Showing 156001 words to 159000 words out of 171161 words

Chapter 53 - MATAN AREWA BOOK TWO COMPLETE PDF .txt

da suka zauna kafin Baba ƙarami ya furta"Hajiya lafiya kuwa?, ita kuma wannan meye kawo ta?". Ya ƙare zancen yana yana tsayar da idanunsa akan Salman da ta rusunar da nata idonun ƙasa. Sai da ta gyara zama kafin ta amsa mishi da"ina kuwa lafiya yanzu yarinyar nan Salma take zuwa min da wani zancen da ya firgita ni". Duk idanu suka zubowa Salman cike da son ƙarin bayani. Yaya Majid ne ya yi musu bayanin komai wani tsantsan ɓacin-rai nake iya hangowa a bisa fuskokin su wanda zan iya cewa tunda nayi wayo na mallaki hankalin kaina ban taɓa ganin makamancin sa a tattare dasu ba.


"Amma Hadiza ta bani kunya matuƙa da hankalinta zata jefa ƴar cikinta cikin wannan yanayin. Tabbas sai ta girbi abinda ta shuka da hannayenta Majid ka tashi kaje ta ƙira mana uwayenku mata a nan muna son ganin su". A ladabce ya amsa da kalmar to yana ficewa daga falon har yaje ya dawo babu wanda ya ce uffan a cikin su illa sautin kukan Salma da yake tashi ƙasa-ƙasa.


Tare da matan gidan duk suka dawo suka zazzauna idanunsu akan Salma kafin Ummanta ta ce"ke kuma Salma yaushe kika zo gidan?". Kafin ta amsa mata tunin Baba ƙarami ya amshe zancen cikin zafin rai da ya haifar masa da rawar jiki yana nuna ta da ƴar manuniyar ƴatsarsa yake faɗin" ba dole ki ganta a nan ba tunda ruɓaɓɓen ƙwai ɗin da kika burne ya fashe warinsa ya game hancin kowa, kin bani mamaki Hadiza matuƙar ban taɓa tinanin rashin ciwon kanki ya kai har haka ba da za ki jefa rayuwar ƴarki cikin halaka". Sai da ta kallo Salman sannan ta ce"ni kuwa malam meye na aikata haka ni Dije?". Ganin yanda ɓacin-rai ya bayyana ɓaro-ɓaro a bisa fuskarsa ya sanya Abba hana shi kuma cewa wani abun sai shi ya mayar da duk zancen da yaya Majid ya yi musu wanda Salman tayi shi. Salati da sallallami falon ya ɗauka kafin Hajiya Babba ta katse ta hanyar faɗin"nima kaina kin bani mamaki Hadizatu da girmanki da hankali da tunaninki har wannan mutumin zai yaudare ki da irin wannan zancen kuma ki aminci, har ki tirsasa yarinyar nan yarda da aurensa ta hanyar yi mata bazarana da za ko tsine mata. Kaicon ki Hadizatu da masu hali irin naki".


Wani kuka ta tuntsire dashi har ta shiɗewa da hakan ya sanya Baba ƙarami ƙara fusata a harsale ya ce"ai ba kuka za ki yi ba kuka ba naki bane Hadiza, aure kuma ko da kaca malam Mamman yake auren Salma sai ya sauwaƙe mata ko kuma mu tona masa asiri duniya su san abinda kuka ƙulla ke dashi, wallahi kin ci albarkin ƴaƴanki amma Allah ya sa ni ba zan iya cigaba da zaman aure da k .....".


Saurin taran numfashi Abba ya yi da cewar"A'a Adamu kar ka yanke hukunci cikin fushi daga baya azo ana da-na-sanin da bata da amfani, Salma dai ta zauna a nan shi kuma malam Mamman zamu san yanda zamu yi dashi" .


"Don Allah malam ka yafe min wallahi sharrin sheɗan ne, asiri ya yi min ta yanda duk abinda yazo dashi bana iya musanya masa".
Tsaki Baba ƙarami ya doka tare da taɓe baki ya ce"ai ba yafiyata ya dace ki nema ba na ƴarki da kika so jefa rayuwarta cikin halaka ya dace ki nema". Yana ƙare zancen ya miƙe ya fice ransa a matuƙar ɓace, nauyayyan ajiyar zuciyar da ta tokare mini ƙirjina na saka kallon Umman Salman gabaɗaya sai naji baya isa na wai uwa ce saboda son duniya zata tura ƴar cikinta cikin wannan lamarin?. Abba ya sallame kowa ya watse daren ranar ban rutsa ba saboda tarin tinane-tinanen da suka uzurawa ƙalbina juyi kawai nake yi har aka yi ƙiran assalatu na miƙe nayo alawala nayi sallan.


