Showing 54001 words to 57000 words out of 171161 words

Chapter 19 - MATAN AREWA BOOK TWO COMPLETE PDF .txt

ni ce a jami'a inda koda a cikin mafarki ban taɓa mafarkin kasancewata a nan ba, ikon Allah ya wuce komai kuma duk yanda ya tsara dole haka ya faru wata zuciya ta bani amsa cike da tabbatarwa. Yarda ya sanya iyayena turo ni wannan duniyar hakan ya sani ƙara ƙudurcewa cikin raina cewar bazan taɓa watsa musu tsakuwa a cikin idanunsu ba sai na fitar dasu kunya na kuma nunawa masu gurɓataccen tinani da rangwamen hankali da hangen nisa cewar ba duk macen da tayi jami'a bace take zamowa lalatacciya kamar yanda da yawan daga cikin mutanen al'ummar mu suke ɗauka tare da yi musu baƙin fanti.


Ban koma baccin ba na jona wayata a jikin caji na fita na haɗa gawayi na ɗaura mana dafa dukan makaroni sai da na gama tsaf na juye a cikin kula saboda har rana nayi su kamar yanda a cikim hirar mu jiya dasu Nawwara suka shaida mini sau biyu suke ɗaura sanwa wataran ma yi suke har dare su huta kuma ko don garwashin ma ya yi lasting.
Ina gamawa na wanke mana kwanukan da muka ɓata daren jiya sannan na shiga wanka cike da ƙanƙani na ƙarisa shiga banɗaki saboda warin fitsarin dake dukan hancina sai da na wanke shi tas sannan nayo wanka na fito lokacin mafi yawan mutane sun tashi kowa yana ƙoƙarin yin wanka ya fice. Wasu kuwa na haɗa gawayi da bin ɗaki suna tambayar garwashi mai wuta har kallo ɗaya nayi wata dake zaune tana ƙoƙarin kunna gawayi cikin munkubarinta na ɗauke kaina saboda munin shigar dake cikinta wata bes ce a jikinta da bata da maraba da tsirara domin bai taimaka wajen suturta komai daga halittan ƙirjinta zuwa cibiyanta ba. Sai kuma wani mini siket da ya matse mata cinyoyi ina gani kamar in tayi wani ƙauƙaran motsi ma kan iya yakewa ya fito da dukkan surarta a bayyane kanta a tsefa na tufke shi ta bayanta da baƙin ribbon.


Har na shige ɗakin ina mamakinta sai dai ban riƙe abin a raina ba domin nayi kyautata zaton cewar ba musulma ba ce tunda makarantar ya haɗa musulmai da chiristan.
Shigowana na iske Nawwara da Nazifa sun tashi suna Nawwara na danna waya Nazifa kuwa tana zaune ta sanya matashi a bayanta ta jingina dashi idanunta a lumshe riƙe da waya a hannunta ƙasa-ƙasa take maganar da ƙaryar mutum ya ce yaji abinda take faɗi koda kuwa a kusa da ita yake. Kuna haɗa ido da Nawwara naga ta saki dariya da ido take yi mini nuni da Nazifa ta matse jikinta waje guda tana sakin wani ƙayataccen murmushi marar sauti. Duk da ban fahimta ba murmusawa nayi ina zama kan gadona na fara sha mai a jikina.


"Kar dai har girki kika yi?, yaushe kika tashi?".


Muryar Nawwara ya katse ni na ɗago na bin ta da kallo tana buɗe kular da na sanya abincin a ciki, mayar da kaina kan shafar mai ɗin da nake yi nayi kafin na ce"da na gama waya ɗazu da yaya Majid na ɗaura kinga mun huta ai".


"Ai kuwa dai mun huta don daman girkin Nazifa ne nasan da yau sai yunwa ta kusa ajalinmu, sai ƙarfe biyu zamu yi karin kumallo in ta fara wannan wayar da yayan nata nan mantawa take yi da komai sai ta tafi wata duniyar ta daban zan ga idan aka fara lectures yanda za ki yi".


