Showing 135001 words to 138000 words out of 171161 words

Chapter 46 - MATAN AREWA BOOK TWO COMPLETE PDF .txt

yaya Amin, Umma tana nan lafiya ƙalau wallahi ya hutu?".


Alhamdulillah ta amsa dashi muka cigaba da hiran mu, har sai da Anty Zakiyya ta shigo ɗakin ta iske ni na miƙa mata suka gaisa kana muka yi sallama. Dai-dai sa'ilin da sallaman goggo Suwaiba ya ratsa kunnuwan mu a tare muka amsa tare da gaishe ta ta amsa mana tana yiwa kanta mazauni a bisa ɗaga daga cikin kujeru biyun da suke ɗakin tana faɗin"Zakiyya har kin shirya kenan?".


"E wallahi goggo yanzu zan shirya naji kin ci da safe zamu koma shiyasa".


Kanta ta jinjina kafin ta ce"ai kuwa an fasa tafiyar nan wataƙil sai zuwa satin gaba". Duk ido muka watsa mata kafin nayj saurin cewa"goggo lafiya?".
Sai da ta sakar mini murmushi kana ta ce"lafiya sumul uwata sai alkhairi kawai wani abun ne ya taso da dole mu zauna a nan zuwa kwana biyu". Shuru muka yi cikin mu babu wanda ya kuma cewa ko kanzil har Umma ta shigo na miƙe na kammala sharan da nake yi kafin na shiga wanka.


A hankali ya soma buɗe marafan idanunsa da yake jin sunyi masa nauyin gaske, kafin ya tashi zaune daga kwanciyar da ya yi yana kamo sunan mahaliccinsa a bisa harshensa. Goshinsa ya dafe da sauri saboda yanda ya sara masa da ƙarfi kafin ya sauƙe idanunsa akan agogon dake manne jikin bangon ɗakin hotel ɗin dake nuni da ƙarfe goma sha ɗayan rana saura mintuna biyar. Take baccin idanunsa ya wartsake ya sauƙo daga kan gadon ya nufi bathroom ya sakewa kansa shower ajiyan numfashi kawai yake sauƙewa akai akai tamkar wanda ya yi gudun ceton rai, ya daɗe cikin bathroom ɗin ruwa yana sauƙa a jikinsa kafin ya ɗaura towel a waist ɗinsa ya fito tare da wani ƙarami yana tsame sumarsa.


Akwatinsa ya nufa ya fiddo da mai da kuma kayan da zai yi amfani dasu ya zube akan gado, sannan ya fara shiryawa a nutse yake yin komai. Tsaf ya kammala shirinsa cikin shigar manyan kaya mai launi ruwan ƙasa ya sanya hula a kansa. Waige-waage ya soma yi yana neman inda ya ajiye wayarsa can ya hange ta a kan site drower ya isa ya ɗauka da nufin ƙiran nurses ɗin da ya kawo gida domin lura da Ummi har su dawo don jin yanda ta kwana da kuma yanayin jikin natan.


Rigis ya iske missed ɗin yaya Majid cikin wayarsa, haka nan kawai ya tsinci kansa da sakin tagwayen ajiyan numfashi sai da ya zauna akan kujeran dake ɗaki sannan ya bi bayan ƙiran. Bai ɗauka ba sai da ƙiran ya kusa tsinkewa suka gaisa da juna cikin mutuntawa da girmama juna sannan yaya Majid ya furta"munyi magana da su Abba sun ce suna buƙatar ganawa da kai a yau idan zai yiyu".


"Ba matsala in sha Allah zan zo nagode".


"Babu godiya tsakanin mu sai kazo ɗin".


Daga haka suka yi sallama zame wayar ya yi daga kunnensa tare da tsura mata idanuna, sosai yake jin wani irin matsanancin faɗuwar gaban da bai san dalilin sa ba. Addu'a da fatan samun nasara ya cigaba da yi cikin ransa domin ganin ya cikawa Ummi wannan burin dake ranta, ba wai don ya yarda da zancen likita akan cewar watanni shida kacal suka rage mata a duniya ba sai don tabbatar da wanzuwar farin-ciki da annuri a bisa fuskanta.


