Showing 81001 words to 84000 words out of 171161 words
Chapter 28 - MATAN AREWA BOOK TWO COMPLETE PDF .txt
zai ji sausacin raɗaɗin da yake ji. Shurun nasan bai sanya ta dakatawa daga ɗaurawa da faɗin"tabbas jinyar iyaye yana da matuƙar ciwo ga zuƙantan ƴaƴansu mussamman idan ƴaƴan sun haifu kamar ka, amma shi duk wanda ya rungumi haƙuri to ya rungumi gagarumar nasarar da ba zai taɓa faɗuwa ƙasa banzan ba. Na fara tinanin ko maganin gida zamu koma yi mata da nema mata taimakon malaman addini".
Jin shurun nasan ya yi yawa ya sanya ta furta kalmar sunansa"Saifuddeen kana jina kuwa?".
Nan shuru bai amsa mata ba kamar yanda bai ko motsa daga inda yake zaune ba, nunfashin da yake sauƙewa a hankali ne ya tsaya da hakan ya sanya ta kiɗimewa sosai. Ta zame daga kan kujerar da take tare da isowa gabansa tana ƙara ƙiran sunansa nan ma bai amsa ba ruwan da aka kawo masa ya sha ya bari ta ɗauka ta watsa masa a fuska.
Sai da ta ƙara watsa masa sannan ya saki dogon ajiyar zuciya yana dafe kansa da yake jin yana sara masa tamkar zai rabe izuwa gida biyu tsabar sarawan da yake yi masa.
"Saifuddeen".
Idanunsa suna a lumshe ya yi ƙarfin amsa mata yana ƙoƙarin ɓoye damuwar da ta bayyana ƙara-ƙara akan fuskarsa. Cikin sanyin murya ta furta"me yasa kake wasa da lafiyarka?, me yasa me yasa Saifuddeen?, me yasa baka tinanin mutanen da suke kewaye kusa da kai?".
Cije leɓɓansa ya yi da matuƙar ƙarfi har yanzun idanunsa suna lumshe ya ce"ina da damuwa ina da damuwa mai tarin yawa a cikin zuciyana jinyar Ummi ya tsaya min a rai na rasa yanda zanyi ga matsalata ga na wajen aiki ga kuma rashin samun aikin Farouk duk ƙoƙarin da nake yi a kai sai komai ya fara ƙulluwa kamar hanyar zata ɓolle sai kuma komai ya wargaje na rasa yanda zanyi da raina na rasa inda zan sanya kaina naji daɗi a rayuwa".
Ƙwalla ce ta ciko masa idanu taf sai dai ya ƙi basu damar tsiyaya domin baya iya basu wannan damar face yana gaban Umminsa. Cikin sanyin murya da hawayen da suka fara wanke mata fuska ta ce"wataran sai labari in sha Allah zanyi magana a wani malami zai taimaka mana kan jinyar ta tan da yardan Allah".
Sai a sannan ya buɗe idanunsa ya yi ƙasa dasu yana faɗin"ba san da wasu kalmomi zanyi amfani dasu wajen gode miki ba, sai dai kawai na dawwama ina miki addu'ar gamawa da duniya lafiya".
"Amin amin kar kaji komai yiwa kaine".
Sai da ya jawo numfashi ya fesar sannan ya sama zarafin cewa "tunda nazo ban ga ƙannena ba ko basa nan ne?"
Ita ma numfashin ta saka kana ta ce" Suna makaranta amma Saifuddeen kana lafiya kuwa ko asibiti zamu je".
Cikin aro jarumta ya yafawa kansa ya ce"I'm ok fa". Ba don ta yarda ba ta barshi tana ɗan jan sa da hira lokaci zuwa lokaci tare da ƙara nusar dashi muhimmancin haƙuri da nasarar dake cikinta.
Bai bar gidan ba sai da yaran suka dawo daga makaranta duk suka kanainaye shi, sosai ya sake mush fuska tare da tattara dukkan damuwarsa ya ajiye su gefe guda sai da ya yi sallan juma'a cikin garin na kano kana ya soma haramar komawa duk yanda suka zo ya zauna zuwa gobe ya tafi ƙi yawa ya yi saboda alƙawarin da ya yi wa Farouk akan yau komai dare zai dawo.
