Showing 39001 words to 42000 words out of 171161 words
Chapter 14 - MATAN AREWA BOOK TWO COMPLETE PDF .txt
zai damen balle ya ɗaga min hankali". Furcin Baba ƙarami kenan cike da bata tabbacin cewar zai iya aikata abinda ya faɗi ɗin domin babu wasa a tattare da furcin nasan.
Goggo Suwaiba ta ce"ni Yaya idan zaka bani izni ma zan ɗauki Zakiyya na tafi da ita wajena tunda yanzu babu kowa a gabana duk na aurar dasu, sai muyi zaman mu har izuwa lokacin da ita ma Allah zai fito mata da miji".
"Hakan ya yi Allah ya yi miki albarka kuma naji daɗin hakan matuƙar dai ba za ki ɗaurawa mijinki wani nauyin ba".
Hajiya Babba ta amsa mata a maimakon su Abba, Goggo Suwaiba ta tabbatar mata da cewar babu matsala daga gare shi. Gyaran murya Abba ya yi kafin ya soma faɗin"sai kuma magana ta biyu akan Na'ima da kuma halin da take a ciki, mun zauna tare da ƴan uwana da kuma Hajiya mun yanke shawarar cewar zata koma makaranta kafin muga abinda da Allah zai yi game da lamarin".
MATAN AREWA
(Book two)
© Maimunah Tijjani Iyam
___________________________________
Page 5⃣5⃣
Kallon kallo aka shiga yi daga wancen ya kalli na kusa dashi sai wannan ya kallo wancen, bakunan su cire fal da maganganu sai dai babu fuskar da zasu furzo shi waje domin sam Abba bai bada damar yin hakan ba tamau ya ɗaure kammalayyiyar fuskarsa da furfura suka fara mamaye saje da gashin bakin dake fuskar nasan.
"Alhamdulillahi wannan tinanin dashi nake kwana nake tashi dashi cikin raina, yanzu babu abinda zai gyara rayuwar yarinyar nan illa komawar makarantar ta tunda ta samu ta kammala babbar sakandiri saɓanin sauran ƴan uwanta da basu yi ba, kawai sai ta tafi makarantar ko ta rabu da wannan damuwar da take ciki tun bayan faruwar wannan lamari, tunda Allah ya yi ikonsa cikin dake cikinta bai zauna ba sai kuma a duƙufa wajen ganin rayuwarta ta gyaru".
Furcin Goggo Jummai kenan da suka sanya Umman Balkisu furzo da zantukan dake cin ranta cike da ɓacin rai ba ma tare da ta san da tana furto su ba domin idanunta sun rufe, a harsale take cewar"haba goggon yara wannan ai ba adalci bane, tunda ba Na'ima bace kaɗai ɗiya a cikin gidan nan bai kamata a bata damar da aka hana sa ga kowa ba. Ko nan Bahijja kafin auran ta taso cigaba da karatu amma aka katse mata shi ta hanyar yi mata aure, sai yanzu ita kuma da yake ƴar gwal ce za'a lamince mata zuwa ƙarin karatu har izuwa matakin da babu wani ɗan da ya taɓa zuwa a tsakanin ƴaƴan dangin nan. Ko nan Majid iyakar sa matakin NCE shi da yake namiji ma kenan kuma babba a tsakanin su to ina ga ita da take ɗiya mace kuma bazawara mai ƙarancin shekaru gaskiya da sake cikin wannan zancen".
A kufule ta ƙare zancen tana wani hucin ɓacin ran dake ba wa mai sauraronta tabbacin cewar ɓacin rai ya makantar da ita ya kuma kurmantar da ita yayin da ta rasa ji da ganinta na wucen gadi.
"Ke Hauwa'u ki san inda kike kuma ki san da waɗanda kike magana, abinda kunnuwanki suka jiye miki tabbas shine hukuncin da muka zartar a tsakanin mu kuma babu wanda zai hana hakan faruwa ko dakatar dashi sai Allah".
