Showing 159001 words to 162000 words out of 171161 words
Chapter 54 - MATAN AREWA BOOK TWO COMPLETE PDF .txt
akan abinda yake gabansa, bashi da yawan shiga cikin jama'a domin a lokuta mafi yawa yafi son kaɗaita kansa ko lokacin da yake yi musu darasi ne.
Yana matuƙar girmama shi a matsayinsa na malaminsa duk da a shekaru sai dai su kara da juna, hakan ya sanya shi shima sakin jiki dashi sosai mussamman da ya ƙara fahimtar yanda ilmin zamanin da yake yi bai sanya shi ginjine na addininsa ba kamar yanda mafi yawa samarin yanzu suke yi, tare da tinanin sun wuce zuwa neman ilmin addini. Har wasu littattafan yake kai masa har ofishinsa da hakan suka ƙara yin sabo ko lokacin aurensa ya ƙira shi a waya tare da yi masa fatan alkhairi.
Da tinanin ya kwana a ransa tare da ƙudurin zama da Yusuf ɗin domin ji ta bakinsa, kwana biyu ya jefa masu kyau yana ƙiran layinsa amma baya ɗauka daga ƙarshe ma idan ya ƙira sai yaji ta a kashe, sannan baya zuwa lecture.
Ranar lecture ɗin ƙarfe goma muke dashi don haka yaya Saif ya ce na jira shi mu fita tare, shima ƙarfe goman sai shiga. Tsaf na gama shirina cikin dogon hijabi zuwan zuma ina zaune a falo ina waya da Ummata da wayar Anty Zakiyya.
Farouk ya fito cikin shigar zuwan aikin da ya fara zuwa ina gidan. Hankalina gabaɗaya yana ga wayar da nake yi da Umma take ƙara sanar dani akan sanin da nayi cewar saura kwana goma Baba ya cika kwanaki arba'in da barin duniya. Jikina a sanyaye ina ganin suffarshi cikin murmushi a idona na ce"Allah ya jiƙan Baba ya masa rahama ya kyautata makwancinsa".
"Amin ya Allah".
Umma ta amsa dashi cike da jimami, kamar daga sama naji an ƙara amsawa da amin nayi saurin ɗago kaina naga Farouk ne ya amsa da yake zaune a kujerar da yake fuskanto ni yana sanya safa a ƙafarsa. Sai da muka yi sallama da Umma kana na gaishe ya amsa yana ɗaurawa da"nifa duk ɓacin autanci da mutane suke faɗin ina dashi ke kin dama ni kin shanye yarinyar nan".
Wani kallo na watsa masa kafin na ce"ni ɗin har wani ɓacin auta nake dashi?, impact ma ni ba auta ba ce don ƙannena sun fi ɗari goma".
Sai da ya dara ya ce"da wa da wa sai muji labari". Lissafo masa su nayi tas ya ce"duk da haka dai bai hana ki ɗebo ɓacin auta ba". Harara na wurga masa zan yi magana fitowar yaya Saif da Anty Zakiyya ya dakatar dani, a jere suka iso cikin falon na bi ta da kallon sha'awa don ba kaɗan ba suka yi kyau, dacewa da juna da kuma burgewa. Sunkuyar da kaina nayi ina ƙara girmama lamarin sarkin da duk yanda ya tsara hakan ne zai faru babu wanda ya isa ya canja. Yau Anty Zakiyya ce cikin gidan aure da mijinta ikon Allah kenan da ba'a cire rai daga rahamarsa.
Gaishe su muka yi suka amsa mana a tare kafin yaya Saif ɗin ya kallo Farouk ya ce"me kake yi har yanzu baka tafi ba Umar?". Ɗan shagwaɓe fuska ya yi yana shafo ƙeyarsa ya ce"Ummi nake jira daman ta tashi ta sha magani da asuba har yanzu bata tashi ba".
Sai da ya yi nisa kafin ya ce"amma ka san ba yanzu zata tashi ba ko?, meyasa kake son fara wasa da aikinka tun kafin ayi nisa?. Ka dai san aikin company daban yake in kaga dama ka mayar da hankali in baka ga dama ba kuma kayi son ranka".
"Zan gyara in sha Allah amma yaya Saif kuma sai ka dunga yi min faɗa akan yara da girmana salon su ka ja min raini".
