Showing 3001 words to 6000 words out of 171161 words

Chapter 2 - MATAN AREWA BOOK TWO COMPLETE PDF .txt

jijoyina da nake jin su tamkar an ɗau ɗaure mini su gam.


Kaina ya sara a karo na barkatai, na runtse idona da ƙarfi sakamakon bayyanar yanda naga maman Anwar da maman Hanan a daren jiya. Zuciyata ta hau dakan lugudai ko a cikin munanan mafarkan da nake yi yayin da na kwantar da haƙarƙarina bai taɓa kimtsa mini mummunan ta'asan da maman Hanan suke aikatawa ba kenan da maman Anwar. Nayi tinanin ƙarƙarfan amincin da take faɗi a tsakanin su tsaftaccen ne, ashe kallon biri nake yi musu suna yi mini kallon ayaba.


Nafi awa ɗaya da rabi kwance amma na kasa baccin, sai faman juyi nake yi kawai ina lura da hajiya Babba da ko motsi nayi tana ankare dani. Sai da na yi sallan zuhr a nan sashin natan, sannan na fito na nufi namu ina tafiya ina haɗa hanya kamar ƴar maye. Duk da kuwa na gama tsayarwa kaina mafita wanda nake tinanin shine mafita gare ni da rayuwata gabaɗaya, har ma iyayena da ƴan-uwana. Nayi aniyar yaƙi da zuciyata akan son yaya Yusuf da yake cikinta sai na fige shi ta ƙarfin tsiya ko da kuwa hakan ba zai yi mata daɗi ba wataƙil har ya raunana ta. Amma zan daure tunda yanzu ta faru ta ƙare wai anyi wa mai dami ɗaya sata, kuma ai don tuwon gobe ake wanke tukunya tunda ni kam ba san zuwan nawa goben ba dole na ragargaza tukunyar.


"Ashe wai Na'ima mijinta ne ya maka mata saki uku rus. Har da naɗa mata ɗan banzan duka sannan ya watso mata kayanta waje cikin dare duk magiyar da ƴan unguwar suka haɗu suna yi masa akan ya barta ta kwana gobe sai ta taho gidan ƙi yawa ya yi. Sai makwabta ne suka taimaka mata suka bata mafaka ta kwan shine yau tun sassafiya ta diroj a gidan nan".


Furcin Umma Balkisu kenan da suka sauƙa a ƙofofin kunnuwana tamkar faɗuwar aradu. Suna zantawa da amaryan Baba Umma Ikilima, ta zaro idanunta waje tare da riƙe haɓarta haɗi da faɗin"Kar ki gaya min Shato, wai auren Na'iman ne ya mutu?, kuma saki uku ai babu maganar kome amma ke a ina kika ji?".


"Na rantse miki har da girman wanda raina yake hannunsa, wannan maganar da na faɗa miki babu kuskure a cikinta. Ai akwai ƴar ƙanwata a layin nasu ita na ƙira ta irge min komai daga farko har ƙarshe. Zaman aka yi a sashin hajiya Babba ɗazun nan da na fita na jiyo Abbansu yana lallashin Ummansu don sai kuka take a sashin su".


Da maɗaukakiyar mamaki Umman Ikilima ta furta"Tirƙashi! ƴar mai gyara auren wasu yau ita ce aka sako ƴarta har saki uku. Mu ɗin dai da aka wulaƙanta ake ganin ƴaƴanmu ba zasu yi zaman aure ba, gashi har yanzu suna ɗakunan mazajensu ai shi Allah baya bacci wallahi, sai tazo su haɗu yaya ta kasa aurowa ga ƙanwa ƙaramar bazawara".


Take naji kaina yana juyawa tamkar bishiyar da guguwa yake wujijjiga ta. Na dafe goshina raina cike da takaici al'umman da nake rayuwa a cikinta da yaɗa jita-jita da ƙarairayi baya musu wahala, kamar jira ake yi abu ya faru a sama abin karawa a faifali ana yamaɗiɗi dashi. Idan har ƴan-uwana makusanta na zasu bini da irin wanna sharrin to ina ga bare?. Zuciyata ta shiga kimtsa mini zantukan da suka kusa zauta ni. Lalle ya kamata ki toshe kunnuwanki sannan ki koyi kawar da kai, ki gani ki ƙi gani kiji ki ƙi ji.