Dab da magrib ya isa duk gajiyar da yake ji a jikinsa da jin alamun motsawar ciwonsa bai hana shi nufar asibitin ba gano Umminsa kamar kullum sai da ya fara zuwa ofishi likita babu abinda ya sauya zani daga furcin da yake labarta masa kullum yau ma dai babu wani cigaba. Cikin sanyin jiki ya fito ya isa ɗakin da take Farouk kawai ya iske yana waya don haka kansa tsaye ya isa gabanta ya tsuguna tare da riƙo hannayenta yana murzawa a hankali tare da tsura mata idano, vai ɗauke idonsa ba har Farouk ɗin ya gama wayar ya iso ya same shi. Sannu da zuwa ya yi masa ya ɗaga masa kansa kawai. Sai ƙarfe sha ɗaya suka baro cikin asibitin suka nufi gida.
Durƙushe take akan gwiwoyinta jikinta gabaɗaya yana rawa, tana sauraron zazzafan faɗar na Anty Binta da take yi tamkar zata yi aron baki. Cikin rawar jiki da na murya ta ce"kiyi haƙuri Anty nima bai sanar dani tafiya tasan ba, sai a ranar da zai yi ta kuma ya sa ni nayi masa alƙawarin cewar ba zan faɗawa kowa ya ce shi da kansa zai ƙira ku ya sanar daku hukuncin da ya yanke da yake ganin shine dai-dai gare s...". Tsawar da ta daka mata ta sanya ta haɗiye ragowar zancen dake bakinta ba tare da ta furzo su ba.
"Dalla rufa min baki munafukar banza munafukar wofi ai daman na daɗe da sanin cewar duk abinda Yusuf yake aikawata kina sane kuma ke ce mai ƙara ingiza shi yin wani abun. To wallahi ahir ɗinki hawainiyarki ta kiyayi ramata an daɗe da yin walƙiya na ganki na kuma gane mungun nufinki akan ƴan-uwana, kun haɗa baki ya tafi can wata uwa duniya daban to wallahi daga ke har shi zaku ga fushina za kuma ku fuskancin hukuncina mai tsauri hatta Na'imar da ta zamto silar faruwa komai sai ta gwanmace ƙida da karatu daga ita har iyayenta, sai sunyi da na sanin abunda suka aikata sai sunyi nadamar sani na a rayuwarsu balle haɗa zuri'a da jinina.
MATAN AREWA
(Book two)
© Maimuna Tijjani Iyam
_________________________________
Page 7⃣9⃣
Shuru tayi mata wasu hawayen suna ɓulɓulowa daga idaniyata suna wanke mata fuska yayin da wani irin abu yake tokare mata ƙirji, da dama da tunin ta miƙe ta maida mata da maganganun da take yaɓa mata ba tare da tinanin komai ba sai dai kash babu wannan damar domin tana da yaƙinin ko ɗan yatsa ta nuna mata a bisa kuskure hakan yana dai-dai da bakin aurenta da bata fatan faruwar wani abun a wannan lokacin. Ko don cigaban ɗaurewar kwanciyan hankali da lafiyar mahaifiyarta da take kwance.
"Ko hawayen jini za kiyi Habiba sai na faɗa miki gaskiya sai kuma kin fuskanci hukuncina, domin na fahimci take-takenki so kike ki raba min kam ƴan-uwa to wallahi ahir ɗin ki".
Fitowar yaya Auwal daga banɗakin da ya shiga wanka kamar an jefo shi, ya sanya Anty Bintan kai kallonta izuwa gare shi tana gyara tsayiwar da tayi kan ƙafafunta. Da sarsarfa ya iso wajen tare da rusunawa ya gaishe ta bata amsa ba illa tsakin da ta doka tana taɓe baki ta ce"Auwal kayi wa matarka kashedi ta tsaya iya matsayinta na matarka da take zaman cin arziki a cikin gidan nan, kar ta nuna zaƙewar da zai zamto silar kawo ƙarshen aurenku".
"Lafiya Anty meya kuma faruwa kuma?".
"Ga matarka nan ka tambaye ta tasan komai kuma ita ta kimtsa komai, da haɗin bakinta Yusuf ya zartar da hukuncin ƙaurace mana ya sanya ƙafa ya shure umarnin da na gindaya masa ya yi tafiyarsa. Yanzu zuwa na gidan nan naji ta da kunnuwana suna waya da shi Yusuf ɗin da na titsiyata ta faɗa min wai ita ma sai sanda zai tafi yake sanar da ita don salon ƙwarewa a makirci".
