Showing 18001 words to 21000 words out of 171161 words

Chapter 7 - MATAN AREWA BOOK TWO COMPLETE PDF .txt

tana riƙe cikinta, ƙaran natan ya jawo hankulan matan gidan duk suka nufo sashin ciki har da Umma da Anty Zakiyya.


"Meya faru da ita Majid?, yaushe tazo gidan?".


Umma ta furta tana kafe yaya Majid da ido bai ce da ita komai ba illa ficewar da ya yi abinsa. Daman kowa ya san zafin ransa da zuciya wannan dalilin ya sanya duk gidan mu ana shakkar sa baga yara kawai ba hatta uwayen su. Shi kaɗai yana iya riƙe gidan ya kuma tsawartar koda kuwa su Abba basa kusa.


Cakumar da Daada tayi mini a wuya har sai da hijabin dake kaina ya yage, cikin hargagi da ɗaga murya take faɗin"dan ubanki me kuka yi mata?, me kuka yiwa ƴata?". Sanƙarewa nayi a waje tamkar gunki na kasa gaba balle baya, illa bin jinin dake gudu a ƙafafun Abasiyya yana sauƙa ƙasa nake yi, hawaye suna sintiri a saman fuskana. Ɓanɓare hannunta nayi daga jikina ina isa inda Abasiyya ta zube zan kamo hannunta naji an figze ni an wurgar da ƙarfin tsiya sai da na bugu da randan ƙasar hajiya Babba dake bakin ƙofar ɗakin. Na rintse idanuna ina jin azabar buguwar har cikin kwanyata.


"Kar ki taɓa min ƴa kuma wallahi wani abun ya same ta ko kuma ɗan dake cikinta to kiyi kuka da kanki daga ke har Majid ɗin, don babu abinda zai hana ni damƙa ku ga hukuma. Inda za a bi min haƙƙinmu tun malam dai kam uwarki ta shanye shi baya iya aikata kataɓus".


Furcin Daada kenan da suka yiwa ƙofofin kunnuwana diran mikiya na bin ta da kallo idanuna suna cigaba da tsiyayar da ƙwalla. Me take nufi dani kenan?, in ce yanda take jin Abasiyyan nan jininta ce nima ai ƴar-uwata ce kuma jini guda. Jin an dafa kafaɗuna ya sanya ni cira kaina Anty Zakiyya ce tsaye a kaina ta jawo hannuna ta ɗago ni tsaye tana karkaɗe mini jikina.


"Kamar yanda kika ce duk abinda ya faru da Abasiyya ko cikin dake cikinta Na'ima tayi kuka da kanta. Kuma za ki sanya hukuma to ki sani kema ki sanya a ranki duk abinda ya sama cikin dake jikin Na'ima ki yi kuka da kanki daga ke har Abasiyyan".


Tana ƙare faɗin hakan taja hannuna muka fice daga sashin Umma tana biye da mu. Cikin ihu Daada ta biyo mu da faɗin"Shikenan mu zuba mu gani, cikin da uban nasan ma bai damuwa dashi ba".


Zaure Umma ta wuce ɗakin yaya Majid mu kuma muka wuce ɗakinta. Kuka nake yi mai tsananin gaske har jikina yana rawa duk abinda Anty Zakiyya take faɗi bana jin su balle na tantance su illa ganin leɓɓanta suna motsi da nake yi. Sai da nayi kukan mai isa ta har ina jin numfashina yana cukurkuɗe mini waje guda sannan na sarara, ba don na daina jin zafin da nake ji a cikin raina ba.


"Kiyi haƙuri Na'ima ki daina wannan kukan sai ka ce kema ba ki san halin Daada ba. Ko yau kika zo gidan nan ya kamata ki fahimci wacece Daada balle kuma cikinsa aka haife ki kika yi wayo har kawo girmanki. Duk abinda ta faɗa ki watsar dasu kar ma ki basu matsuguni a cikin ranki balle har su dame ki, ko ba don ke ba don abinda yake cikin cikinki ki sausautawa kanki wannna damuwar ba'a son masu ciki suna ɗaga hankalinsu irin haka".


Jin zantukan natan kawai nake yi amma damuwa kam ai mun ƙulla aminta mai ƙarfi tsakanin mu da ita. Ta ya ya zan iya fice wannan damuwar da tashin hankalin da nake ciki daga cikin raina?, na jefawa kaina tambayar a gaugauce.


