Showing 33001 words to 36000 words out of 171161 words

Chapter 12 - MATAN AREWA BOOK TWO COMPLETE PDF .txt

sikirinin wayar -ZAUJI- da aka rubuta da manyan harrufa na ƙurawa ido cikin rawar jiki zuciyata tana harbawa da sauri da sauri kafin na zame nayi zaman ƴan bori dirsham na tisa wayar gabana ina bin ta da wani irin kallon da yake haifar mini da tinanin abubuwan da suke gabata a rayuwata. Har na fara zurmawa cikin tafki tinanin rurin da wayyr ta kuma yi suka dawo dani cikin hayyacina figigi na zame hannuwana daga tagumin da na zagba a karo na barkatai na kuma bin wayar da kallon da har yanzu take rurin alamar neman agaji kafon nayi wani yunuri hawaye suka biyo gefe da gefen kunva suna wanke mini fuskarta da idanuna suka yi gululu alamar rashin bacci bayyane akanta.




"Meyasa yaya Yusuf meyasa?, meyasa ba zaka bar zuciyata ta huta kuma ta warke daga ciwon daka sanya ta ba. Meyasa ba zaka bar raunin dake cikinta ya haɗe ba? ka barni kayi rayuwarka nayi tawa tunda guguwar ƙaddara ta giggige alaƙar dake tsakanin mu sai mu koyawa zuƙatanmu haƙurin rabuwa da juna, sai ka ce akan mu aka fara rabuwar aure kuma ai ba mune ƙare ba".A bayyane nayi maganar tamkar yana gabana ko kuma wacce ke jiran ya maido mata da amsa, dai-dai nan ƙiran ta kuma katsewa.


"Na'imatu in ce dai ina zaune a ɗakin kika bar wayar nan duk ta cika min kunnuwa da ƙara".




Furcin Hajiya Babba kenan da suka ratsa ƙofofin kunnuwana da suka sanya ni saurin share hawayen da har yanzu suke gudu a fuskana tare da ɗaukar wayar lambar gabaɗa nayi blocking ɗinta sannan na goge ta daga cikin wayar don banga amfanin ta a gare ni ba na ɗaga matashin da nake kwana kansa na sanya wayar na fita falo wajen Hajiya Babba. Da kallon tuhuma ta bini har na zauna kafon ta numfasa haɗi da faɗin"wai waye yake ƙiranki haka?, kamar mai bin bashi ko tara".


Sai da na jawo numfashina na fesar ta baki kana na sama zarafin cewa da ita"wata ce wanda muka yi makaranta tare take ta damuna da ƙira". Sai da ta ƙare mini kallon tsaf kana tayi nisa kafin ta ce"to kin ɗaga kinji dalilin ƙiran?"


"E wai bikinta za'a yi sati mai kamawa shine ta ƙira ta sanar mini".


"To Allah ya kaimu ya basu zaman lafiya kuma ya fito muku da mazajen ku tafi ɗakunan ku".




"Amin".


Na amsa dashi a taƙaice ina miƙewa ma fice daga falon don matuƙar na cigaba da zama to ba sai tayi wahalar gano cewar ƙarya na faɗa mata ba, ni da kaina zan iya fallasa kaina har ta fahimta. Sashin mu na koma nayi zamana a ɗakinmu tsakancewar na tarar da Umma da wasu baƙin mata a ɗakinta suna tattauna wanda nake da yaƙinin matan da suke zuwa wajenta neman shawarwari ne. A nan na wuni ba tare da na taɓuka komai ba sai shigowar yaya Majid ne ma lura da yanayin da nake a ciki ya sanya shi jana da hira har da nuna mimi wasu hotuna a cikin wayansa nan ma ban bashi cikakken hankalina ba balle nutsuwar fahimtar abinda yake mini nuni dashi cikin wayar, sai da ya ambata mini sunan Madina Ɗahiru mai shano da kuma Badiriya Tijjani Alarawi sannan ya sama hankalina saɓanin da da kawai ni yake gani a zahiri ina can duniyar tinani.