Murmushi na kuma yi a karo na biyu dai-dai sanda na gama shafa mai ɗin na furta"da gaskiyarta ai sunyi kewar ta ne ita ma haka kinga kuwa dole su ɗau lokaci suna waya tunda ba ganin juna ake yi zahiri b...".
Dariyar da Nawwara take ƙyalƙyalawa ya sa ni haɗiye ragowar zancen ba tare da na furzo su ba, na zuba mata idano har ƙasa ta kwanta tana dariya da riƙe ciki yayin da idanunta suka kawo ruwan hawaye tsabar dariyar da take. Sosai nake bin ta da kallon mamaki domin na lura ita kam sam abin dariya ba ya yi mata kaɗan.


Sai da ta tsagaita don kanta kana ta miƙe ta zauna tana kallon Nazifa da take banka mata harara tamkar idanunta zasu faɗo waje ta ce dani"kinji yaya watau kin zata yayanta na jini ko?, to cousin ɗinta ne kuma saurayinta ne soyayya suke in gaya miki yaya Amin in suka fara waya sai kin manta da cewar kuɗi suke sakawa a wayar sai su shafe awanni ba tare da sun gaji ba, iyayen soyayya kenan kike ji da gani a nan Hajiya Nazifar yaya Amin sai dubu ta taru".


Ta faɗa tana ƙara tuntsirewa da wata dariyar, ala dole Nazifa ta kashe wayar itama tana dariyar kafin ta furta"faɗi kanki tsaye ai ranar aurenmu za'a sha kallo wallahi domin auren soyayya za'a, kinsan shine first love ɗina fa kuma daga kanshi na rufe ƙofa".
Shewa Nawwara ta saka tana sake waƙar Naziru sarkin waƙar nan ta an kulle da maƙulli, suna ta dariya da ƙyar na jawo numfashina na fesar faɗin frist love da Nazifa tayi sai hakan ya tino mini da nawa watau malam Yusuf yanzu ko yana ina oho ko yana wani hali duk ban sani ba wataƙil ma ya daɗe da mancewa dani ya rufe babina ya buɗe sabo da wata can daban da zata maye gurbina a cikin ƙalbinsa.
Ban san hawaye sun fara tsiyayo mini ba sai tambayoyin dasu Nawwara suke jera mini ya yi nasarar dawo dani hayyacina, ƙirƙirarran murmushi na dasa akan fuskana kafin na ce"ba komai kawai na tina da wani abun ne da ya wuce can a baya".


Na faɗa ina ƙara yalwata fuskana da murmushi, ba sai sun furta mini ba domin fuskokinsu ma sun bayyana basu yarda da abinda na faɗa ba sai dai basu ce dani komai ba, Nazifa ta zubo mana abinda da na girka muka ci kafin mu gama ci ma sai da yaya Amin ya ƙira ta Nawwara ta ɗaga ta ce masa tana cin abinci ya yi haƙuri ta gama har yasa ta ƙware, nikam yanda suke ba wa junan sh kulawarsu ba kaɗan ba abin ya birge raina sai dai wata zuciyar tana karanto mini duk wata alaƙar soyayya da haka ta fara kafin gumi tayi gumi ayi yunwa halin kowa ya bayyana sai dai bana yiwa Nazifa wannan fatan.
Koda muka gama ci Nazifa ce ta kwance kwanon sannan suka yi wanka suka ce mu shirya mu zagaya cikin makarantar kafin gobe mu fara fita lecture hakan aka yi duk muka shirya muka rufe ƙofar ɗakinmu, dai-dai sanda zamu fice daga cikin arean muka yi kiciɓus da wannan matar da na gani ɗazu tana huta gawayi.


Tsam na ƙame sa'ilin da naji bakin Nawwara ya ƙira matar da sunan - Rahila Abdullahi-, don nikam gurbin da zuciyata ya bata ban yi zaton cewar musulma bace har suka gama gaisawa muka fita igiyar firgicin bai gama saki na ba Nazifa ta riga ni faɗin abinda ke raina.


"Nifa wallahi Rahilan nan ba burge ni take yi ba, sanda muka zo yin rejista da yaya Amin da ita muka fara haɗuwa naga sai wani satar kallonsa take yi, cikin raina nayi ta yin lahaula don nayi tinanin mayya ce ga wani shegen dressing da tayi da aka ciwa atamfa mutunci".