Baba ya yi maganar idanunsa ƙar kan Umman Balkisu da har yanzun bata bar huci ba, ni dai sam na gaza yi wani ƙwaƙwƙwaran motsi balle na cira kai na kalli su Abba har na kai ga samun zarafin furta musu abinda yake cikin bakina. A hankali wasu siraran hawaye suka shiga zirarowa daga jemammen kurmin idaniyata ina jin bugawan da zuciyata take yi a raunane kuma a hankali sosai da hakan yake bayyanar da bata aikinta yanda ya kamata, nasan daman dole hakan zata faru a duk lokacin da aka taso da wanga zancen sai dai ban yi tinanin za'a yi shi a nan kusa ba kamar yanda ko a cikin mafarki ban taɓa kawowa cikin raina cewar wai su Abba zasu lamince mini na ɗaura da karatu na ba duba da tarihin gidan mu da babu wacce ta taɓa wuce matakin ƙaramar sakandiri a fannin karatun boko illa yaya Majid da yake da kwalin NCE yake kuma aikin koyarwa, nima darajar aure ne ya bani damar kammala babbar sakandirin fannin karatu addini kam alhamdulillahi domin ba'a aurar da yarinyar sai ta haɗa sittin cif a kanta.
Sautin muryar Baba da nayi sa ɗarau a masarrafan jina su suka dawo dani izuwa duniya zahiri daga katarun wasiƙar jakin da nake yi.
"Bamu bambamta Na'ima da raguwar ƴaƴan ba, domin dukkanin su ɗaya suke a wajen mu kuma babu wanda yafi kuwa duk dai-dai suke. Ita ta kammala babbar sakandiri saɓanin sauran da basu yi don haka dole ita ce zata je jami'a kafin su ba zamu tauye su a wannan fannin ba domin muma yanzu mun sama haske tare da fita daga duhun kan da muke dashi akan karatun ɗiya mace, ta sanadiyar fahimtar da mu da Majid ya yi don haka cikin su duk wacce take da sha'awar cigaba da karatunta bayan ta kammala wanda take yi a yanzu to mu bamu da matsala da wannan, haka nan kuwa duk wacce take ganin aure zata yi to muna maraba dashi sai ta fito da miji a aura mata shi idan ya cire sharruɗan da addinin islama ya gindaya yayin bada aure. Waɗanda suke ɗakunan mazajen su kuma waɗannan bamu sa iko a kansu don haka sai su tuntuɓi mazajen su idan sun amince musu to falillahil hamdu".
Tsawon ɗaƙiƙa biyu babu wanda ya tanka sai Ammi autar ɗakin su Ikilima ta furta"Baba nima ina son na ɗaura da karatu idan na gama wanda nake yi yanzu".
"To alhamdulillah in sha Allah za ki yi sai kuma waye yake da wannan burin bayan ita?".
Tsif wajen babu wani wanda ya ce wani abu ganin hakan ya sanya Baba ɗaurawa da faɗin"to alhamdulillahi iya adalci dai kenan a tsakanin ku mun kwatanta mun kuma baku dama ga duk wacce take da sha'awar karatu ta fito ta furta, amma naga kamar bayan Ammi babu wata mai irin wannan burin. Don haka mun gama magana Na'ima makaranta zata koma in sha Allahu, amma kafin nan ke Zakiyya fa? ban ji kinji komai ba shin kema za ki koma makaranta ko kuma akwai wani tanadin da kika yiwa rayuwar goben kin?".
"Baba makaranta kam yanzu lokacinta ya wuce gare ni, su dai ƙannen mu su yi Allah ya sanya musu albarka a ciki ya kuma basu sa'a. Amma nikam a'a".
A wannan sa'ilin Hajiya Babba ce ta amshe zancen da faɗin"ai shi karatu baga yaro kawai yake ba bakya jin ana faɗin cewar a harkan neman ilmi ba'a girma kuma ba'a tsufa. Ko ni nan tsofai-tsofai dani idan ina so zan iya komawa makaranta na zauna a cikin aji malami yazo ya koyar dani". Cikin sigar zolaya da son sauya yanayin mutane da yawa zuwa na annashuwa Hajiya Babba ta ƙare zancenta na ƙarshen, sai dai haƙarta bata cimma ruwa ba domin ko tafi babu wanda ya yi balle akai ga murmusawa. Jan jikina nayi kaɗan na iso gaban su Abba cike da tsantsan girmamawa ɗauke a cikin laffuzan da suke fita daga bakina cikin hawayen da har yanzu basu bar fareti saman kuncina ba nake faɗin"na gode na gode Allah ya saka muku da mafificin sakayyarsa, haƙiƙa duk inda ake neman iyayen na gari sun wuce waje sun cika iyayen da ko wani ɗa ba ƙwarai zai yi bugun ƙirji ya yi alfahari da fitowarsa daga tsatson su. Yanda muka yi ƙoƙarin samar mini da farin ciki ina roƙon Allah ya samar muku da kwatankwacin sa ranar alƙiyama".