Ware idonsa ya yi"wasu waye yaran a nan?".
"Na'ima mana ai sai ta raina ni". Ya faɗa yana nuna ni da ɗan yatsarsa, tsaki yaya Saifuddeen ɗin ya saka yayin da Anty Zakiyya ta tuntsire da dariya. Gabaɗaya haushi suka bani don haka ko kalma guda ban ce dasu ba, har suka je ɗakin Ummi suka fito muka fito haraban gidan ban ce ƙala ba sai ma ƙara ɗaure fuskana da nayi.
Har bakin hall ɗin da zamu yi lectures ɗin ya kai ni da zan fita ya bani kuɗin abin hawa ya ce in mun gama na koma gida, godiya na masa na fice ina jin makarantar wani irin don har yanzu Nawwara da Nazifa basu dawo ba. A hankali yake tafiya kansa a ƙasa kamar mai neman wanj abun, kamar an ce ɗaga kanka yana ɗagowa idanunsa suka sauƙa akan Yusuf da yake zaune akan rest bench gefe kaɗan. Da sauri ya isa wajen tare da taɓo kafaɗarsa idanunsu suka sarƙe cikin na juna.
"Yusuf".
Bai amsa ba illa duƙar da kansa da ya yi, hannunsa ya kamo tare da miƙar dashi muka bar wajen ofishinsa ya buɗe suka shiga suka zauna. Shuru duk suka yi babu wanda ya yi magana sai can Yaya Saifuddeen ɗin ya fara faɗin"Yusuf meyasa ranar baka sanar dani abinda ya faru ba?".
"Wani abu kenan malam?". Cire leɓɓansa ya yi"stop it Yusuf kar ka nuna min baka kamar baka gane abinda nake nufi ba". Kwashe duk labarin da Anty Zakiyya ta sanar dasu ya yi ya gaya masa. Ƙarƙarfan ajiyar zuciya mai sauti ya sauƙe tare da dafe goshinsa saboda matsanancin sarawan da yake jin kansa yana masa.
"Meye Na'ima ta aikata maka da kayi mata saki uku a lokaci guda Yusuf?".
"Ban saki Na'ima ba har yanzun ita matata ce".
Wani kallo ya jefa masa cike da rashin fahimta ya ce"ka dawo hankalinka domin a labarin da Zakiyya ta sanar dani a rubuce ka rubuta mata sakin kuma baka taɓa musantawa ba sai yanzun".
Numfashi ya sauƙe yana janye hannunsa daga saman goshinsa tare da ɗaura idanunsa a bisa fuskar yaya Saifuddeen ɗin"ina cikin hankalina kuma duk abinda zan sanar da kai yanzu to wallahi ina cikin hayyacina ba hauka nake yi ba, sannan kwakwalkwata lafiya take saɓanin kallon da mutane suke yi min na zautacce tun bayan rabuwa na da Na'ima. Malam zan sanar da kai abunda yake sirrin da na alkinta a cikin zuciyata, zan sanar da kai abunda ban taɓa sanar da wani mahaluƙi ba, zan sanar da kai wani sirrin da ya daɗe a cikin zuciyata, zan sanar da kai damuwata zan sanar da kai ciwon dake damun zuciyata. Zan sanar da kai ɓoyayyan sirrin da ko ɗan-uwana da muka fito ciki ɗaya dasu ban taɓa gigin sanar da su ba saboda kai kaɗai naji zuciyata ta nutsu da ta fallasa maka sirrin dake cikinta".
Sai da ya numfasa ya ɗaura da"ban saki Na'ima ba har yanzun ita matata ce shiyasa na kasa daina bibiyarta, shiyasa zuciyata ta kasa nutsuwa ta kuma kasa haƙurin rashin ta a kusa dani. Na rantse maka har da girman zatin Allah da na san na saki Na'ima kuma babu igiyoyin aurena a kanta, da na ba wa zuciyata haƙurin rashinta da na mance da ita da na sama ƙwarin gwiwan cigaba da fuskantar rayuwarta. Da na samu kwanciyar hankali na kuma rungumi ƙaddarar da ta gilma tsakaninmu da hannu bibiyu".
