Showing 84001 words to 87000 words out of 171161 words
Chapter 29 - MATAN AREWA BOOK TWO COMPLETE PDF .txt
jummai kamar yanda ƙwaryan sama yake dukan na ƙasa. Duk abinda zai haɗa ni da malami ma ni ba son shi nake yi ba balle har akai ga zuwa a tarda shi a ofishinsa nima da nake namiji kenan balle kuma ga ƴaƴa mata masu rauni".
Figitit na dawo cikin hayyacina sakamakon dariyar da naji ya amsa hall ɗin na fara raba ido da nufin gano abinda ke gudana. Har aka gama lectures ɗin ban tsinci abu guda ɗaya kwakwkwaran da zan iya faɗi kai tsaye ba lamarin da bai taɓa faruwa dani ba kenan tun shigowa ta cikin jami'ar.
Hostel muka koma muka yi wanka, Nawwara ta tafasa mana taliyar da muka rage ragowarta da safe muka ci sannan muka fita lectures ɗin yamma na Mr Saif, yanda ƴan mata suke gwaɗale da wani ɗokin zuwansa har mamakin abin yake bane ni dai kam har cikin raina ban ga wani abu na mussamman game dashi ba da hakan ya bambamta shi da raguwar leccarurin da har za'a yi wannan abun a kanshi. Tsiririyar tsaki na saka tino da randa muka hange shigar Billy ɗawisu cikin ofishinsa da yanda ta dawp cikin hostel tana kuka shame-shame.
Dai-dai lokacinsa na cika muka hange shi ya tunkaro hall ɗin, a nutse yake tafiyar kansa a ƙasa kamar mai neman wani abun hannunsa na hagu riƙe da wayarsa ya yin da ya rataya jakarsa a hannun. Wani shewa mai dukan dodon kunnuwa ƴan matan da suka cika hall ɗin suka saka banda ƴan set ɗin har da ƴan gabanmu a hall ɗin wai duk sun zo ganin lecture ɗinsa. Yana sanya ƙafarsa hall ɗin ya ɗauki shuru kamar bashi bane daƙiƙu kaɗan ya cika da shewar nan ba gaishe shi aka fara yi sai dai bai amsa ko ɗaya ba illa hannunsa da ya ɗaga tare da ƙoƙarin canza yanayin fuskarsa izuwa na fara'a da annuri.
Laptop ɗinsa ya ciro daga cikin jakar tare da fefen attendance da ya miƙawa class rep, ya fara gudanar da lecturing ɗin cikin tsantsan ƙwarewa da sanin makaman aikinsa bayan ya maƙaka microphone a kunnensa ya kuma ajiye speaker saboda yawan mutanen da suka cika hall a ƙoƙarin ganin kowa ya ji me yake faɗi.
One hour lecture ne amma kowa sai da ya ji kamar kar a daina saboda yanda ya isa kama hankalin mai sauraronsa idan yana bayanin abu dalla-dalla. Bayan an gama yi masa tambayoyi kamar ba gobe yana amsawa ya ce a miƙo masa attendances ɗinsa.
Jujjuya fefan yake yi a hannunsa yana ƙara ƙare mana kallom tsaf ya ce"The number of people in the attendance list is less than the number of you peoples present here, the rest they don't write the attendence or what?".
Nan fa ido ya raina fata aka tsilli-tsilli da idanu class rep ya ce bai san meya faru ba, kansa kawai ya jinjina yana rufe laptop ɗinsa da speaker ya sanya cikin jakar yana riƙe da fefar attendances ɗin a hannunsa ɗaya ya yin da ɗayan ya zura ta a cikin aljihun ruwan sararin samaniyar yadin dake jikinsa da ya amshi fatarsa sosai da sosai.
"I known wasun ba ƴan department ɗin nan bane but they use to follow their friends,their boyfriend or girlfriend su shiga lecture ɗin da there not belong to their department. Hakan babban laifi ne babban idan baku sani ba you're now in this university may be that why you don't all this kar wani ya bi wani ko wata ya shiga lecture ɗin da ba nasu ba hakan laifi ne kuma idan aka kama mutum doka zata hau kansa, if i find someone da ba ɗan dep ɗin mass com ya yana attending lecture ɗin nan zan hukunta shi if you don't agree try me last time and see".