Kalmar amin amin amin ce take fitowa daga bakunan su Abba, Hajiya Babba, Goggo Jummai, goggo Suwaiba, Umma, Anty Zakiyya da kuma yaya Majid sai wasu tsirari daga cikin ƴan uwana babu ƙauƙatawa. Kafin su Abba su haɗe mu gabaɗaya cikin jimla guda su sanya mana albarka tare da yi mana nasiha mai ratsa jini da jijiya.
Miƙewa da yawa daga cikin matan gidan suka fara yi ƴaƴansu suna rufa musu baya tun kafin a rufe taron suna fice, daga kan su Abba har Hajiya Babba babu wanda ya yi yunƙurin dakatar dasu. Illa ma goggo Jummai da ke jan Anty Zakiyya da zolayar cewar ta zamo ƴar nguru da ƙarawa da cewar zata ci kifi har ta ture don sosai Allah ya albarci garin da yalwan kifi.
Bamu bar falon ba har sai da su Abba suka tabbatar mini da cewar yaya Majid zai yi mini komai na komawartawan makaranta kama daga kan ciro mini sakamako da dai sauran su. Godiya ba shiga ƙara yi musu su Umma suna taya ni ina jin tamkar na tashi naje na rungumo su na sanya a jikina tare da sakin kukan murnar da na gaza samun sikelin da zan auna adadin farin cikin da nake ciki a wannan lokacin. Allah ya sani tun bayar rabuwar mu da yaya Yusuf bab ƙara sintar kaina cikin farin-ciki, annashuwa, walwala da murna kamar wanda nake ciki a yanzu ba koda muka koma sashin mu ana ƙiran sallan magrib Hajiya na fara iskewa a tsakar gida tana tuƙa tuwo cike da fara'a take ƙara taya ni murna da addu'o'in alkhairi fuskata a washe nake amsawa da amin kafin Salma da Abasiyya da suka fito tare daga ɗakin mu suma suka ƙara yi mini haka nan ma Hanifa da Asma'u da ko wacce take ƙunshe da cikinta da aka yi auren su lokacin muna tsaka da rubuta jarabawar jamb suka yi mini fatan alkhairi. Alwala nayi na wuce ɗakin mu na gabatar da sallan magrib ban tashi daga kan sallayan ba har aka yi ƙiran isha'i nayi. Su Asma'u suka yi mini sallama domin duk mazajen su sun zo ɗaukar su na musu fatan saura lafiya sai dai tun bayan fitowata daga sashin su Abba banga da yawa daga jama'ar gidan namun ba ban damu ba balle na mayar da hankalina akan hakan illa ma tashi da nayi na nufi ɗakin Ummata tana bisa sallaya na iske ta tana wuridi na yiwa kaina mazauni kusa da ita har ta iddar da addu'ar muka shafa tare kafin ta kallo sosai sannan ta ce"Na'ima ina son muyi wata magana dake".
Gyara zamana nayi ina mata dukkan hankalina dana tattara gare ta na ce"to Umma wacce magana ce?".
"Ina son ki sanar dani gaskiya shin ke kika sama iyayenku maza da zancen kina son komawa makaranta?, ko kuwa Hajiya Babba kika tunkara da batun ina son sani".
Musgutawa nayi haɗi da cewar"wallahi Umma cikin su babu wanda na tunkara game da zancen komawa ta makaranta, hasali ma ni tun bayar rabuwar mu da yaya Yusuf na yanke ƙauna ga cigaba da karatu ban san wanda ya gaya musu ba".
Shuru tayi da hakan yafi kama da nazari tare da tantance maganganun nawan kana ta sauƙe numfashi ta ce"shikenan to daman ni magana ce bana so irin ta gidan nan, nasan za'a yi ta cecekuce akan komawar ki makarantar nan sai dai ki toshe kunnuwanki ki ji ki ƙi ji ki gani ki ƙi gani Allah ya dafa muku ba ki ɗaya ya shiga cikin lamarin ku".