Ya daɗe zaune a wajen yana saƙa da warwara cikin ransa har izuwa sanda akan knocking a ƙofar ɗakin sai da ya ja dogon numfashi ya fesar kafin ya bada iznin shigowa. Farouk da Abdul-aziz ne suka shigo a tare sai kuma ma'aikacin hotel ɗin da ke bin su a baya ɗauke da abin karin kumallo a hannunsa akan center table ɗin dake tsakiyar ɗakin ga ajiye ya juya ya fice bayan ya gaishe su.


"Sai yanzu ka tashi?, tun ɗazu fa nazo nayi knocking baka buɗewa ba na koma".


Kansa kawai ya ɗaga masa yana miƙa musu hannu suka yi musabaha, daga nan ya shiga dialing lambar nurse mai kula da Ummin bugun farko ta ɗaga tare da jefo masa gaisuwa. A taƙaice ya amsa yana tambayarta jikin Ummi ta shaida masa da sauƙi babu wani damuwa umartanta ya yi akan ta bata wayar ta miƙa mata suka gaisa ya yi mata yaya jiki ta amsa kafin ta soma tambayar shi yaya suke.


Sun ɗau tsawon mintuna suna wayar kafin suka yi sallama, ya ɗago ya kalli Farouk da ya fara cin abin karin da aka kawo a nutse ya furta"ba'a kai maka ɗakinka bane?".


Sai da ya haɗiye chips ɗin da ya sanya a bakinsa sannan ya sama damar faɗin"an kai min tuntunin kawai nakan ne ya burge ni that's why". Murmushi kawai ya yi ya cigaba da cewa"Majid ya ƙira ni wai su Abba nason ganawa dani, so ku shirya after zuhr prayer sai muje".


Kwantar da murya Abdul-aziz ya yi ya ce"calm down my man ka kwantar da hankalinka ok, in sha Allah komai zai zo da sauƙi". Bai ce dashi komai ba illa kansa da ya jinjina masa.
A cikin hotel ɗin suka yi salla cikin masallaci sannan suka shigo mota suka fice, inda suka yi parking jiya nan yau ma suka ajiye motar sai da duk suka fito sannan ya zaro wayarsa da nufin ƙiran Majid ya sanar dashi isowar sa jin an riƙe rigarsa ya dakatar dashi daga ƙiran, idanu ya zubawa yaron dake sakar masa da murmushi yana faɗin"wajen yaya Majid kuka zo ko?". Murmushin shima ya maida masa tare da tsugunawa a gabansa ya riƙo hannunsa ya ce"wajen sa muka zo, da zaka taimaka mana kafin zafin ranan nan ya gama kona mu ka shiga ka ƙira mana shi da zamu yi maka godiya da yawa".


"Bari naje na faɗa masa ya taho da wuri kar rana ya ƙona ko to ". Ya ƙarishe zancen tare da zugawa a guje ya yi cikin gidan, da kallon sha'awa duk suka raka shi dashi babu jimawa suka fito tare da yaya Majid musabaha suka yi da juna ya wuce gaba suna biye dashi har cikin falon su Abba da daman zaman jiran zuwan sa suke yi tun bayan da suka dawo daga sallan zuhr daga masallaci.


Ciken da tsantsan girmamawa danƙare cikin lafuzan su suka haɗe baki wajen gaishe da su Abba, suka amsa musu cikin sakim fuska kafin shurun wucen gadi ya karaɗe falon har izuwa lokacin da Baba ya kawar dashi ta hanyar faɗin"mun sama labari daga wajen Majid na game da tattaunawan da kuka yi shiyasa muka buƙaci ji daga gare ka".


Ƙasa ya yi da kansa yana faɗin"haka ne ranka ya daɗe na nema ya nema min izni daga wajen ku".
"Madalla ina so ka sanya tsoron Allah a cikin dukkanin abunda zaka ce damu a nan, idan ka ɓoye mana ba zaka ɓoyewa wanda yake sama kuma masanin abinda yake ɓoye da na zahiri ba. Shim har cikin ranka kaji kana son Zakiyya ko kuwa so kake ka saka mana bisa taimakon da muka bada game da rashin lafiyar da Allah ya jarabci mahaifiyarka dashi?".
Ɓoyayyan ajiyan zuci ya saka ya ce"tabbas ganin na saka muku ta hanyar kyautata mata idan Allah ya mallaka min ita yana daga cikin dalilin da ya sanya ni neman auren ta, na yaba da nutsuwa da kuma hankalinta hatta mahaifiyata da makusan tana suna sun bani goyan baya".


