Showing 87001 words to 90000 words out of 171161 words
Chapter 30 - MATAN AREWA BOOK TWO COMPLETE PDF .txt
muka tafi lecture muna samum interval ɗin awa ɗaya muka nufi ofishin Mr Suleiman bayan mun tambayi Class rep ya kwatanta mana.
Duk bugun da ƙirjinmu yake yi hakan bai dakatar damu daga nufar ofishin da muka yi gadan-gadan ba, har muka iso bakin ƙofar a kan sunan dake maƙale saman ofishin na fara zube idanuna da aka rubuta da manyan harrufa.
MR. SULEIMAN SAMBO.
Ɓoyayyiyar ajiyar zuciya na sauƙe lokacin da nake knocking a ƙofar sai da nayi har na gaji sannan aka bada iznin shigowa, muka kutsa kai bakunan mu ɗauke da siririyar sallama bai amsa mana ba har muka ƙarisa shigowa. Yana zaune kan kujera ya ɗaura ƙafarsa kan babban teburin dake gabansa ya ɗaura ɗaya kan ɗaya idanunsa suna lumshe yayin da yake ɗan waina kujerar a hankali. Haɗe baki muka yi wajen gaishe shi nan ma bai amsa mana ba sai da muka gaji da tsayiwa kan ƙafafunmu da suka yi sanyi ƙalau kafin ya ce"what brought you here?".
"Sir we come to collect my scrip". Sai a sannan ya buɗe lumshashshun idanunsa ya zuba mana su da suka yi jajir saurin rusunar da namu ƙwayayan idanunmu ƙasa muka yi kafin muryarsa dakakkiya ta dira a ƙofofin kunnuwanmu.
"All of you?".
"No Sir only me".
Kamar ba zai yi magana ba don tsabar wulaƙanci da kuma mulki, sai da muka fidda rai sannan ya ce"cewa nayi kizo ko karɓa scrip ɗinki ban ce ki tattaro min duk friends ɗinki kuzo ku cika min office ba, for that reason ku fice min daga office. Je kuma duk ranar da kika shirya zuwa karɓan scrip ɗinki you can come idan kuma ba ki dawo ba is your own cup of tea za ki gani a portal ɗinki ku ɓace min daga gani".
A tsawace ya ƙare zancen nasan na ƙarshe cikin maƙurar ɗaga murya, da ya haifar mana da rawar jiki har muna karu da juna muka fice daga ofishin da sarsarfa muka ɗauki hanyar ficewa daga wajen kamar daga sama nayi karo da mutum nayi saurin matsawa tare da janye jikina gefe guda ɗago kan da zanyi na ga Mr Saif ne tsaye hannayensa zube dukka cikin aljihun wandon ruwan tokan yadin dake jikinsa. Babu shiri na ɗauke idona daga kansa ina ƙara shan ruwan jikina cikin rawar jiki da na murya na ce"sorry sir". Daga haka muka fara ƙoƙarin barin wajen dakakkiyar muryarsa ta dakatar damu"from where are you?".
Duk shuru muka yi sai da ya kuma maimata mana a zafafe kafin Nawwara ta aro jarumta ta furta masa"mu kai wa Malam Suleiman assigment ɗin mu ne".
Daga kallon da yake mana kaɗai ya isa ya tabbatar mana da cewar bai yarda da abinda ta faɗa masa ba, har ya buɗe baki da nufin cewa wani abun wayarsa da ta fara ruri ya katse shi sai da ya zaro ta daga aljihun gaban rigarsa kafin ya yi man alama da ido kana mu bar wajen ya yi picking ɗin wayar.
Kara wayar ya yi a kunnensa yana sauraron manager ɗin gidan gonan nasan da yake maganar a matuƙar kiɗime kamar zai datse harshensa.
"Yallaɓai akwai gagarumin matsala kajin da muka zuba na salla ne da raguwar gabaɗaya yau an wayi gari babu ko ɗaya sun mace".
MATAN AREWA
(Book two)
© Maimunah Tijjani Iyam
_________________________________
Page 8⃣2⃣
Jiri ne mai ƙarfin gaske ya fara walagigi dashi amma ƙarfin hali da dakewar zuciya irin tasa ya hana sa nuna matuƙar kaɗuwar da yake ciki akan fuskarsa. Dafe goshinsa da jijiyoyin kansa suka fara bayyana raɗau-raɗau a saman goshin nasan ya yi tare da cije leɓɓansa da ƙarfin gaske yana maimata kalmar hasbunallahu wa ni'imal wakil a cikin ransa a ƙoƙarin ganin mai rasa nutsuwarsa ba.
