Showing 141001 words to 144000 words out of 171161 words

Chapter 48 - MATAN AREWA BOOK TWO COMPLETE PDF .txt

yi mana mai kyau".


Tare muka zauna da jaririyar da sam bata da matsalar koke-koke, tunda na kwantar da ita bata tashi ba sai dai mu juya ta mu bata ruwa tasha ta koma. Sai da muka yi sallan magrib Nazifa ta ɗauko ta muka fito mayar da ita, a baranda muka yi kiciɓus da Billy ɗawisu tana fitowa daga ɗakin su zata shige wanka haske mu yi da hasken fitilla tocilan wayarta dake hannunta ta ce"ku kuma ɗan waye kuka samo?".


"Babyn Mama Marry ce".


Na faɗa a taƙaitacce muna ɗaukar hanyar ficewa daga hostel ɗin, tana harhaɗa kayanta muka tarar da ita ga mai adaidaitan da yake kawo ta ya mayar da ita kullum yana jiran ta. Taya ta muka yi ta shigar da kayan ciki sannan ta amshi babyn daga hannunta.
"Na gode fa sannu sannunku da ƙoƙari na haɗa ku da wahala".


Ta faɗa tana ƙoƙarin aza jaririyar a bayanta, murmushi muka saka a tare na ce"daman bamu iya wankan baby bane da har wanka zamu yi mata". Ita ma murmushin ta maido mana dashi ta ce"a hankali zaku koya wuyarta kuyi auren ne ku haifo". Tuntsirewa muka sake yi tare da yi mata sai da safe ta shige adaidaitan suka wuce, hanyar hostel muka ɗauka dai-dai lokacin maza suke fitowa daga sallan magrib da aka iddar mintunan kaɗan da suka gabata, ganin hakan ya sanya mu ƙara sauri don mu wuce har mun kusa wucewa naji an ƙira sunan cak duk muka tsaya ba tare da mun sama kuzarin waigowa ba.
A hankali muka fara jin sautin tafiya yana ƙara tunkaro mu, har lokacin cikin mu babu wanda ya juya sai da ya iso gaban mu kafin na kai idona gare shi ganin Mr Saif ya sa ni saurin ɗauke nawa ƙwayoyin idanun nayi ƙasa dasu.


"Daga ina kuke?".


Bamu amsa masa ba sai ma jefa masa gaisuwa da muka yi a maimakon bashi amsar tambayarsa, kallo ya kafe mu dashi ya ce"answer me frist".
"Daga wajen Mama Marry mai masa muke".


"Ina masan da kuka sayon?". Ya ƙara tambaya cikin tsare gida hasken sololin da suka dalle wajen yake bamu damar satar kallon fuskarsa, a wannan karon Nawwara ce ta amsa mishi da"babyn ta muka kai mata".
Sai da ya ɗauki wasu sakanni kafin ya ce"ku daina fitowa a irin wannan lokacin ok". Kan mu muka ɗaga masa muka wuce ta gefensa. Bai bar wajen ba sai da suka ɓacewa ganinsa sannan ya wuce wajen motarsa ya shiga wayarsa da ya bari a ciki ya ɗauka ya turawa Abdul-aziz saƙo akan shi ya wuce sai gobe sannan ya tada motar ya nufi gida.
A hankali yake driving ɗin har ya isa gida, shuru falon babu motsin kowa don haka kai tsaye ya wuce ɗakin Ummi nan ma babu kowa illa motsin mutum da yake ji a banɗaki da ya bashi tabbacin ita ce a ciki, ɗakinsa ya nufa yana tafe yana dialing lambar Farouk da yake ƙira baya tafiya har ya isa ya shiga ya zauna akan kujera yana zame hulan kansa.


A hankali idanunsa suka sauƙa akan farar fefen dake kan teburin dake tskanin kujerun ya miƙa hannu ya ɗauka tare da buɗewa, saƙo ne Farouk ya ajiye masa akan ya je wajen wanj abokinsa ba zai daɗe ba zai dawo ba.
Ajiyewa ya yi a gefe guda ya ɗaga kansa sama yana ƙarewa rufin ɗakin kallo, kamar wanda aka tsikarawa matsilla haka ya zabura tinawa da ya yi yau ne cikar kwanaki ukun da suka yi da Zakiyya akan zata yi istikara duk abinda ya faru zata sanar dashi.