"Ta ya ya zata kasance matarka ta ya ya Yusuf?, bayan duk duniya kallon ba matarka suke yi maka ba hatta ita kanta da iyayenta".
Murmushi ya saka mai ciwo da raɗaɗi a cikin zuciya tare da musgutawa ya ce"tabbas kowa kallon hakan yake yi, na san kasan hukuncin matsayin sakin da aka tirsasa mutum ya yi shi a addinance ko?". Izuwa yanzu kam kallon ya raina masa wayo yake yi masa sai da ya gama nazartan yanayin fuskarsa ya ce"ƙwarai na sani amma kai waya tirsasa ka?".
Shuru ya biyo bayan zancensa na ƙarshe sai daƙiƙu suka shuɗe kafin ya furta"yayata wacce nake wa kallon uwa da uba a gare ni, wacce nake kallo a matsayin dukkanin wanj gatana a nan gidan duniya. Ita ta zamto silar rugurguza ginin farin-cikin da na daɗe ina tsarawa rayuwata, mun kasance masu yi mata biyayya akan komai na rayuwa bama taɓa ƙetare umarninta akan mu, ko da kusa ya saɓawa son ranmu domin amanar mu iyayenmi suka damƙa a gare ta tare da yi mana umarni da muyi mata biyayya dai-dai gwargwadon iyawarmu, kar mu taɓa barin ta yi kuka damu. Bata barin kowa ya raɓe mu domin indai a kan ƙaunar da take yi mana ne to bata yarda da kowa ba, a kanmu aurenta yasha mutuwa. Ita take juya lamuran gidanmu gabaɗaya tun kafin na auri Na'ima yayanta ya sanar dani ƙudirinta akan son komawa makaranta na kuma yi alƙawarin cewar ban bata wannan damar, daga lokacin muka fara samun matsala da Anty Binta domin ta fito fili ta fayyace abinda yake ranta na cewar bata amince ba ganin abinda zan yi bai saɓawa mahaliccina ba ya sani tsayiwa tsayin daka har sai da na tabbatar da Na'ima ta sama gurbin kararu a makarantar da nake koyarwa. Tun daga lokacin Anty Binta ta ɗauki karan tsana ta ɗaurawa Na'ima da tinanin cewar ita ta sanj dole akan sai ta koma makaranta har na bijirewa umarninta, Na'ima ta rayu a cikin gidana tare da bayyanannan tsanar Anty Binta a gare ta wanda ko bata taɓa buɗar baki ta furta min ba na fahimce komai. Lokaci guda hakan nan naji na gaji da zama da ita, bana ƙaunar ganinta balle jin sautin muryarta na ƙaurace mata a shinfiɗa na daina harkanta. A wani dare Anty Binta ta ƙira ta zaunar dani tare da ajiye min takarda da biro ta ce dani na rubutawa Na'ima saki uku, ban yi musu da ita ba balle jin dalilinta na son na aiwatar da hakan nan take na rubuta sakin ta kuma umarci akan a daren na bata takardan sakin ba sai na jira wayewar safiya ba. Yanda ta ce dani hakan nayi duk wanda zai tambaye ni dalilin sakin bana iya bashi wani gamshashshen hujja. Bayan wani lokaci da rabuwar mu da kunnuwana naji Anty Binta tana waya da malamin da ya yi mata aiki a kaina har na rubutawa Na'ima takardan saki cikin gushewar hankali. Nayi kuka lokaci kuka mai tsanani tare da nadamar abinda na aikawata, naji na tsani komai na duniyar na kuma tsani kaina da kowa naji bana ƙaunar ganin ta amma hakan bai hane ni yi mata nasiha ba da nuna mata irin illar da tayi wa zuciyata. Gabaɗaya zaman garin ya fice min a ka wannan dalilin ya sanya na nema gurbin karatu nazo nan, duk da na tabbatar da igiyoyin auren akan Na'ima amma na tabbatar na rasa ta kenan domin nasha yunƙurin ganawa da ita ko kuma wani makusancinta amma bana samun wannan damar. A idanunta ina kallon tarin tsanar da tayi min da kuma fusatan da danginta suka yi a kaina, ta ina zan fara warware wannan ƙullin malam?, waye zai yarda da dani balle fahimtar raunin da nake rayuwa dashi a cikin ƙirjina?".