"Kedai malama kawai kishinki ya motsa kina tsoron a lashe miki muradin ranki". Fari Nazifa tayi da idanunta kafin ta ce"to laifi ne don mutum ya yi kishin abinda yake so Na'ima don Allah gaya mata gaskiya".
Murmushi kawai nayi kafin na kai ga furta wani kalma wayata da nake riƙe da ita ta soma ruri ganin sunan Baba ya sani saurin ɗagawa a ladabce na gaishe shi ya amsa yana tambayata yaya makaranta na ce dashi alhamdulillah gobe ma zamu fara lecture fatan alkhairi ya yi mini sosai tare da nasiha kafin muyi sallama na ba wa su Nawwara suka gaishe na ce musu Babana ne. Sai tsokalata suke yi wai ƴar gata ƴar Baba da Abba don jiya da Abba suka gaishe murmushi kawai nake yi musu, muka cigaba da zagaya makarantar sai da aka yi ƙiran zuhr muka koma hostel.


Wayewar garin ranar muka tashi cike da zumuɗin zuwa lectures ɗin farko tun kafin ƙarfe bakwai muka gama shirin mi tsaf cikin farar riga long sleeve da baƙin siket sai kuma baby hijab fari da muka ɗaura a kai, Nazifa tayi ta yi mana hotuna kafin mu tafi. Ƙarfe takwas dai-dai muka shiga lectures ɗin mune a front site muka mai da hankali sosai.
Lecturer ɗin namiji bashi da sakakken fuska domin kamar anyi masa dole haka ya shigo fuskarsa a ɗauke tamkar hadirin gabas. Kansa ya fara gabatarwa da faɗin sunansa Mr Sulaiman Audu sannan ya fara bamu course outline na course ɗin da zai ɗauke mu MAC 101 introduction to math com, tambayarsa ta farko ya fara da what is the defination of math com.


Da yawa sun ɗaga hannunsu ciki kuwa har dani don jiya na ɗan yi search kafin na kwanta, sai dai bai ba wa kowa damar amsa wa sai furtawa da ya yi" hey you black lady what is math com?".


Yana nuni da Nazifa dake zaune kusa dani"me sir?" ta mayar masa da tambayar a tsawace ya ce"oh do you see someone black apart from you here?".


MATAN AREWA


(Book two)


© Maimunah Tijjani Iyam
________________________________________




Page 6⃣4⃣




Dariyar da sauran ɗaliban dake ajin suka yi ya ƙara turniƙe mini raina da yake tafasa, ina jin ƙarar takun da Mr Suleiman yake yi yana sauƙowa daga kan ɗan stage ɗin da yake tsaye ya tako har gaban seat ɗin da muke zaune.
A gefen ido nake kallon Nazifa da tayi ƙasa da kansa, kafin ya iso nayi saurin tura mata ƴar fefan da na rubuta abinda na samu daga search ɗin a jikinta domin ta karanta ta faɗa masa. Bata kula ni ba illa ma ture hannuna da tayi har ya iso wajen bata ɗago idonta ba.


Tsawar da ya daka cikin faɗin"shut up". Ya sanya dukkan ajin ɗaukar shuru a lokaci guda kamar ba shi ne ya rikice da suturu da dariya ba yanzu- yanzun nan. Tsif kowa ya shiga tairayinsa babu mai yin wani ƙauƙaran motsi maganar da ya ɗaura ya ƙara sanya idanu dawowa kan Nazifa.


"Madam am asking you what is math communication?".


"No idea Sir".


Ta furta cikin rawar muryar dake tabbatar da cewar tana dab da sakin kuka, taku uku ya ƙara yi ya iso dab da seat ɗin mu ya ƙura mata idanuna na tsawon daƙiƙun da ba zasu haura biyu ba kafin ya janye idonsa tare da tsirtar da miyau yana ƙara yamutse fuskarsa da babu ɗigon annuri balle fara'a akan ta.


"Nonsense black pot".