Lambar Goggo Suwaiba ya fara laluma cikim wayarsa ya soma ƙira sai da ya kusa tsinkewa aka ɗaga, Goggo ce ta ɗaga don haka sai da suka gaisa kafin ta miƙawa Anty Zakiyyan. A sanyaye tayi sallama ya amsa mata sannan ta gaishe shi, shuru duk su biyun suka yi suna sauraran fitan numfashin junan su.


Har izuwa lokacin da ya kawar da shurun ta hanyar faɗin"na ƙira naji sakamako ne daga gare ki, domin tun ranar hankalina ba a kwance yake ba har yanzu".


"To ka bani mintuna biyu na kammala wani abu sai na faɗa maka".


"Ok take your time".


Ƙatse ƙiran ya yi ajiye ta akan cikinsa yana kallon sama, mintuna kaɗan tsakani ya ji ƙaran shigowa saƙo cikin wayarsa sai da ya ɗau lokaci kafin ya duba ganin da lambar Goggo ne ya sanya shi saurin gyara zamansa.


"Bayan kammmala istikan da nayi na ba wa Allah zaɓi, haƙiƙa na tsinci kaina cikin wani sabon yanayin da can da ban shi ba. Idan har hakan ake ƙiran da so to tabbas ka sama karɓuwa a zuciyata".


Iya abinda saƙon ya kunsa kenan, haka kawai ya tsinci kansa da sa ki murmushi shi kaɗai. Ya fahimci kunya ce ta sanya ta yin amfani da wani aiki ta sanya shi katse ƙiran ta sanar dashi ta sigar rubutacciyar saƙo. Hamdala ya yi Allah ya ajiye wayar tare da miƙewa ya fara rage kayan jikinsa ya shiga wanka, bai ɗau lokaci ba ya fito bayan ya ɗauro alwala, jallabiya fara tas ya sanya a jikinta ya fita izuwa ɗakin Ummi hashasho irin matsanancin farin-cikin da zata yi yake yi idan ya sanar da ita ya shirya yin aure a yanzu, da kuma yarinyar da ta kasance zaɓinta tun kafin ta gan ta a zahirance.


MATAN AREWA




(Book two)


© Maimunah Tijjani Iyam


__________________________________


Page 1⃣1⃣2⃣




Tun kafin ya ƙarisa cikin ɗakin yake jiyo tashin muryoyin su da Farouk suna hira, a ƙofar ɗakin ya tsaye tare da naɗe dukkan hannayensa a ƙirjinsa ya zuba musu idanu. Farin-cikin dake kan fuskoki da annurin da ya wanzu shi yake addu'ar cigaba da ɗaukewar sa har izuwa fitar numfashin su na ƙarshe. Ya ɗau tsawon mintoti tsaye a wajen yana kallon su ba tare da su sun lura dashi ba kafin ya yi gyaran muryan da ya jawo hankulansu izuwa gare shi.
A nutse ya rako har cikin ɗakin ya zauna kusa da inda Ummi take zaune, fuskanto ta ya yi sosai ya ce"zan je sallah when i back ina da kyakykyawan labarin da zan ba ki".
Laulausan murmushi ta sakar masa haɗi da faɗin"to Allah ya dawo daku lafiya". Fuskarsa shima ya ƙawata da murmushi ya ce"Amin".
Miƙewa ya yi ya ɗauki hanyar ficewa daga ɗakin har ya kai ƙofar fita Farouk ya dakatar dashi da faɗin"yaya Saif bari nayi alawa yanzu sai muje".


"I can't wait for you".


Ya furta a daka ya fice daga ɗakin, shagwaɓe fuska Farouk ya yi yana cewa"Ummi kin gan sa ko fushi ya yi dani". Cike da kulawa ta ce dashi"ka tashi ka bi shi". Kafin ta gama rufe bakinta tunin ya miƙe ya rufa masa baya har ya kusa ficewa daga gidan ya cin masa duk zancen da yake yi masa babu wanda ya tanka masa har suka isa masallacin ya shige ciki ya barshi shi kuma ya tsaya yin alawala kana ya shigo.