Sosai tayi ta kwantar mini da hankali da nuna wannan ba komai bane, sannan ta buƙaci jin musabbabin faruwar lamarin na labarta mata komai. Jin hayaniyar ta dawo sashin mu ya sanya ni tinanin sun baron sashin hajiya Babban ina jiyo hargagin Daada tana faɗin a ƙira mata Sagiru mijin Abasiyyan yazo su tafi asibiti gashi nan ana ƙoƙarin kashe masa ahalin guda mata da ɗa tun kafin yazo duniya ana binsa da sharri. Duk sauran matan gidan suna ƙara ingizata Hajiya ce kawai ban ji muryarta ba haka nan ban ganta a sashin Hajiya Babban ba.


Mintuna a tsakanin hayaniyar ta ɗan tsagaita sai tashin ƙananun maganganun da gidan baya rabuwa dashi dama tun can, kamar wacce iska ya wurgo haka hajiya Babba ta shigo ɗaki ɗaurin zaninta na neman faɗowa a kiɗime ta shiga faɗin"Na'imatu me yake faruwa ne?, sanar dani meya hargitsa gidan haka?, tun daga maƙota nake jiyo hayaniya na iske yara damƙam a ƙofar gida an fita da Abasiyya na zubar jini rashin nutsuwar da nake ciki ya hana ni tambayar uwarta da take faman cika da batsewa".


"Wai Daada ce ta ƙira Abasiyya ta sanar da ita abinda ya faru jiya, shine ita kuma ta wanko ƙafarta tazo gidan nan wai da zummar ramawa mahaifiyarta rashin kunyar da Na'ima tayi mata yaya Majid kuwa ya faffala mata marin da ya haddasa mata zubar jini".


Dirsham Hajiya Babba ta zame ta zauna tallafe da kuncinta cikin matuƙar damuwar ta shimfiɗa ɓarau-ɓarau a saman fuskarta.


"Kai suhbanallahi wai shin sai yaushe Halima zata san annabin ya ƙafu ne?, tashi Zakiyya kije ki ƙira min Majid ɗin naji ta bakinsa".


Tashi Anty Zakiyya tayi da nufin aiwatar da umarnin hajiya Umma, babu jimawa suka dawo tare da Umma da yaya Majid ɗin. Hajiya Babba ta kalle shi har yanzu cikin ɓacin rai yake don fuskarsa ma ta riga da ta bayyanar da abinda ke cikin zuciyarsa sai da ta sauƙe numfashi kafin ta ce dashi"zauna babban mutum".


Ba don yaso ba ya zauna sai don girman da yake ba wa hajiya Babban, ya matsa hannunsa waje guda gaɓoɓin ƴan ƴatsunsa suna bada sauti ɗas ɗas.


"Babban mutum faɗa min meya faru?".


Sai da ya cije leɓɓansa kafin ya ce"ba abinda ya faru illa abinda kika ji". Ta sauƙe numfashi haɗi da cewar"kai ne babba a cikin gidan nan kai ya kamata ka hukunta duk wanda ya yi ba dai-dai domin matsayin uba kake a gare su, hukuncin da ka ɗaura ya yi min dai-dai kuma bari iyayen nakun su dawo mu zauna dasu tashi kaje abin ka".


Miƙewa ya yi ya fice ba tare da ya kalli kowa ba, har ya ƙai baranda ya dawo ya ɗago labulen kamar an masa dole yake faɗin"Na'ima ki tashi ki shirya ki fito muje asibiti kema a duba ki".


"Yaya Majid ni bana jin wani ciwo a jikina".


Na faɗa muryata a karye sai a sannan Umma ta ce wani abun"a'a Na'ima ki tashi kuje kawai kema kina buƙatar ai a duba lafiyarki".


Ban yi musu ba na miƙe na saka hijabina domin nima kaina nasan ina buƙatar ganin likita a halin da nake ciki ko don nauyin da ƙirjina ya yi mini ga kua cushewar numfashin da nake fama dashi, yana gaba ina biye dashi muka fice daga cikin gidan idanun kowa a kan mu, rashin ganin fuska daga yaya Majid ya sanya kowacce haɗiye abinda yake bakinta.