Yana gama faɗin hakan ya ajiye attendances ɗin akan desk ya ce ba zai karɓa ba ya yi ficewarsa, hayaniya ya ƙaraɗe dukkan kusurwan hall ɗin wasu har da Allah ya isan su ga wanda suka shiga lecture ɗin daga wasu department da hakan ya sanya shi ƙin karɓan attendances ɗin kowa ya rasa.
Mu dai hostel muka koma har aka yi ƙiran sallan magrib muna ɗaki, ranar ko zaman dare bamu yi ba bayan sallan isha'i muna tattauna batun zuwa ofishin Mr Suleiman kamar yanda ya buƙata sai Nazita taje ya bata script ɗinta yaya Majid ya ƙira wayata jikina duk a sanyaye na ɗaga ƙiran wayar tana ajiye a tsakiyan mu na sanya ta handsfree. Gaisawa muka yi da juna cikin kewa da marmarin juna kafin ya ba wa Umma da Hajiya Babba, Goggo Jummai, Hajiya, Daada da kuma Salma duk muka gaisa dasu muna tsaka da hirar mu da Salma Yaya Majid ya amshi wayar yana faɗin"to ya isa haka kar ku ƙarar min da ɗan canjin nawan".
Dariya na saka su Nawwara suna taya ni jin su ya ce na basu su gaisa na tura musu wayar gabansu duk suka gaisa dashi, a Nazifa ya ce"lafiya ya naji ku duk wani iri ko dai akwai wata matsala ne?".
Kallon kallo muka yiwa junan mu tare da sauƙe ƙatun numfashi a tare kamar mai raɗa cikin karyewan murya Nazifa ta ce"ni kam gwara mu faɗawa ko yaya Majid ɗin ne wataƙil ya samar mana da mafitar da muka gaza samu".
"Gaskiya kam mu san yanda zamu gamo bakin saren tun kafin saƙan ya warware dukka".
Cewar Nawwara bani da wani zaɓin sama da nasu don haka nima nayi mubaya'a, Nazifa ta faɗa masa komai tana ƙarawa da cewar"wallahi mun rasa yanda zamu ɓullowa lamarin sam malamin bashi da daɗi shiyasa nake tsoron zuwa na tarar dashi a ofishinsa".
Shuru yaya Majiid ya yi tamkar mai nazarin wani abun har sai da muka soma tinanin ko baya ji ne ko kuma ƙiran ya katse, na jawo wayar gabana tare da faɗin"hello yaya kana ji na?".
Sai a sannan ya ce"ina jinku Na'ima shawaran da zan baku yanzu shine kuje dukkan ku ya baku script ɗin idan kuka yi zuwa ɗaya bai baku ba to kar ku ƙara zuwa kuma ku dunga zuwa dukkan ku bayan nan ku canja wajen da kuke zama yayin ɗaukar darasin sa, sannan kuma ku daina zama waje ɗaya kowacce ta zauna ita kaɗai".
"Muma dai daman tsoro muke yi taje ofishinsa don ni wallahi duk malaman nan bana musu kallon akwai na Allah a cikinsu ko a labarinsu da muke ji a wajen mutanen da suka gabace mu suka yi mu'amala dasu, ni kam yarinya na ganki kin shiga ofishin malami ma kallon ƴar iska nake miki".
Dariya sosai yaya Majid ya saka kamar zai shiɗe sai da ya yi mai isar sa ya tsagaita don kansa kafin ya ce"Na'ima kin fahimci abu a baibai ne kar ki bari zuciyarki ta zargi duk wacce kika gani a ofishin malami balle har ki suffanta ta da kalmar ƴar iska, wasun uzuri ne yake kai su wasu kuma dole ne kamar yanda a wasu kuma kamawa take yi idan an buga ba'a kai ga samun mafita ba. Hasalima zuwa ofishin malami ko a dokar makaranta ba laifi bane domin shi malami kamar madubi yake ga rayuwar ɗalibansa da suke hango tasu rayuwar a cikinta don mace taje ofishin malami ba shi yake nuna cewar daga ranar ta zama ƴar iska ba ko kuma marar kamun kai ba sai dai abinda ake so idan za'a je ɗin kije da ƙawarki haka sannan kuma uwa uba tsoron Allah ga malamai da ɗaliban gabaɗaya".
