Showing 57001 words to 60000 words out of 171161 words
Chapter 20 - MATAN AREWA BOOK TWO COMPLETE PDF .txt
Amma Ummanta ta ƙi yarda da hakan ta ce daga nan kotu zata huce".
Sai da na tallafo kuncina sannan na ce"Allah sarki gaskiya na tausayawa Hanifa daga haihuwa kuma ga wannan ƙalubalen, amma Ummanta ma fa tana da gaskiya gwara ayiwa tufkan hanci tun yanzu don da zafi zafi ake dukan ƙarfe".
"Haka ne amma lamarin yana buƙatar a bishi a tsanake kuma a kwantar da hankali".
"To Allah ya kyauta in sha Allah zuwa gobe ma gaisa da Hanifan".
Da haka muka cigaba da hiranmu sosai kafin muka yi sallama bayan na gama loda mata saƙon gaisuwana ga Salma da tunda na tafi bamu yi waya da ita ba.
MATAN AREWA
(Book two)
© Maimuanh Tijjani Iyam
_____________________________________
Page 6⃣5⃣
Ya daɗe yana tsaye akan ƙafafunsa da suka yi masa sanyi ƙalau, kafin ya fara sulalewa ƙasa a hankali ya durƙushe kan gwiwoyinsa yana sauƙe numfashi da ƙyar da yake jin zuciyarsa tamkar an sanya masa ƙatoton dutsi. Lumshe idanunsa ya yi yana cire leɓɓansa tare da karanto dukkan addu'ar da ta fara ziyartar kwanyarsa a wannan lokacin.
Zuciyarsa da take tafasa take ƙara bashi tabbacin cewar wannan shawarar da ya zarta shine dai-dai kuma maslaha ɗaya tal da zai dai-daita rayuwarsa da ta gama tarwatsewa tsawon watannin bakwai kenan abubuwan da suka fara sun kasa barinsa balle har ya koma kamar da ya shima kansa yasan cewar hakan ba mai yiyuwa bane, shiyasa ya yanke hukuncin da yake tinanin zai fishsheshi.
Zumbur ya miƙe kamar wanda aka watsawa ruwan sanyi, yana cigaba da shirya kayansa a cikin akwati kaf ya kwashe kayansa fiye da rabi domin baya jin wannan tafiyar da zai yi zai dawo nan kusa har zai ya kwakwalwarsa ta mance da komai sannan ya waigo. Sai da ya gama ya faɗa banɗakin dake cikin ɗakin ya yi wanka ya fito ya shiga shigar manyan kaya ya yi kamar ko yaushe farar yadi ne tas haka nan ya bar kansa ba tare da ya sanya hula ba bai wani ɗau lokaci ba ya gama ya fito riƙe da akwatinsa.
Maman Hanan ce kaɗai a tsakar gidan ta haɗa kai da gwiwa da alamar tayi niso cikin tafkin tunanin da take niyo a cikinsa, kallo ɗaya ya yi mata ya kawar da kansa kafin ya tako ya iso gabanta tsugunawa ya yi kan ƙafafunsa akwatin na gefensa ba tare da ya kalle ta ba ya furta"Anty lafiya kuwa?".
Sai a lokacin ta dawo hayyacinta tare da ƙirƙiran murmushi da ya tsaya iya kan leɓɓanta ta ce"lafiya ƙalau ina zaka ta fito da akwati haka niƙi-niƙi?".
"Zan miki bayani amma fara amsa min tambayar tawan tukunna".
"Yusuf babu komai kawai bana jin daɗin jikina ne".
Ta faɗa cikin muryarta da ta fara rawa tana tino abinda da ya wakana tsakanin su da yaya Auwal a daren jiya. Ta gaza gano inda bakin zaren yake balle har tayi masa kyakykyawan ƙullin da ba zai kuma warwarewa ba. Maganar da ya soma yi ya dawo da ita cikin ainihin hankalinta.
"Karki yi ƙoƙarin ɓoye abinda fuskarki ta riga ta nuna, akwai matsala menene?".
