta nawa a nan bata san inda kanta yake ba sai yau ta samu kanta amma mu rasa abinda zamu fara faɗa mata sai irin wannan maganganun ai ya kamata mu bari sai t...".
Saurin dakatar da Salman daga maganar da ta ɗaukar Ummanta tayi, tana aika mata hararar da ta sanya ta rusunar da ƙwayoyin idanunta izuwa ƙasa. Cike da zallar ɓacin ran da ya bayyanar a cikin furcinta ta soma cewar"ke dalla banza me kika sani game da rayuwar duniya da har za ki dakatar dani?, koda yake ke har yanzu yarinya ce ba za ki fahimta ba. Amma nan gaba kaɗan za ki fahimci hatsarin waɗannan mutanen da nake nuna miki kike runtse idanunki ke ala dole ga mai ƴar uwa ko?, in ce dai ai ba ke ɗaya bace ƴar uwarta meyasa sauran bazo sun tsaya a kanta ba ai sanin hali yafi komai, wuce mu tafi gida".
A sanyaye Salma take faɗin"kiyi haƙuri zan zauna a nan tare da ita".
Sai a sannan Umma tayi magana bayan ta sauƙe wani ƙarƙarfan ajiyan numfashin da kunnuwana suka jiyo mini sautinsa ta furta"Salma ki wuce kuje kawai ba komai Allah ya yi miki albarka".
"Albarka kam ko ba ki sanya mata ba, tana ganin haske cikin lamuranta tunda mu dai da Allah muka dogara ba da wani malami zaure ba".
Zantukan Umman Salma kenan da suka sanya Anty Zakiyya miƙewa tsaye tsam ta nufo ta Umma ta dakatar da ita a zafafe ta ce"koma ki zauna Zakiyya ki koma ki zauna na ce bana son wani tashin hankalin kuma".
Kallon ɗaɗɗaya Umman Salma ta bimu dashi kafin ta fizgo hannun Salman da take tsaye bata da niyyar fita suka fice. Dai-dai sa'ilin da Anty Zakiyya ta saki kukan dake cin ranta muryarta har tana harɗewa wajen guda take furta"haba Umma! haba Umma wai sai yaushe zamu sama ƴanci a cikin gidan ubanmu?, Umma ko a waje kika yi cikinmu kika shigo dashi cikin gidan nan wulaƙanci da taka mu da za'ayi wallahi sai haka. Me take nufi da wannan zantukan natan? ".
A taushashe Umma ta kallo ta kallon ido cikin ido kafin ta ce da ita"Zakiyya komai lokaci ne wataran zai wuce". Furcin Umman ya sanya ni buɗe bakina da nayi kamar an ɗaure mini shi ta ce"Umma tun muna ƙanana kike faɗa mana wannan kalmar, wai shin sai yaushe ne komai ɗin zai wuce?, sai yaushe komai zai zo ƙarshe gobe ko jibi?".
Bata amsa mini illa goge mini hawayen da suke sintiri a fuskana da ta fara yi, Anty Zakiyya ma ta dawo kusa da Umma ta kifa kanta akan cinyarta tana sakin wani sabon kukan. Nima kukan nake yi marar sautin ina ƙara jin wani irin azababben ciwon ciki yana murɗe ni.
Mun ɗau lokaci a haka kafin muka tsagaita da kukan don kawunan mu saboda shigowar wasu nurses guda biyu da suka duba lafiya tare da yi mini wasu tambayoyin da na amsa musu shi.