MATAN AREWA
(Book two)


© Maimunah Tijjani Iyam
__________________________________


Page 3⃣5⃣


Ban sani ba ko lura da tsayiwa ta a wajen shi ya sanya su yin shuru oho. Kame-kame suka fara tare da borin kunya tunda ance tabarmar kunya da hauka ake naɗe ta. Ban ce dasu komai ba nayi wucewa ta ɗakin Ummata, Anty Zakiyya kawai na iske a hankali nayi sallamar da bai zamto lalle taji ba, na zauna tare da jingina kaina jikin kujerar ina lumshe idanuna.


"Lafiya kuwa Na'ima?".


Ba tare da na buɗe idona ba na ce da ita"kaina ke mini ciwo".
Sannu tayi mini kafin ta miƙe ta kawo mini paracetamol ƙwara biyu a cikin sachet ɗinsa ta fita domin ɗebo mini ruwa. Fitan ta ya yi dai-dai da sauƙe wata shirgegiyar ajiyar zuciyar da na saka.
Ina ta jujayin zantukan nasu Umman Balkisu a cikin raina da yake cunkushe da tsananin baƙin-ciki, yau na ƙara tabbatarwa da cewar lamarin gidanmu sai addu'a kowa kansa da ƴaƴansa kaɗai ya sani musamman a irin wannan yanayin.


Har Anty Zakiyya ta dawo ban daina saƙa da warwaran zaren tinanin da nake kimtsawa ba a cikin raina, maganin nasha Salma ta shigo mini da abinci sam na kasa ci koda loma guda ne. Kunun da ta kawo mini shi kaɗai na ɗan zuƙa. Ta kallo ni cike da kula ta ce"Na'ima wallahi na kasa gaskatawa wai malam Yusuf ne ya sake ki, kuma saki ba laifin tsaye balle na zaune hakan ya ƙara jefa min tsoro da fargaban mazan yanzu a cikin raina. Idan har irin soyayyar da malam Yusuf ya nuna miki tun kafin aure har aka yi bata sauya ba, zai iya rabuwa dake to ina ga wanda daman ba soyayyar?".
Shuru nayi mata hakan ya bada damar ɗaurawa da"Gwara kema Na'ima tunda ko ba komai kin san yanzu babu aurensa a kan ki, nifa da ban san makomar aurena ba".


"Babu auren da baya zuwa da nashi matsalar ko ƙalubale, sai dai kawai na wani ya zarce na wani tunda shi mai ɗaki shi yasan inda yake masa yoyo. Wannan rayuwar muyi fatan dacewa kawai".


Furcin Anty Zakiyya kenan da ya sanya mu amsawa da kalmar amin, kafin ta fice ta bamu waje mun tattauna sosai da Salma har naji nauyin da ƙirjina ya yi mini ya ɗan ragu. Koda Umma ta dawo daga sashinsu Abba ita ma matsa mini tayi akan naci abinci koda kaɗan ne, ganin ta matsa da yawa ya sanya ni jawo kwanon abincin da ta dire mini a gabana na ɗan caccakala na ce na ƙoshi. Da yamma hajiya Babba ta aiko mini dambun da tayi da kanta kaɗan naci na kwanta, ɗakinmu na da muka kwana tare da Salma duk kewar rayuwarmu ta da ya addabe ni da kewar Abasiyya da Balkisu.


Ganin da gaske bacci ya yi mini ƙaura ya sanya ni tashi na ɗauro alwala nazo na fara gabatar da sallan nafila. Tunda aka yi sallan asubahi malam Yusuf bai motsa daga inda yake ba, kifa kansa ya yi kan gwiwoyinsa tare da lumshe idanunsa da daren jiya sam bai samu bacci ba yanda yaga rana haka nan yaga dare. Ransa yana masa wani masifafffen ƙuna da raɗaɗi gani yake yi tamkar mafarki yake da kuwa hakan ne zai fi kuwa farin cikin idan ya farka.
Dogon numfashi yaja ya fesar a karo bartakai, kafin ya datse leɓɓansa da haƙurinsa da matuƙar ƙarfi. Ya rasa yaya aka yi hannayensa suka rubuta wannan sakin da tunda ya aikata ya kasa samun sukuni balle ya yi walwala kamar kowa, ya kasa samun nutsuwa balle farin-ciki ya samu gurbin zama cikin ƙirjinsa da yake jin tamkar ana musayan kifiyoyin wuta.