Asibitin dake kusa damu muje aka duba ni aka tabbatar mana da babu wani rauni a jikina, kuma jaririn dake cikina na yana lafiya wanda yazo a lissafin da nayi ya doshi satikai goma watanni uku kenan da ƴan satikai a kai sai dai har yanzu bai wani fito sosai ba. A hanyar mu ta komowa gida mashin ɗin ta sama matsala sai da yaya Majid ya tura ta muka iso har wajen mai gyara a ƙasa, ya gyara kafin muka tafi hakan yasa kuma ɓata lokaci har masallatan da suke yin zuhr ɗaya saura suka fara ƙira.


Tun muna dosa layin nake hango yaran da suka cinciringo a ƙofar gidan mu, har yaya Majid ya faka mashin ɗin muka sauƙa ya kore yaran kafin muka sama damar shiga cikin gidan don sun mamaye ƙofar shigar gabaɗaya suna leƙawa ciki da son jin abinda yake faru don hayaniya ce sosai ta kaure a gidan tamkar ann gudanar da yaƙin duniya na biyu.


"Yauwa gasu nan sun dawo".


Asma'u ta faɗa tana nuni damu da muke tsaye ba tare da munsan abinda ya kuma faruwa ba, tsam Daada ta miƙe Anty Hasina da ban san sa'ilin da tazo gidan ba tana riƙe ta saboda jirin dake kwasarta a hakan sai da tazo gabana ta tsaya tana aiko mini da wani figitaccen kallon da nake nakasa mini jiki gabaɗaya.


"Hankalinku ya kwanta yanzu ai sai ku zuba ruwa a ƙasa ku sha, kun kashe min jika tun kafin yazo duniya kunyi abinda kuke so kun cuce ni kun cuci rayuwar ɗiyata. Ba zan taɓa yafe muku ba daga har uwarku kuma ku shirya ziyartan kotu domin Sagir ya yi rantsuwa kuma ya lashin takobi akan ba zai yarda ba da salwantar masa da ɗa da aka yi tun a ciki hakan yasa yazo duniya ba rai uwarsa ta haife ba tare da ta shirya ba, Don haka ya ce ƙararku zai shigar amma kafin a kai ga haka wallahi kema sai uwarki taji zafin raɗaɗin rasan jikan da nayi sai na ɓarar miki da cikin dake cikinki".


Kafin nayi wani yunƙuri naji ta kai mini duka a cikina, zata ƙara kai min wani a karo na biyu yaya Majid ya yi saurim janye ni. Umma da Anty Zakiyya suka taso cikin ɓacin rai Umma take faɗin"dan Allah Halima ki sawa ranki ruwan sanyi a dai-dai lamarin nan kisan kai kike ƙoƙarin aikatawa".


"Shi Majid kuma ai ba kisan kan ya yi ba ko?, tsabar son zuciya irin naki da yake ƴaƴanki sune abin so".


Ta ƙare maganar tana fizgewa daga riƙon da Anty Hasina tayi mata, ta rarumo bokatin ƙarfe da niyyar buga mini. Hajiya Babba ta shiga tsakani ta sauƙe mata shi a goshinta.


Dai-dai sa'ilin da sallamar su Abba suka ratsa kunnuwan duk wanda yake tsaye a wajen.




MATAN AREWA


(Book two)


© Maimunah Tijjani Iyam


_____________________________________


Page 4⃣4⃣


Hajiya babba tayi baya luu zata faɗi yaya Majid ya yi saurin taro ta, ta faɗa jikinsa gidan ya ƙara rikiciwa sosai babu abinda yake tashi illa hayaniyar da ta karaɗe kowacce kusurwa.


"Me yake faruwa ne?".


Baba ya yi maganar yana ƙare mana kallon ɗai-ɗai, babu wanda ya amsa masa sai da ya daka wata ƙatuwar tsawa yana maimata tambayar a karo na biyu kafin Umma su Anty Kubra ta amsa masa da faɗin"Halima ce taji wa hajiya Babba rauni a ka".


Cicciɓan hajiya Babba aka yi aka wuce da ita sashinta duk muka ɗunguma da nufin bin bayan ta Abba ya daka tsawar da ta sanya kowa dakatawa jiki na kyarma.


"Ina zaku je?, ku bita kuyi mata meye duk wanda yake son ransa ya yi mummunan ɓaci to ya sanya ƙafa a cikin sashinta".