Da taimakon Anty Zakiyya na tashi zaune na shiga bayin dake cikin ɗakin nayo wanka sannan na fito don bani da tsarkin da zan yi salla, ban gusa daga kan inda nake zaune ba su Abba suka shigo shida Baba sannu suka ƙara yi mini sannan suka ce maza na cinye namar da suka kawo mini ban don ina jin ɗanɗanonsa a bisa harshena ba haka kawai nake tusa shi ina haɗiyewa da ƙyar. Ganin ina ɗan ci ya sanya su ficewa izuwa ofishin likitan da yake duba ni, bayan sallan magrib hajiya Babba, goggo Jummai da Hajiya suka zo duba ni sunyi mini yaya jiki cikin ƙarfin hali nake amsa musu da kalmar alhamdulillah. Har aka yi ƙiran sallan isha'i suna nan sai da yaya Majid yazo ya ce su fito su tafi har Anty Zakiyya Umma kaɗai aka bari a wajena muka kwana tare da ita.
Koda dare ya tsala sam bacci ya gagari idanuna, Umma tana kan sallaya tana nafilfilin da na santa dasu. A hankali na cije leɓɓana na ƙasa ina runtse idona har ƙasan raina nake son ji da ganin halin da yaya Yusuf yake a ciki sai dai waye zan fara tunkara da zancen hakan a cikin ƴan uwana?, ba zama fara yiwa Umma maganar ba don yanda nake ji Anty Zakiyya da yaya Majid ba zan iya fallasa musu sirrin raina ba a wannan lokacin. Na gwammace na cigaba da danne shi a cikin zuciyata koda kuwa hakan zai yi sanadinyar tsayawar numfashina. Maganganun Umman su Anty Kubra suka fara dawo mini tiryan tiryan cikim kwanyata tabbas tana da gaskiya a wani dalilin zan ɗaurawa kaina damuwar wanda bai san ina yi ba a wani dalilin zan jefa rayuwata cikin hatsari na kuma hana iyayena kwanciyar hankali akan wanda ya juya mini baya a lokacin da nake tsammata masa tsayiwa tare dani har na ƙarshen rayuwarmu.
Ƙarƙarfan ajiyar zuciya na sauƙe ina shafa ƙasan marata a hankali kafin wasu hawaye suka fara biyo gefe da gefen kuncina, shikenan na rasa wannan cikin abinda ya rage tsakanin mu da yaya Yusuf shima yazo ƙarshe don haka bani da wata sauran alaƙa dashi balle tinaninsa ko damuwa da sanin halin da yake ciki su sama muhallin zama a ƙalbina. Jin an dalle mini idona da tocila bayan an ɗauke wutar lantarki ya sanya ni saurin rintse idanuna.
"Lafiya kuwa Na'ima kamar kuka ma kike yi?".
Umma ta faɗa da damuwa ƙarara a cikin furcinta, saurin kawar da hawayen idanuna nayi kafin na shiga shirya abinda zan faɗa ya gamsar da ita sai can na ce"Umma yanzu shikenan na rasa wannan cikin kena?". Bata amsa mini ba sai da ta taso daga kan sallayan ta dawo kusa dani cike da kulawa da tsantsar tausayin dake tsakanin uwa da ƴa take cewa dani"Na'imatu ki cire wannan damuwar daga ranki ba wayonki ko dabararki bace daman ya ba ki Allah ne ya ba ki kuma shi zai ƙara ba ki a karo na biyu. Ki cire wannan damuwar daga ranki domin jiya likitoti sun tabbatar mana da cewar kina ɗauke da lalurar hawan jini shan magani kuwa kaɗai ba zai sauƙaƙa ciwon ba har sai kin rabu da wannan tinane-tinane".
Shuru nayi mata domin nasan ko nayi yunƙurin cewa wani abun bakina ba zai bani haɗin kai wajen aiwatar da hakan, na lumshe idanuna a hankali ina jin tofin addu'ar da take yi mini har bacci ya ɗauke ni. Washe gari tun safe Anty Zakiyya da yaya Majid suka zo banyi mamakin rashin ganin Salma a tare dasu ba, domin daman nayi tinanin hakan Ummanta ba zata barta ta zo inda nake ba koda ita tayi niyyar kusantata haka nan ma Abasiyya nidai kam tunda na buɗe ido ban ganta ba haka nan ma Balkisu.