Gyaran murya Abba ya yi haɗi da faɗin"zamu so ji wasu bayanai naka na karan kanka da zai taimaka mana wajen gudanar da binciken da zamu yi, kamar iyayenka da kuma asalinka".


Ji ya yi gabaɗaya jikinsa ya yi sanyi laƙwas, wanj irin kwarjini suka ƙara yi masa a idanunsa fiye da dukkan zuwan sa biyu gidan, zazzafan iska ya fesar daga bakinsa kafin ya sanar dasu komai da suka buƙata ji daga gare shi. Jinjina kai Baba ƙarami ya yi cike da tausayawa ya ce"Allah ya jiƙan shi da rahama, zaka iya ganin ta yanzu kafin ku tafi har izuwa lokacin da zamu kammala namu binciken mu neme ka".


A zuciyansa ya amsa da amin yayin da su Farouk suka amsa a bayyane, so yake yi ya yi musu godiya sai dai ganaɗaya bakinsa ya yi masa wani irin nauyi da ya gaza furta ko kalma ɗaya. Sai Abdul-aziz ne ya soma faɗin"mu gode Allah ya saka da alkhairi Allah ya ƙara lafiya da nisan kwaa mai amfani". Cike da jin daɗi suka haɗe baki wajen amsa addu'ar tasan da amin, miƙewa suka yi suka fice izuwa sashin Hajiya Babba suka gaishe ta nan yaya Majid ya sanar da ita komai sosai tayi farin-ciki da jin hakan da kanta ta aika aka ƙira Anty Zakiyya izuwa sashin ta.


Da sallama ta shigo ta zauna da dukkan su suka amsa mata, ta gaishe su suka amsa miƙewa Hajiya Babba tayi ta shige ɗakinta yayin da Abdul-aziz da Farouk suka tashi tare da yaya Majid suna faɗin su na zuwa.
Ganin duk sun watse ya sanya Anty Zakiyya yunƙurin miƙewa tana faɗin"na barka lafiya, bari na shiga daga ciki Hajiya ta aika ƙira na".
Bai ce komai ba har sai ta gama miƙewa tana ƙoƙarim shigewa ɗakin da Hajiya Babba ta shiga ya dakatar da ita da faɗin"Hajiya ce ta ƙira ki amma don ni tayi ƙira da za ki dawo ki zauna muyi magana".


Cike da rashin fahimta ta waigo da ido ya tabbatar mata da abinda ya faɗa, inda ta tashi ta koma ta zauna kanta a ƙasa. Sai da kusan mintuna biyar suka shuɗe cikin su babu wanda ya yi koda tari kafin ya soma faɗin"aiko ni aka yi gare ki". Da sauri ta ɗago kanta tare da sauƙe idonta akan fuskarsa sai kuma tayi ƙasa dasu ta ce"waye zai aiko ka waje na?".


"Zuciyata".


Ya faɗi zancen kai tsaye shuru tayi masa ba tare da ta ce komai ba, hakan ya bashi damar ɗaura da faɗin"ta ce na sanar dake cewa ke ce mahaɗinta da ta daɗe tana nema". Cak zantukan nasan suka tsaya zai da ya haɗiye wani miyau mai kauri kafin ya ɗaura da"Zakiyya na nema aurenki a wajen iyayenki kuma sun bani damar yin na nema yardan ki, haƙiƙa na yaba da nutsuwa, tarbiya da kuma hankalinki tun kallon farko da nayi miki wannan dalilin ya kwaɗaita wa zuciya son mallakan ki a matsayin abokiya rayuwa gare ni, zan so kiyi tinani akan hakan zan jira naji daga gare ki komai tsawon lokac..". Bai kai ga ƙarisawa ba ta miƙe ta shige ɗakin Hajiya Babba da gudu rufe da fuskanta, da kallo ya bi ta yana sauƙe ƙatuwar ajiyan zuciya tare da lumshe idanunsa.


Wani iri yake ji a cikin ransa da ya kasa fasalta menene, yaudara yake ƙoƙarin yi ko kuma zamba cikin aminci?, tabbas yasan zantukan da ya furta ba hakan suke har cikin zuciyarsa ba.