Ya faɗa yana barin wajen ya koma kan stage ɗin, yana ƙara maimaita tambayar ga raguwar ƴan ajin wani namiji ne ya miƙe ya amsa tambayar amma sai meye?, maimakon yabo sai ma kwale shi da ya yi ya ce bai amsa dai-dai ba, sai da mutane huɗu suka amsa bayansa duk yana cewa ba dai-dai ba sannan shi ya bada wani defination nasa daban da bashi da marafa da wanda yake rubuce akan fefar dake gabana. Mafi yawan ɗaliban cike suke da tsoro domin a tashin farko da yazo mana da zafi yazo kuma baya ɗaukar kuskure ko kaɗan balle ya fahimci ma'anar kalmar nan ta uziri har ya yi aiki da ita a aikatace cikin aikinsa. Haka muka yi awa biyu zaune muna lectures ɗin kafin ya fita ƙarƙafan ajiyar zuciya na sauƙe daman haka jami'ar take?, ko kuwa mune bamu shigo da ƙafar dama cikin sa'a ba?. Ni dai kam ba haka malaman mu na sakandiri suke yi mana ba haba-haba muke dasu ayi dariya ayi wasa, dariyar da wasu zugan maza suka saka ya dawo dani hayyacina daga tinanina da na fara zurmawa na ɗago kaina ina bin su da kallo Nazifa suke nunawa suna dariya tare da maimaita sunan da Mr Suleiman ya ƙira ta dashi BLACK POT.


Kafin na miƙe na amar musu da balbalin masifar dake raina, Nawwara ta riga ni.


"Malamai meye haka?, will you guys stop that or other wise i show you who i am?".
Dubansu suka maido gare ta kafin ɗaya daga cikin ya yunƙuro da nufin yin magana, sauran suka gijjiga masa kai alamar kar ya yi cije lips ɗinsa kawai ya yi bayan ya gama ƙare mana tanadin kallo suka fice.


Muma fita muka yi domin attending lectures ɗin da zamu yi yanzu, gaban mun gama kwantarwa Nazifa hankali har ta daina kukan. Ba laifi wannan lectures ɗin na fahimta sosai domin tambayar da aka yi ni na tashi na amsa ta kamar lectures ɗin Mr Suleiman ba da zafinsa ma kaɗai ya hana kowa fahimtar abinda yake yi balle har ayi masa tambaya akan abinda ba'a gane ba.
Ƙarfe sha biyu muka fito domin shima awa biyu muka yi, bamu da wani lecture sai uku zuwa huɗu don haka muka wuce hostel muka ci abinci tare da yin wanka.
Muna ta lallashin Nazifa da ta suƙure ni dai kam wallahi banga wani baƙin Nazifa ba har da zai solewa mutane ido suyi mata ba'a tabbas tana da duhun fata sai dai launi ne mai kyau da kuma ɗaukar ido irin mai sheƙin nan ne mai dususu ba. Ga ta da manyan idanu da suke farare tas kamar an ɗiga musu zeba ga karan hanci, Nawwara kam fara ce sosai ni ce tsaka tsakiya a tsakanin su. Lecture ɗin ƙarfe uku zuwa huɗu bamu yi domin malamin bai zo ba kowa ya watse, da yamma Nawwara ta yi mana indomie muka ci bayan munyi sallan isha'i al-ƙur'anina na ɗauko cikin kayana na fara karantawa a hankali na daɗe ina karantun har Nazifa da take bacci ta farka ta fita ta wanke idonta ta dawo ta ƙura mini ido tun ban lura ni take kallo ba har na fahimta na ɗago kaina tare da sauƙe idanuna akam fuskarta na ɗage mata dira ɗaya alamar lafiya. Murmushi ta saka ba ta ce mini komai ba har sai da nake ayar ƙarshen suratul rum da na ɗauko kafin ta katse ni da faɗin"masha Allah nima za ki na ƙara min na gyara haddata".


Murmushi nayi mata ta ce"ƙwarai kuwa mai zai hana, amma sai dai ke ki ƙara mini".
"A'a ai ni yanzu na sama malama a kusa kullum ina zaune a kunkuminki". Daga ni har ita dariya muka saka shigowar Nawwara ɗakin kamar wacce aka wullo daga sama ya sanya mu datse murmushin babu shiri muna bin ta da kallon da yafi kama da na son jin ƙarin bayani.


"Ke Nawwara lafiyarki kuwa za ki shigo kamar kin faɗo daga bishiya?".