Ba tare da ya ce komai ba ya zare wayar daga kunnensa maganar da aka yi ya tilasta masa buɗe ɗago idanunsa ya sauƙe su akan fuskar mamallakin muryar.
"Malam Saifuddeen lafiya kuwa kake?".
Duk yanayin da yake cikin hakan bai hana shi ƙirƙiro murmushin dole ya yaɓa a fuskarsa ba tare da faɗin"lafiya ƙalau kar ka damu Abdul-aziz".
"Ko dai jikin Hajiyan ne ya motsa kake ƙoƙarin ɓoye min?".
"A'a ba jikin Ummi bane wani abun ne na daban, ga key ɗin office ɗin na ka rufe min ka riƙe a wajen ka zuwa gobe zan karɓa".
Yana gama faɗin hakan ya juya cikin sauri zai bar wajen da sarsarfa Abdul-aziz yake bin sa bai cim masa ba sai da ya isa wajen motarsa zai shige ya riƙe ƙofar yana maida numfashin saurin da ya dunga zabgawa ya ce"Haba Saifuddeen wai meye yake faruwa ne?, wallahi baka cikin hayyacinka na tabbata ba zaka iya sarrafa motar nan ba".
Bai ce dashi komai ba illa zama da ya yi mazaunin driver tare da ɗaura kansa jikin sitiyarin motar yana sauƙe numfashi tamkar wanda ya yi gudun ceton rai, har yanzun yana nanata kalmar hasbunallahu wa ni'iman wakil jin hannun Abdul-aziz saman kafaɗarsa hakan bai sanya shi ɗagowa ba balle furta masa koda kalma ne. Cikin sanyin murya ya soma faɗin"Saifuddeen dan Allah ka bari na kai ka duk inda zaka je".
Nan ma bai ce komai ba illa miƙa masa key ɗin motar da ya yi, ya tashi ya koma mazaunin ɗan zaman banza sai da suka fice daga makarantar suka yi nisa sosai sannan Abdul-aziz ya tambaye shi inda zai kai shi kamar wanda aka yiwa dole ya furta"gidan gonana".
Cikin mintunan da basu gaza ashirin ba suka isa wajen suka fito hannayensa dukka zube cikin aljihun wandonsa kamar kullum, ya ɗaga idanunsa yana ƙarewa faffaɗan wajen kallo babban waje ne da ya tsaru matuƙa cikin kyawun zubi da kuma tsari ga yawaitan ma'aikata ta ko'ina masu kula da wajen.
Yana tsaye a wajen ya hango manager ɗinsa ya nufo inda yake tsaye cikin sauri kamar zai kife akan fuskarsa, har ya iso wajen bai ɗauke idonsa daga kansa ba.
"Yallaɓai ka ƙariso ka shigo ka gansu".
Bai ce komai ba ya bi shi suka shiga inda kaji, zabbi, agwagi, ɗawisu, gis, jimina, kifi da kuma jinsin shanuka suke kowanne da nasu ɓangaren ƙarƙarfan ajiyar zuciya ya sauƙe sa'ilin da idanunsa sunka yi masa tozali da gawarwakin su hatta shanukan duk sun mace ga wani irin farin kumfan da yake fitowa daga bakinsu, manyan dam ɗin kifayen ya nufa ya tsura musu idanu suma duk sun mutu sun hauhau sama ruwan da ya sauya launi ya sanya hannunsa a ciki yana ɗan karkaɗawa kafin ya ciro ya shinshina a hancinsa.
"Yallaɓai ban san meye ya faru ba yau na shigo da wuri saboda costomer da zasu zo yau suyi sarin kwai, da kaina duk na dudduba su kafin na shiga ofishina misalin ƙarfe tara na fito na gansu duk suna magagin mutuwa kafin muyi wani yunƙuri duk sun mace kifin ne kawai muka tsira dashi tunda daman su ana cin su haka".
Wani murmushi mai ɗauke da ɓoyayyun manufofi ya sakar masa yana takuwa ya iso har gabansa tare da ɗaura hannunsa na dama saman kafaɗarsa karantar yanayin fuskarsa kawai yake yi da ta bayyanar da tsantsan tsoron dake ƙunshe ƙasan ƙalbinsa. Sai da ya fesar da zazzafan iska daga bakinsa kafin ya ce"karka damu Habib tsausayi ne kuma cikin ko wani kasuwanci akwai riba kuma akwai faɗuwa duk wacce ta faɗawa mutum dole ya karɓe ta hannu bibiyu ya yiwa Allah godiya, Allah ya sa da abinda hakan ya tare ya musanya min da wani alkhairin".