Ƙaruwar ajiyar zuciya yaya Auwal ya sauƙe yana satan kallon Maman Hanan da tun ɗazun kanta yana ƙasa kamar yanda ruwan hawayen basu bar gudana akan dandamalin tudun fuskarta ba. A sanyaye ya furta"Anty kiyi haƙuri ban san da wannan zancen amma ina mai ba ki haƙuri a madadinta Allah ya huci zuciyarki".
Wani tsakin mai dogon zango ta kuma tsirtarwa haɗi da faɗin"yanzu za'a bani wajen zama ne ko kuma matsayina bai kai ba?".
A tare suka miƙe suna rige-rigen shimfiɗa mata tabarma ta zauna tana watsawa Maman Hanan wani kallo kafin ta ce"sai ki tashi ki bamu waje ko, zan yi sirri da ɗan-uwana an zauna an kasa kunnune da son jin ƙwaƙwaf".
Miƙewa Maman Hanan tayi idanunta cike taf da wasu sabbin hawayen, da wani suna ya dace ta ƙira wannan ƙaddararren auren da babu komai a cikinsa face ƙunci, baƙin ciki da kuma tarin damuwa faɗawa ɗaki tayi tare da rufo ƙofar ta cigaba da kukan da ba zai amfane ta da komai illa ƙara mata girman damuwar dake ƙirjinta.
Musgutawa tayi har yanzun idanunta akan yaya Auwal da yake durƙushe a gabanta cikin tsantsar biyayyar da ya sanya ta jin daɗi a cikin ranta, ba ta fatan zuwan koda yini ɗaya ne da ƴan-uwan natan zasu bijire mata ko kuma daina yi mata biyayya shiyasa take tsaye akan ƙafatar da dukkan dabaru koda zata hauce hanyar addini hakan bai dame ta ba matuƙar buƙatarta zata biya ta zaɓi duniya sama da inganta lahirarta. Yusuf ne kawai mai kawo mata cikas a cikin dukkan lamuranta.
"Daman nazo ne naji dalilin ƙauracewa zuwa inda nake da kayi kwana biyu, sannan na sanar da kai cewar iyayen Safwan zasu turo nema masa auren Husna".
"Aiyuka ne suka yi min yawa a kasuwa shiyasa bana samun lokaci, maganar Safwan kuma ai Anty mun gama ta tare da ke nayi wa Husna da yaron nan tsakani amma akan idonki take bujirewa wannan umarnin nawan duk binciken da zan yi akan yaron nan nayi shi kuma ya nuna cewar ba yaron kirki bane har shaye-shaye an tabbatar min da cewae yana yi, kuma ba ɗan garin nan bane asalinsa gidan wan mahaifiyarsa yake zaune a nan garin. Domin gujewa da na sani da nadamar da bata da amfani a gaba ni dai a gani na kawai gwara ta haƙura da yaron nan tayi haƙuri har izuwa lokacin da Allah zai fito mata da wani mijin tayi aurenta tunda naga hakan kika fi yi mata sha'awa".
Harara ta banka masa kafin ta ce"ban gane mutumin banza bane Auwal?, shikenan don mutunen da basu wuce biyu ba sun baka shaida akan yaro sai ka ɗauka ka hau ka zauna. Bayan kasan duk wani wanda Allah ya rufawa asiri a cikin al'ummanmu sai ya sama mahassada da masu bin sa da bin ta ƙulli to wallahi auren Husna da Safwan tabatacce ne matuƙar ina numfashi a bayan ƙasa kuma ko mutuwa nayi shine abu na farko da nake son ku fara aiwatar min bayan biya min bashin dake kaina, ban da ubanta mai gadon tsiya da talauci ma har zan tuntuɓe ka ne akan wannan batun".