Jin an taɓo kafaɗarsa bai sanya shi ya ɗago kansa ba illa buɗe rinannun idanunsa da ya yi, yaya Auwal ne tsaye ganin ya buɗe idonsa ya sanya shi zama a gabansa tare da lankwashe dukkan ƙafafunsa waje guda. Yana bin sa da wani irin kallo mai kama da na ƙurilla har wani rama ya yi ta fuska tsakanin yau da jiya ga idanunsa da suka ƙara ƙanƙancewa suka yi can ciki. Sai da ya fesar da numfashi ta bakinsa kafin a sanyaye ya furta"Yusuf". Bai tanka masa ba illa bin sa da ido da ya yi, hakan ya tabbatarwa yayi Auwal cewar lalle yana sauraronsa.


"Yusuf meyasa baka koma gida ba jiya?, meyasa ba kwana a nan?, meyasa kake kuka? meyasa?".


Janye idonsa malam Yusuf ya yi daga kansa tare da mayar da idonsa ya lumshe su a hankali yake faɗin"Dan Allah ka barni ku barni, nayi muku yanda kuke so nima yanzu dan Allah ku barni nayi abinda naga zai fi dacewa dani. Hawayen nan da nake yi shine kaɗai hanyar da nake jin raɗaɗin dake cikin raina yana raguwa. Wallahi yaya Auwal zuciyata bugawa take yi da ƙarfi da ƙarfi inda na tuna yanda hawayen suke gudana a fuskar Na'ima yayin da bakina ya furta maka kalmar saki, yaya Auwal har roƙo tayi amma na kasa tsayiwa balle na saurare ta".
Sosai jikin yaya Auwal ya yi sanyi ganin halin da ɗan-uwan nasan yake ciki, ba ƙaramin abu bane yake sanya shi zubda ƙwalla zai iya cewa rabon da yaga hawaye kamar haka a fuskarsa tun lokacin rasuwar iyayensu. Yana da matuƙar juriya da ƙarfin zuciyar da yake iya danne komai a ransa amma tabbas wannan lamarin yafi ƙarfinsa tunda har ya koka masa. Matsowa ya yi ya janyo hannunsa tare da sanyawa cikin sa, yana kallon fuskarsa da har yanzu hawaye ne yake fita daga cikin idonsa ya ce"Yusuf kayi haƙuri shi aure rai gare shi matuƙar wa'adinsa ya yi to fa ko da so sai an rabu, kayi tawakkali kamar yanda na sanka dashi. Ka ɗauki hakan a matsayin ƙaddararku daga kai har ita kayi mata fatan alkhairi kai ma Allah ya baka wacce tafi ta. Ita ƙaddara idan ta ratso to babu abunda yake katange ta sai dai addu'a yana sausauta tsananin ta, da ilminka Yusuf amma kake wannan abun ya kamata ka rarrashi zuciyarka, yanzu ka tashi muje gida na san ko abinci ma baka ci ba".


Ajiyan zuciya kawai yake sauƙewa a kai a kai, tunda yaya Auwal ya fara maganar har ya kai aya, sam ya kasa yarda wai shine ya saki Na'ima farin-cikin rayuwarsa. Shi dai ya san ba shaye-shaye yake yi ba balle ya ce shawuwa ya yi ya aikata wannan aikin da ya jefa shi tafkin da-na-sani. Jan hannunsa da yaya Auwal ya yi ya tilasta masa miƙe tafiyar kawai yake amma ba tare da ya san inda yake ajiye ƙafarsa ba, a mashin ɗinsa yaya Auwal ya ɗauke sa suka nufi gidan Anty Binta tunda suka nufo layin gidan natan yake jin bugawan da zuciyarsa yake yi yana tsananta kamar ya yi tsalle ya dira daga mashin ɗin haka yaji.
Sallamar su ya sanya Anty Binta bankaɗo labulen ɗakinta ta fito kamar an jefo ta, idanunta sun yi ƙululu kamar zasu faɗo ƙasa da sarsarfa ta iso gare su tare da riƙo Yusuf cikin hawayen da suka wadacin rinannun idanunta take faɗin"Yusuf Yusuf Yusuf ina ka shiga?, ina ka shiga ka bar mu cikin tashin hankali dare jiya ko runtsawa ban yi ba".