"Amin ya Allah".
Abdul-aziz ya amsa dashi a sanyaye yana jifan Saifuddeen ɗin da kallon tausayi, cigaba da zagayawa cikin wajen suka yi babu wani abu mai rai a wajen da ya yi saura duk sun mace macewar da ba'a san dalilin faruwarsa lokaci ɗaya ba, ma'aikatan wjaen da ƴan unguwan suna ta jajanta faruwar lamarin tare da yi masa addu'ar Allah yasa da abunda hakan ya tare ya kuma kawo masa wani hanyan ta inda bai yi tsammani da zato ba. Abu ɗaya ya sanyawa ransa kuma ya sama nutsuwa a kansa shine dukkan abinda ya same bawa muƙaddari ne daga Allah kuma daman tun fil azal rubutaccen lamari ne a cikin littafin ƙaddarar rayuwarsa. Sai da aka kwashe komai daga wajen aka fita dasu kiyafen kawai aka bari da kuma ƙwayayen kajin shima ya ce ma'aikatan su raba a tsakanin su. Sai da kowa ya fice daga wajen kafin Abdul-aziz ya ja motar suka fice suma asibiti wajen Ummi ya ce ya kai shi, har suka isa bai ce komai ba illa jingina bayansa jikin kujerar motar da ya yi ya lumshe idanunsa.
Farouk suka iske zaune a ɗakin sallamar da Abdul-aziz ya yi ya sanya shi ɗago kansa tare da miƙewa ya basu kujerar da yake zaune a kai sai da suka zauna sannan ya gaishe da Abdul-aziz da fara'a ya amsa masa tare da tambayarsa jikin Ummin yana miƙa masa hannu suyi musabaha amma ya shanye nashi yana ɗan sosa ƙeya.
Shi kam sosai Farouk ɗin yake burge shi saboda tarbiya da sanin ya kamatansa wannan dalilin ya sanya shi nacewa Saifuddeen ɗin sun yi aboka tunda aiki ya haɗa su amma sam ya kasa samun kansa. Muryar Farouk ɗin ya katse masa hanzari"yaya Saif lafiya kuwa kake?".
Da ido ya yi masa alama da meye ka gani?, ya sunkuyar da kai ya ce"kawai naga yanayinka ya canja ne duk da abu ne mai wahala bambamce yanayin nan biyu a gare ka na farin-ciki ko akasin hakan amma ni ba zaka ɓoye min ba wani abun ne ya faru?".
Bai kula shi illa kama hannun Ummin da ya yi ya sanya cikin nasa yana murzawa a hankali tare da sauƙe ajiyar numfashi a kai a kai, har kullum bai cire rai ga samun lafiyarta ba balle jin sautin muryarta a kunnuwansa ko ba yau ba yana tinanin gobe koda goben tazo burinsa bai cika ba yana saka ran jibi haka har ƙarshen rayuwarsa. Jin Farouk kusa dashi ya sashi saurin kai dubansa gare ta raurau ya yi da ido ya ce"please Yaya Saif menene?".
Yana shafa kansa ya yin da ɗayan hannunsa har yanzun yake cikin na Ummin ya ce"Umar ba wani abun bane babba wani iftila'i ne ya faɗa wa gidan gonan mu duk sun mutu yanzu ma daga can naje na sallami dukkan ma'aikatan domin babu amfanin cigaba da zamansu a waj...".
Tun kafin ya ƙarisa Farouk ya miƙe tsaye a kiɗime ya ce"wait yaya Saif bangane ba wai duk sun mutu ina wanda aka zuba domin shigowar ramadan da kuma salla wai dukkansu?, garin yaya hakan ta faru ina su ma'aikatan suke?".
Da sauri Abdul-aziz shima ya tashi ya riƙe Farouk ɗin da hawaye suke zirara masa daga idanu ya ce"ka nutsu mana Farouk ka iya maimata innalillahi wa inna ilaihir raji'un a cikin ranka faɗin manzon Allah ne duk wanda wani musifa ta faru dashi to ya koma ga Allah domin shi kaɗai ne yake iya juya lamuran bawa kamar yanda yake juya yanayin zafi zuwa sanyin dare zuwa safiya in sha Allah wani hanyar zai fito, shima kansa Saifuddeen ɗin yana cikin matuƙar kaɗuwa game da faruwar lamarin nan kar kaso kaga yanayin da ya shiga a lokacin".