Sakakken ajiyar zuci Yaya Saifuddeen ya sauƙe yana janye idanunsa daga kallon fuskarsa da yake yi duk sa'ilin da ya fara zancen, wani irin tausayinsa ne ya kama masa zuciya da kuma salon yanda ƙaddara take walagigi da rayuwarsa. Wani numfashi ya kuma sauƙe a karo na biyu muryarsa cike da tausayawa ya ce"haƙiƙa kana cin wani yanayin da ba ko ne zai fahimta ba, amma shurun da kayi kan lamarin zai iya lalata komai ya kuma ɗarsar da shakku akan duk abinda zaka furta. Tabbas akwai igiyoyin aurenka akan Na'ima domin malamai masana ilmin warware hukunce-hukuncen sakin aure sun yi fashin baki game da hakan. Wani daga sharuddan da saki ba
ya inganta sai da shi, shi ne nufi wato
wanda zai yi sakin ya zama ya ƙudurta
cewa wannan kalma da yake furtawa ta
saki yana nufin aiwatar da saki ne da
ita, don haka mutumin da ya saki
matarsa a halin yana maye ko kuma ba
da niyyar yin saki ba to sakin bai yi ba.
Kamar yanda wanda ya furta saki
a sakamakon takura da dole da aka yi
masa, nan ma sakin dai-dai yake da
sakin mahaukaci wato ya bi ruwa.
Wadannan su ne wasu daga cikin
muhimman sharuddan da sai sun cika
kafin saki ya inganta. Wannan bayanin yazo cikin
littattafan da suka yi bayani kan
hukunce hukuncen aure da saki a
mazhabar Ahlul Baiti (A.S.). Yusuf kana som matarka har yanzu har cikin ranka da dukkan gaskiyarka?".
Sai da ya kai hannunsa ya tare ƙwallan da suke shirin ɓalle masa kafin ya ɗago kansa tare da zube idanunsa a kansa, ya bayyana abinda yake zuciyarta cikin kalmomin baki"ina son Na'ima ina son Na'ima ina sonta har cikin raina, domin babu abinda ya canja matsayinta a cikin ƙirjina sai ma ƙaruwan da ya yi".
Tashi yaya Saifuddeen ya yi daga mazauninsa ya dawo kujerar dake fuskantar Yusuf, sai da ya sausauta amon muryarsa ya ce"nayi maka alƙawarin in sha Allah zan tsaya maka har sai matarka ta dawo gare ka, duk na san zaka fuskanci ƙalubale domi kai ma kayi kuskure shurun da kayi ka bar abin a ranka ba tare da ka sanar da kowa ba. Inda ƙaddara ta sanya a tsakanin wannan lokacin ta yi wani auren kaga ta anyi aure kan aure kenan cikin rashin sani".
Kansa kawai ya jinjina masa don zuciyarsa wani irin zafi take yi masa aihun, baya buƙar sai an faɗa masa domin shima kansa ya san ya aikata babban kuskure sai dai dole ne ya sanya shi aikata haka ba bisa dom ransa ba. Rarrashinsa ya cigaba da yi tare da bashi tabbacin cewar in sha Allah matarsa zata koma gare shi.
Muna gama lectures ɗin na hau adaidaita na koma gida, sai yamma sosai yaya Saif ya dawo duk muna zaune a falo ya shigo lokaci har Farouk ma ya dawo daga aiki. Duk sannu da zuwa muka yi masa ya asma yana zama kusa da Ummi tare da tambayarta yaya jiki?, fuskarta ɗauke da murmushi ta amsa da alhamdulillah.
Sai da muka ci abinci sannan kowa ya je ya kwanta, duk yanda suka yi da yaya Yusuf wani irin kuka mai tsuma zuciya ta saka tare da faɗawa jikinsa a hankali yake shafo fuskarta zuwa wuyanta yana fura mata iska a fuskarta da bakinsa. Sosai ita ma ta goya bayan ƙudurin da ya zartar akan lamarin a haka bacci ya ɗauke ta.
Kwana biyu tsakani muka shirya domin zuwa potiskum har da Ummi sadakan arba'in ɗin Baba, Farouk kawai aka bari domin shi aikin su babu hutu. Duk wani jinin ahalin ya bayyana a gidan ƙur'anai, carbi da bototi aka rabawa jama'a sannan aka yi masa tarin addu'o'in neman rahamar Allah.
