Showing 129001 words to 132000 words out of 171161 words
Chapter 44 - MATAN AREWA BOOK TWO COMPLETE PDF .txt
hancinsa ya fuskanto su sosai haɗi da bada dukkan hankalinsa gare su kana ya ce"we can talk like this ba matsala?". Kansa ya ɗaga masa don ya fahimci zancen nasan inda ya dosa saboda kasancewar Abdul-aziz ne a wajen.
"Sakamakon gwajin da aka yi mata ɗazu da safe ya fito a iya tsawon lokacin da ta yi kwance tana jinya a wannan asibitin, a dukkan gwajin da ake yi mata bamu taɓa ganin wani abu a tare da ita ba haka nan gwajin da ake yi mata bai taɓa nuna tana ɗauke da wani ciwo ko lalura a tare da ita ba sai wannan lokacin". Tsagaitawa ya yi na tsawon daƙiƙai kafin ya ɗaura da"wannan sakamakon ya nuna tana ɗauke da ciwon daji wanda yanzu take a matakin ƙarshe, a ilmin likitanci ba zata haura watanni shida ba komai zai iya faruwa ciki har da rashin t...". Zaburan da Saif ɗin ya yi tare da kai bugu ga teburin dake gaban sa ya sanya likitan yin shurun dole kafin cikin shigar kwantar masa da hankali game da bashi ƙarfin gwiwa ya cigaba da cewa"ka kwantar da hankalinka ai ilmin gaibu Allah shi kaɗai ya barwa kansa sani, tabbas sai wa'adin mutum ya cika sannan ruhinsa ya yi bankwana da gangan jikinsa amma ita tana matakin ƙarshe ne a ciwon mataki mafi hatsari. Da wuya ta cigaba da rayuwa saboda ciwon ya ci jikinta sosai idan akwai wani abun da take buƙata daga gare ku da makusantan ta ko kuma wani buri ko muradin da take son cika wannan lokacin ne ya dace duk kuyi mata wannan, zamu ɗaura ta akan wasu magungunan da zasu taimaka sosai na shiga tashin hankali sosai da tun farko muka kasa gano hakan sai yanzu".
Har ya ƙare Saif bai ɗauke idanunsa daga kansa ji yake yi kamar bacci ya kwanta abubuwan suke gudana cikin mafarki da zaran ya tashi komai zai wuce, ko jinyar da Ummin nasun tayi bai sanya zuciyarsa yi masa zafi kamar na jin wannan zancen ba ajiyan zuciya kawai ya cigaba da sauƙewa tamkar wanda ya yi gudun ceton rai.
"Amma likita kun tabbatar da sahihancin wannan sakamakon kuwa anya ma na ta ne?. Don mu dai ba'a taɓa ce mana tana ɗauke da wani laluran ba balle wannan da har ya yi worst haka".
Furcin Abdul-aziz kenan da ya yi cikin tsantsan damuwar dake tattare cikin kalamansa, musgutawa likitan ya yi kafin ya ce"tabbas babu kuskure cikin wannan sakamakon na ta ne, domin nima da farko ban yarda ba sai da na yi da kaina na tabbatar da hakan".
"Yanzu babu yanza za'a yi kenan?".
"Akwai maganin da zamu ɗaura ta a kai in sha Allah zai taimaka".
Runtse idanunsa da ƙarfi Saif ya yi yana jin ƙirjinsa ya yi masa wani irin nauyin gaske, a hankali ya soma buɗe idanunsa yana sauƙe su akan fuskar likitan haɗi da cewar"try your best doctor ita kaɗai muke da". Cike da bashi tabbaci ya ɗaga masa kansa miƙewa ya yi ya fice daga ofishin sai Abdul-aziz ne ya tsaya ƙarban takardan sakamakon gwajin a inda suka zauna ɗazu ya iske ya ƙurawa hanyar shigowa ido sai tun daga kallon farkon da ya yi masa ya fahimci hankalin ba anan ya ke ba domin ya daɗe da yin nisa da barin gangar jikinsa, kusa dashi ya zauna a sanyaye ya ke faɗin"kayi haƙuri Saifuddeen ko ɗauki hakan a matsayi jarabawar rayuwar da duk wanda ya cika muminin ƙwarai baya guje mata kuma baya fushi inda ta riske shi, addu'a shine babban makamin da zamu riƙe yanzu sai kuma shawaran da likita ya bayar na cika mata wasu muradanta kayi haƙuri ta taushi zuciyarka tabbas na san abin is not easy but try".