Janye hannunta ya yi daga jikinsa ya ce"na tafi inda zan samu nutsuwa ne".
Bata kuma cewa komai ba ta baje musu tabarma duk suka zauna kafin yaya Auwal ya faɗa mata inda ya same shi. Ta hanyar wani abokinsa da ya ce sunyi sallan asuba tare dashi kuma ya barshi a masallaci.


"Yusuf kayi haƙuri mana ka ɗauki wannan ƙaddarar da ta faɗa maka sai ka ce ba mai ilmi ba haba. Inda macece zaka samu ko wacce kala kake muraɗi, matan da gasu nan burjik araha kamar jamfa a jos don haka ka kwantar da hankalinka, ka koma harkokinka kamar yanda kake".


Bai ce komai ba illa yaya Auwal da ya ce"nima dai abinda na faɗa mishi kenan ya yi addu'a kawai Allah yasa haka ya shine alkhairi a gare shi da rayuwarsa gabaɗaya".


"Shine magana yanzu bari na ɗauko maka fura kasha na san babu abinda ka saka a cikinsa tun faruwar lamarin nan. Mu za muyi asara idan damuwar daka saka a ranka zuciyarka ta buga ka mutu, ita Na'iman da kake yi a kanta babu abinda zai dame ta balle ya sha mata kai. Wataƙil izuwa lokacin tunin ta mance da kai tana shirin amarcewa da wanin ka".


"Ba zamu taɓa mancewa da juna ba ni da Na'ima har abada, ko barin duniya nayi na tabbata soyayyata a zuciyar Na'ima ba zata kau ba".


Sai da ta kalle shi tsaf ta taɓe baki ta miƙe ta shige ɗaki, zama tayi shirif akan gadonta sai yanzu take kuma jin raɗaɗin turaren body sprayn da ta fesa a idanunta domin su kumbura suyi jajir a hankali tayi tsaki tana sake sabon shiri a zuciyarta game da lamarin.
Ƙullin maganin ta ware ta zuba kaɗan a cikin damanmiyar furar don har ta canja mata kala ta juya sannan ta fito. Har yanzu yaya Auwal bai bar kwantar masa da hankali ba ta ajiye masa furan ko kallon ta bai yi ba, sai da yaya Auwal ya matsa masa sannan ya buɗe ya ɗaga ludayin zai kai bakinsa Anty Binta tayi saurin taran sa da faɗin"Ka sha sosai in ma baka ƙoshi ba akwai wani sai na dama maka da kaina ƙanina".


Bai ce komai ba ya kai bakinsa ajiyan zuciya ta sauƙe a ɓoye don buƙatarta ta biya tunda bata ji ya yi bismillah ba. Daman burinta ta mantar dashi hakan. Cikakkiyar bismillahn da taji ya rangaɗa ya yin da kai lugayi na biyu ya katse mata zancen zucin da take yi.


Ras! gabanta ya faɗi gargaɗin malamin yana dawo mata cikin kanta, cewar da ya yi lalle ta tabbatar da bai yi bismillah ba yayin da zai sha furar in kuwa ya yi tabbas aikin ba zai yi tasiri ba a jikinsa balle har a samu biyan buƙata. Tunin wasu zuffa suka tsatstsafo masa, tana tina yawan kuɗin akuyarta da ta siyar ta kai wa malamin kafin ya bata wannan maganin idan ya lalace tabbas ta kaɗe har ganyenta. Ludayi uku ya yi ya ture ƙwaryan daga gabansa yana miƙe. Kamar mai ciwon baki ya ce"Ni zan tafi".


"Ina zaka Yusuf?".


Yaya Auwal ya yi saurin furtawa bai amsa ba sai da ya kai bakin ƙofar ficewa ya ce"Zan kaɗaita kaina daga shiga jama'a, na nema kusanci da mahaliccina domin ambatonsa ne kaɗai yanzu yake mantar dani damuwata".


Daga haka ya fice mashin ɗinsa ya hau ya wuce gida domin yin wanka ko makaranta yau baya jin zai iya zuwa. Maman Hanan ya iske a tsakar gidan ta zagba tagumi sai da ya yi sallama baki biyu kafin ta amsa. Sama-sama suka gaisa ya shige ɗaki ya daɗe yana ƙarewa ɗakin kallo kafin ya sauƙe tagwayen ajiyan zuciya, ya shiga wanka bai ɓata lokaci ba ya gama shiryawan don zaman gidan ji yake yi kamar yana kan ƙaya.