Cikin sanyin muryar dake bayyanar da tsantsar ladabi da biyayyarsa gare ta ya soma faɗin"shikenan Anty Allah ya sanya alkhairi Allah kuma ya kawo su lafiya, daman ina som nayi miki magana akan wani zancen da naji yana tashi a cikin unguwa har wajen sana'ata aka biyo ni aka faɗa min, game da zaman da kike yi a gidan Baban su Husna bayan kowa ya san da cewar kun rabu dashi rabuwar da aure ya haramta a gare ku har sai kin ƙara wani auren kafin ki koma gare shi. Tun Husna na zanin goyo kuka rabu amma hakan bai sanya ki bar cikin gidansa ba shima kuma hakan bai hana sa zuwa cikin gidan lokaci zuwa lokaci ba tun wancan lokacin nida Yusuf mun zaunar da ke tare da nusar dake illar hakan da haramcinsa a addinance amma kika yi kunnen uwar shegu da zantukan mu sai ma ce mana kika yi wai ya mallaka miki gidan tun kafin rabuwarku. Dan Allah Anty Binta ki taimake mu kar kija mana wani abin faɗa a cikin gari yanda kike shirin aurar da ƴa ya kamata ita ma ki kankaro mata mutunci da daraja a idanun wanda zata auran da kuma danginsa gabaɗaya ta hanyar kame kanki".
Salati ta saka tare da sallallami haɗi da tafa hannayenta"na shiga uku Auwal yau ni kake kallon tsabar idona kake faɗa min waɗannan kalmana?".
"Anty ki fahimci ni ba wai ina son...".
Katse sa tayi ta hanyar faɗin"ba abinda na buƙata ba kenan Auwal, yau da kai za'a haɗa baki a tona min asiri a idon duniya ko meye?, in banda munafurcin banza da wofi da shiga harkan bayin Allah irin na mutane meye ruwansu da rayuwarta balle yanda nake gudanar da ita ya tsole musu ido. Yanzu da kake wannan maganar idan na fita daga gidan nan ina kake so na haɗa kayana na tafi? ko so kake yi na dawo cikin gidanka na tare matarka da bata da ta ido ta ƙarisa raina ni sauran ɗan mutuncina da ya rage a idanunta shima ya ɓare. Iyayenmu duk su rasu babu wasu ƴan-uwan da suka rage mana daga mu sai junanmu duk abinda nake yi domin inganta rayuwar gobenku ne da kuma sauƙe amanar ku da Baffa ya damƙa min a hannuna zamana cikin gidan nan shine rufin asirina da naku gabaɗaya hasalima gida nawa ne domin ko a takardun gidan sunan ƴaƴana ne a kai ba na Hashimu ba don haka zama daram daram mai naƙuda ta sama katifa".
"Allah ya huci zuciyarki ba nufi na kenan na ɓata miki rai ba".
"Ba komai Auwal in ma da wata manufar ka faɗa to don kanka, Allah ya jinƙan Baffa na tabbata da yana raye ba ka isa ka kalla idanuna ka furta min makamamcin maganar nan ba".
Cikin sheshsheƙar kukan makirci ta ƙare zancen tana fece majinar da ta zo mata da gefen zaninta, tare da miƙewa ta fice daga cikin gidan duk magiya da kalaman ban haƙurin da yake jeranta mata wani na bin wani bai sanya ta dakatawa ba balle tsayawa sauraronta haka ta fice daga cikin gidan. Jallabiyarsa kawai ya shiga ɗaki ya ɗauka ya saka ya fice ba tare da ya kai dubansa ga Maman Hanan ba balle ya ce da ita wani abun ya fice a matuƙar hanzarce.
Yau da ta kasance monday tun da muka yi sallan asubahi bamu komar da haƙarƙarinmu da sunan kwanciya ba, tun shida da rabi muka gama shirinmu muka fice muna ƙara duba handout ɗin Mr Suleiman da mukeda gwajinsa yau tsabar sanin luggan mungunta tun kafin takwas ta cika ya iso wajen ya kuma ce duk wanda yazo bayan shigowarsa ba zai rubuta gwajin ba balle ma ya shiga cikin hall ɗin.
Printing tambayoyin gwajin ya yi ya raba wa kowa bayan ya wawwatsa mu mutum bibiyu a benci ɗaya ga wani uban tazaran dake tsakani.