Daga haka ya ɗan tsagaita kafin ya ɗaura da"Da yawan wasu malamai ana musu wani kallo na daban wanda sai ka raɓe su zaka gane cewar sam ba hakan suke ba, lokacin da muke NCE 1 zangon farko akwai wani malamin da ya ɗauke mu Physcology ya ƙware sosai a ilmil sani da karantar halayyan ɗan adam ko ƙarya kayi masa nan take yake ganewa sai dai kawai ya barka da halinka. Akwai wata yarinyar da duk sanda zai shigo idanunsa suna kanta tun bamu fahimta ba har kowa ya fahimta a haka muka gama zangon muka dawo zango na biyu babu abinda ya canja kwatsam sai ta daina zuwa ta shafe satikai bata zuwa kuma shima malamin baya zuwa sai dai jita-jita yana yawo cikin makarantar cewar ana ganin motarsa a bakin hostel yana ɗaukarta a motarsa su fita, sai dab da zamu fara jarabawa ta fara zuwa a lokacin kowa yana ankare da duk wani motsin ta da nashi domin dukkan mu kallon mutumin banza muke masa wanda ya ci amanar aikinsa na koyarwa ita kuma muna mata kallon marar kamun kai wacce ta ci amanar yardan da iyayenta suke yi mata da hakan ya basu damar turo ta karatun. A jarabawar mu ta ƙarshe muka ƙudiri gano abinda ke ɓoye tsakaninsu daren ranar muka kwana a hostel misalin ƙarfe sha ɗaya ya faka motarsa can nisa da hostel ɗin ita kuma ta fito ta same shi ya ja motar suka tafi basu dawo ba sai da dare ya raba koda ya shigo cikin makarantar lokacin tunin a sanarwa SUG da muƙarrabansa wasu fusatattun matasa suka far masa aka fasa masa gilashin motarsa tare da jawo shi waje ana dukansa. Securities ne suka yi ƙoƙarin ƙwarar sa amma abun ya ci tura sai da aka yi masa jina-jina aka sumar dashi kafin aka yi nasarar cetonsa, aka wuce dashi college clinic a lokacin kafin gari ya waye labarin tunin ya baɗe gari akan an kama malamin da yake ɗaukar ɗalibansa yana karuwanci da ita kwana biyu ya yi kafin ya dawo cikin hayyacinsa aka buƙaci jim gaskiyar lamari daga bakinsa amsar da ya mayar shi ya karyar da zuƙatan mutane tare da sanya hawayen idaniya tsiyaya. Cewa ya yi tun a zangon farko yake lura da yarinyar yayin da yake yin lecture bata iya sama waje ɗaya ta dunga murtsukuku kenan ya ankara da hakan ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba, wata rana ya sanya aka samo masa lambarta ta hanyar wani saurayin da ya yi amfani dashi yake gare ta. Ko da ya ƙira akan yana son jin matsalarta da yake hana ta zama kamar kowa fashewa tayi da kuka mai tsanani ya yi yunƙurin jin matsalarta a karo ba adadi amma ko yaushe kuka take yi masa sai a ƙarshe ta furta masa cewar ta tsinci kanta cikin harkan lesbian tun a makarantar sakandiri da abin ya bi jikinta koda taxo hight insititution ba ta daina ba illa ma ƙara samun partners da tayi to yanzu matsalarta shine ta kamo da infection sosai da kuma wasu cututtukan da ya sanya gabanta fitar da wasu tsutsutsi da suke hana ta zama wajen guda sai ta sanya ƙunzugu irin na yara kafin ta sama nutsuwa shima cikin awa huɗu yake cika da tsutsutsin taje asibiti ance sai anyi mata tiyata domin wajen ya ruɓe kuma bata da hanyar samun kuɗin, jin hakan ya sanya shi alƙwarin zai ɗauki nauyin jinyarta har ta warke bayan ya sanya ta yi mishi alƙawarin cewar ba zata sake komawa ga wannan harkan ba ita kuma ta roƙi da ya rufa mata asiri. Hakan ya sanya dukkan dare yake zuwa yake ɗaukar ta zuwa asibiti har aka yi mata aikin ba tare da kowa ya sa ni ba tana zuwa ana duba wajen. To kunga irin wannan malaman kamar Malam Shu'aibu duk mun kasance marasa adalci a gare shi ta hanyar yanke masa hukunci ba tare da mun san abinda ke gudana ba, da yawan malamai ana musu irin wannan kallon alhali ba haka ɗin bane mafi kyawun abu shine mu kyautatawa kowa zato".