Bata kula ta sai da ta zauna akan gadonta tana ƙwafa tare da sakin huci, na kallota kafin na furta"lafiya kuwa?".


"Wallahi zan yi rashin mutunci a cikin hostel ɗin nan ga duk wacce na ƙara kamawa tana gulman mu".


Haɗe baki muka yi da Nazifa wajen faɗin"meye faru?". Ta gyara zamanta kafin ta soma faɗin"ɗakin su Sadiya naje na kama Hindu tana tsegunta musu abinda ya faru a lecture ɗin wancan Mr Suleiman ɗin abinda yafi bani haushi har da ƙarin gishiri abinda bai faruwa ba sai da ta ƙara".
Sakakken ajiyar zuciya Nazifa ta sauƙe ta ce"Nawwara kenan kar ki damu da hakan ni wallahi na ma manta da abin kema ina so ki cire shi daga ranki ki manta dashi, su kuma ai wanda ya yi na gari don kansa".


Jinjina kaina nayi tare da faɗin"haka ne kam amma wallahi nima fa abin ya tsaya mini a rai wannan ai cin zarafi ne ba koyarwa ba".


"Ɗan iska ba sai ka ce shi ɗin ma wani farin launi gare shi, yana nan dususu dashi ga gajarta da shege tumbi kamar mace mai shirin haihuwa har zai kushe halittan wani. Wallahi Nazifa ta bi shi kyan launi sau dubu".


A zafafe Nawwara ta ƙare furcin dake bayyanar da cewar har yanzu abin yana cin ranta, rurin da wayarta ta soma shi ya katse Nazifa daga maganar da tayi niyyar furtawa. Annurin da ya wanzu kan fuskarta tare da koran damuwar dake fuskar shi kaɗai ya isa ya tabbatar mana da cewar yaya Amin ne ya ƙira. Ɗagar wayar tayi ta kwanta lamau nida Nawwara muka haɗa ido muka sakarwa juna murmushi, nikam karatuna na cigaba da yi har ƙarfe takwas ta yi sannan na rufe alƙur'anin na ciro wayata dake caji tunda aka ɗauke wutan ban ciro ta ba kallo Nazifa nayi naga har yanzu wayar take yi na jijjiga kaina ina dannan lambobin cin bashin layin mtn na ci naira ɗari do dare ya yi bana tinanin samun masu saidawa a nan kusa na ƙira Umma har ƙiran ya katse bata ɗaga ba ina shirin danna mata wani sai ga ƙiranta ya shigo na ɗaga da sauri cike da kewarta dake addaban rai da ruhina ji nake yi kamar nay tsuntsuwa naje na ganta. Sosai muka gaisa sai tambayata take yi babu wata matsalar ko?, na saki murmushi kafin na amsa da cewar babu ta kuma tambaya ina ƴan-uwana da muke ɗaki ɗaya. Na sanya wayar a handsfree suka gaisa kafin na cire na karata a kunnena.


"Umma lafiya kuwa nake ta jiyo hayaniya?".


Ina iya jiyo ajiyar zuciyan da ta sauƙe kafin ta ce"Hanifa ce tazo gida". Tun kafin ta ƙarisa na tari numfashinta saboda dokawan da ƙirjina ya yi na ce"Hanifa kuma?, meye faru Allah yasa lafiya?".


Lafiya Na'ima amma ba ƙalau ba da yamman nan ta haihu ta haiho ɗanta namiji sai dai zabiya ne yaron. Shi kuwa mijinta ya yi tsalle ya dire ya ce alankatafur ba ɗansa bane duk su zuri'ar kaf babu zabiya balle a haiho sa".


Ƙarƙarfan ajiyar zuciya mai ƙarfi na sauƙe ina lanƙwashe ƙafafuna waje guda tausayin Hanifa duk ya mamaye mini rai yarinya shuru-shuru da ita abinta marar son hayaniya Allah ya jarabce ta da wannan ƙalubalen, sai da Umma ta fara faɗjn hello hello sannan na dawo hayyacina na ce"inajinki Umma".


"To shine dai ake ta rikicin yanzu, su Abbanku sunce a bari tukunna ayi suna ta huta domin ta wahala sosai wajen haihuwar har da su borin jini tayi.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login