"Abdul-aziz ba na shiga cikin ɗimuwa game da faruwar lamarin nan bane don asaran da nayi, a'a sanda Habib ya sanar dani faruwa lamarin dubban ma'aikatan da suke ci, sha, sutura, ɗaukar nauyin karatunsu wasu har da iyayensu da suke ƙarƙarshin wajen sune suka fara zuwa raina. Domin ba zan yaudari kaina ba tabbas bani da kuɗin da zan iya farfaɗo da wajen nan yanzu dole sai dai a rufe shi wanda hakan zai taɓa rayuwarsu yaya zasu yi?, wani rayuwa zasu fara yi sanadin hakan?, wannan tinanin shi ya hana ni nutsuwa har yanzun".
Shuru ɗakin gabaɗaya ya ɗaukar baka jin komai sai sauƙar numfashinsu, fizgewa Farouk ya yi daga jikin Abdul-aziz ya kifa kansa kan cinyar Saifuddeen ɗin yana sakin wani kuka mai ban tausayi da karyar da zuciyar mai sauraronsa.
A hankali yake shafa sumar kansa zuwa bayan wuyansa idanunsa suna kan Umminsu cikin sanyin murya yake faɗin"Farouk dole rayuwa sai da ƙalubale da kuma jarabawa yarda da hakan shike nuna cikar mumunintakan mutum, dole nasan zaka yi kuka domin wannan gidan gonan shi kaɗai ne gamu da tinanina kai ma ka fara zuwa can kafin Allah ya kawo maka wani aikin sai kuma ga yanda Allah ya yi dashi babu yanda kuma iya domin kana naka ne daman Allah ya na nashi kuma lissafinsa shine dai-dai a ko yaushe ".
Daga haka ya dakata tare da ɗago kan Farouk ɗin ya tallafo haɓarsa idanunsa cikin nasa ya ce"Haba gudan jini ka manta faɗin nan na Ummi cewar duk wanda ya rungumi haƙuri to haƙiƙa ya rungumi babbar nasara a rayuwa da ba zata taɓa barin sa ya faɗi ba a rayuwa?".
"Yaya Saif ko yaushe rayuwarmu cikin haƙuri take wai har sai yaushe ne komai zai zo ƙarshe?".
"Matuƙar da rai da rayuwa to ka sanya a ranka komai mai wucewa ne Umar".
Shuru ya yi bai ƙara cewa komai ba illa sautin kukansa da yake tashi a hankali, tare suka wuni da Abdul-aziz a asibitin sai yamma lisis Saifuddeen ya tilasta masa tafiya gida cikin ƙarfin hali yake tsokalarsa kar madam ta ga ya daɗe bai dawo ba ta fara cikiya. Murmushi kawai ya yi masa don yasan duk wani abunda Saif ɗin yake yi a halin yanzu ƙarfin hali, juriya, uwa uba yarda da hukuncin Allah gare shi ne kawai.
MATAN AREWA
(Book two)
© Maimunah Tijjani Iyam
_________________________________
Page 8⃣3⃣
Tun bayan barowar mu ofishin Mr Suleiman bamu koma raguwar lectures ɗin da muke dasu a ranar ba muka wuce hostel kowacce da tinanin da take yi cikin ranta.
Nawwara tana tsaye tann zagaye ɗakin riƙe da ƙugunta take faɗin"tabɗijam lalle ma malamin nan cikakken tantiri ne na bugawa a jarida wallahi sai ya riƙe script ɗin idan ana ci sai ya kwaɗa ya cinye da yaji, babu abunda ya isa ya yi miki matuƙar Allah ya bai rubuta hakan a gare ki ba Nazifa don haka ki kwantar da hankalinki ki ɗauki duk wannan maganar na nasan a matsayi suki butsunro da kuma hargagi".
"Nawwara bana son duk wani abun da zai haɗa ni da malaman jami'ar nan, mussamman malam Suleiman da yake bi na da wani nufin da ban san meye yake ƙule a ƙasa ba ace daga shigowa ta ko semester ɗaya ban yi na fara cinkaro da irin wannan matsalar ai kuwa kinga dole hankalina idan ya yi dubu duk su tashi".
