Showing 60001 words to 63000 words out of 171161 words
Chapter 21 - MATAN AREWA BOOK TWO COMPLETE PDF .txt
ta faɗa cikin sahun matan da suke bin sa da kallo baki da ido a hangame sannan ta dawo hayyacinta, na watsa mata wani kallon meye haka?. Ya murmusa kawai ba tare da ta ce dani wani abun ba Nazifa ma murmushin tayi muka maida hankalinmu ga bayanin da yake yi.
Uzurin da ya hana shi zuwa last week ya faɗa wai mahaifiyarsa ce tayi accident shiyasa bai zo ba, nan hall ɗin ya ƙara rikicewa da faɗin kalmar suhbanallahi masu rawar kai da zumuɗin cusa kai suna ta masa ya mai jiki yana amsawa don na lura kamar bashi da ɗagon kai balle ƙyaliya.
Sai da shur ya baƙunci hall ɗin sannan ya ba mu course outline ya kuma fara yi mana bayani briefly akan abinda course ɗin ya ƙunsa kafin muka fara cikin asalin course ɗin gadan gadan, tabbas na gaskata abinda muka ji ƴan 200 level suna faɗa akan sa ba ƙarya ya iya koyarwa kuma duk daƙiƙancin mutum zai yi wuya ya shigo lectures ɗinsa ya ce bai fahimta komai ba sai dai ya faɗi son ransa.
Duk da lectures ɗin awa biyu ne amma sam bamu gaji ba domin ya iya kama hankalin mai sauraronsa cikin hikima da dabara ba tare da mutum ya ƙosa ko kuma lectures ɗin ya gundure sa ba. Bayan ya gama ya buɗe ƙofa ga masu tambayar question wata yarinya ta miƙe tana faɗin"sir your name".
Dafe kansa ya yi kafin ya haɗe hannayensa alamar ban haƙuri ya ce"oh sorry i forget to tell you my name, my name is Saiffudden M Akuma but you can call me Saif".
Yana dasa aya anan ya fara haɗa tarkacensa ya fice da ɗan sauri saboda wayarsa da take ta vibrating tun yana lecture ɗin bai ɗaga ba, saboda tun farko ya ce cikin dokarsa babu picking ɗim calls a class ɗinsa shima kuma baya yi. Har muka fito daga hall ɗin maganarsa ake ta yi daga matan har mazan abin ya ƙara bani haushi sosai, don ni ban ga abinda suka hango gare shi ba da ya sanya ruɗewa haka kamar sun ga wani sabon abu a jikinsa da babu a jikin sauran mutane.
Nawwara ta tsaya yi mana yi mana attendances ɗin da bamu yi, gaba nayi na bar Nazifa da ta tsaya amsa ƙira na tsaya jikin wata mota ni kaɗai ina ta surutai ni ɗaya na haushin da matan suka bani.
Ina tsaye a wajen class rep ɗinmu ya nufo motar idanuna akansa har ya iso ya ce"ɗan matsa na bashi attendance ɗinsa".
Cikin rashin fahimta na ce"waye?".
"Mr Saif mana motarsa kike tsaye a jiki ai yana ciki". Wani ras gabana ya faɗi sumi sumi na janye jikina ya yi knocking a windown motar a hankali ya fara zuge gilashin motar fuskarsa ya bayyana har yanzu wayar tana kunnensa sai dai yanayin fuskarsa ta sauya aihun ba kamar yanda ya shigo hall ɗin ɗazu ba.
Maganar da class rep ɗinma yake masa bai amsa ba illa miƙa hannu da ya yi kawai ya amshi attendance ɗin ya mayar da gilashin motar ya rufe, ban motsa daga wajen ba har ya figi motar ya fice daga cikin makarantar da matuƙar sauri. Dai-dai nan Nawwara da Nazifa suka iso wajen na watsa musu wata uwar harara tare sakin tsaki na bar wajen ina jin sun suna bin bayana tare da ƙira sunana amman ban tsaye ba har da na kai bakin hostel suka cim mini.
"Ke Na'ima wai meye ne haka?".
Ban kula su har sai da muka shiga room ɗin mu na zare hijabina sannan Nazifa ta ƙara maimaita mini tambayar a karo na biyu. Nayi ciki-ciki da fuska na ce"wallahi kuna bani haushi da kuka biyewa masu yabon wannan lecture ɗin".