Tsif gidan ya ɗauki shuru tamkar anyi ruwa an ɗauke sumi sumi kowa ya shige ɗaki, cike da fargaban abinda zai je ya dawo. Tagumi na zabga magangagun Daada suna dawo mini cikin kwantaya tiryan tiryan. Wai Abasiyya ta haihu ba rai kuma Sagiru ya ce kotu zai maka mu shikenan mun shiga tara munyi kisan kai. Wani ƙarƙarfan kuka na tuntsire dashi ina kallon Ummata ita ma da ta yi jumgum na ce"Umma da gaske fa munyi kisan kai ko?".


"A'a Na'ima baku yi kisan kai ba, tunda ina da tabbacin bada wani nufin Majid ya mata wannan marin ba. Sai dai komai da sila shine dai ya zamo sila".
Muƙut na haɗiye wani miyau mai ɗacin gaske da ya wuce ta hanyar wuyana da ƙyar, duk muka yi shuru ina son ganin Abasiyyan tunda ban ganta cikin gidan ba na tabbatar tana can asibitin ne, amma na tabbatar Daada ba zata bar hakan ya faru ba wata zuciyar ta ce dani ko ita ma Abasiyyan ba zata saurare ki ba a halin yanzu. Shigowar Salma ɗakin ya katse mini hanzari na bita da kallo har ta zauna kusa dani tare da cewar"ki kwantar da hankalinki Na'ima, ita ma fa Abasiyyar tana lafiya kawai dai sun ce tana buƙatar hutu ne shiyasa suka ce sai gobe zasu sallame ta, amma ƙalau take".


Na bita da kallon mamaki kafin na ce"daga wajenta kike ne?". Ta ɗaga mini kai sama haɗi da faɗin"e ai tare da Daada muka je kai ta asibitin ai sai da Anty Maimuna taje ne ma na taho".
Ƙarƙarfan ajiyan zuciya na sauƙe ina jin abinda ya tokare mini ƙirjina ya wuce, na furzar da zazzafan iska daga bakina ina zame hannayena da nayi tagumi dasu daga kuncina can ƙasan maƙoshina na furta"alhamdulillahi mun gode Allah".


Ranar ko ɗaura sanwa ba'a yi ba kasancewar girkin Daada ne kuma ga abinda ya faru har yara suka taso daga makaranta. Sai da aka kwan a ka kuma yi wani yinin, lokacin har an sallamo Abasiyya ta dawo gida duk yanda naso muyi maganar fahimtar juna da ita taƙi saurara na balle bani haɗin kai, Daada kuwa tana kan bakanta na cewar Sagir ya maka mu a koto don ran jikanta ba sai salwanta a banza dole a bi masa haƙƙinsa. Daga kan Abba, Baba har Baba ƙarami basu ce komai ba game da laamrin, sai dai sun hana kowa shiga sashin Hajiya Babban illa goggo Jummai ita ke mata komai. Kwana biyu a tsakani har lokacin kai ka ce yau abin ya faru saboda kumfar bakin masifar da Daada take yi, Ranar bayan magrib kuwa su Abba suka yi mana ƙiran gabaɗaya a falon Hajiya Babba manya da yara har su Nurain duk muka halalta don yayin ƙiran Abba ya ce zai zartar da hukuncin ƙarshe ne.


Abba ya yi gyaran murya yana kallon Daada ta ƙasan ido kafin ya furta"Halimatu".


"Na'am malam".


Ta amsa tana kuma cika da batsewa, gyara zamansa ya yi yana ɗauke idanunsa daga kanta kafin ya ce"ke kika ƙira ƴarki Abasiyya kika sanar da ita abinda ya faru tsakanin ki da Na'ima bayan a nan muka kashe maganar nan kuma ta ba ki haƙuri cike da nadamar abinda ta aikata miki cikin fushi, amma ke duk hakan bai yi miki ba sai da kika sako ƴarki a ciki ita ma da yake shashashe ce kamar ki ta wanko ƙafarta tazo".


"E malam ni na ƙira Abasiyya na sanar da ita, domin ni hukuncin da kuka yanke ba'a yi min adalci ba".


Tas ƙaran marin da Abba ya sauƙe mata a gefen fuska ya bada da ya amsa falon. Hakan ya sanya kowa ƙara nutsuwa da shiga taitayinsa domin da wuya kaga ɓacin rai a fuskar Abba irin haka Baba ƙarami ne ƙaramin su amma duk yafi su zafin rai da faɗa sai kuma Baba amma Abba kam yana da sanyin halin su ɗaya da goggo Suwaiba.