Tare dasu muka wuni sai yamma lilis su Abba suka zo suka duba jikin nawan likita ya ce in sha Allah gobe ma za'a iya sallamana zuwa gida naji daɗin hakan domin sam zaman asibitin bana jin daɗin sa. Ranar da su Hajiya Babba, Hajiya da goggo Jummai suka zo duba ni da dare Hajiya Babba ta ce Umma yau ita ma taje gida ta huta Hajiya ta kwana tare dani hakan kuwa aka yi Umma ta wuce gida tare dasu Hajiya ta zauna dani. Kamar kullum yau ma ban iya runtsawa ba duk da kuwa nayi ƙorafin hakan ga likitotin suka bani maganin bacci amma hakan baya tasiri a jikina, Hajiya da ita ma bata runtsa ba saboda yawaitan sauro a ɗakin ta dafo kafaɗana haɗe da faɗin"ba ki yi bacci ba Na'ima?".
Kaina na ɗaga mata da hakan ya bata damar ɗaurawa da"ki sawa kanki sallama domin shima Yusuf ɗim jikinsa da sauƙi kuma yana cikin asibitin nan".
Dan dam ƙirjina ya bada duk kasalar da nake ji a jikina suka wartsake na bita da kallon mamakin ta yaya aka yi ta san abinda yake raina kenan, murmushi ta sakar mini tare da ɗaga mini kanta alamar tabbatarwa kafin ta ce"ƙwarai kuwa Yusuf yana cikin asibitin nan".
MATAN AREWA
(Book two)
© Maimunah Tijjani Iyam
________________________________________
Page 4⃣9⃣
Ƙuri nayi da idanu ina kallon ta tamkar sokuwa cike da son hango gaskiyar zancen natan cikin ƙwayoyin idanunta. Kafaɗata da ta dafo ta janye hannunta daga jikina sai da tayi nisa kafin ta furta mini zancen da suka saka ni jin tamkar notunan kaina sun since don su zo mini a bazaran da ban taɓa tsammanin su koda a duniyar mafarkan da nake yi yayin bacci.
"Kamar yanda na faɗa tabbas Yusuf yana cikin asibitin nan kuma iyayenku maza sun sani har da Ummanki da ragowar mutanen, lokacin da kike cikin halin ciwo kina kwance rai a hannun Allah ba ki san waye a kan ki aka tabbatar da cewar cikin dake jikinki ya zube tabbas Ummanki ta shiga matuƙar tashin hankali musamman da likitotin suka shaida cewar tsananin damuwa da kuma tashin hankalin da kike ciki da hakan ya sanya jinin hau shi ne musabbabin fitar cikin. Nan har cikin ɗakin nan Binta taso tana faɗin wai daman suna da tantama akan cikin bana ɗan uwanta bane, kawai sunyi shuru ne tare da zuba ido har izuwa lokacin da za ki haihu aje ayi gwaji ƙwayoyin halitta a tabbatar da ɗan waye ne zafin hakan ya sanya Babanku ƙara harzuƙa har ya kai ga sun hana shi Yusuf ɗin duba ki duk kuwa yanda ya kafe musu da roƙo da makiya. Ummanki tasha kuka kamar idanunta zasu faɗu ba".
Tunda ta fara zancen nake sakin ƙwalla musamman da ta ambaci sunan yaya Yusuf, wani tuƙuƙun baƙin ciki ya zarge mini raina tabbas soyayya bata yi mini adalci ba ko kuma ince gabaɗayan mu bata yi mana ba tarasa wanda zata ba wa muhallin zama cikin raina sai wanda ya haramta a gare ni. Ta wani gefen zuciyata ina jin sanyi yana tsirga mini ji da nayi ta ce yaya Yusuf yazo roƙon su Abba domin duba ni hakan na nufin kenan yaji sauƙi hamdala na saka a cikin raina kafin na watsa rikiɗaɗɗun idanuna ga fuskar Hajiya da ita ɗin dai ni take kallon haske tocilan wayarta da ta kunna ta ajiye sakamakon ɗaukewar wutar nepa shi yake bani damar ganin fuskarta, muryata a dishashe nake kokuwa da numfashina kafin na zama sararin faɗin"meyasa Anty Binta zata jefe ni da wannan mummunan zargin?, Allah ne shaida ta ban taɓa keɓewa da wani namijin ba haka nan babu namijin da ya taɓa riƙe koda ɗan yatsata ne bayan Yusuf da aure ya halalta mana junan mu".