Nawwara ta gwalala mini manyan idanunta ta ce"ke Na'ima anya ke kuwa mutum ce?, yanzu wannan tsulelen guy ɗin ne bai burge ki ba, nikam wallahi tubarakalla masha Allahu".
MATAN AREWA
(Book two)
© Maimunah Tijjani Iyam
___________________________________
Page 6⃣7⃣
Tsaki na kuma yi tare da ɗauke kaina ma gabaɗaya daga gare ta na cigaba da abinda ke gabana kafin na faɗa wanka. Girkin Nazifa ne kafin na fito ma har ta haɗa gawayi ta aza mana sanwa tana zaune gefe tana danna wayarta annuri fal akan fuskarta. Wata ƴar gefen room ɗin mu ta fito zata shiga banɗaki ta kallo Nazifa haɗi da faɗin"sarkin danna waya Nazifa ke kam ko gajiya bakya ji".
Ɗago kanta tayi ta yi murmushi ba tare da ta ce komai ba, ta mayar da kanka kan wayarta muka haɗa ido da yarinyar ta sakar mini wani laulausan murmushin da na kasa ganon ma'anarsa da kuma manufarta ta yinsa dab da ni ta iso idonta a cikin nawa kamar yanda nima ban ɗauke nawa idon daga cikin nata ba.
"Na'ima Muhammad Kabir".
Ta furta a sanyaye kamar mai yin raɗa, ta ɗaure fuskana tamau don Allah ya sa ni sam yarinyar bata birge ni saboda irin shigar da take yi na rashin ɗa'a da kuma rashin ta ido watau kunya, uwa uba bakinta babu linzami balle birki komai yazo maka kan harshe furta shi take yi ba tare da ta tauna ba balle ta yi masa tankaɗe da rairaya.
Na ce"wani abun ne?".
"Babu komai sai alkhairi bari na fito daga wanka zan zo muyi magana".
Ban ce da ita komai ba don na gaji da sauraranta nayi shigewa ta ɗakin na saka kayana, sannan na gyara mana ɗakin duk da ba wani datti ya yi ba, ina gamawa Nawwara tana dawowa daga sayo mana kayan miyar da ta fita yi a bakin hanya. Lokacin ni da Nazifa duk muna ɗaki ta shigo bakinta har kunne tsabar murmushin da take yi ta zube akan gadon da Nazifa take zaune ta ture ta gami da faɗin"ke lafiyarki wannan ai sai ki ɓalla min cinya".
"Ke dai bari wallahi akwai labari bari na watso ruwa na dawo".
Tana faɗin hakan ta fice da sauri tare da ɗauka bucket, abubuwan da aka yi mana muke ta dubawa ni da Nazifa har ta sauƙe girkin dai-dai ana ƙiran sallan magrib alwala muka fito yi muka tarar da an haɗa dambe wai anyi satan kuɗi a room ɗin su Rahina yanda take zazzago ruwan ashariya babu koma balle fulsitof kamar bamagujiya da masifa tamkar zata yi aron baki shi ya tabbatar mini da cewar kuɗinta aka ɗauka.
Aka ceje ko'ina a cikin ɗakin nasun da kuma wacce ake zargin ta ɗauki kuɗin, mamakina bai ƙaro ba sai da idanuna suka gano mini wacce ake zargin wacce muka yi magana da ita ne ɗazu da yanzu naji an ambace da kalmar sunan Shato sai rantse rantse take yi da abinda zai kashe ta akan ita ko idon kuɗin bata gani ba balle ta ɗauka.
Alwalan mu muka yi muka koma ɗaki da hayaniyarsu ta addabe mu muka rufo ƙofar mu, sai da muka yi sallan isha'i sannan muka ci abinci.
"Ba ki bamu labarin da ɗazu ya sanya ki murnar da kika shigo da ita ba".
Na faɗa ina kallon Nawwara tare da murmushi akan fuskana kafin muka haɗa ido da Nazifa muka tuntsire da dariya Nazifa ta ce"tawan ko dai ƴan sulalla kika sinta ne naga bakin ki ya ƙi rufuwa yanzu mu kasa yau ko meye dare mu fito sayo gashashshiyar kaza".