"Kin ƙure haƙurina Halima kin ƙure ni matuƙar, har kina sanya ni aikata abinda ban yi niyya ba sanya hannu a jikin mace da sunan duka. Abin nakin ya wuce muzali domin kin wuce gona da iri, wani irin adalci kike buƙata bayan wanda aka yi miki?, ince dai yarinyar nan ta ba ki haƙuri a gaban kowa, har za ki ƙira ƴarta daga gidan auren ta ƙarba miki faɗan to yanzu wa gari ya waya?".


Tsif tamkar baby wasu halittun masu numfashi zaune a falon, sai can Abba ya ɗaura da faɗin"izuwa yanzu bazan ɗauki rashin mutumci ba Halima ba zan ɗauka ba, abin nakin ya wuce kan kowa sai kan mahaifiyata uwata. Don haka kije ki na sauwaƙe miki shikenan kin huta sai kije inda kike tinanin za'a miki adalci tunda ni na gaza yin hakan a gare ki".


Tunin surutai suka fara tashi kafin Baba ya katse shurun ta hanyar faɗin"amma yaya Muhammad da an yi mata gar....".Saurin ɗaga masa hannu Abba tayi haɗi da cewar"uwar tawa Adamu ta rotsewa goshi sannan ka ce nayi mata gargaɗi, haba kar ka bani kunya mana ta fice min daga gida bana ƙaunar ganin ta".


"Muhammad inda don ta ni ne da baka yanke wannan hukuncin ba, na yafewa Halima abin tayi min amma tunda ka zartar da hukunci sai dai muyi fatan Allah yasa hakan ya fi zamtowa alkhairi gare mu".


Furcin Hajiya Babba kenan da ya sanya Daada dasu Abasiyya rushewa da wani matsanancin kuka, Daada ta jawo jikinta izuwa gaban Hajiya Babba tana faɗin"Hajiya ki bashi haƙuri na tuba na amsa laifina kuma nayi nadama dan Allah ki roƙe shi ya mayar dani ɗakina na zauna kan ƴaƴana. Ina zanje yanzu muna tare dashi tunda jajayen ƙafafu sai yanzu da tsufa ya kama ni sai sake ni nake gida na ce nazo zawarci ko meye, jama'a dan Allah ku bashi haƙuri".


Tunin naji hawaye sun kuma taruwa mini a idaniya tunda na buɗe ido nayi wayo nake ganin Daada cikin gidan a matsayin matar mahaifina uwar ƴaƴansa uku sai gashi yau a ta dalilina sun rabu, wanu irin kallo ƴaƴanta zasu yi mini?, ta yaya zan kuɓuta daga zargin da zai ɗarsu a zuƙatansu akan ni ce sliar mutuwar auren uwarsu.


"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un".


Na furta numfashina yana cushewa waje guda kafin na jawo da ƙarfi har na sama zarafin faɗin"dan girman Allah Abba kayi haƙuri ka maida ita ɗakinta idan baka komar da ita ba wallahi har abada ba zan bar tinanin ni ce silar wargajewar alaƙar da tun ina ƙarama yake tsakanin ku na roƙe ka Abba".


Na ƙare zancen ina haɗe dukkan hannayena biyu alamar roƙo tare da lumshe idona, muryar Abba da kunnuwana suke zaton ji ba ita naji ya sauƙa a masarrafan ji na ba, muryar Anty Hasina ce cikin tsananin fushin da har a kalamanta sun bayyana take faɗin"ai daman ce ke sanadi Na'ima kuma wallahi ba zamu taɓa yafe miki ba kin cuce mu kema ki saurara jiran abinda kika shuka".


"Ku rufe min baki bana son jin komai daga kowa hukunci ne na riga da na yanke, ke kuma Hasina da Abasiyya bana son yamma tayi muku suna gidan nan kowacce ta koma gidanta".


"Allah ya huci zuciyarka Abbansu amma ai Abasiyya jego take yi, a ɗaga mata ƙafa ko kwana arba'in ne sai tayi".


Furcin Umma kenan muryata a karye kamar zata yi kuka alamar ita ma bata ji daɗin hukuncin na Abban ba amma rashin ganin fuska daga gare shi ya sanya ta yin kurum. Bai ce komai ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login