Showing 96001 words to 99000 words out of 171161 words

Chapter 33 - MATAN AREWA BOOK TWO COMPLETE PDF .txt

Sannan ya juya ga mai gadin ya cigaba da faɗin"Baba ka dai tina babu wani baƙon da Habib ya yi a ranar?".


Nan ma shuru ya yi alamar yana tariyo abinda ya wakana ranar a tare Farouk da Abdul-aziz suke sauƙe ajiyar zuciya da tafi kama da na fargaba da tsoron abinda zai faɗi wataƙil ya ci karo da hashashen zuciyoyinsu suke saƙa musu.


"Tabbas akwai wata da tazo wajen sa domin har nan waje ya rako ta, sannan wannan matar ba baƙuwa bace domin ta sha zuwa nan suna haɗuwa dashi Habib ɗin a duk lokacin da yallaɓai baya nan duk da bai cika zuwa ba sai jifa-jifa".


"Mace? kuma wajen Habib? ko zaka iya suffanta mana ita koda kamanninta ne haka?".


"Ƙwarai kuwa yaro tana da tsayi ƙwarai da hasken fata sosai ga shigarta sam ba ta yi kama da ta ɗiyoyin hausawa ba, duk sanda tazo nan da masifa take zuwa duk wanda ya shiga harkanta bata jin nauyin yi masa rashin mutunci kuma kowa yasan cewar ba siyayya ke kawo ta wajen nan ba kawai tana zuwa su gana da Habib ɗin ne".


A gaugauce Farouk ya zaro ambulan ɗin dake aljihunsa ya zaro hotunan Mina ya miƙawa mai gadin cikin sarƙewar harshe ya ce"dubi nan Baba ita ce wannan?".


Karɓan hotunan ya yi ya duba cike da bata tabbatacin abinda yake faɗi ya ce"shakka babu wannan ce yarinyar dake zuwa wajen Habib ko ranar da wannan abun ya faru tazo nan kuma har waje ya biyo ta cikin tashin hankali yana mata magana bata kula shi ba ta shige motar ta ta bar wajen, amma lafiya kuke yi min wannan tambayoyin?".
Tagwayen ajiyan zuciya Farouk ya saka take jikinsa ya ɗauki rawa tamkar ana jona masa mazari wani irin gudu yana gilmawa ta idanunsa tare da maye gurbin hasken da yake iya hangowa, rurin da wayarsa ta soma yi ya sanya shi haɗiye zancen da yake son furzowa tsoro yake yi kar abinda yake tinani ya zamto gaske kar ƙullin da yake yi a cikin ransa ya zamto hakan ne tabbas ba zai iya ɗauka ba.


Sai da Abdul-aziz ya taimaka masa ya zaro wayar daga aljihunsa dishi-dishi yake kallon sunan BLOODY ɗinsa da yake yawo cikim screen ɗin wayar da ya ƙara raunana masa zuciyarsa da take a matuƙar harzuƙe.


MATAN AREWA


(Book two)




© Maimunah Tijjani Iyam


________________________________




Page 8⃣8⃣


Ajiyan numfashi ya cigaba da sauƙewa tamkar wanda ya yi gudun ceton rai, rashin ɗagawan sa hakan bai sanya Saifuddeen ɗin daina ƙiran wayan a kai a kai ba. Ganin ba za'a daina ƙira ba ya sanya Abdul-aziz sanya wayar a airplane sannan ya ɗago Farouk ɗin ya riƙe hannunsa gam a nutse yake faɗin"haba Farouk calm down mana wannan fa duk hashashe ne muke yi ba wai ya zama gaske bane, mu koma asibitin kar ya fara tinanin wani abun". Kansa kawai yake iya ɗaga masa saboda sosai yake jin wani jiri yana tafiya dashi da ƙyar ya iya tsayawa kan ƙafafunsa godiya Abdul-aziz ya yi wa mai gadin tare da bashi wasu ƴan kuɗaɗe ya sayi goro suka wuce tun da suka baro wajen Abdul-aziz yake kwantar masa da hankali da bashi tabbacin cewar zai gama sauran aiki shi dai kawai ya kwantar da hankalinsa kar ya bar wani alamar da zai sanya Saif ɗin zargin wan abun. Da hakan suka isa asibitin a haraban asibitin suka tarar dashi ya fito domin ƙiran sallan zuhr ɗin da aka soma yi kallo ɗaya ya yi musu ya ɗauke kansa tare da wucewa inda babban masallacin dake cikin asibitin yake da sauri Farouk ya saki ƙofar motar ya bi bayansa cikin sauri har ya cin masa haɗe hannayensa waje guda ya yi yana faɗin"afuwan yaya Saif wallahi nima ban yi tinanin zamu daɗe har haka ba kuma sai da muka iso naga ƙiran ka na bar wayan a mot....".