Wani dariyar muka ƙara bushewa dashi sosai muke ƙyaƙyƙyalawa babi ƙauƙautawa kamar waɗanɗa aka ba wa wankin gardi, sai da muka yi mai ishashar mu muka dakata don kanmu tare da zubawa Nawwara da take kwance tana danna wayarta na jiyamu saboda yanda tayi mana banza ko tanka mana bata yi ba.
Na kai hannu na fizge wayar na ce"meye haka muna miki magana kin wani share mu". Sai a sannan ta tashi zaune tare da cewar"ai jinku kawai nake yi ina kuma tsara yanda zan faɗa muku haɗuwar abinda yau nayi katari dashi". Gyara zama muka yi tare da bata hankalinmu sosai cikin zaƙuwar son jin abinda zata furta mana.
Sai da tayi gyaran murya kana ta soma faɗin"in gaya muku ɗazu fita na sayo kayan miya naje inda muke sayowa ya ce min babu komai a wajensa sai gobe zai je sari, na tsallaka ɗayan wajen na saya a wajensa har ya gama haɗa min komai saura na bashi kuɗi kamar ance min ɗaga kai kanki ai kuwa ina ɗago kaina idanuna suka sauƙa akan kyakykyawan fuskarsa mai cike da haiba, cikar kamala da kuma kwarjini wayyo Allah guy ɗin ya haɗo over and over ina gaya muku sai dai har na baro wajen ban ji ya ce komai ba naso jin muryarsa wallah...".
Saurin katse ta nayi da wata tsaki mai dogon zangon da na saka ba tare da ta ƙare zancen da ta ɗauke mai ban haushi ba a gare ni, tsam na miƙe kan ƙafafuna ina mai faɗin"aikin banza daman duk akan namiji ne kika zaunar damu haka?, to wallahi Allah ya isa lokacina da kika sanya na ɓata wajen sauraronki".
Dariya duk su biyun suka sanya kafin Nawwara ta ce"wallahi don ba ki gan shi bane na tabbatar kema sai ya burge ki". Kafin nayo magana Nazifa tayi saurin amshe zancen da faɗin"kar kice min yafi Mr Saif haɗuwa?".
"Wuce nan wallahi yafi shi nisa ba kusa ba duk yanda zan siffanta miki shi to sai na rage wani abun komai nashi cif cif".
A kufule na ce "Allah ya sauƙe wallahi, wai ni ne namiji zai birge ni tam lalle kin kama aiki ai ba'a yi shi ba kuma ba za'a taɓa ba. Namiji ya bar mini taɓon da ba zai taɓa gogewa ba a cikin tarihin rayuwata ya bar mini ciwon da kullum nake jinsa sabo a cikin zuciyata ya bar mini darasin da haddansa ba zai taɓa gogewa daga cikin kwanyata ba".
Shuru nayi saboda ƙwallar da suka ciko mini kurmin idaniya, duk suka miƙe suna tambayata lafiya kuwa?, ban tanka musu ba na bar wajen na kwanta abi na basu haƙura ba suka cigaba da yi mini tambaya sai dai ba ta sauya zani ba nan ma shuru na yi musu ala dole suka haƙura suka bar ni.
Daren ranar sam ban iya runtsawa ba sai faman juyi nake yi kan katifar idanuna a bushe ƙas, raina yana wani irin tafasan da ban san dalilin faruwar hakan a gare ni ba. Wayata na ɗauka da niyyar ƙiran yaya Majid naga har ƙarfe sha ɗaya nasan yanzu ya riga ya kwanta in dai ba wani dalili mai ƙarfi bane ya tsayar dashi. Ganin da gaske ba zan iya baccin ba ya sani tashi naje na ɗauko alawa nazo na tada salla raka'a biyu nayi na sallame na rasa abinda zanyi domin sam na gaza yin addu'ar ma, ban ankara ba naji ɗumin hawaye suna bin kuncina tare da zarcewa izuwa tudun wuyana, kalaman Nawwaran suna dawo mini cikin kwanyata tiryan-tiryan wai in na ganshi dole ya burge ni.