MATAN AREWA
(Book two)
© Maimunah Tijjani Iyam
____________________________________
Page 8⃣1⃣
Ƙarƙafan ajiyar zuciya mai nauyin gaske da ya tokare mini ƙirji na sauƙe haka nan ma Nawwara da kuma Nazifa da duk muka bada kafatanin hankalinmu ga sauraron zancen yaya Majid ɗin.
"Tab lalle kam sai dai kawai Allah ya yafe mana amma tabbas ana ɗaukar alhakin wasu malaman da dama don ko muma nan munyi aikata makamancin hakan".
Cewar Nawwara tana musgutawa daga zaman da tayi, kafin yaya Majid ya soma faɗin"gaskiya kam shiyasa ko addinin ya haramta yin mummunan zato ga mutum ko kuma zargin mutum akan abin da baka da cikakken hujja akan sa, sai dai suma malaman wani lokacin da nasu laifin domin bahaushe yana cewa wake ɗaya shike ɓata dukkan miya".
Kaina na jinjina tamkar ina gabansa kafin na sama damar faɗin"to yanzu dai meye mafita kenan yaya Majid?".
"Mafitar ɗaya ne shine ku haɗa kanku kuje ku same shi domin idan kuka ƙi zuwa ma yana iya kama ku da wani laifin akan hakan, kuje idan bai baku ba kuyi tahowarku ku bar masa scrips ɗin sannan kuma idan kunje ku kama kanku domin ko da ya kasance yanda kuke zato to sai ya ga fuska zai iya bayyana muku ƙudirinsa abu mai muhimammanci kuma ku bashi girmansa koda wasa kar ku raina sa balle gaya masa wata maganar ta rashin tarbiya a matsayinku na ƴaƴa mata".
"In sha Allah".
Muka haɗe baki wajen furtawa kafin na ce ya miƙa wayan cikin gida mu gama magana da Salma, ya kai mata ina jin muryarta na ce"ƴar-uwan ko dai bacci kika fara yaya Majid ya ɗago ki?".
Murmushi ta yi kana ta ce"ke dai bari kawai wallahi gajiya ce ke ɗawainiyya dani dukkan aiyukan gidan nan sun dawo kaina Allah dai ya fito min da miji ko wani iri ne na samu nayi aure na na huta da wannan rayuwar takaicin da baƙin-ciki".
"A'a Salma ki dai yi addu'a Allah ya kawo miki na gari kuma wanda yake mafi alkhairi a gare ki, amma ko wanne kika san wanda zai zo miki?. Shiyasa na shawarce da ki koma makaranta ko babban sakandiri kika kammala idan Allah ya fito miki da miji na gari ki yi aurenki ala bashi idan mai son ilmin ne ko kina gidansa za ki ɗaura".
Ina iya jiyo ajiyar numfashin da ta sauƙe haɗi da faɗin"Na'ima kenan ke dai kiyi karatunki tunda kin yi ai shikenan kin wakilce mu". Kaina na jijjaga kawai domin na san babu abinda zai faɗa mata a wannan lokacin har ya yi nasarar karkato da hankalinta ya yi nisan zango gare ni don haka na miƙawa su Nawwara suka gaisa kafin muka yi sallama.
Ranar a gadona na kwanta bayan tsawon satin da na shafe ina kwana ana Nawwara bayan mun gama yanke shawaran cewar gode zamu je ofishin Mr Suleiman a tare gudun faruwar wani abun da kuma zargin ƴan makaranta.