Sausauta amon muryata nayi ina fuskanto Nazifa da take zaune dirsham a ƙasa na ce"kifa kwantar da hankalinki Nazifa in sha Allah babu wani abun da zai faru da yardan Allah ga watan ramadan ne ma yake tunkaro mu yanzu tinga muna da damar da zamu kai dukkan kukan mu ga wanda zai iya mana".
Kanta kawai ta ɗaga mana ta miƙe ta kwanta akan gado babu daɗewa wayarta ta soma ruri, haɗe baki muka da Nawwara wajen faɗin"yaya Amin ya ƙira".
Bata kula mu illa juya mana baya da tayi ta fara wayarta muka cigaba da dariyarmu don izuwa yanzu mafi yawan mazauna hostel ɗin sun san sunan na yaya Amin saboda yawan ambatan da Nazifa take yi duk inda ta zauna, da yamma ni nayi mana abinci muka ci bayan munyi sallan isha'i Nawwara ta ƙira kawunta suka gaisa sannan ya miƙawa mahaifiyarta har muma duk muka gaisa dashi tana ta sanya mana albarka tare da yi mana nasihar mu maida hankali muyi abinda ya kawo mu kar mu biyewa ƙawayen banza da samarin da zasu gurɓata mana rayuwarmu ta hanyar jan ra'ayinmu da ƙyalƙyali banza, sun ɗan taɓa hiran kafin suka yi sallama Nazifa tayi mana wanke-wanke sannan muka kwashi handout muka tafi area class karatu.
Zaune yake akan kujerun da aka yi su da siminti domin hutawan ɗalibai, ya harɗe hannayensa wajen guda tare da tsurawa hada-hadan ɗaliban a yalwataccen farfajiyar jami'ar da ƙwayayen sololi suka haske wajen tamkar ba dare ba, sosai ya yi zurfi cikin tafkin tinanin da ya faɗa da zantukan da suka tattaunawar da suka yi da Anty Binta a waya yake dawo masa tiryan-tiryan da yana da iko da cikakken isa akan Husna da tabbas ya yi fatali da wannan auren da ake shirin ƙullawa tsakaninta da Safwan da kuɗi da kuma sanayyar iyayensa a cikin unguwar suka haɗu suka rufewa Anty Binta idanu da har bata iya ganin aibunsa balle hango rashin cancantarsa ga ya zamto miji ga Husna.
Ƙarƙarfan ajiyan zuciya ya sauƙe a karo na barkatai tinowa da ya yi cewar a yanda ta labarta masa cikin wayar da suka yi cewa bayan sallan azumi da satikai biyu aka tsayar da lokacin bikin, yanzu kam bakin almakashi ya bushe babu abunda da zai iya yi domin ganin dakatar da faruwar lamarin sai dai ya taya su da addu'ar Allahu ya albarkaci auren. Yana da burin ganin ta sama ilmi ingantaccen da zata iya riƙe kanta koda bayan ƙasa ya rufe musu idaniya ba zata wulaƙanta ba kuma ba zata dogara ga aljihun wani ba sai dai kash bahaushe yana cewa gurbin ido ba zai taɓa zama ido ba da ace ƴarsa ce ta cikinsa da nan ne sai nuna iko da gadaransa akan ta.
Dafe goshinsa ya yi tinawa da ya yi shima yanzu da wataƙil ɗansa ko ƴarsa ta da ta ko ya da ta, wataƙil ma har ya ɗauke shi ya yi masa wasa sai dai ƙaddarar Allah ta shafe faruwar hashashen zuciyarsa cikin da ko haife shi ba a kai ga yi ba Allah ya zartar da hukunsa a gansa.
"Allah ya jiƙanki Hanan ya tona asirin waɗanda suka aikata miki wannan mummunan aiki, ya hana su samun kwanciyar hankali Rabbi ya sanya ki zamto mai ceto iyayenki ranar karɓan sakamako".
A hankali yake furta maganar tana ganin gilmawan hotunan Hanan ɗin masu motsi a cikin idanunsa. Ya daɗe zaune a wajen kafin ya miƙe ya ɗauki hanyar komawa hostel ɗinsu na maza wayarsa dake ruri ya ciro daga cikin aljihunsa ganin sunan yaya Auwal ya bayyana cikin screen ɗin wayar ya sanya shi ɗaha ƙiran tare da kara wayar a kunnensa yann tafe suna