Ƙyaƙyƙyawan ajiyar numfashi na sauƙe bana jin akwai wani namijin da zai yi mini kyan gani a bisa idaniyata balle har zuciyata ta gamsu dashi naji wai ya burge bayan malam Yusuf da na so da dukkanin gaskiya irin son da ban taɓa yiwa kowa ba, dashi na fara soyayya kuma daga kanshi na gama na kuma rufe wannan babin a cikin rayuwata. Babu wanda zan iya so a yanzu domin ko soyayyar da nayi a baya bata amfane ni da komai ba sai ma cutar da zuciyar da bata san komai ba da tayi.
Sai bayan asubahi na sama bacci ɓarawo ya ɗauke ni, kasancewar lectures ɗin ƙarfe goma muke dashi ya sanya su Nawwara basu ma tashe ni ba. Sai goma saura na tashi ina kamo sunan mahaliccina cikin bakina lokacin su Nawwara har sun gama komai wanka kawai nayi na shirya muka ci abinci muka fita.
A hanya Nawwara take bani haƙuri wai ko maganar da tayi mini jiya ne ya ɓata mini rai har ya sanya hawayena zuba, na nuna mata ba haka bane kawai na tina da wani abun ne. Awa ɗaya zamu yi a lecture ɗin muna fitowa muka shiga na ƙarfe sha ɗaya zuwa ƙarfe ɗaya daga haka muka tsaya group ɗin mu na assigment da aka ce a raba kafin muka wuce hostel don iya lectures ɗin da muke dashi a ranar kenan.
Haka na ƙarar da wunin ranar kamar wacce aka zarewa laka a ciki, su Nawwara sai tambayata suke yi amma na nuna musu babu komai ganin hankalinsu ya soma tashi ya sanya ni kore dukkan damuwar raina ko don su da suka kasance masu son farin-cikina.
Da yamma muka yi wanki gabaɗayan mu don mun tara kayan wanki sosai sanda muka gama magrib ta kawo kai wanka muka yi muka ci abinci sannan muka fito zamu je area class domin muyi karatu.
Turus nayi ganin manyan motocin da suke fake a ƙofar hostel ɗin ga ƴanmata tsaye a jikinsu. Mamaki ya gama bayyana a kan fuskana don nikam tunda nazo ban taɓa fita a irin wannan lokacin ba shiyasa ban san wainar da ake toyawa ba. Gam Nazifa ta riƙo hannuna saboda rawar da ilahirin jikina ya ɗauka muka bar wajen cikin sauri kamar zamu kife kan fuskokinmu, hostel muka koma don motocin da suke wajen ba zasu ratsu ba muna isa ɗakin na zube kan gwiwoyina ina maida numfashi kamar wacce tayi gudun famfalaƙin ceton rai.
Muryata har ta fara rawa na ce"nifa bangane ba waɗancan motocin da ƴan matan fa?".
Nawwara ta saki ajiyar zuciya kafin ta ce"Duk wacce kika gani ɗalibar makarantar nan ce kuma mazauna cikin hostel ɗin waɗannan masu motocin kuma da kike gani cikin su gabaɗaya babu ƙaramin mutum wakilan manyan ƴan siyasa ne da suke aikowa a ɗauki ɗalibai ana kai musu har inda suke suna ruɗar su da maƙudan kuɗi, a irin haka yara da yawa suke faɗawa cikin halaka wasu su lalace har su rasa mutuncinsu da suka baro gidan iyayensu dashi, wasu kuma su faɗa harkan shaye-shayen miyagun ƙwayoyin da in basu yi sa'a ba daga karshe su rasa hankalinsu gabaɗaya. Wasu kuma su ɗauki juna biyu wasu kuma su haɗu da cuta mai karya garkuwan jiki".
Daga haka ta tsagaita kafin ta ɗaura da"duk ƴan matan da kika gani a waje suma da kuɗi aka yaudare su, da yawansu rashin wadatar zuci ne ke kai su ga afkawa tafkin nadama da kuma cizon ɗan yatsa daga ƙarshe. Wasu iyayensu basu da ƙarfin samar musu da komai na buƙata makarantar ma da ƙyar aka turo su hakan ya kan sanya su biyewa mungayen ƙawayen da zasu kwaɗaita musu wannan hanyar. Iyayensu suna can gida suna alfahari dasu amma su nan sunyi fatali da wannan yardar tasun akan su".