Ana iddarwa suka wuce gida, a compound ya tsaya suna waya da Abdul-aziz tare da labarta masa yanda suka yi da Zakiyya, yana iya jiyo ajiyar numfashin da ya sauƙe kana ya damar faɗin"amma kamar ba zasu ga kayi gaggawa ba iyayenta, duba da yanda ba wani daɗewa kuka yi tare ba dole zasu buƙaci lokaci domin su yi shirin zuwan bikin da abinda zasu yi mata".
Sai da ya zube dukkan hannayensa cikin dogon wandon dake cikin jallabiyan da ya sanya, ya fara zaga wajen a hankali idanunsa suna ƙasa kamar mai neman wani abun ya soma cewa" nima nayi wannan tinanin, sai dai ba na son bikin ya wuce nan da sati uku ayi komai a gama".


"To shikenan ka sanarwa Ummi then sai zamu yi magana later". Da haka suka yi sallama ya shige cikin gidan yanzun a falo ya iske su, an jere dinner a gaban su zama ya yi kamar yanda suka saba sai sun fara zubawa Ummi ta ci sannan suke ci yanzun ma hakan suka yi sai da suka gama ciyar da ita sannan suka zuba nasu. Tunda ya ɗaura idonsa akan plate bai ɗago ba har sanda Farouk ya soma faɗin"Yaya Saif ba fa wani waje naje ba, wajen Abbas naje ya duba min CV na da nake son na tura a wani company" . Kansa kawai ya jinjina masa da hakan ya sanya Farouk ɗin ƙara marairacewa ya ce"please haba mana bloody ni bana son fushin nan".


"Why can't you call my phone and tell me zaka fita so that na dawo na zauna da Ummi, tunda maid ɗin tun yamma suka tafiya".


Haɗe hannayensa wajen guda ya yi alamar roƙo ya ce"na ƙiran wayanka not available shiyasa fa amma na tamabayi Ummi, Ummi ba na tambaye ki ba na ce miki zan je wajen Abbas?".


"Haka ne kam ka sanar dani hasalima ni na baka damar tafiya".


"To kuma yaya Saif gashi ka ji".
Idanunsa ya tsayar a kan fuskan Farouk ɗin da yake jiran ƙiris ya tuntsire da kuka yana ajiye spoon ɗin dake hannunsa ya ce"shikenan ya wuce".


"Yauwa ko kai fa Babana ina jinka wani magana ka ce zaka sanar dani ɗazu".
Sai da ya sauƙe manya-manyan ajiyan numfashi a haɗe a lokaci guda yana yin ƙasa da kansa hakan ya furta"daman magana ne akan Zakiyya ina son na tura gidan su a sanya rana".
"Ina jinka ko shikenan?". Da sauri ya ɗago idanunsa don ya gaza fahimtar zancen natan a take, walwala fal ya hanga akan kamalalliyar fuskarta. Fusktarta tamkar gonar auguda ta ce"nayi matuƙar farin-cikin jin wannan zancen sai dai yanzu waye kake ga zai je a matsayin waliyinka duk ƴan-uwana da na mahaifinku ba'a a raye a duniyar nan".


Sosai ya ji kansa ya yi masa wani irin nauyi, miyau ɗin bakinsa ya ɗauke lokaci guda tamkar rijiyan da ruwan cikinta ya kafe kansa yana sarawa da matuƙar ƙarfi. Sai da ya jawo numfashinsa ya fesar kana ya sama zarafin cewa"zan yi magana da Abdul-aziz mahaifinsa zai je in sha Allah". Shuru tayi ba tare da ta ce dashi wani ba tana nazarin kalaman nasan tare da hashashowa a cikin ranta wataƙil da mutuwa bata yi musu tonon silili tare da yaye labulen sirrinsu ga duniyar da mutane masu zuciyar tsoron Allah suka ƙaranci a cikinsa ba. Da mahaifinsa ne zai je karɓa masa aure kamar yanda kowa mahaifi ko danginsa suke zuwa masa, ba mahaifin aboki ba sai dai ƙaddara ta riga fata Allah baya barin wani don jin daɗin wani.


Idanu ya zuba mata don shima irin tinanin da yake yi kenan cikin ransa, ko mutuwa ta ɗauke musu mahaifi ai suna da ƴan-uwan da zasu yi iya tsayiwa akan lamuran su. Da sauri ya kai bayan hannunsa ya mayar da ƙwallar dake son kwaranyo masa tare da musgutawa ya ce"Ummi ko akwai wani matsalan ne naji kin yi shuru?".