Sai da ta sauƙe ƙarƙarfan ajiyan zuciya da har na iya jiyo sautin fitar sa kana ta ce"ai na gaya miki tun ba yau ba Binta ta wuce duk inda kike tinani, hange ko kuma tsammani shu'uma ce da ta iya takunta ba tare da ta bar wani alamar da za'a bibiyi bayanta ba. Babban abin tsoro game da ita shine duk abinda tasa a gabanta da nufin kawar dashi da sai ta cimma nasara". Sai da ta sausauta amon muryarta sosai kafin ta ɗaura da cewar"bana ko shakkar faɗin sakin da ya gifta tsakanin ku da Yusuf ma da sa hannunta haka nan zubewar wannan cikin ma duk shirinta ne tunda har ta iya faɗin wai daman suna tantanmar kasancewar cikin bana ɗan uwanta bane Binta zata iya aikata komai ba tare da tinanin raɗaɗin da zuƙata zasu shiga ba matuƙar buƙatarta zata biya to a wajen komai dai-dai tunda daman ance in jifa ya wuce kanka to ya faɗa kan uban kowa".
Tagwayen ajiyan zuciya na sauƙe na ma rasa abin faɗi saboda yanda zuciya take yi mini dakan lugudai babu ƙauƙautawa da ƙyar na jawo numfashina kafin na ce"kowa ya yi nagari don kansa Hajiya, ai kowa ya yi mai kyau ya sani haka nan ma duk wanda ya yi akasin sa".
A raunane na ƙare zancen ina jin maganganun Hajiyan suna yi mini yawo a cikin kaina duk yanda naso yakice su abinda ya gagara domin bana ma son su sama gurbin zama a zuciyata balle har ta kwaɗaita mini yin aiki dasu na zargi Anty Binta kan abubuwan da suke faru a halin yanzu.
Maganar da Hajiya ta ɗaura dashi suka dawo dani izuwa cikin hayyacina daga karatun wasiƙar jakin da nake yi.
"Na'ima kina son ganin Yusuf shima kuma yana son ganin ki. Ku dukka biyun har yanzu kuna yiwa junanku matsanancin soyayyar da bakwa iya ɓoye ta sai da ta bayyana cikin idanunku har yanzu kuna son kasancewa a tare a matsayin mata da miji. Sai dai makiricin Binta ya raba ku rabuwar da zai yi wuya ku kuma cure ku dunƙule matsayin ma'aurata kamar yanda kuke a da, ta fatattaki farin cikinku gabaɗaya yayin da ta maye gurbinsa da baƙin cikin da ya yi bake-bake cikin rayuwarku. Ta kuma zamto sanadiyar zubewar cikin dake jikinki Na'ima ko ki yarda ko kar ki yarda komai da yake faruwa kuma yake kan faruwa a yanzu shirin Binta ne". Shuru na kuma yi mata ba tare da na ce da ita komai ina ta juyayin zantukan natan a cikin raina tare da yi musu tankaɗe da tarairaya. Ban dawo daga tinanin da na ƙara zurmawa cikinsa ba sai da ta kuma furta"ni nayi miki alƙawarin zan kai ki har ɗakin da Yusuf yake ko kuma naje shi na sanar dashi yazo nan ɗin".