Sosai na matso ina tsurawa fuskar idanu ina iya jiyo ƙarƙarfan ɓoyayyiyar ajiyan zuciyar da ya saka. Ganin ban fahimta abinda suke gabatarwa domin sunayen manyan ƙasar nan kawai suke kamowa tare da yi musu barka da zuwa ya sani zuba masa idanuna cike da son ƙarin bayani. Sai da ya muzguta kafin ya ce dani"HIKAYATA kenan gasar gajerun ƙagaggun labaran da BBC hausa take shiryawa ko wacce shekara domin mata zalla". Na ƙara ƙurawa fuskar wayar ido ina ƙara bin wajen da kallo da aka ƙawata da launin ja da fari da ya yi matuƙar ɗaukar ido da birgewa ga kuwa manya baƙi fitattatun fuska ta ko ina, can na hango gwanata Madina Ɗahiri tsaye suna magana da wani. Sai da na ƙare kallon faifayin bidiyon tsaf na kuma dawowa dashi baya miƙewar da yaya Majid ya yi shi ya tilasta mini ɗauke idauna daga kan wayar na zube su akan fuskarsa.


"Ki cigaba da kallonki bari naje sashin Hajiya Babba kafin kin gama".




Kaina na ɗaga masa ya fice na cigaba da kallona, tagwayen ajiyar zuciya ya sauƙe dai-dai yana tura kai falon Hajiya Babba tare da sakin siririyar sallama kafin ta amsa har ya shigo ya zuana ya gaishe ta amsa cikin sakin fuska, karantar yanayi sa akwai damuwa ya sanya ta faɗin"babban mutum lafiya kuwa?".


"Wata magana ce ta kawo ni Hajiya".


"To inajinka".


Ta faɗa tana daɗe fuskantarsa yayin da shi kuma ya musguta kafin ya furta"akan Na'ima ne sanin kuwa yasan tana cikin damuwa akan abubuwan nan da suka faru, ina tsoron har hakan ya taɓa lafiyarta shine na ce ko za ki yiwa su Abba magana ko makaranta ce sai ta koma".




MATAN AREWA


(Book two)


©Maimunah Tijjani Iyam


________________________________


Page 5⃣2⃣




Musgutawa tayi tare da sauƙe numfashi kana ta furta"tabbas wannan ma shawara ce mai kyau, kuma abin dubawa ce kima zamu zauna da iyayenku maza sai mu tattauna akan lamarin".


"Yauwa Hajiya mai ran ƙarfe Allah yaja kwana gawa ta ƙi rami".


Murmushi ta saka sosai fuskarta fal annuri ta ce"babban mutum ai ni nan da kake gani har jikokinku da yardan Allah sai na gani". Shima dariya ya mayar mata yana miƙe tare da cewar" kai mata ki lafa mana".


Da haka ya fice zuciyarsa cike da farin-ciki da addu'ar samun amincewar su Abba game da lamarin, inda ya barni nan ya iske ni ko gusawa banyi ba kamar yanda ban ɗauke idona daga fuskar wayar ba har yaya Majid ya ɗago labulen ɗakin yana daga tsaye ba tare da ya ƙarisa shigowa ba ya ce"wai bakya gajiya ne da kallon su nikam?".




"Wallahi yaya Majid suna burge ni ne irin sosai ɗin sun san aikinsu cike da ƙwarewa suke komai nasu".


Na faɗa ina faɗaɗa murmushin da ya ƙi barin fuskana, murmushin ya maido mini kafin ya ce"to bani wayata fita zan yi". Shagwaɓe fuska nayi tare da marairaicewa aihun ina faɗin"haba Yayana kayi haƙuri na ƙarisa wannan shine na ƙarshe".


"A'a ki bari sai na dawo sai na ba ki kiyi ta kallo kar a neme ni ko?".


Ba don naso ba na miƙa masa wayar tare da yi masa addu'ar dawowa lafiya ya amsa mini cikin jin daɗi sannan ya fice, ya bar ni zaune tare da zagba tagumin da ya zamo mini jiki yanzu ganin ina ƙoƙarin faɗawa tafkin tinani ya sani tashi na nufin ɗakin Ummata a baranda nayi kicɓus da ita tana saka hijabinta. Idona a kanta nake cewar"Umma ina zuwa haka?Har baƙin nakin sun tafi?".


"E sun tafi zani wata unguwa ce nima nan kusa yanzu zan dawo".