Kansa kawai ya iya ɗaga masa kafin a hankali ya furta"thanks for standing at my side in this situation". Murmushi kawai Abdul-aziz ya sakar masa don ya fahimci ƙarfi hali kawai yake yi wajen ɓoye tarin damuwar dake cikin ƙalbinsa ba tare da sun bayyana bisa fuskarsa ba, sun ɗau lokaci a wajen cikin su babu wanda ya kuma yi magana kafin suka koma ɗakin bacci suka iske ta tana yi ganin hakan ya sanya su fita izuwa masallaci domin gabatar da sallan asr. Tun a hanya Farouk yake tambayar sa dalilin ƙiran da likitan ya yi masa cikin gaggawa amma sam ya ƙi bashi gamshashshiyar amsa sai ma sauya zancen da ya yi da wani daban.
Sai da aka jera kwana biyu a tsakani bai bari Farouk ya fahimci komai ba, a yinin na ukun suna zaune a ɗakin wayarsa ta soma ruri jikinsa a sanyaye ya fiddo da ita daga cikin aljihunsa ba tare da ya tsaya duban mai ƙiran ba ya ɗaga ya kara a kunnensa jin muryar yaya Majid ya sanya shi gyara zama suka gaisa sosai nan yake sanar dashi sai yanzu ya kunna wayarsa yake cin karo da saƙonsa da ya yi matuƙar sanya shi cikin farin-ciki sosai suka taɓa hira sannan suka yi sallama bayan ya gama jaddada masa saƙon godiyansa ga su Abba kafin ya zo mussamman ya yi shi da kansa.
Yana ɗago idonsa suka haɗa ido da Ummin, saurin rusunar da nashi ƙasa ya yi don baya iya kallon cikin idanunta matuƙar ba bacci take yi ba wani irin tausayinta na mussamman da su ma kansu ne ya mamaye masa rai da ruhinsa ji yake yi kamar ya fice titi ya yi hauka ko zai ji sanyin raɗaɗi da sukan da yake ji cikin zuciyarsa. Murmushi ya ƙaƙalo ya dasa a fuskarsa kafin ga ce"wannan shine wanda mahaifinsa ya yi sanadiyar samun lafiyarki Ummi mutanan nen sun yi min abunda b zan taɓa mancewa dasu ba a cikin rayuwata".
"Allah sarki Alllah ya saka musu in sha Allah nima zaka kai ni har inda suke nayi musu godiya da kaina". Amin duk suka haɗe baki wajen faɗi shi da Farouk da kuma Abdul-aziz kafin Ummin ta cigaba da cewa"baka sanar da ni sunan ta ba?".
Cike da mamaki ya ce"waye kenan?". Sai da ta kuma yin wani murmushi ta ce"wacce na ganku a hoto". Ƙatuwar ajiyan zuci ya saka kai tsaye ba zai iya fitowa ya faɗa mata cewar bai san sunan ta duk da a gabansa Majid yasha ambatan sunan amma bai taɓa damuwa da ya riƙe ba
Ka sanya a ranka cewar duk wani abun da ya same ta Allah ne ya ƙaddara shi domin shi likita bashi, ganin ya carke ya sanya Abdul-aziz saurin faɗin"Zakiyya sunan ta Ummi". Kanta ta jinjina ta ce"sai yaushe zan ganta Saifudeen?".
"Za ki ganta Ummi ai da yake ba a kusa take bani ta kin ganta". Ya faɗa yana haɗiye wani miyau mai kauri da ya taro masa a baki, wani kallo Farouk yake bin sa dashi na son ƙarin haske game da maganganun nasan wacece Zakiyya?, a ina suka san juna dashi da har yake faɗin sun ɗau lokaci tare?. Bai kai ga cimma amshoshin tambayoyin da ya yi wa kansa ba muryar Ummi ta katse mata hanzari"zan so na ganta kwana kusa domin yanzu bani da wani burin da ya wuce naga aurenku Saifuddeen kai da ɗan-uwanka".