A nan nake jin wai Abdallan Salma ya dawo don shi da iyayensa har gaisuwar ta'aziyya suka yi gidanmu, tare da bada haƙuri ga su Abba da neman sulhu. Sosai ni kam nayi murnan hakan duk da a yanda naji zancen Salman taƙi amincewa ko sau ɗaya su haɗu kuma har yanzu yana garin don ya ce ba zai koma ba har sai ta yafe masa ta mance komai sun koma rayuwarsu kamar na da. Sai da su Abba suka yi mata nasiha sosai tare da tinatar da ita cewar har yanzu shi ɗin mijinta ne domin ko tana gidan malam Mammam ya dawo to zata iya komawa gidansa. A shari'ance zaɓi za'a bata duk wanda ta zaɓa a tsakanin su.
Yaya Saifuddeen tare da Yusuf suka zo sai dai bai zo gidanmu ba, yaya Majid ya tunkara da zancen tare da fayyace masa komai kamar yanda suka zanta da Yusuf ɗin. Sosai ya shiga cikin matuƙar kaɗuwa gami da ruɗewa jin zantukan su Abba ya sanarwa komai suma hankalin su ba kaɗan ba ya tashi. Yusuf ɗin suka nema zama dashi domin jin ta bakinsa ya kuma labarta musu komai a take a wajen Baba ƙarami ya ƙiran waliyinsa kawunsa ya sanar dashi komai shima nashi hankali ya yi mummunan tashi tare da yin Allah wadarai da hali irin na Binta.
Da kansa yaje har gida da Yusuf ɗin ya yi mata tatas sai da kuma ya sanya ta amsa laifinta a gabansa. Kana ya buga mata zazzafan sharaɗin kar ta kuma shiga lamarin gidajensu balle ta tunda kashe musu aure.
Satikai uku aka sanya komawar Salma gidan Abdallah bayan su Abba sun yi masa zazzafan nasiha mai ratsa jiki, tare da nusar dashi illar abinda ya aikata. Haka muka koma ni dai baiwar Allah ban komai ba tun daga lokacin nan ban ƙara sanya yaya Yusuf a cikin idona ba haka nan ko Anty Zakiyya ban kuma jin ta yi zancensa ba. Hakan ya sama mini sukuni a raina na saki jikina mussamman da Nawwara da Nazifa suka dawo makaranta domin an gama gyare ɗakunan kwanan an kuma zuba tsoro sosai akan duk wacce take zaune a ciki. Bani da abokin da ya wuce Farouk a gida don jn ya dawo daga aiki dashi muke jan hiran mu, idan ina da lectures ɗin safe kuma yaya Saif ba zai fita da wuri ba shi yake kai ni makarantar kasancewar ya sayi mashin sabuwa dal su Nazifa har suna zolayana wai ko sona yake yi nayi banza dasu.
Matsowar komawar Salma ya sanya mu fara shirin zuwa potiskum, tun bayan dawowar Anty Zakiyya da Ummi suke gyara mini jiki a cewar Ummi wai so take yi nima na samo miji asha biki ban kawo komai a raina ba game da lamarin, domin na san da wuya wai kama kare ta wuya don sam ba mazan bane a gabana yanzu.
Ana saura kwana uku muka zo potiskum, yaya Saif da Farouk kuma sai ranar ɗaurin auren zasu zo da samu taho Farouk ya bani sabuwar waya dal ya ce zamu na magana kafin na dawo. Gidan ya cika maƙil da dangi Hajiya Babba ta tsage damtse sai gyare Salma take yi da kayan ƙamshi wani lokacin nima ta kan ce nayi mana tare.
Komai tare ake yi mata hatta ƙunshi da kitso iri guda aka zirara mana, ranar ɗaurin auren muka sha anko dasu Abasiyya da suka zo da ƴaƴansu abin gwanin ban sha'awa da burgewa su Firda'usi ma da ƙaramin cikin su da ya yi musu ɗas.
Sanda za'a kai amarya da aka kai ta sashin su Abba ya ce nima nazo. Zama nayi kaina a ƙasa ƙirjina yana dukan tara-tara. Cikin taushin