A kaushashe ya yi maganar yana matsa yatsun hannunsa da ƙarfin tsiya, yasan akwai matsala kawai ƙoƙarin ɓoye masa take yi sai dai fuskarta ta daɗe da bayyanar da rufaffen sirrin dake zuciyarta. Sai da ta sauƙe tagwayen ajiyar zuciya kana ta furta" abinda dai ka riga ka sani ne Yusuf shine har yanzu babu abinda ya sauya zani, na kasa gane meye faruwa idan so nane Auwal baya yi gwara ya sauwaƙe min na huta da wannan azabartawar da yake yi min ta hanyar take haƙƙina da addinin ya ɗaura masa".
Wani irin ƙullin baƙin-ciki ne ya kuma zarge masa ƙahon kogon ransa, cak yawun bakinsa ya tsaya tamkar rijiyar da ruwan cikinta ya kafe ƙas. Yana ƙara matse yatsun hannunsa kamar ba wani sassan jikinsa yake yiwa hakan ba sai da ya jawo numfashinsa da ƙarfi ya fesar kafin ya samu zarafin cewa"na san kina haƙuri a cikin zaman aurenku da yaya Auwal, kasancewarsa ɗan uwana ba zai sa na take gaskiya bayan ina ganinta bayyananniya a zahiri ba. Kinyi matuƙar haƙuri, juriya da kuma kauda kai ga al'amura da yawa kuma har yanzu kina kan yi sai dai duk wanda ya rungumi haƙuri baya taɓa faɗuwa ƙasa banza sai ya tarar da ribarta a gaab ko mai daren daɗewa. Shawaran da zan ba ki ta ƙara dagewa da addu'a sannan ki sanar da iyaye da ƴan-uwanki koda wani taimakon sai a nema miki shima kuma in sha Allah zamu zauna dashi muyi maganar duk da wannan bashi bane karon farko da muke tattauna da shi akan hakan".
Tunda ya fara maganar tayi ƙasa da kanta har ya kai aya bata ɗago ba, da hakan ya bashi tabbacin cewar kukan zuci take yi mai tsananin ƙuna gami da raɗaɗi, wani iriyar kifiyar tausayinta ne ya caki ƙalbinsa shi kansa abin yana matuƙar ci masa tuwo a ƙwarya amma babu yanda ya iya yasha zama da yaya Auwal ɗin akan lamarin su tattauna ya kuma tabbatar masa da cewar lafiya garas yake kawai shi sha'awar hakan ne bai da ita. Duk kuwa yanda zai so fahimtar dashi cewar haƙƙinta ne wannan ɗin da Allah ya rataya masa a wuyarsa da zai tuhume shi game da hakan ranar sakamako akan yanda ya tafiyar da rayuwar auren ba wai ra'ayin kansa bane kunnuwansa sun kurumce.
Ganin har yanzu bata kuma cewa dashi wani abu ya sanya shi faɗin"dukkanin damuwa maganinta Allah kuma duk wani abunda ya yi zafi ga bawa to tasirin addu'a yana iya sausata shi kiyi haƙuri wataran sai labari". Kanta ta ɗaga masa kafin ba haɗiye wani kuka mai ƙarfin dake shirin kubce mata tayi jarumtar faɗin"ina zaka je Yusuf ka fito da kaya haka?".
Gigitacciyar ajiyar zuciya mai sauti ya sauƙe tare da raba yatsun hannunsa da tun ɗazu ya matse su waje guda ya furta"tafiya zanyi tafiya zanyi waje mai nisa da ba zan dawo da wuri ba sai lokacin da Allah ya nufa dawowata".
"Tafiya mai nisa?, ina zaka je kuma meye dalilin tafiyar?".
A jere ta watsa masa dukka tambayoyin ba tare da bashi damar da zai fara amsa ta farkon ba balle ya dira ga ta biyu, sai da ya shafo gefen fuskarsa sannan ya soma faɗin"tafiya zanyi Anty zanje can inda zan samu nutsuwar da na rasa a nan, zan je inda hankalina zai kwanta koda kuwa na wuce gadi nena dai ji sauƙi cikin raina kona daƙiƙa ɗaya shine burina".
Daga haka ya tsagaita sai da ya furzar da zazzafan iska mai ɗumi daga bakinsa kafin ya ɗaura da"na rasa komai nawa tunda na rasa maginjinar da zan jingina naji daɗin rayuwata, na rasa Na'ima rasawar da nake ji har abada ba zan kuma mallakarta a matsayin da na same ta a baya ba. Gwara nayi nisa da garin ko zan sama salama tunda bani da wani hanyar da zan iya koda nemar yafiyarta ne hukuma ta shiga tsakaninmu da ita ban da ikon taka inda take zan tafi zan tafi kawai".