Kallon da ya yi masa ya sanya saurin gimtse bakinsa tare da rusunar da ƙwayoyin idanunsa ƙasa jikinsa yana cigaba da rawa, dab dashi ya iso yana kallon fuskarsa a hankali yake furta"Umar yaushe ka fara ƙarya?".


Kansa kawai yake jijjiga masa da hakan ya bashi damar cigaba da faɗin"ban damu da dai na san inda ku ka je ba, but meye nayi min ƙarya Umar bayan kasan na tsani hakan ko yaya kayi hakan zan gano ka".


Rau-rau Farouk ya yi da idanu ya ɗago ya kalli Saif ɗin"afuwan yaya Saif ba zan ƙara ba ba zan ƙara yi ba na tuba". Yana ƙare faɗin hakan ya rungume Saif ɗin tsam a jikinsa wasu siraran hawaye suna tsiyayo masa daga gefe da gefen fuskarsa, bubbuga bayan sa yake a hankali tare da zame jikinsa daga nasa ya ɗan rankwafo da kansa dai-dai kunnensa yake masa raɗa"ya isa haka kar ka tara min mutane ace wani abun nayi maka, kawai ka san bana son daɗewa idan ka fita bana son wani abun ya same ka Umar sannan kar ka ƙara yi min ƙarya".


"Ba zan ƙara ba yaya Saif ba zan ƙara ba".


Kuncinsa ya lakato yana faɗin"Good boy". Sannan ya juya ga Abdul-aziz da tun ɗazu yake kallon su da ido ya yi masa alama kan suje suyi alwalan ya taho suka wuce suka yi alwala suka shiga masallacin.


Tunda aka fara azumi wahala ya kuma yi mana yawa ga zuwa lectures da kuma gwajin da muke yi a kai a kai saboda cikin azumi za'a rantsar damu mu zama cikakkun ɗaliban jami'ar bayan salla kuwa babu ɗaga ƙafa zamu fara jarabawa. Ga azumi ga aiki ga kuma zuwa lectures haka kullum muke ta fama zaune nake a ɗaki fitowa ta daga wanka kenan ina shafa mai sama sama a jikina tino ranar da idanuna suka gane mini yaya Yusuf ya yi mini dirar mikiya a cikin kwantaya gani nake tamkar yanzu abubuwan suke wakana wani haushi da takaicin kaina ya mamaye ni sai yanzu nake dana sanin meyasa ban yi masa magana ba? meyasa ban tare shi naji dalilin zuwan sa cikin jami'ar ba? meyasa na bar shi ya tafi ba tare da na baje masa tulin ƙullin zantukan da nake dakon su a raina ba?.


Tsam na tashi babu shiri ina tsirkar da tsakin takaicin kaina tare da yin hamdala ina ƙara godewa Allahna da bai bani ikon tarar sa nayi masa magana ba, wani zuciyar tana kimtsa mini cewar to ma a wani dalilin zan yi masa magana? bayan hukuma ta shiga tsakanin mu tayi mana iyaka dashi babu shi babu ni da dangina gabaɗaya, har na saka kayana ban daina tsakin ba na ɗauko wayata da nufin ƙiran yaya Majid na sanar dashi abinda yake faruwa wata zuciyar ta hane ni da yin haka na mayar da wayar na ajiye na bayyano waje inda Nawwara da Nazifa da raguwar mazauna hostel ɗin suke ta hada hadan haɗa kayan shan ruwa.


Bokati na jawo na zauna a kai ina faɗin"wash Allah". Nawwara ta hararo ni haɗi da faɗin"raguwar banza da wofi kawai ba abunda kika tsinana amma kin fi kowa raki". Sai da na dara sosai kamar zan zube ƙasa kafin na ce"ai ke dai sannun ki da ƙoƙari yanda kike ɗawainiyya damu Allah ne kaɗai zai biya ki".