MATAN AREWA


(Book two)




© Maimunah Tijjani Iyam


_______________________________________




Page 1⃣1⃣0⃣


A kalla ya kai kusan mintuna biyar zaune a wajen sosai ya yi nisan kiwo cikin duniyar tinanin da ya faɗa, a bayyane ya sauƙe ƙatuwar ajiyar zuciya yana kafe ƙofar ɗakin da ta shige da kallo. Wayarsa da key ɗin motar dake zube a gabansa ya ɗauka tare da miƙewa ya fice daga falon a ƙofar gida ya tarar dasu Farouk suna ta zance da Majid da fuskarsa take bayyanar da tsantsan farin-cikin da ya yi zaman dirsham a cikin ransa. Jikinsa a sanyaye ya ƙarisa wajen Abdul-aziz ya kallo shi haɗi da faɗin"ka fito?".


Kansa ya daɗa masa kawai ya ce"mu je mu gaisa dasu Mama mu wuce". Gaba Majid ya yi suna biye dashi har izuwa sashin mu, muna zaune a filin tsakar gidan ina karanta wani littafin hausa da tun a makaranta na tura mai suna SALON ƘADDARATA cikin wayata, a karo na barkatai na sauƙe wata gwauruwan ajiyan zuciya tare da zame hannuna daga tallafe kuncina da nayi ina ƙara tabbatar da sahihancin wannan zancen na kowa irin tashi SALON ƘADDARAn shi cikin wannan rayuwan. Sosai tausayin jarumar cikin littafin mai suna Ummukursum ya maƙale mini a makwallaton raina, yanda nasu ƙaddaran ta zo musu ta ɓangaren uban su da ya kasance mai shaye-shaye kuma shugaban ƴan cacan da ya sanya a caca aka cinye shi ya bada aurenta.


Gyaran muryan da yaya Majid ya yi shi ya dawo dani cikin hayyacina daga duniyar karatun da na lulu tsabar kyawu da tsaruwan zubin labarin cikin ingataccen hausa har ganin abinda yake rubutun nake yi cikin idanuna ina imagine ɗin su.


Umarni yaya Majid ya bada akan mu kimtsa baƙin zasu shigo, kowa ya zaro hijabi ya sanya a jere suka shigo suka tsuguna akan ƙafar su suka haɗe baki wajen gaishe da matan gidan da suke wajen, Umma da Hajiya ne kawai basa zaune a wajen don haka dasu ne kawai basu gaisa ba suka fice.


Da kallon mamaki na bi su har suka ƙarisa ficewa daga cikin gidan, kafin na fara waige-waige da zumman gano Anty Zakiyya ko ta dawo daga ƙiran da Hajiya Babba tayi mata amma ban gano ta ba, har wani zuciyar ta raya mini na bi ta na gano sai kuma nayi zama na.


"Oh ni Zainabu wallahi iyayenku maza da jaye-jaye suke, ko ina suka kwakuso mana waɗannan kuma oho".


Furcin Umman su Anty Kubra kenan da ya sanya Umman Balkisu amsawa cikin faɗin"kema dai kya faɗa wataran sai kun kawo wanda zai yi ajalin su ai. Zancen ta na ƙarshe ya tilasta mini saurin kai dubana gare ta kafin na janye idona cikin raina ina faɗin"Allah ya kyauta". Kamar ko yaushe har jikin motar su yaya Majid ya yi musu rakiya suka wuce.


Kamar wacce aka jefo haka ta faɗo ɗakin Hajiya Babba tare da zama kusa da ita, cikin wani irin yanayi da yafi kama da na ruɗu take faɗin"Hajiya kaina yana juyawa ki fitar da ni daga cikin wannan duhun da lokaci guda ya kore hasken dake gilma min, meye wannan mutumin yake sanar dani?, kuskure ya yi ko kuma son raina min hankali yake son?, ko kuma yaudara na yake son yi?".