Yanda ya ƙare zancen a raunane ga ƙwallar da ta ciko masa kurmin idaniya shi ya fi ƙaryarwa Maman Hanan zuciya tabbas yana cikin wani irin halin da ba zai fasaltu cikin kalmomin da baki kan iya furtawa ba addu'a kawai shine abinda yafi buƙata a halin yanzu fiye da komai.
Sai da ta kai bayan hannunsa ta tare hawayen da suke ƙoƙarin zubo mata kafin ta ce"Yusuf yanzu ka gama faɗin duk abinda ya yi zafi maganinsa Allah, ka cigaba da addu'a Allah ya yi maka zaɓi mafi zamowa alkhairi a gare ka ya kuma baka mace ta gari da zata mantar da kai Na'ima ta samar maka da farin-ciki marar yankewa ta kuma silar fitarka daga halin ƙuncin da kake ciki in sha Allahu komai zai wuce duk abinda ya yi farko ai ƙarshen sa yana nan zuwa ko ba dare ko ba jima Yusuf. Amma nikam a shawarce da ka haƙura da wannan tafiyar kayi zamanka ga kuma aikinka shi kuma yaya zaka yi dashi kenan".
Ɓoyayyan ajiyar zuciya ya sauƙe yana ƙara jinjina zancen na Maman Hanan a cikin ransa domin yasan haka ɗin ne, sai da ya ɗan musguta akan ƙafafunsa da yake tsugune kafin ya ce"haka ne nima yanzu babu abinda nake da burin ganin face a waye gari na mance da komai, komai ya wuce kamar bai taɓa faruwa ba sai dai tafiyar tawa shine mafita a gare ni sannan karatu zan ƙara don na sama gurb..." .
Tun kafin ya ƙarisa Maman Hanan tayi saurin taran numfashinsa da faɗin"karatu Yusuf ka rufa mana asiri in ce dai ba bin ta makaranta zaka yi bayan anyi muku tsakani".
"Ba nufi na ba kenan Anty, karatun dai da na faɗa miki shi zai kai ni kuma na ma canja ba jami'ar da nake tunanin zata je bane wannan wani ne daban. Addu'arki kawai nake bara sannan babu wanda yasan da tafiya daga yaya Auwal har Anty Bintan kuma bana ma so su sani sai bayan na tafi".
Ƙuri tayi masa da ido tana bin sa da kallo tamkar ba da hausa ya yi mata zancen ba, sai da tayi nisa kafin ta ce"ina zaka sama kuɗin ɗauƙar nauyin kanka da na karatun a can ɗin bayan ba wani aiki zaka yi a can ɗin ba?".
"Albashina zai cigaba da shiga asusuna duk ƙarshen wata, domin makarantar ma na sanar musu zan je ƙarin karatu ne don haka a ƙa'ida albashina ba zai yanke ba zai ishe ni nayi komai don nayi rejista ma a makarantar".
"Bazan ce kar kaje ba tunda kana ganin hakan shine mafita a gare ka, sai dai ina jiyewa kaina tsoron abinda kan je ya dawo musamman ta wajen Anty Binta idan tasan da cewar nasan da wannan tafiyar nakan".