Cokali ta wurgo mini nayi sauri kaucewa ina rarraba idanu don ganin ban ga Nazifa a wajen ba har na buɗe baki da nufin tambayar Nawwara sai ga ta ta shigo riƙe da baƙin leda a hannunta cikin zumuɗi ta iso ta zauna akan tabarman da Nawwara take tana faɗin"kun san mena ji yanzu da na fita?".


Haɗe baki muka yi wajen faɗin"A'a". Ta gyara zama ta ce"yau tafsirin da za'a yi a masallaci mr Saif ne zai yi shi bayan an sha ruwa".


"Ki rantsa da Allah Nazifa?".


Nawwara ta faɗa cikin gwalalo idanu waje cike da bata tabbacin zancen natan Nazifa ta ce"na rantse miki da Allah Nawwara bakya bi na bashin rantsuwa yau shi zai fi can na jiyo a cafe Amir na MSSC yana faɗa zai yi bayan a sha ruwa a masallaci".


Taɓe baki nayi tare da kawar da kaina gefe kamar ban ji su ba, ina yin abinda zai fishshe ni ina ta karanto sunayen mahaliccina ɗari ba ɗaya cikin raina. Har suka yi suka gama ban ce da su komai ba bayan mun sha ruwa muka ƙira gida muna musu sannu da shan ruwa muna gamawa aka fara shirin tafiya tafsirin da ake gudanarwa tun farkon kamawan watan ramadana da ake yi a babban masallacin dake cikin jami'ar mai ɗauke da ɓangare biyu na mata da na maza.


Tun kafin mu ƙarisa muke jiyo sautin ƙira'an alƙur'anin da aka sanya, muka sama waje muka zauna mata suna saman beni da suke iya hango mazan da suke zaune a ƙasa ta cikin gilashin da ya raba tsakanin su.


Ihun da aka sanya shi ya ja hankalina tare da ɗauro kaina na kai idanuna wajen da sautin yake tashi, sanye yake cikin shirgar larabawa tamkar limamin masallacin karami a hankali yake tafiyar ɗalibai suna rufa masa baya har ya ƙariso inda aka tanada domin sa wani ihun aka kuma sanyawa cikin sanyi ya fara karanto karatun al-ƙur'ani domin dawo da nutsuwan da aka rasa a wajen tsit ko'ina ya yi tamkar ba shine ya rikice da suturu daƙiƙai kaɗan da suka gabata ba.


Cikin fitar da haƙƙin ko wani harafi ya soma yin karanto suratul ankafut daga kan izufi ashirin wala tujadulu. Baka jin komai a wajen illa ƙaran fankoki da Acn da ya karaɗe dukkan girman masallacin, sai ya karance shafin farko tsaf kana ya dakata aka sanya kabbara sosai. Ya kuma wajen da aka tanada domin malaman ya zauna shi ya yi limamin aka gudanar da sallan isha'i da kuma tarawi sannan aka soma tafsirin alƙur-ani mai girma da tsantsan ƙwarewa yake yin pieces pieces da ayoyin sutarul baƙara kamar kar ya rufe bakinsa don daɗin tafsirin nasan da ya sanya kowa yin shuru shi kaɗai ake saurara saɓanin kwanakin ramada nan da suka gabata da wasu malaman ake ɗaukowa su zo suyi tafsirin sai anyi da gaske ake samun ɓangaren matan su yi shuru kowacce harkan gabanta take yi wasu har waya wasu kuwa su kafa daban hira da tsegumi.


Sai ƙarfe goma da rabi aka tashi aka fara watsewa yayin da wasu ƴan matan suka kafa suka tsare akan sai sunga fitowar sa sunyi masa wai sannu da shan ruwa, ko kallo basu ishe ni balle na tufa albarkacin bakina cikin hiran nasun da nake ɗaukar ta a matsayin rashin sanin darajan kai da kuma kima da martaban su na ƴaƴa mata ko lokacin da nake budurwa a gida tare da su Abasiyya bamu yi irin wannan watsar da kan ba balle yanzu da kan balbale ya waye.