"Babu wani matsala Saifuddeen, amma bana son ka ɓoye mata komai dangane da rayuwarka da ita da danginta su ji komai a bakinka ba sai daga baya su ji a wani wajen ba". Kansa ya jinjina haɗi da faɗin"in sha Allah Ummi".


"Yaya Saif amma dai a nan gidan za ku zauna ko?". A karon farko tun bayan da suka fara maganan da Farouk ya ce wani abu kenan, sai da ya kallo sa kafin ya ce dashi"a nan zamu zauna Umar".


"Saifuddeen kar ka yanke wannan hukuncin ba tare da ka ji daga gare ta ba, da yawa matan zamanin nan ba za son zama muhalli guda da iyayen miji don haka ka tuntuɓe ta don samun ɗaurewar zaman lafiya a tsakanin ku".
Murmushi mai ciwo ya sakar"Haba Ummi har kina tinanin zan je irin waɗannan gidaden neman aure?, na tabbatar ba zan sama matsala daga gare ta in ma an samu to sai dai na haƙura da ita don ba zan iya zaman aure da wacce zata iya kallon ido ta furta min cewar ba zata iya zama tare da mahaifiyata ba".


Ba ta ce komai ba illa murmushin da ta cigaba da sakar masa, daren duk zancen da suka yi kenan har lokacin kwanciyar Ummi ya yi suka taka ta ɗakinta tare da bata ragowar ruwan rubutun da ya yi ta shanye shi sauran ta shafe jikinta dashi ta kwanta. Sai da bacci ya ɗauke ta sannan suka nufi nasu ɗakunan, wanka ya yi ya ɗauro alawala tare da sauya shiga izuwa wasu marasa nauyi da takura ya ɗauko wayarsa ya shiga dialing lambar Goggo har ta soma ruri idanunsa suka sauƙa akan agogon wayar dake nuni da ƙarfe tara da rabi, kamar zai kashe saboda tinanin cewar ba wayarta ba ce bai kuma ya fasa jin har ya shiga yana ruri. Sallamar da ya sauƙa a kunnensa shi ya dawo shi cikin hayyacinsa, a nutse ya amsa jin ba Goggo Suwaiba ya amsa sallama yana ɗaurawa da"na zata kin yi bacci ai, har nayi tinanin kashewa kar na dami Goggo".


"A'a ban kwanta ba yanzu dai nake son na kwanta, na mayar mata da wayan ƙiran ya shigo"
Jingina bayansa ya yi jikin fuskan gadon kana ya ce"naga saƙonki kuma ina godiya matuƙa".


"Uhmm".


"Idan an bani dama ina son na turo manyana ayi magana". Sai da ta ɗan yi jim domin ganin komai take yi tamkar cikin bacci yake faruwa wai yau ita Zakiyya ita ce take waya da saurayi har da maganar aure, sai da ya ƙara maimatawa a karo na biyu kana ta sauƙe numfashi ta ce"bana ce komai ba sai dai kuyi magana da yaya Majid sai ya sanar dasu".


"Ai dole sai na fara neman yardanki da amincewanki tukunna, sannan ina son muyi wata magana dake".


"Ina jinka".


Cire leɓɓansa ya yi kafin ya furta"misali za ki iya zama da uwar miji a waje guda?". Murmusawa tayi kamin ta soma faɗin"me zai hana matuƙar ina ƙaunar ɗanta babu abinda zai hana ni zama da ita, domin nima haka na taso na ga iyayen mata suna zaune tare da mahaifiyar su Abba su na bata girmaman ta ita kuwa ta ɗauke su tamkar ƴaƴan cikinta".
Sosai ta gama burge shi lumshe idanunsa masu ɗauke da bacci gami da gajiya ya yi, yana shafa sumarsa a hankali yake cewa"yanzu za ki iya zama da uwar miji kenan?".
"Idan har zan iya jure zama da tawa uwar to ita ma in sha Allah zan iya zama da ita".


"Madalla da mace mai irin halinki Allah ya yi miki albarka, yanzu bari na bar ki ki kwanta kar Goggo ta leƙo". Sai da ta dara kafin ta ce"gaskiya kam".


"To sai da safe a tashi lafiya kar a manta da addu'a".


"Allah ya kaimu, na mance ban tambayi ya mai jiki ba ya jikin?". Sai da ya zame ya kwanta ya amsa da"jiki ya warware sosai".
"Alhamdulillah Allah ya ƙara sauƙi".
"Amin".