Cikin salon kwantar mata da hankali ya ce"kar kiji komai in sha Allah ba zama ta sani ba sai na isa zan ƙira na faɗa mata". Ba don ta yarda da zantukan nasan ba kawai ta gyaɗa masa kai tare da yi masa fatan alkhairi da addu'ar Allah ya kai shi inda zashi lafiya ya kuma bashi sa'an karatun da zai fara. Karatu muke yi babu kama hannun yaro tare da mayar da hankali yayin darasi da kuma bitar duk abinda aka yi mana kafin mu kwanta bacci, yayin da matuƙar shaƙuwa da ƙaunar juna ke ƙara girmama tsakaninmu da Nawwara da Nazifa a cikin kwana goman da muka yi tare su Abba duk sun sansu haka nan ma Nawwara ƴan-uwanta kaf muna gaisawa dasu da kuma Nazifa bamu da wata matsala. Haka nan ma munyi ɗan sabo da mutane da yawa a hostel da kuma department ɗin mu, duk inda ka hangi ɗaya to dole ka ga sauran mu zamto tamkar wata ne da zara, hanta da jina ko kuma ince harshe da haƙori ƙarshen shaƙuwa. Bama shiga shirgin kowa haka nan duk wanda ya shiga namu bama yi masa da wasa, don duk sakin fuska da faran-faran ɗin Nawwara tana da matuƙar zafi idan aka taɓo ta ko kuma aka taɓo ɗaya daga cikin mu, nida Nazifa munfi kama ta ɓangaren halayya domin ita ma akwai sanyin hali matuƙar gaske, bamu yarda da wani abokanta da namiji ba balle har wani sabo ya shiga tsakaninmu rayuwarmu muke yi dai-dai ruwa dai-dai tsaki.
MATAN AREWA
(Book two)
© Maimunah Tijjani Iyam
________________________________________
Page 6⃣6⃣
Yau ta kasance monday muna da lecture ɗin mr Suleiman tunda muka yi sallan asuhabi bamu koma ba muke ta hada hadan ficewa lecture, amma Nazifa tana nan kwance ba tare da ta ko motsa ba balle yunƙurin faɗawa wanka har ta shiga. Ina zuba mana abincin da Nawwara ta girka mana a plate na kallon ta a nutse kafin na furta"Nazifa ba za ki tashi ki shirya bane lokaci fa ya yi, kuma kinsan in muka yi late ba zai bar mu mu shiga ba".
Siririyar tsaki ta saka kafin ta gyara kwanciyar haɗi da faɗin"ba zan je ba ni". A tare muka ware idanunmu akan ta cike da son ƙarin bayani Nawwara ta ce"ke ban gane ba za ki je ba, ba ki da lafiya ne ko meye?".
"Lafiyata ƙalau kawai bazan je bane don bazan ɗauka wannan cin mutuncin nasan ba".
"Meye kuma haka?, har akan wannan dalilin kice ba za ki je ba dalla ki tashi muje kar ki ƙara cewa komai bana son ji kuma ban nema ba".
Na furta ina ajiye plate ɗin da na shaƙe mana da dafa dukan taliyar yara, kafin na fizgo hannunta ta tashi tsaye tunin Nawwara ta kai mata ruwa ta wuce tayo wankan kafin ta dawo muka gyare ɗakinmu fes don mun sama wannan yabon daga bakunan mutane da yawa mazauna hostel ɗin cewar ba ɗakin da ya kai namun kasancewa kullum cikin tsaf da kwalliya duk da kuwa bamu wani ɗau lokaci a hostel ɗin ba, bama barin koda wanke-wanke ne ya kwana balle wani ƙazantar muna amfani da abu zamu tsaftace shi mu maida shi gurbinsa.
Nazifa na fitowa muka tsaya ta shirya sannan muka ci abincin a gaugauce saboda lokaci ya ƙarato, muka rufe ɗakin muka tafi turus muka yi ganin Mr Suleiman har ya shiga wani wawan fargaba ya ɗarsar mana muka damƙe hannuwan junan mu gam ni ce nayi ƙarfin halin furta"excuse us sir can we come?".
Cak ya tsaya da yin lectures ɗin da yake yi cikin tsare gida kamar satin da ya gabata fuskarsa nan babu walwala ko kaɗan ya watso mana idanunsa da ya sanya mu rusunar da namu ƙwayayen ƙasa ya tako har bakin ƙofar tare da ƙarfe mana tanadin kallo tsaf kafin kaukauran muryarsa suka doki na'uran jiyo mana sautuka.
"From where are you? what is your time now?".
Duk shuru muka yi na tsawon daƙiƙu kafin nayi ƙarfin halin kuma faɗin"Sir we're sorry".
Bai amsa mana ba har sai da muka cire rai ga samun amsarsa sannan ya ce damu"go back to where you come from i don't tolerance nonsence".
"We're sorry sir".