Hostel muka muje har muka isa hiran tafsirin ake yi ranar kuwa tsawon daren cas aka ƙarar ana wannan zancen, muna daga kwance a barandan ƙofar ɗakin mu saboda zafin da ake tsulawa ga rashin wutan nepa da muke ta fama dashi a tsakiyar watan nan mai alfarma yayin da ƙanƙara ta gagari ɗan talaka ita ake yiwa kirarin nan na koda kuɗinka to fa sai rabonka ya tsaga wasu lokutan kafin magrib Amir ɗin MSSC da kuma SUG suke sanyawa a kawo ƙanƙara a rarraba duk da ba kowa yake samu ba amma alhamdulillah koda da sannu bata cire ciwo amma tana daɗin ji.


Zancen yake tashi daga daban da aka haɗa a filin hostel ɗin iska ya ɗebo ya zube su a ƙofofin kunnuwa.


"Ku ce nayi missing? naso na ganshi wallahi lokacin da yake yin tafsirin sai dai abubuwa sun yi wa kaina zafi ana fita tunin nima na fice farautan makaman cigaba da rayuwa, banzaye cikin ku gabaɗaya babu wacce tayi ko irin video ɗin nan ne?".


Furcin Bintu kenan da wata da ban iya tantance muryarta ba ta amsa mata da faɗin"ke to ai bana tinanin akwai wacce tayi vidoe,ma domin idan kika ɗaura idanunki a kansa ba za ma ki so ki cire ba balle har kiyi tinanin ɗaga waya kiyi vidoe amma ke ina kika je haka Bintu? a wannan watan ma ba za ki lafa ki koma ga ubangiji ba nafa lura ko sallan tarawin nan ba zuwa kike yi ba balle kuma wasu aikin ladan da zasu ƙara kusanta ki zuwa ga mahaliccinki a cikin wannan watan".


Wani uban ashariya Bintu ta lailayo ta kwaɓa mata mai wahalar maimata kafin ta ɗaura da faɗin"ke Hannatu ki fita daga harkata wallahi idan ba haka ba zan miki rashin mutuncin da ko sunana kika ji an ambata sai gabanki ya faɗi banda mutunci Hannatu. Idan ban fita na nemawa kaina abinda zan ci ba so kike na naɗe ƙafa yunwa tayi ajalina ko kuma meye?, dole ne karatun nan kamar yanda abincin ma ya zamto dole cin sa kin ganni nan ko hutun makaranta aka yi a wannan zango bana jin zan koma gida".


Ban iya jin raguwar zantukan da suka ɗaira dashi ba saboda wani tuƙiƙin ajiyan zuciyar da na sauƙe da ƙarfi, ina tino wani zancen da na taɓa ji amma na mance a ina cewar duk wanda bashi da ƙarfin ɗaukar nauyin ɗawainiyyar ƴarsa to kar ya fara tura ta jami'a domin matuƙar ya gaza ɗaukar nauyinta ta kuma kasance bata ƙoshi da tarbiyya ba abinda zata jawo masa sai ya gwammace da bai taɓa sanya ta a wani makarantar ba. Allah ya rufa mana asiri ya kare mana zuri'a da kuma duk wata budurwan da take jami'a ya ƙara mata tsoronsa da kuma wadatan zuci ya Allah ka hane ta watsawa iyayenta ƙasa a idanun su.




MATAN AREWA


(Book two)


© Maimunah Tijjani Iyam


_________________________________




Page 8⃣9⃣


Sai da ya fito dag cikin masallacin ya nufi inda ya faka motarsa ya ci karo da tarin missed call ɗin Abdul-aziz da kuma na gudan jininsa, iske ya fesar daga bakinsa yana mamakin rashin zuwan Abdul-aziz wajen tafsirin bayan sai da ya ta jaddada masa cewar ya tabbatar yazo wajen kafin ya iso sai da ya ƙara ƙiran sa ya tina masa ya ce dashi gashi a hanya sai dai har aka tashi bai zo ba.


Abdul-aziz ɗin ya fara ƙira bai ɗauka ba, kar ya fara dialing lambar Farouk ƙiran Abdul-aziz ɗin ya shigo wayarsa sai da ya tsirtar da siririyan tsaki kana ya ɗaga ƙiran game da karawa a kunnensa ba tare da ya ce komai ba, daga ɗayan ɓangaren Abdul-aziz ya furta"ina ta ƙiran wayanka baka yin picking na tura maka da saƙo ta what's app ɗinka address ɗin wani waje ne kazo wajen yanzu please".