Da haka suka yi sallama juyi-juyi kawai yake yi a gadon ya kasa runtsawa duk baccin dake idona mintuna kaɗan da suka gabata ya ji gabaɗaya ya wuce, ganin da gaske babu baccin a idanunsa ya sanya shi miƙewa ya je ya dubo Ummi sannan ya dawo ya tada sallan nafila. Da yaya Majid suka yi magana akan zuwan manyansa da yake son su yi cikin sati mai kamawa, ya sanar da su Abba suka basu dama. Mahaifin Abdul-aziz da babban yayansu su suka je tambayo masa auren ƙafa da ƙafa har cikin garin yobe, har izuwa lokacin matan gidan mu babu wajen ta san abinda yake gudana ko baƙin da aka yi su Abba cewa suka abokan su ne da aka ɗebi lokaci ba'a haɗu ba suka kawo musu ziyara.


Kamar yanda suka roƙa a sanya bikin nan da sati huɗu hakan aka yi aka sayar da wannan lokacin, a wajen suka bada sadaki da kuɗin na gani ina na so da goro da alewan sa rana.


MATAN AREWA


(Book two)


© Maimunah Tijjani Iyam


_________________________________________


Page 1⃣1⃣3⃣


Zaune nake ina wanki a harabar hostel ɗin kasancewar yau juma'a gabaɗaya bamu da lectures sai monday, Nawwara tana gyara mana ɗaki ita kuma Nazifa tana yi mini ɗauraya jifa-jifa muna ɗan taɓa hiran mu.
Fitowar Shatu daga ɗaga ɗakinsu a guje tana sakin ihu ya jawo hankulanmu izuwa gare ta, nufo mu da yi don muna da yawa waɗanda muke wankin wajen. Binta ta ɗago tana gyara ɗaurin ƙirjin dake jikinta tare da jefa mata harara ta ce"ke dalla meye haka?".


"An sake result wallahi ku hau portal ku duba".


Sake doguwar rigata da nake wankewa nayi ina kafe ta da ido ban san sanda bakina ya furta kalmar"don Allah da gaske kike?, ko ɗazu ma fa na hau na duba".


"In kin hau yanzu kin duba kin ga ba'a ɗaura ba, sai ki ce dani haka". Tana gama faɗin ta bar wajen ta faɗa wani ɗakin, gabaɗayan mu bamu yarda ba don haka sai da muka gama wankin mu muka shaya tare da wanke bokatayen muka shige ɗaki.


Muka sanar da Nawwara da muka tarar kwance tsam ta miƙe tana rarumar wayarta ta fara dubawa, kewaye ta muka yi muka zubawa hannunta ido da take shigar da ID number tare da password ɗina, kamar a mafarki sai da result ya bayana hakan ya sanya mu buɗe na Nawwara ita ma tana ya bayyana sannan na Nazifa, murna da farin-cikin dake kan fuskokin mu ne tsaf suka ɗauke tamkar anyi ruwa an ɗauke sakamakon tozali da result ɗin Nazifa. Duk cikin mu ita kaɗai take da carry over guda ɗaya da wani irin razani akan fuskokin mu muka furta"Mr Suleiman".


Muna kallon juna ajiye wayar Nawwara tayi tana dafe goshina tare da furta"innalillahi wa inna ilaihir raji'un wai mutumin nan me yake nufi damu ne?". Sauƙe numfashi nayi"abinda ya furta dai sai da ya aiwatar dashi".
Shuru ya baƙunci ɗakin na ɗan wani lokaci kafin Nazifa ta kawar dashi ta hanyar faɗin"kar ku wani damu wallahi ba komai haka Allah ya ƙaddara".
"Wani irin ƙaddara kike magana a kai Nazifa?, ƙaddara ko kuma sharrin wannan baƙin mutumin main mungun nufi". Furcin Nawwara kenan a zafafe idanunta har wani ruwa-ruwa yake kawowa tsabar ƙololuwar gejin ɓacin ran da take a ciki, dafa kafaɗarta nayi cikin sanyin murya na furta"muyi haƙuri Nawwara in hankali ya gushe dole hankali za'a amfani dashi wajen nemo shi, amma tabbas mutumin ya cika mungu ko mai haifa ba dai ai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login