Saurin girgiza mata kaina nayi hawaye masu zafi suna bulbulowa daga koramar idaniyata na ce"a'a Hajiya bana son ganin sa bana ƙaunar yin tozali da fuskarsa balle wata magana ta haɗa mu. Ki barsa kawai ya yi zaman sa inda yake nima na zauna a inda nake, addu'ar samun lafiya mai ɗaurewa kuma ba zan fasa yi masa ba wanda inda yaƙinin ko bamu ga juna ba Allah ya zai amsa mini ita". Wani murmushi naga ta sakar mini da hakan ya tilasta mini bin ta da ido a ƙoƙarin son fahimtar ma'anarsa ta hanyar karantar yanayin fuskarta sai dai sam ta hana ni damar hakan domin ta ƙi yarda mu haɗa idona.
"Kar kiyi ƙoƙarin boye sirrin da fuskarki ta ruga da ta daɗe da bayyana ta. Har ki cutar da zuciyar cutarwa mafi muni da raɗaɗi domin ciwon so bashi da makari ko kuma magani ta hanyar nunawa mutane cewar ba abinda yake damun ki, kin ganni nan nasan so na kuma san lahanin da take yiwa mutum a faƙaice ba tare da ya farga ba. Wallahi da don har na koma ruwa ba sai na nunawa Binta cewar duk makircinta a tafi hannuna take zagaye kuma na nuna mata iyakarta".
Saurin ƙara watsa mata idanuna nayi a idonta kaɗaj na hangi cewar da iya gaskiyarta tayi maganar, na rasa bakin magana domin Hajiya ta gama fahimtar dukkan sirrin dake raina babu wani abunda zan faɗa mata da zan gamsar da ita hashashanta ba haka bane, don haka shuru kawai nayi tunda an yankewa zabiya harshe ai babu sauran waƙa kuma. Nayi saurin rusunar da idona ƙasa domin wani kunyarta da ta yi mini lulluɓi.
"Yanzu dai ki kwanta in sha Allah da asubahi zanje ɗakinsa na sanar dashi, tunda sunce kema gobe za'a iya sallamarki".
Furcin Hajiya na ƙarshen kenan na buɗe baki da zummar yi mata godiya ta dakatar dani ta faɗin"ba godiya tsakanin mu Na'ima kema ƴata ce yanda na ɗauki su Hajara haka kema na ɗauki, don haka ki kwanta kawai". Ta ƙare zancen tana miƙe ta isa ga shimfiɗar da tayi a ƙasa ta kwanta lumshe idanuna nayi kamar bai bacci sai dai raina fal damuwa ce da fargaba wani sashin kuma ina ƙara girmama ƙarfin so da ƙaunar da Hajiya take gwada mini a wannan rayuwar, tabbas ta cika cikkakiyar masoya a gare ni irin wacce take tsayiwa da kai a lokacin tsanani lokacin da kowa ya juya maka baya kuma suka liƙawa kunnuwansu gayan tuwo suka kasa fahimtarka. Saƙa da warwara nayi tayi cikin raina na ƙulla wannan na since wannan har aka yi ƙiran assalatun farko ban runtsa ba, jin motsin Hajiya kamar zata tashi ya sani ƙara maƙe idona kamar mai baccin gaske banɗaki ta shiga tayo alawa tazo ta tada sallan sai da ta gama azkar ɗinta ta shafa doguwar addu'ar ta take yi kafin tazo ta fara tashi na ta hanyar bubbuga matashin da nake kwance a kai da kuma ƙiran sunana a hankali. Buɗe idona nayi ina kallon ta ce dani na tashi nayi salla na amsa da bani da tsarki ta jinjina kanta kafin ta ɗauki hanyar ficewa daga ɗakin.
Saurin dakatar da ita nayi da cewar"Hajiya wallahi tsoro nake ji kar Abba ko wani yaji cewar mun gana da Yusuf ko kuma Anty Binta ta kuma yi musu wani tijaran da daga ƙarshe rayuka zasu ƙara