Na daɗe kwance kan gadon ina lissafin kwanakin da suka rage mu shiga watan ramadan wata mai falala, kwanaki goma sha biyu cif cif suka yi saura kuma an ce kafin salla za'a rantsar damu a matsayin cikakkun ɗaliban jami'ar watau matriculation bayan salla kuwa zamu fara rubuta jarabawa.
Cikin baccin da ya fara saɗɗata nake jin ana shafa mini sangalalen ƙafata da zanin jikina ya ɗan yaye ya dawo iya gwiwana, da farko na zata mafarki nake yi sai da naji abin ya yi gaba ana ƙoƙarin zarcewa har inda bana tsammani ana yunƙurin rabani da zanin dake jikina babu shiri na ƙwala wani gigitaccen ƙaran da ya sanya Nawwara da Nazifa farkawa a kiɗime kasancewar babu wutar nepa suka kunna tocila.
Cikina har wani kerma yake yi tsabar tsoritan da nayi na kasa yin komai balle cewa wani abun kamar yanda hawayen da suke cin raina suka kasa zubowa daga cikin koraman idaniyata da suke kwance luf.
A tare Nawwara da Nazifa suke rige-rigen jefo mini tambayar lafiya sai dai kamar suna yi da dutsi ko kuma sassaƙaƙƙen gunkin india da bashi da wani dama ko ikon sarrafa kansa. Kan ka ce kwabo duk ƴan sauran ɗakunan sun bayyanu waje tare da direwa a ɗakinmu suna tambayar lafiya.
"Na'ima wai meye ne lafiya kuwa meye faru kika tsala wannan uban ihun?".
Furcin Nazifa kenan tana jijjiga ni da ƙarfin gaske, da ido kawai nake bin ta ina jin wani abun mai ɗaci yana gaurayewa da miyau ɗin bakina tare da wanzuwa cikin ko wani kusurwa. Ban ce da ita ko kanzil ba illa janye idanuna da nayi daga kanta ina bin mutanen da suke tsaye curku-curku da kallo har izuwa lokacin da Nazifa ta ƙara maimata mini tambayar sai a sa'ilin nan na ce"wata ce ta shigo ɗakin nan take shafa mini jiki kuma na tabbatar da tana cikin nan".
Salati aka saka kafin Shato cikin gwatsale ta ce"ban gane kin tabbata tana cikin nan ba?, kina nufin kenan wata daga cikin mu ne ta shigo muku ɗaki bayan duk muna zaune a fili ana hira".
Ba tare da tsoron komai ba Nawwara ta ce"ƙwarai kuwa abinda kunnenki suka jiye miki hakan bakinta ya furta, to idan ba a cikin nan take ba a ina kenan take?. Wannen karo na biyu da irin hakan yake faru ko don a na farkon munyi shuru mun bar abin iya tsakanin mu shine aka ƙara biyo dare yau aka shigo?, to wallahi tallahi na rantse da wanda raina yake hannunsa zan ci kutumar uban duk wacce take shigo mana ɗakin tana mana wannan abun ta tsorici ranar da zamu yi ido huɗu da ita zata ga yabawa aya zaƙinta".
"To har meye a jikinta da bamu dashi da har za'a biyo dare ana shafa ta?, ince dai ita ma macece kamar mu nan babu wani bambamci tsakanin mu don hakan banga dalilin da yarinya zata dunga gaya min maganar banza nayi gum ba kuje can ku nema mai shigo muku ɗaƙi a inda take ehe".
A zafafe Ikilima tayi zancen da ya sanya Nawwara miƙewa ta nufo ta kamar kububuwa suka fara cacar baki tamkar zasu daki juna, da ƙyar aka raba su aka janye Ikilima ta fice Nazifa ta riƙe Nawwara da take ta faman huci. Duk tsananin zafin da ake yi a ranar ga rashin wutar nefa haka muka kwana ƙofa a rufe kirif ko bacci banyi ba sai bayan assalatu.
Washe gari duk zancen ya karaɗe cikin hostel ɗin kowacce dashi da fara karyawa, Ikilima sai ikirarin take yi na rashin mutuncin da ta tanadar mana da zaran mun shiga shirginta bamu biye ta muka shirya