Kaina na jinjina mata tare da raka da addu'ar da ta amsa tana sanya mini albarka, duk da kuwa raina cike yake da tinanin inda zata domin bata taɓa ɓoye mana komai nata ciki kuwa har da wuraren da zata. Har na ɗaga labulen ɗakin shewar da Umman Balkisu da Umman su Anty Kubra suka saka har da tafa hannuwansu ya sanya ni dakatawa tamkar wacce aka kafe.




"Ahayye ayi dai mu gani in tusa tana hura wuta kuma ai shi munafurci dodo ne mai shi yakan ci, kamar yanda sharrin yake ɗan aike duk nisan da ya yi sai ya dawowa mai shi".


Furcin Umman su Anty Kubra kenan da suka daki kwalwata tare baƙanta mini rai da ruhina, na cire leɓɓena da ƙarfi ina ƙarisa shigewa ɗakin raina duk babu daɗi domin nasan duk maganganun nasun gogan zane da ba'a ne gare ni da kuma Umma da lokuta da dama abin yake damuwa da sanya ni cikin matsanancin damuwa. A hankali nake bin Anty Zakiyya da kallo da take kwance kafin na kai hannuna saman goshinta nayi saurin janyewa sakamakon zafin da ilahirin jikinta ya ɗauka. Na tsura mata ido na tsawon daƙiƙu kafin na janye, ƙiran sallan asr da aka yi shi ya tilasta mini tashin tayi salla sannan ta koma kan sallayar ta kwanta ina ta aikin yi mata sannu har Salma ta shigo ta jona ni da ƙyar ta iya yin cokali uku a shinkafan da waken da Salma ta shigo mana dashi ta fara ƙaƙagin amai. Muka taimaka mata ta fito waje domin duk jikinta babu ƙwaru sosai take kwaranyar da amar tamkar zata amar da dukkan kayan cikinta, tunin na fara ƙwalla nikam Salma ta fita da saurin ta domin ƙira yaya Majid yazo mu kai ta asibiti domin yanda take aman kaɗai ya isa ta tsorita duk wani wanda yake tsaye a wajen. Sai ba a fuskokin kowa na hangi tausayin halin da Anty Zakiyya take a ciki ba illa taɓe bakin da Umman Balkisu tayi gami da furzo furcin da suka ƙara dulmiyar mini da tinanina tare da ƙarar da ruwan kaina da suka suka sanya ni zubewa akan gwiwoyina babu shiri sakamakon jirin da naji yana walagigi dani tamkar tsuntsuwar dake shawagi a sararin samaniya.




"Wannan abu da alamar tambaya domin babu rami kuma meya kawo zancen rami, to Allah ya saka ba abinda nake tinani bane hashashena ya tabbata gaske".


Caraf Umman su Anty Kubra ta karɓe zancen da faɗin"me kike tinani?, domin nima nan wani abun zuciyata take saƙa min game da yarinyar nan?".


"Ke dai bari don ni nawan mahangar da na hangi lamarin Zakiyya duk alamomin masu juna biyu sun bayyana a tattare da ita"


Salati raguwar mutanen wajen suka saka dai-dai sa'ilin da Salma da yaya Majid suke shigowa sashin tare da Goggo Jummai, basu maida hankali ga tsantsar mamakin dake kwance saman fuskokin mu ba suka nufi wajen Anty Zakiyya da take durƙushe tana sakin wani azababben kuka marar sauti. Sannu suke jera mata tamkar zasu mayar da ciwon jikin su kafin yaya Majid ya ɗago ta ya kalle ni, nima hawaye ne kawai suke zarya a tudun fuskana sakamakon sauƙar furcin Umman Balkisun da suka yi nasarar tarwatsa mini kuzari da ƙwarin gwiwana.


"Ke kuma meye na kukan?, ɗauko mata hijabinta ku fito muje asibiti".


Da ƙyar naja ƙafafuna da nake jin su tamkar basa a cikin jikina na shiga ɗaki na ɗauko mata hijab ɗin na saka mata tare da riƙo hannunta da nufin miƙar da ita tsaye. Tirjewa tayi tana kaɗa mini kanta hawaye suna cigaba da ziraro mata a hankali leɓɓanta suke motsawa da bana iya jiyo abinda take faɗi, ƙarfin halin danne hawayena kawai nayi duk da kuwa har yanzun ina jin zafin raunin da furcin nan na Umman Balkisu suka yiwa ƙalbina na miƙar da ita muka ɗauki hanyar ficewa daga sashin muryar Umman Salma suka sanya mu dakatawa tsam tamkar waɗanda aka kafe su a wajen.