"Ummi har cikin ranki wannan yana ɗaga daga cikin burin da cike son cimmawa?". Kai tsaye ya jefa mata tambayar ta ɗaga masa kanta tare da faɗin"ƙwarai kuwa ko ranar na mutu to tabbas kun cike min babban giɓin dake cikin zuciyata" . Sai da ya sauƙe ajiyan numfashi kana ya ce"kin kusa ganin wannan ranar Ummi zan cika miki wannan giɓin". Yana kawowa nan ya miƙe ya fice da sauri ya bar cikin ɗakin saboda hawayen da suka taru masa a kurmin idaniyan sa, da sauri Farouk ya rufa masa baya Abdul-aziz ma ya miƙe sai da ya yi mata sallama da addu'ar Allah ya ƙara lafiya sannan ya fice.
Yana fita cikin haraban asibitin ya zarce ya shiga motarsa ya yi lock ɗin kansa tare da ɗaura kansa kan sitiyarin motar, a hankali hawayen da suka cika koramar idaniyarsa suke tsiyaya suna wanke masa fuska. Knocking Farouk ya fara yi a hankali don ya ga shigar sa cikin motar sai ya ɗauki tsawon mintoti yana yi har Abdul-aziz ya ƙariso sannan ya buɗe, shiga suka yi Farouk ya zauna a gaba yayin da Abdul-aziz ya shiga baya.
"Yaya Saif wai duk wannan wasan kwaikwayon na menene?, wacece wannan Zakiyyan a ina kuka haɗu kuma yaushe?, meye kike ɓoye min cikin kwanakin nan? na fahimci kana cikin matuƙar damuwa amma ka ƙi bani damar tambayarka".
A jere Farouk yake jefo masa tambayoyin da ya sanya shi cije lebbansa kafin ya ce"wacce Ummi ta ga hotonta a cikin wayana ita ce Zakiyya". Da sauri ya tari numfashinsa"to yaushe kuka san juna da ita meyasa Ummi ta damu da maganarta?, meye dalilin shigar ka damuwa a wannan lokacin da ya kamata muyi farin-ciki da godiya ga Allah bisa warakan da ya sauƙarwa Ummi".
"Saboda na cika mata burinta Umar, Ummi tana ɗauke da ciwon cancer wanda take matakin ƙarshe likitoti sun ce ba zata wuce watanni shida a raye ba. Wanna shine burinta na ƙarshe da take nema a gare mu ta yaya kake tinanin zan iya kallon idanunta na gaya mata cewar babu wanj alaƙa tsakani na da yarinyar da ta gan mu a hoto tare bayan abinda zuciyarta take faɗa mata kuma ta zauna akan sa?, ta yaya kake tunanin zan iya kallon idonta na furta mata cewar hashashenta ba gaskiya bane ta yaya zan sanar da ita cewar burin da take muradi a kan mu ban shirya yin shi ba yanzu?. Ba zan iya ba ba zan iya ba Umar dole ce ta sanya ni yin komai".
Kuka mai sauti Umar ya fashe dashi tare da faɗawa jikinsa, jikinsa har wani rawa yake yi a filin yake bayyanar da raunin dake cikin ƙalbinsa. Cikin zubda hawaye Abdu-aziz ya furta"duk ni naja komai ni ne sila da ban ɗauki wannan hoton na turo maka ba, wataƙil da duk hakan bai faruwa ba wataƙil ta baka aikata abunda ya kasance ba halinka bane watau ƙarya ga mahaifiyarka".
"Babu laifinka Abdul daman tun can Allah ya ƙaddara faruwan sa shiyasa kaga ƙaddara ta sanya mu tsayawa a jahar yobe". Sai da ya ɗago Farouk ɗin da har yanzu yake jikinsa yana share masa hawayen fuskan sa yake faɗin"ka daina kuka ka daina addu'a za ka yi mata Umar shi zata fi buƙata, sannan kuma ai maganar likita ba zancen Allah bane da zamu bada dukkan yarda da yaƙinin mu gare ta babu wanda ya san ranar mutuwar wani mai wanda rai da rayuwa yake hannunsa. Duk abinda kaga ya faru da ita to ka sanya a ranka cewar daman hakan Allah ya rubuta a gare ta kaji?".