"Amin".
Na amsa dashi a sanyaye kafin na waiga ɗakin na ce"ina Anty Zakiyya fa?, amma dai ba yau bazu wuce ngurun ba don naga dare tayi?".
"Tana sashin Hajiya Babba, ai goggon nakun ma zata kwana biyu kafin ta tafi".
Kaina na jinjina muka cigaba da hirar mu tare muka ci abincin dare kafin na duba magungunan Anty Zakiyya naga bata sha su na ɗauka na bita sashin Hajiya Babbab dasu cak na tsaya sakamakon maganganun da iska suka ɗebo daga ɗakin Umman Balkisu suka juye shi a kunnuwana jikina ya ɗauki mazari.
"Ai dai mu gani idan tusa zata hura wuta, ba dai boko ba to in sha Allah dasu har Hajiya Babban da take ɗaure musu gindi suke yanke duk wani hukuncin bisa son ransu ba tare da ta tsawatar musu sai sun yi kuka da idanun lokacin da zata jajiɓo musu wani abin kunyar a dalilin bokon da suka tura ta".
MATAN AREWA
(Book two)
© Maimunah Tijjani Iyam
__________________________________
Page 5⃣6⃣
Sosai kalaman suka daki kwakwalwata kwatankwacin yanda maƙeri yake dukan ƙarfe tare da munana ƙalbina, jikina ya ƙara yin sanyi ƙalau kamar kazar da aka jefa da ruwan gishiri zuciyata tana hawa da sauƙe kwatankwacin yanda kayan masarufi yake hawa da sauƙa a kasuwannin ƙasata najeriya. Kunnuwana sun gaza tantance mini aihinin wanda ya yi zancen amma tabbas daga ɗakin Umman Balkisu ya fito a wahale na sauƙe numfashi ina ɗaga ƙafata da kyar na fice daga cikin sashin izuwa na Hajiya Babba sai da na tsaya na saisaita nutsuwata ta hanyar jawo numfashina na fesar da ƙarfi kana na kutsa kai cikin falon Hajiya Babba da tun kafin na shiga nake jiyo tashin hirar da su goggo Jummai suke yi.
Kusa da Goggo Suwaiba na zauna ina miƙawa Anty Zakiyya ledar magungunan ta, kwaɓe fuska tayi da alamar ba zata sha ba sai da Hajiya Babba ta karɓa da kanta ta bata sannan tasha. Mun ɗan taɓa hira har su Abba suka shigo yiwa Hajiya a kwana lafiya kamar yanda suka saba yi a kowacce dare, tare da Hajiya Babba muka kwanava ɗakinta goggo Jummai da goggo Suwaiba suka kwan a falo.
Ƙurawa rufin ɗakin kallo nayi duk da baƙin duhun daren da ya gaurayen dukkan wani kusurwan ɗakin, zantukan ɗazu suna yi mini amsa kuwa a masarrafun jina a hankali na furzar da zazzafan iska mai ɗumi daga bakina ina yiwa zancen tankaɗe da tairaya a cikin kwanyata.
Shin wai da gaske ne duk wacce taje jami'a shikenan ta zama lalacacciya kenan?, kamar yanda kunnuwana suka jiyo mini zancen da ya fito daga ɗakin Umman Balkisu da ta haɗe kafatanin ƴan matan tayi musu kuɗin goro, tagwayen ajiyan numfashi na saka ina gyara ƙwanciyata da nake jin duk muƙamuƙaina suna yi mini ciwo dai-dai sa'ilin da wayata da take silent a ƙasan matashin da na ɗaura kaina ta fara vibration sai ya kusa kintsewa na jawo ta don bana tsammanin ƙiran kowa musamman a wannan lokacin da dare ya tsala.
Turus nayi ganin baƙuwar lamba ce hakan ya sani ƙura mata ido har ta gama ta katse aka ƙara ƙira a karo na biyu shima ban ɗauka ba sai dai har yanzun ban kawar da idona daga kan fuskar wayar ba. Sai da aka jera ƙiran har sau huɗu ba tare da na ɗauka ba a karo na biyar ɗin naji ƙaran shigowar saƙo.