"Tabbas akwai ƙamshin gaskiya a cikin zantukan ku kuma ko nima nayi wannan tinanin cikin raina, wannan jinya da taƙi ci taƙi cinyewa kamar cin kwan makauniya da walakin goro a miya. Babu mamaki ciki taje ta ƙunso shiyasa uwar ma gabaɗaya cikin kwanakin nan bata cikin nutsuwarta bata zaman cikakken awa ɗaya zata zari hijabi ta fice koma menene ake ɓoyewa dai in tayi tsami maji".


Wani gigitaccen numfashi yaya Majid ya fesar mai zafi tare da cije leɓɓansa da matuƙar ƙarfin kamar zai huda su kafin ya watsowa Anty Zakiyya da jikinta yake karma kamar kazar da ruwa ya yi mata mungun bugu idanunsa da suka fara canja launi da jijiyoyin kansa suka yi raɗau-raɗau akan goshinsa. Karkarwa kawai bakinsa yake yi amma ya gaza furta abinda yake sukan ransa da yi masa kai koma a ƙirjinsa. Durƙushewa ƙasa Anty Zakiyya tayi tana sakin wani kukan da sautinsa ya karaɗe yalwataccen filin tsakar gidan namun, maganar da Goggo Jummai ta soma yi duk shi ya dawo damu cikin hayyacin mu.


"Ke Zinaru ciki fa kika ambata ciki?, Zakiyyar ce ɗauke da ciki?".


"Goggon yara ai ga ta nan a gaban ki sai ki tambaye ta tunda ba a ƙarya kusa da gida, tabas ciki take ɗauke dashi domin laulaye-laulayen masu ciki duk su take yi".


Cike da tabbaci Umman Salma take furta maganar dake bayyanar da ƙwarin gwiwa tattare da ita, zafin da nake ji a ƙirjina ya kuma tsananta ina jin tamkar ana hura mini wuta a cikinsa. Ƙafafuna suna ƙoƙarin yasar dani ƙasa saboda rawar da suke yi, so nake na danne abinda nake jin yana taso mini a raina ko don na rarrashi Anty Zakiyya daga kukan da take yi da nake jinsa har cikin kwanyata, fizgan da yaya Majid ya yi wa hannun Anty Zakiyya da babu shiri ta miƙe tsaye kan ƙafafunta shi ya dawo dani cikin hankali da ya raba yin nisan ciwo da barin gangar jikina. Sosai yake janta har sai da ya iso gaban Umman Salma ya saki hannunta idanunsa gabaɗaya sun ƙanƙance zallar ɓacin rai kawai nake iya hanga a shimfiɗe akan fuskarsa nuna ta yake yi da yatsa jikinsa har wani jijjiga yake yi take furta" ciki! ciki!! ciki!!! ince ko ba ciki kika ce ba?, to ga Zakiyya nan ba zan hana kowa yin duk wani zargi a kanta ba amma idan har aka tabbatar da cewar bata ɗauke da abinda kuka yo mata ƙazafinsa to duk wani girma da mutuncin ku da nake gani zan ajiye shi ne a gefe guda na nuna muku aihinin wanene Majid Muhammad Kabir"




Tsif wajen ya ɗauki shuru kamar babu kowa saboda yanda ya yi maganar sam babu wasa a tattare da furcinsa balle kuma fuskarsa, daga haka bai ƙara cewa komai ba illa ƙara jan hannun Anty Zakiyya da ya yi ya nufi hanyar ficewa da sauri na bi bayansa Salma ta rufa mana baya, sai da muka je zaure ya dakatar da Salma da cewar"ki koma gida kawai ki jira dawowar mu". Magana da fara ƙoaarin yi nayi saurin riƙo hannunta tare da yi mata alama da kaina akan tayi shuru kawai domin a matuƙar fusace yake aihun, shawaran tawan tabi ta koma gida tana tare ƙwallar da ta ciko mata idaniya muna fita muka sama abin hawa muka hau muka nufi asibiti. Gwaji aka fara yi wa Anty Zakiyya kafi aka maƙala mata robar ƙarin zuba saboda rashin kuzarin jikiida take fama dashi sam mun kasa tsaye balle zaune sai safa da marwa kawai muke yi a wajen tausayin yaya Majid ya kama mini raina don ba kaɗan ba ya shia cikin tashin hankalin da fuskarsa ta fallasar da sirrin dake zuciyarsa.