Kansa ya ɗaga masa cikin dushashewar murya ya ce"to yanzu yaya zaka yi da yarinyar fa?". Numfashi ya sauƙe a wahale saboda nauyin da ƙirjinsa ya yi masa kana ya ce"zan nema auren ta idan har ba ayi mata miji ba, zan aure ta ko don cikawa Ummi burin ta".
MATAN AREWA
(Book two)
© Maimunah Tijjani Iyam
__________________________
Page 1⃣0⃣7⃣
Tsif cikin motan ya ɗauki shuru ba a jiyo ko wani sauti illa na ajiyar numfashin da suke sauƙewa akai a kai, a hankali ya mayar da jikinsa ya jingina jikin kujeran motar tare da lumshe idanunsa yana jin nauyin da ƙirjinsa ya yi masa yana ƙara hauhawa. Sunan mahaliccinsa ɗari ba ɗaya yake ambatowa cikin ransa a ƙoƙarin samarwa kansa nutsuwar rai da kuma ruhi. Maganar da Farouk ya soma yi cikin dishashewar muryar shi ya tilasta masa buɗe marafan idanunsa da yake jin har wani zafi-zafi suke yi masa ya zube su akan sa.
"Yaya Saif Allah ya dubi kyakykyawan niyyarka akan wannan abun ya kawo maka komai da sauƙi, ya ba wa Ummi lafiya mai inganci".
A cikin zuciyarsa ya amsa da amin yana ƙoƙarin danne abinda yake jin yana taso masa a cikin zuciya, ya sakar masa da taƙaitaccen murmushi kafin Abdul-aziz ya soma faɗin"yanzu ta ina zaka fara? idan kuma an riga da anyi mata miji fa yaya kenan?".
Ƙatuwar ajiyan numfashi ya saka haɗi da faɗin"duk yanda zanyi domin cikawa Ummi wannan burin, amma kafin nan ina so a ƙara yi mata gwajin wannan laluran don na kore kokunton dake raina".
Jinjina kansa Abdul-aziz ya yi ya ce"abinda ya kamata kenan Allah ya sa mu dace". Haɗe baki suka yi wajen furta kalmar amin kafin suka fito suka nufi masallaci saboda ƙiran sallan da aka soma yi.
Haka kawai yau na tashi gabaɗaya na rasa gane kaina, takamanmen abu guda ba zan iya kamawa na ce shi yake damuna ba kamar wacce aka zarewa laka haka nake aiwatar da komai. Ina zaune a ɗakin mu ina shafa mai sama-sama a ƙafata wayata ta soma ruri ganin sunan Nawwara ya bayyana cikin screen ɗin wayar ya sa ni ɗaga ƙiran na sanya ta a handsfree na cigaba da shafa man.
Gaisawa muka yi tare da tambayar lafiyar juna sannan ta sanar da ni cewar mr Saif da wasu malamai biyu sun ɗaura masa tests ɗin su a portal na duba. Muna yi sallama da ita na zara doguwar rigata tare da ɗaura hijabi a kai na nufi ɗakin yaya Majid ban iske shi a nan ba don haka na nufi sashin Hajiya Babba ko zan same shi a can, ai kuwa tun kafin na ƙariso na hango takalmansa a bakin ƙofar falonta na shiga na zauna tare da gaishe su su duka suka amsa mini cike da so da kulawa sannan na sanar da yaya Majid abinda yake tafe dani cikin faɗin"daman yanzu muka gama waya da Nawwara take sanar dani cewar an ɗaura mana wasu tests a portal, wayana babu data shine nake so na duba a naka wayan idan akwai".
Sai da ya zaro wayar daga aljihunsa ya miƙo mini tare da cewa"gashi ki duba Allah yasa aga alkhairi". Da saurina na amsa da "amin ya Allah". Na ƙarba wayan cikin rawan jiki da fargaban ban san abinda zan tarar ba na fara sanya matric numberna da password bayan na shiga page ɗin jami'ar a manhajan chrome. Wani nauyayyen ajiyar numfashi na saka tare da hamdala a tare yayin da nayi tozali da kyakykyawan sakamako a dukkan gwajin, na miƙawa yaya Majid ya gani sannan ya miƙawa Hajiya Babba washe baki tayi duk da bata fahimta komai a rubutun tana faɗin"Allah ya sanya alkhairi takwara". Amin muka amsa tare da yaya Majid kafin ya gyara zama ya soma faɗin"Hajiya na mance ban faɗa miki ba ina waɗannan mutane da zaka zo kwanaki yayin bikin su Ikilima har suka kwana biyu, malaman makarantan su Na'ima?". Kanta ta ɗaga masa alamar ta gane zancen tare da ɗaurawa da"waɗanda suka amshi ruwan rubutun a mahaifiyar su ko? ko yaya jikin natan yanzu?".