Kamar bazan buɗe ba sai kuma na buɗe zumbur na tashi na zauna tamkar wacce aka tsikarawa matsilli ina ƙara watsa idona akan fuskar wayar don tabbatar da ingancin lafiyar idanuna da tinanin ko sune basu gano mini saƙon dai-dai ba.
- _Dan Allah ki ɗaga wayar nan Na'ima, ko daƙiƙa biyar ne ki bani daga cikin lokacinki muyi magana Yusuf ne-_
Da sauri sauri ƙirjina yake bugawa duk wani farin ciki da annashuwan da nake a cikinsa naji gabaɗaya sun kau yayin baƙin ciki da ƙunci suka maye gurbin su, tunin naji ƙwalla sun ciko mini kurmin idaniyata haka nan kawai na sinci kaina da mayar masa da amsa kamar haka.
_Yusuf dan girman Allah ka rabu da ni ka rabu dani ka barni na huta, ka bar ni nayi rayuwa cikin salama shin meyasa ba zaka ɗauki ƙaddarar da ta faɗa mana ba?.
Ina gama turawa na komar da kaina bisa matashin na kwanta tare da lumshe idanuna da hakan ya ba wa ƙwallar da suka wadaci kurmin idaniyata damar tsiyaya.
Jin ƙaran shigowar saƙon cikin wayata ya sani saurin buɗe idona ina dubawa.
_"Ba zan iya ba Na'ima wallahi ba zan iya ba, naso ace ina da iko akan zuciyata ta yanda zan iya tanƙwarata har na sanya ta yakice abinda take so dan Allah ki saurare ni". _
Ban iya mayar masa da amsa ba illa gudun famfaƙin da hawayen da suke wanke mini fuska da suka ƙaru, na damƙe wayar gam a hannuna ina mai cigaba da tsiyayar da hawaye a lokacin ƙiransa ya kuma shigowa cikin wayan wani irin bugu ƙirjina yake yi tamkar zai ɓalle allon ƙirjina ya faso waje ya daka ruwan disko.
Gani kawai nayi hannuna ya aiwatar da abinda bai yi shawara da zuciyata ba wajen aiwatar dashi, domin ji muryar yaya Yusuf nayi sun daki ƙofofin kunnuwana da sai a lokacin na farga da cewar na ɗaga ƙiran nasan. Kamar wanda yasan abinda nake shirin yi a gaugauce ya ce dani"dan Allah kar ki kashe wayar dan girman Allah Na'ima ki saurare ni kiji abinda zan faɗa miki ba don ni ba".
A raunane ya ƙare zancen nashin na ƙarshe tamkar mai shirin fashewa da kuka da hakan ya ƙara tarwatsa mini hargitsatstsiyar zuciyata da take gab da tarwatsewa. Maganar da ya kuma yi suka sanya ni runtse idona da matuƙar ina jin sautin muryarsa suna ratsawa har cikin kwanyata.
"Dan Allah Na'ima na roƙe ki kina jina?".
Sai da nayi namijin ƙoƙari wajen danne kukanmai ƙarfin da yake ƙoƙarin kufce mini kafin na sama zarafin cewa"dan Allah Yusuf na gama ka da darajan iyayenka da suke kwance a cikin ƙasa ka rabu dani ka kyale rayuwata haka nan domin ka azabtar dani matuƙa ka tausayi mini, muyi haƙuri da juna mana mu ɗauki ƙaddara kasan fa wannan wayar da muke yi bai halalta a tare mu tunda babu sauran igiyoyin aure a tsakanin mu. Ina son na roƙe ka don girman Allah kar ka ƙara bibiyata ka rabu da dani hakan nan na gaji da damuwarka Yusuf ka kyale ni na fuskanci sabuwar rayuwata da nake ƙoƙarin ginawa".
Shuru ya ɗanyi mini har ina ƙoƙarin zame wayar a kunnena da zummar kashe ta sai a sa'ilin nan naji ya katse ni ta hanyar faɗin"zan barki Na'ima amma sai na tabbatar da cewar na gano bakin ƙullin abubuwan da suka faru a tsakanin mu, wallahi ki yarda dani ban san yanda komai ya faruwa ba ban sa yanda na