Ina zaune a bisa sallayan da nayi sallan ina tasbihi da yatsun hannun muryar Salma ya katse ni. A sanyaye take cewa"oh ni kuma salon tawa ƙaddarar kenan duk auren da nayi bana yin dace" Sai da na tausasa amon muryana na ce"Salma kenan ki godewa tunda ke da rabon yin auren ma a cikin ƙaddaranki, ƴan-mata nawa ne suke zaune a gidajen iyayen su babu mai zuwa neman auren?. Komai kiga ga ya sama bawa to dama can Allah ya ƙaddara faruwarsa tun kafin samuwar ruhinsa a baya ƙasa don haka ki miƙawa Allah lamuranki". Kuka ta fashe dashi da sai da na tsorita a taku ɗaya na iso kan katifar da take kai.
"Na'ima zuciyata zafi take yi min idan na tina wannan abun da ya faru, meyasa Umma zata yi min haka?".


"Bata aikata hakan domin bata ƙaunar ki ba Salma. Sai dai ita har zuciyarta hakan tana ganin gata ne tayi miki da tinanin za ki sama hutu a gidan kamar yanda suka yi wa juna alƙawari. Kar ki bar wannan abun ya sama matsuguni a cikin ranki har ki ƙullace mahaifiyarki ko kuma ya hana ki yi mata biyayya".
Kanta kawai ta ɗaga mini tana sauƙe ajiyar zuciya wani na bin wani a haka har ta sama bacci. Kwanaki biyun nan gabaɗaya Baba ƙarami ya ɗaukewa Umman Salma ko gaisuwarta ya daina amsawa balle wanj dogon zancen ya gilma tsakanin su, don da a son ransa ne tun ranar zai sauƙe mata sai dai Hajiya Babba da Abba da suke tausan sa. Tun ranar da Salma tazo gida su Abba suka zauna da malam Mamman tare da warware masa komai ya dubure akan ƙarafi ake yi masa sai da aka yi abin ba daɗi kafin ya sauwaƙewa Salma. Ban taɓa zaton taimakon da nayi na dawo da Salma gida ba zai zame mini matsala ba sai bayan da malam Mamman ya sauwaƙe mata. Mussamman Umman su ta ƙira har ɗaki tana tuhuma ta da zamtowa silar mutuwar auren ƴarta da kuma mussabbin rikici tsakanin ta da mijinta, ranar naci kuka har na godewa rabba sai dai ko Ummata ban sanarwa ba balle Salman.


Ina zaune a sashin Hajiya Babba ina karanta jaridar da na ɗauko a ɗakin yaya Majid, Baba ya shigo gaishe shi nayi tare da yi masa sannu da zuwa cikin girmamawa. Ya amsa mini cikin kulawa yana zaunawa ya ce"karatu ne ake yi?". Kaina na ɗaga masa ya ce"to karanta a bayyane nima naji".
Tiryan-tiryan na karanto masa shafin farko tsaf, yana bina da kallo ya ce"masha Allah, Allah ya ƙara ilmi mai amfani mamana".


"Amin".


"Kin ga shi ilmi yana da daɗi kuma yana ƙarawa mamallakinsa wani daraja na mussamman, kar ki yarda wasu su ruɗe ki ta hanyar ƙawata miki ilmi boko fiye da na addininki wanda zai amfane ki a nan duniya da kuma lahira". Cike da gamsuwa da zancesa na jinjina masa kaina, nasiha ya yi mini sosai har Hajiya Babba ta fito daga wankan da ta shiga ta iske mu. Ban baro sashin ba sai bayan isha'i na yiwa Hajiya Babba sai da na safe.


Asubahin ranar duk wani ahalin gidan a gigice ya yi sa, domin tashin da muka yi da Baba cikin matsanancin jinyar da ko idanunsa baya iya buɗewa bayan ƙalau ya yi sallama da kowa daren jiya ya kwanta. Tun kafin gari ya gama wayewa aka wuce dashi asibiti, taruwa muka yi a tsakar gidan muka yi jumgum domin Abba, Baba ƙarami da kuma yaya Majid ne kaɗai suka kai shi asibitin ba'a je da kowa ba hatta Hajiya Babba tana gida. Kowa da tinanin da yake saƙawa cikin ransa ƙarfe goma ta gota muka jiyo ƙaran tsayiwar mota a ƙofar gidan tunin ƙananan yaran suka ruga a guje suna faɗin ga Baba ya dawo ga Baba ya dawo.