"Su dai jiya munyi waya dasu suke shaida min cewar ta sama lafiya don har magana ma tana yi, suke nayi wa su Abba godiya sosai kafin su zo da kansu suma".
"Kai masha Allah alhamdulillah amma nayi farin-ciki wallahi sosai, ai jinya akwai tashin hankali mussamman na iyaye Alllah dai ya ƙara mana lafiya mai inganci".
"Amin".
Na amsa dashi a sanyayye ina godiya da Allah ya da ba wa wannan baiwar tasan lafiya, bana mance ranar farko da mr Saif ɗin bai shigo ya yi mana lecture ba sati da ya zagayo yake faɗin mahaifiyarsa ce tayi hatsari tana kwance a asibiti aka ta yi mata fatan samun lafiya. Zance suka cigaba da tattaunawa har su Abba suka shigo yaya Majid ɗin ya sanar dasu, sosai suma suka nuna matuƙar jin daɗin su game da lamarin tare da ƙara yi mata addu'ar samun lafiya.
Sai da na koma sashinmu na ke sanar da Anty Zakiyya da kuma Umma gabaɗayan su sunyi matuƙar farin-cikin jin labarin, ina zaune Zainab ta shigo wai Salma ta aiko na je tana daga ni har Umma haɗe baki muka yi cikin faɗin"lafiya".
"Nima ban sa ni ba Umman su ne ta aike ni gidan, shine Anty Salman ta ce na ƙirawo mata ke kije da sauri". Zainab ta faɗa tana miƙewa ta fice daga ɗakin saboda ƙiran da Ummanta ta ƙwalo mata.
"Tashi kije ko wani abun ne mai muhimmanci". Umma ta faɗa cikin bada umarni hijabina da yake kaina na gyara masa sama na fice cikin sauri, a zaure na tarar da Nurain ya dage sai ya bi ni na riƙo hannunsa muka fice reras muka iske tulin yaran gidan zaune da iyayensu suna yi musu rabon koko kuwa riƙe da kofinsa. Har ƙasa na tsuguna na gaishe su suka amsa mini suna aika mini wani kallon da na gaza gano ma'anarsa, tsam na miƙe na shige ɗakin Salma kamar an jefo ni kan gadonta na iske ta ta kwanta ruf da ciki kusa da ita nayi wa kaina mazauni ina ƙarewa mata kallo don ko shigowata bata ji balle zaman da nayi kusa da ita sai da na taɓo ƙafarta ina faɗin sunanta sannan ta tashi zauna tana mirtsike guntun hawayen da ya maƙale a idanunta.
"Kin iso?".
Idanuna ƙar a kanta na ce"na iso Salma menene yake faruwa naga kamar kuka kike yi?" Ƙaton gwauron numfashi ta saka kafin ta sama zarafin faɗin"akwai matsala Na'ima babban matsala wallahi". Tunin na fara taburcewa na ce"subhanallahi wani irin matsala kuma?".
Nurain na kallo sanda nake ƙarƙare zancen da yake zaune kusa dani yana wasa da wayata, karɓa nayi na buɗe na kunna masa kallo na ce yaje kan kujera ya zauna sannan na maido da hankalina ga Salman da ta yi ƙasa da kanta na ce"ina jinki menene?".
"Na'ima ko yaushe cikin tunina dalilin Umma na tirsani auren malam Mamman, amma cikin kwanakin da nayi cikin gidansa na fara fuskantan wasu abubuwa da suka fara sa ni zargin tabbas akwai wata a ƙasa. Ta baya yake kusanta ta nayi masa ƙorafin haramcin hakan a addini da kuma lafiya amma sai ya hau min faɗa akan cewar ba ya aure ni don hakan bane hasalima saboda wata manufarsa ta daban ya auro ni da zaran ya cimma burin sa zai iya rabuwa dani".
"Tirƙashi lalle kam ƙatuwar matsala, amma ki kwantar da hankalinki dole