Sauƙe numfashi Hajiya Babba tayi tare da kamo hannunta ta sanya cikin nata ta riƙe gam tana fuskantan ta sosai ta ce"ki kwantar da hankalinki ki sanar dani meye ya ce da ke?".
Cikin mai da numfashi ta ce"cewa ya yi wai cewa ya yi zuciyarsa ta aiko shi wajena tana roƙon na zama mahaɗinta". Murmushi mai kyawu da ya ƙara fitar da dattaku gami da kamalan dake shinfiɗe bisa kamalalliyar fuskanta Hajiya Babba tayi, kana ta shiga faɗi cikin tausassan laffuza"to don wannan ne kika tada hankalinki?, ki ji ni da kyau wannan ba abon tada hankali bane hasalima godiya ga Allah ya dace kiyi da ya nuna mikin wannan ranar cikin rayuwarki, shekarunki yanzu ashirin Zakiyya duk ƙannanenki da sa'anninki suna gidajen mazajen su wasu ma har da ƴaƴa biyu zuwa uku, ki nema zaɓin Allah game da wannan lamarin kafin ki bashi amsa akan batun da yazo miki da shi idan alkhairi ne a gare ki Allah ya tabbatar idan kuma ba alkhairi bane Allah ya musanya miki da wani mafi zamowa alkhairi a gare ki".
Tunda ta soma maganar tayi ƙasa da kanta har ta kai aya bata ɗago ba, illa ɓoyayyun ajiyan zuciyan da take sauƙewa akai-akai wani irin nauyi ƙirjinta ya yi mata jin komai take yi tamkar a mafarki domin ta daɗe da cire rai da zuwan irin wannan ranar a cikin rayuwarta ta daɗe da miƙa wuya, da fawwalawa Allah dukkan lamuranta da tawakkalin cewar ba kowa bane akwai aure a rubuce a cikin kundin littafin ƙaddarar rayuwarsa. Sai da Hajiya Babba ta taɓo ta sannan ta dawo hayyacinta ajiyan zuciyan ta kuma sauƙewa a karo na barkatai a sanyaye ta furta"in sha Allah zan yi istikara akan lamarin kafin na ce dashi komai".


"To madalla Allah ya yu muku albarka ya haskaka muku rayuwarku ya tsare gaban ku da bayan ku".
"Amin" ta amsa dashi a raunane, sosai Hajiya Babba ta cigaba da kwantar mata da hankali da kuma bata shawarwari ƙiran sallan asr shiya sanya ta dawowa sashin mu, ina alwala a gindi bishiya tare da Nurain Anty Zakiyya ta ta shigo wucewa tayi kanta tsaye izuwa ɗakin Umma ba tare da ta waiwayi kowa ba da kallo na raka ta ina mamakin sauyiwar yanayinta don ba haka ta fita ba.


Tare muka iddar da alwalan da Nurain ya cife domin zuwa masallaci, tana zaune a bisa kujera na iske ta ta rafka tagumi hannu bibiyu da alama ko shigowa ta bata lura dashi ba balle tsayiwar da nayi a kanta. Sai da na ƙare mata kallon tsaf kafin na ce"lafiya kuwa".
"Lafiya amma ba ƙalau ba kiyi sallan dai muyi magana".


Ban iya bata amsa da baka ba sai gyaɗa mata kaina da nayi na shinfiɗa sallaya tare da fuskantan alƙibla na tada sallan, ina raka'an ƙarshe Umma ta shigo fitowar ta kenan daga wanka da ta ce dani na kai mata ruwa. Sai da na gama addu'o'ina na shafa na ninke sallayan kafin na dawo kusa da Anty Zakiyya na zaune, zanyi magana Umma ta tari numfashi da faɗin"je ki ƙira min Abdul-majid" miƙewa nayi na fita na nufi ɗakinsa muka yi kiciɓus dashi yana dawowa daga masallaci tare da Nurain sanar dashi saƙon Umma nayi muka juyo tare izuwa ɗakinta.
Sai da muka zauna kafin Umma ta soma cewa"magana nake so muyi akan wannan yaron na tabbatar kin ji komai izuwa yanzu, ina son ki fara neman zaɓin Allah kafin ki yanke ko wani irin hukunci sannan tun jiya Hajiya ta ce bata son zancen ya fita ya tsaya a iya tsakanin mu don haka bakinku ya zama ƙanin ƙafarku".
Da kalmar to suka amsa mata yayin da ni kuma suka bar ni da aikin rarraba idanu ina bin su da kallo ɗaya bayan ɗaya, haka Umma ta cigaba da zancen da na gaza gane tushinsa balle gindinsa da ido kawai nake bin su sai da gama tsaf kana na ce"Umma kun sa ni a cikin duhu wani magana ne wannan?".


Bata amsa mini ba sai yaya Majid ne ya ce dani"Saifuddeen ne Saifuddeen ne ya zo neman auren Zakiyyaa". Wani irin sufa nayi a taku ɗaya ya kawo ni kan kujeran

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login