Mama Hanan tana tsaye ta dakatar dashi ta hanyar miƙa masa farar takardan dake hannunta.


MATAN AREWA
(Book two)


© Maimunah Tijjani Iyam


________________________________________




Page 3⃣6⃣


Sai da ya ƙarewa takardan kallon tsaf yana ɗan jujjuyata a hannunsa kafin ya sauƙe idonsa akan maman Hanan, da ita ma ɗin shi take kallo a taƙaice ya ce"Ta mecece?".


"Ka duba zaka ga me take ƙunshe dashi".


Bai kuma cewa komai ba ya buɗe takardan, tunda ya fara karantawa dukkan jikinsa suka ɗauki mazari kamar wanda ake jonawa wutar lantarki. A firgice ya kuma kallon maman Hanan da ita ma ɗin har yanzu shi take kallo cikin rawar baki da na jiki ya soma faɗin"Anty Habiba waya ba ki takardan nan?, a ina kika same ta?".
Ɗauke idanunta tayi daga gare sa tana furzar da iska daga bakinta kafin ta ce"Na'ima ce ta bar min ita ta ce na baka ita da kaina, abinda taje yi maka albishir kenan lokacin da lamarin nan ya afku".


"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un".


Ya furta yana dafe goshinsa da yake tsatstsafo da wani maiƙon zuffa tamkar ba yanzu ya yi wanka ba. Ganin yana ƙoƙarin zamewa ƙasa ya sanya maman Hanan ɗauko masa kujera ya zauna. Sosai idanunsa suka ƙara rikiɗewa izuwa launin ja sosai, dafe ƙirjinsa da yake jin tamkar ana bugawa masa guduna ya maƙeri yana dukan ƙarfe ya yi . Kalmar innalillahi wa inna alaihir raji'un kaɗai yake ambata cikin ransa da kuma a bayyane da ya ke rage masa zafin da yake ji cikin ƙirjin nasa.


"Kayi haƙuri Yusuf amma tabbas da ka saurari Na'ima a wancan lokacin da abubuwan basu dagule har haka ba. Ina da yaƙinin ba zaka taɓa samun mace kamar Na'ima ba, domin ta nuna maka tsananin soyayyar da babu algus a cikinta, soyayyar tsakani da Allah kuma kowa ya shaida tana yi maka biyayya dai-dai gwargwadon iyawar ta".


Shuru ya yi yana sauraron maganganun maman Hanan ɗin, da zai iya suffanta su da ihu bayan hari domin ta faru ta ƙare kuskure dai kam ya tafka. A hankali ya zame hannunwansa daga goshinsa ya ce"Anty nima na san ba zan taɓa samun wacce zata maye mini gurbin Na'ima ba a cikin raina ba. Amma ganin wannan takardan ya sanyaya min sashin ruhina da nake ji kamar ana watsa min garwashin wuta ko ba komai akwai jinina da yake rayuwa cikin Na'ima. Dan Allah Anty Habiba kiyi min wani taimako bana son kowa ya san da wannan labarin koda kuwa yaya Auwal ne balle Anty Binta dan Allah ya tsaya iya tsakanin mu".


Sai da tayi nisa kana ta furta"nayi maka alƙawarin babu wanda zai sani, amma menene dalilinka na ɓoye haka?, ai shi ciki komai daren daɗewa dole zai bayyana a jikinta har kowa ya farga".


"Zasu ji amma a lokacin da ya dace kowa ya sani, amma ba yanzu ba ke dai kawai na gode". Ya faɗa yana miƙewa tsam zai fice tayi saurin dakatar dashi da cewar"Ka kuwa je gidan su Na'iman?". Kansa kawai ya jijjiga mata alamar a'a hakan ya bada damar ɗaurawa da faɗin"Ina son zuwa amma ba zan gane gidan nasun ba tunda ba zuwa na taɓa yi ba, sai dai kwatance da take yi min".


Ƙara kwatanta mata gidan ya yi har ta gane sannan ya yi ficewarsa. Makaranta ya wuce ya shige ofishinsa sam baya gajiya da karanta takardan kafin a tashi sai da ya kusa haddace dukkan rubutun cikin kaf a kansa, a cikin drawernsa ya saka takardan ya saka key ya kulle.
Wata gwauruwar ajiyan zuciya mai cike da fargaba da zulumi maman Hanan ta saka tana dafe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login