Tsawan da ya daka mana ya sanya jikkunan mu gabaɗaya ɗaukar rawa tamkar mazari don na wasa ya yi mana ba, a zafafe ya soma cewar"ke ce maganaɗisu ko uwar magana?, su ɗin kurame ne da ba zasu bayar da haƙurin ba sai dai ke gwanar na iya. Will you shut up your mouth or i will deal with you over there".
Miɗik na cinye dukkan raguwar zantukan da suke cikin bakina har ya gama masifarsa kamar zai yi aron baki cikin mu babu wanda ya yi gigin ƙara faɗin komai balle yunƙurin bashi haƙuri. Awa biyu zai yi don haka ya ce mu jira sai ya yi awa ɗaya sannan mu shiga.
Hakan bai dame mu ba don buƙatarmu dai shine shiga lecture ɗin ko wannan halin nasan ma bai sace mana gwiwa ba balle har mu zuciya mu tafi kamar yanda da yawa suke yi idan suka zo late aka hana su shiga suke tafiya. Muna nan tsaye a waje har ya yi awa ɗaya ya ce mu shiga duk idanuwa suka dawo kanmu kafin aka kwashe da wata mahaukaciyar dariya bai hana su ba balle ya dakatar dasu sai ma ɗauke kansa da ya yi kamar bai ji su ba.
Zama muka yi muka fito da abin rubutunmu muka kwafan abinda ya rubuta akan board da aka yi babu mu, muryarsa ta hatse mana hanzari.
"Hey Black pot what is your name?".
Cikinmu babu wanda ya ɗago kansa balle ya amsa tambayar tasan da hakan ya ƙara fusata shi aihin kamar zai kai mana bugu ya nufo mu gadan-gadan haɗi da cewar"Hey you am talking to you".
"Sir my name is Nazifa not black pot".
Cire leɓɓansa ya yi bai ce komai ba ya juya ya cigaba da lectures ɗinsa muka yi attendance sannan ya ce next week zai bada group assigment class rep ɗinmu ya yi grouping ɗinmu into five group of students. Next lecture muka nufa muna gaba wasu da suke bayan mu suna ta jinjina baƙin halin mr Suleiman da kukan rashin iya lecture ɗin da bai iya ba, shima awa biyu muka yi sai lecturer ɗin da yazo last week bashi yazo yau ba. Ba ƙaɗan ba muka fahimta domin sosai ya iya koma akwai daɗi course ɗin a gajiye muka fito duk munyi wugiga wugiga kai tsaye muka wuce hostel duk muka zube akan katifa muna mayar da numfashi sai da muka huta kafin muka watsa ruwa muka yi salla sannan muka cika tumbinmu muka fara shirin komawa. Tun a hanya muka jin wasu ƴan 200 hundren level suna ta yabon lectures ɗin da zai ɗauke mu course ɗin, biyu saura mintuna biyar yazo duk idanu suka koma kansa domin ba yanda muka yi zato muka ganshi ba.
Tunda muka shigo kaina yake ga wayata da jiya Nawwara ta seta mini whatsapp ina bibiyar chart ɗin da muka yi da yaya Majid da na ce masa ya turo mini wancan vidoe ɗin wayarsa na ƴan jaridun bbc hausa ɗin nan. Ƙananun maganar da suke tashi da kuma kalmar wow, masha Allah, Alhamdulillah ya karaɗe cikin hall ɗin ya sa ni ɗago kaina tare da kai duba na ga lecturer dake tsaye yana ciro wasu takardu daga cikin jakar da ya shigo da ita goye a bayansa.
Matashi ne mai ƙarancin shekarun da ba zasu haura ashirin da bakwai ba yana da matuƙar tsayi sosai don a dogayen maza za'a saka shi a lambar farko. Bashi da jiki sosai sai dai yana hasken fata aihun bamu yi mutuwar tsaye ba sai da sautin muryarsa mai zaƙi suka yiwa ƙofofin kunnuwoyi sallama.
"Good afternoon ladies and gentle men, i am the one going to take the you the course history of nigerian mass media which is MAC 102".
Ƴan matan da suke ta bin sa da kallo ne yafi komai bani haushi da ɗura mini tulin takaicin da ya turniƙe mini raina, ciki-ciki na tsirkar da tsaki ina mayar da idona ga wayata na kashe datar na fara ciro alƙalami da takardan da zanyi jotting daga cikin jakata. Sai da na taɓo Nawwara da ita ma