Yana faɗin hakan ya datse ƙiran bin bayan ƙiran ya soma yi amma sam baya samu daga nashin har na Farouk babu wanda yake shiga, dole ya kunna data ya hau what's app ɗin ya ga message ɗin Abdul-aziz ɗin sosai yake ƙarewa adireshin da ya turo masa ɗin da kallo sai can daga bisani ya ajiye wayar gefe guda tare da tayar da motar ya fice daga cikin makarantar adireshin ya nufa ƙirjinsa yana tsananta bugun da yake yi.


Bai ɗau wani lokaci ba ya isa wajen kamar jira Abdul-aziz yake yi sai ga ƙiran sa ya shigo wayarsa, cikin sauri ya ɗaga yana faɗin"wai meye haka ne tun ɗazun nake neman wayoyin ku basa tafiya meye cewa nazo nan da kuka yi meye kuke shiryawa Abdul-aziz ina Umar yake?".


Sai da ya sauƙe ƙatuwar ajiyar zuciya kana ya ce"calm dowm Saif na hango ka bari na fito na shigo da kai". Bai bashi damar cewa wani abun ba ya kashe wayar ya fito daga cikin gidan da ya kasance mallakin yayansa da yanzu baya ƙasar can gefen gidan ya hango motar Saif ɗin ya nufe ta tun kafin ya ƙarisa wajen ya ɓalle marfin motar ya fito.


Rawa bakinsa ya soma dake alamta yana da abin faɗi amma sam ya kasa lura da hakan ya sanya Abdul-aziz ɗin riƙe hannunsa yana faɗin"muje". Daga haka ya cigaba da jan hannunsa har suka ƙarisa shiga cikin gidan sai da suka wuce wani falo kana suka zarce izuwa wani ɗakin da yafi kama da babu mazauni a cikinsa babu komai a cikin ɗakin illa baƙin duhun da ya hana shi ganin koda tafin hannunsa ne balle abunda yake a kusa dashi.


Kamar walƙiya haske ya fara gauraye dukkan ɗakin a sannu a sannu ya game ko'ina idanunsa da ya runtse saboda hasken wutan ya fara buɗewa a hankali yana ƙarewa ɗakin kallon caraf idanunsa suka sauƙa akan Habib dake takure waje guda hannayensa ɗaure ta bayansa da kuma ƙafafunsa ga fuskarsa da ta sauya alamar ya sha mungun bugu ba na wasa ba. Wani irin zabura ya yi ya nufi inda Habib ɗin ya ke ya durƙusa a gaban sa tare da fara sunce masa ɗaurin hannu da ƙafansa sai da ya warware masa su dukka kafin ya zube idanunsa akan fuskarsa muryarsa har wani shaƙewa take yi yake faɗin"Habib waya kawo ka nan? waye ya yi maka haka?".


Sunkuyar da kansa ƙasa ya yi domin bashi da ƙarfin gwiwan haɗa idanu dashi balle amsa masa tambayoyin nasan da ya jera masa su wani na bin wani, sai yanzun idanunsa suka yi masa tozali da Farouk dake zaune akan ɗayan daga cikin kujerun roba uku dake ɗakin kansa na sunkuye ya tallafi kuncinsa da dukka hannayensa biyu da sauri Saif ɗin ya miƙe daga tsugunan da ya yi gaban Habib ɗin da wani irin hanzari ya isa ga Farouk ɗin tare da ɗauke shi da wani irin gigitaccen marin da ya sanya Abdul-aziz tsoro ba kaɗan ba a iya sanin da ya yi masa babu abu mafi soyiwa a cikin rayuwarsa gabaɗaya fiye da waɗannan halittun biyu Umminsa da kuma gudan jininsa Farouk ɗin bai taɓa ɗaga masa murya ba balle sanya hannu a jikinsa da sunan duka sai dai soyayyar da yake masa hakan bai sanya shi ya bar shi ya taso a sangarce babu kwaɓa ba da ɗauke kansa daga dukkan lamarinsa da kuma share shi yake hukunta sa a duk sa'ilin da ya sauƙa daga gwadabe.


Yanda ya cakumo kwalar Farouk ɗin yana wugiggiga shi shi ya fi komai ƙara jefa tsoro a ƙirjin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login