MATAN AREWA
(Book two)
© Maimunah Tijjani Iyam
_________________________________
Page 6⃣8⃣
Take dukkan jikina ya ɗauki jikina ya ɗauki mazari tamkarana jona mini wutar lantarki a jikina, hakwarana suna datse harshena. Ƙwalla tana ɓulɓulowa daga idanuna maganar nan ta Umma Salma suka ziyartar ƙwaƙwalwata tare da yi mini amsa kuwa cikin masarrafar jina babu shiri na runtse idanuna tare da matse hannuna waje guda.
Tabbas mafi yawan zancen natan suna kan gwadaben gaskiya, tunda gashi yazo idanuna sun gane mini komai a zahirance yanda bahaushe yake cewa gani ya kori ji yau hakan ya kasance a gare ni.
Lamau na zauna a wajen ƙauƙaran motsi ya gagare ni balle yunƙurin tashi akan ƙafata dake yi mini rawa ina daga zaune, jin an dafo kafaɗata ta baya ya sa ni cira kaina tare da yin ƙarfin halin watsawa Nazifa idanuna.
Itama idanunta taf da kwantattun hawaye ta miƙa mini hannu na riƙe na tashi daga durƙushewar da nayi na zauna akan katifarta. Kafin tayi ƙarfin halin furta"ke kuma Nawwara ina kika san duk wannan zancen?".
Sai da ta numfasa kamin ta ce"naji su a wajen yayata domin ita ma tayi makarantar nan yanzu shekararta ɗayda rasuwa kuma itama ta sinci kanta cikin irin wannan halin na bibiye bibiyen maza a sanadiyar zaman hostel da hakan ya zamto sanadiyar rayuwarta gabaɗaya".
Idanuna a waje na furta"duk da hakan kuma shine kema aka turo ki makarantar Nawwara".
Wasu siraran hawaye da suke fara ziraro mata ta yarce tare da zuƙe majinar kukan da tazo mata kana ta soma faɗin"mu biyar ne a wajen mahaifiyarmu duk su ukun sun rasu mu biyu kaɗai muka yi saura, sai kuma ƴaƴan uba da muke dasu guda goma sha ɗaya. Mahaifiyarmu victim ce ta auran wuri kuma kamar da yawa daga cikin ƴaƴa mata ita ma tana da burin yin karatun zamani sai dai hakan bai samu ba a gare ta. Don haka ta ɗaura buri akan mu don ganin munyi karatu duk da kuwa Abbanmu ya nuna cewar ba zai iya ɗaukar nauyin karatunmu mu duka ba, ita kaɗai take faɗi tashi wajen ganin munyi kasancewar Anty Mami babba a ɗakinmu ya sanya Umma ta siyar da filinta na gado ta biya mata kuɗin zana jarabawa har cikin ikon Allah ta zama admission a wannan jami'ar Umma ita ke ta faɗi tashi akan karatunta".
Babu shiri ta tsagaita ba don ta gama ba sai don saboda wani kuka mai matuƙar sauti da ya kubce mata, cikinmu babu mai lallashin wani domin duk mu ɗin ma kukan muke taya ta tun kafin ta dire izuwa ƙarshen labarin natan. Sai da tayi kukan sosai kafin ta ɗaura da faɗin"Duk muna can muna murnar kasancewarta a wannan jami'ar koda Umma zata rasa zanin ɗaurawa bata taɓa kuskurewa biyawa Anty Mami dukkanin ɗawainiyar makarantarta da zata taso ba. Babu ko sisin Abba har suka shiga 200 level karɓan kuɗin da take yi wajen Umma da sunan zata yi amfani dasu a makaranta ya ƙaru duk da hakan kuwa Umma bata taɓa kawo komai cikin ranta ba burinta bai wuce inganta rayuwar Anty Mami da karatun da ita ta rasa ba. Bamu sani ba ashe bama zama take yi a cikin makarantar ba balle har ta ɗauki karatun da ya kawo ta duk kuɗin da take karɓa wajen Umma yawo suke zuwa gari gari da ƙawayenta da sunan shaƙatawa wai a hakan ne zasu sama mijin da hannunsa yake cuɗar bayansa idan