Mintuna ashiri ya bada a amsa tambayoyin goma sha biyu, goma objective ragowar biyun kuma essay ina na ƙarshe ya wafce fefarsa wai lokaci ya yi. Haka muka fito muna tausayin waɗanda basu sama damar shiga ba da suka tsilli-tsilli da ido cikin rashin sanin abinda ya dace su yi domin kuɓuta daga gare shi. Har wani sati ya zagayo kowa baya cikin kwanciyar hankali, burin kowa yaga sakamakon abinda ya yi a gwajin har sallan dare muke yi da kai kukan mu ga Allah akan ya kwace mu daga hannunsa don yanda ƴan gabanmu suke kambama rashin mutuncinsa, rashin ɗaga ƙafa, da kuma muguntar kaɗai ya isa ya tsurar da mutum ga kuwa tulin masu carry over ɗin course ɗinsa da suke shigowa.
Tsif hall ɗin yake tun kafin ya shigo kowa da tinanin da yake yi cikin ransa da kuma irin saƙa da warwaran da yake yi, ganin shigowar motarsa ya ƙara sanya mutane da yawa shan jinin jikinsu a bakin hall ɗin ya yi parking, sai da ya ɗauki wasu mintoti sannan ya buɗe ya fito ya shigo hall ɗin. Lecuture ya fara yi sannan daga ƙarshe ya zaro scripts ɗin daga jakansa da kansa yake ƙira kuma ya faɗi score ɗinka tare da ruguzin baƙar magana mai ɗaci a zuciya. Sanda aka ƙira sunana bugun ƙirjina ya daɗa tsananta a ɗaɗare na miƙe na karɓa sai da ya ƙare mini kallon tsaf kafin ya miƙa mini yana kawar da kai ya ce"she score 81/2 over 10".
Sai a sannan na saki wata sakakkiyar ajiyar zuciya, sai da aka ƙira mutane biyu sannan aka ƙira Nawwara score nata 8 cif-cif. Har ya gama tsaf bamu ji ya ƙira sunan Nazifa ba sai ma cewa da ya yi duk wanda bai ji sunansa ba ya same shi a ofishinsa waɗanda basu yi gwajin ba kuwa ruwan su domin shi ba ya yi make-up test.
A tare ƙirjinmu ya bada sautin ɗas ɗas kamar yanda idanunmu suka sarƙafe cikim na juna kowacce na maimata zancen zuwa ofishin nasan a cikin ranta.
MATAN AREWA
(Book two)
© Maimunah Tijjani Iyam
____________________________________
Page 8⃣0⃣
Yana dasa aya anan ya fice daga cikin hall ɗin ya barmu bakunan mu a buɗe hangal kamar sokaye, kallon Nazifa da tayi shuru kamar dasasshen dutsi ta gaza motsi balle wani maganar hannunta na riƙe gam na ce"kar ki damu tashi muje kinji kar kiji komai".
Kamar abun da mayan ƙarfe yake jansa haka kawai take bi na, Nawwara na rufa mana baya ɗauke da jakakkunanmu a hannunta muka fice daga cikin hall ɗin.
"Ƴar baƙa ta Mr Suleiman wataƙil ta fi kowa ci ne shiyasa ya ce dole sai taje ofishinsa zai bata".
Furcin wasu samari uku da suma suka fito daga cikin hall ɗin kenan da suka yiwa ƙofofin kunnuwar mu sauƙar angulu daga sama. Cak Nawwara da bata raina ruwan shuka fahimtar mayar musu da martani take da burin yi ya sa ni riƙo hannunta itama ina jijjiga mata kai.
Ina iya jiyo ƙwafan da tayi muka bar wajen duk da muna da lecture amma sai da muka biya ta hostel Nazifa ta ɗan dawo hayyacinta sannan muka kuma fitowa tafiya lectures ɗin.
Duk ƙwarewar lecture ɗin hakan bai sanya ni fahimtar komai da aka yi mana ranar ba, wani tsoro na mussamman yana ƙara yi mini lulluɓi mussamman na tino lokacin da muke ƙaramar makarantar sakandiri yaya Majid yana matakin ƙarshe a FCE da wani abokinsa ya kawo masa ziyara naje kai mishi ruwa sha nake jin suna zantawa akan lamarin karatunsu cikin hirar na tsinci wata zancen da ya zauna mini daram-daram a cikin kwanyata tamkar rubutun da aka yi shi a bayan dutsi mai wahalan gogewa.
"Ai Majid kai dai kawai kayi addu'a Allah ya raba ka da malaman FCE lafiya, domin wallahi duk halinsu guda ne ɗan juma ne da ɗan