Muna cikin wannan halin nurse tazo ta ce damu likita nason ganin mu sakamakon gwajin da aka yiwa Anty Zakiyya ya fito har muna rige rigen shiga ofishin, sai da muka zauna ya fara yi mana bayanin abinda yake damun ta da ya labarta mana cewar malaria ce da taifot suka yi mata mungun kamu. Dukkan mu ba wanne a gaban mu ba abu ɗaya muke son ji shine akwai cikin ko babu.


"Likita gwajin ya nuna akwai juna biyu ko kuma babu?".


Yaya Majid ya katse masa hanzari daga bayanin da yake yi da ya masa cikin faɗin"babu ciki domin gwajin da aka yi mata bai nuna tana ɗauke da ciki ba".


Kusan a tare duk mu biyun muka sauƙe ɓoyayyen ajiyar zuciyar da suka tsaya mana a maƙoshi kamar ƙayan kifi.


MATAN AREWA
(Book two)


© Maimunah Tijjani Iyam


___________________________________


Page 5⃣3⃣


Duk raguwar zantukan likitan jin su nake yi kawai kamar busar sarewa naji wani abu mai nauyin da naji ya tokare mini ƙirjina ya sauƙa, sosai yake bayanin yanda ciwon ya yi mata mungun kamu ba tare da mun farga ba. Godiya yaya Majid ya yi masa tare da ɗaukar sakamakon gwajin muka nufi ɗakin da aka kwantar da Anty Zakiyya tana kwance tana bacccin wahala muka iske ta fuskarta tayi fayau da ita saboda ƴar ramar da tayi ga ruwar da aka ƙara mara maƙale a hannunta da har yanzu bai ƙare ba.


Zama nayi kusa da ita ina bin ta da kallon da take bayyanar da zallar tausayinta da ya yi kane kane cikin birnin ƙalbina. Rurin da wayar yaya Majid ta kuma yi a karo na barkatai suka tilasta mini janye idona daga kallon ƙurillan da nake bin Anty Zakiyya dashi, cikin ƙarfin halin na furta"yaya Majid dan Allah ka ɗaga wayar nan ma tun ɗazu ba ake ƙira wataƙil su Abba ne".


Sai da ya sauƙe ƙarƙarfan ajiyar numfashi da sai da kunnuwana suka jiyo mini sautinsa kafin ya ce"su ne ma ba sai na ɗauka ba ai sun ce in ruwan ya ƙare ma sallaman ta zasu yi bari naje na amso magungunan da suka rubuta". Yana dasa aya a nan ya fice ba tare da ya bani damar cewa wani abu ba, nima ajiyar numfashi na saka ina wasassafo munanan furcin Umman Balkisu akan Anty Zakiyya yanzu da bincike ya bayyanar da gaskiya ko da wani idon zasu kalle ta oho, wani sashin zuciyata tana cewa dani a shi gangar jikin da tayi rashin ta ido babu abinda ba zata iya aikatawa ba.


Ƙarewar ruwan ya yi dai-dai da farkawan Anty Zakiyya da shigowar yaya Majid tare da likita duba ta ya yi tare da jera mata tambayoyin ina yake mata ciwo yanzu kanta kawai ya jijjiga masa alamar babu wasu rubuce rubuce ya yi kafin ya ce" za'a iya sallamarta tunda jikin natan ya yi kyau sai dai a kiyaye ta dunga kwana cikin gidan sauro ta kuma daina zama wajen damshi domin shi yake kawo yawaitan sauro har su sama damar zukar mutum su zuba masa ƙwayoyin cututtuka".


"In sha Allah likita duk za'a yi ƙoƙarin kiyaye ababaɗen da ka lissafa".


Yaya Majid ya faɗa suna yin musabaha da likitan da ya ƙara yiwa Anty Zakiyya fatan samun sauƙi kafin ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login