Nurain ne ya fara dawowa yana jan ƙafarsa da ƙyar, Umman su ta tambaye shi lafiya?.
"Umma su Abba ne kawai suka dawo basu dawo da Baban ba" . Jin tabbacin cewar su ɗin ne suka dawo ya sanya mu duk miƙewa zamu leƙa dai-dai nan yaya Majid ya shigo yanayinsa ya sanya kowa shan jinin jikinsa.


"Ke Abdul-majid lafiya ina Baban nakun?". Hajiya Babba ta jefa masa tambayar, muryarsa bata fita sosai ya ce"gashi nan za'a shigo dashi". Yana rufe bakinsa masu ɗauke da makara suna shigowa, har suka ajiye babu wanda ya yi wani motsi mai ƙarfi balle cewa wani abun har Abba da Baba ƙarami suna iso Abba ya ce su kai shi sashin Hajiya Babba.


Ganin duk yawan mu har yanzu babu wanda ya ce wani abun ya sanya Abba cewa"sai dai muyi haƙuri Allah ya yi masa cikawa".


Kuka da salati ne ya gauraye filin tsakar gidan da hakan ya sanya Abba ficewa yana tare hawayen da suka wadaci kurmin idaniyarsa, zama nayi dirshan a ƙasa ina jin zantukan Abban da suke yi mini amsa kuwwa a kunnuwana tamkar a mafarki.


"Innalillahi wa inna alaihir raji'un". Na furta a bayyane ina sakin wani kukan da yazo mini ƙanƙame jikinmu muka yi waje guda ni da Salma muna tsiyayar da hawaye, kafin a kai shi tunin duk sauran yayyen mu da suke daƙunan mazajensu na kusa sun iso gidan ya cika maƙil a sashin Hajiya Babba aka yi masa wanka kayi masa sutura sannan aka fara ƙiran Hajiya Babba da matansa su je su yi masa addu'a, sannan raguwan matan gidan kana muma muka je sosai nake jin kaina ya yi mini wani irn nauyin gaske duk da idanuna sun gane mini shi kwance babu numfashi amma zuciyata ta kasa aminta da cewar ya rasu. Sikenan Babba ya yi tafiyar da babu waiwaye balle dawowa innalillahi wa inna ilaihir raji'un, tabbas lafiya ba ita alamar ba za'a mutu ba domin sam bai yi dogon jinya ba hasalima ya kwanta cikin ƙoshin lafiya da kuzarin jiki.


Nasihar da ya yi mini daren jiya da ya zamto zancen na ƙarshe dashi nake ta tinanowa, Anty Zakiyya da Anty Hajara ne kaɗai basu kalli gawarsa ba domin sai bayan da aka kai shi suka iso kasancewar ba a kusa suke ba.


Sosai gidan ya nutse tamkar waɗanda aka yiwa wahayin shiriya, hatta ƙananan yara sun san anyi rashi a gidan. Zuwa dare hawan jinin Hajiya Babba ya tashi sai da aka sanya mata ƙarin ruwa da wasu allurai na bacci, Goggo Suwaiba da tun kafin jana'ida ta iso tare da mijinta ta zauna tare da ita.
Anty Zakiyya ma da yaya Saif suka zo, washe gari Farouk da Ummin su suka zo basu tafi ba sai da aka yi sadakan uku suka koma suka bar ita Anty Zakiyyan a nan. Har aka yi sadakan bakwai duk dare sai mun haɗu a sashin Hajiya Babba mun karanta al-qur'ani iya abinda ya sawwaƙa tare da addu'o'in neman rahama ga Baba.
Sai da aka yi sati uku da rasuwan Abba ya ce kowacce ta koma ɗakin mijinta domin zaman da aka yi babu abinda yake ƙarawa kullum sai tada hankali da sanya ciwo ga wasu, domin duk haɗuwar da aka yi sai an yi kuka an zubda hawaye haƙiƙa mun yi babban rashin da ba zamu taɓa samun wanda zai maye mana gurbin Baba ba a zuƙatan mu.
Yaya Saifuddeen ne yazo ɗaukar Anty Zakiyya da kansa ya roƙi su Abba akan mu tafi tare tunda ma mun fara lectures hostel ɗin ne dai har yanzu ba'a gyara ba amma an cigaba da karatu. Da ƙyar Abba ya amince don a tsarin gidan mu babu wacce take zuwa gidan yayarta ta zauna haka siddan.


Kwanan mu uku da komawa ranar muna kitchen tare da Anty Zakiyya muna haɗa abincin rana, yaya Saifuddeen ya ƙira ta waya yake sanar da ita zai aiko wani ya karɓa masa wasu takardun da ya mance a ɗaki. Mintuna kaɗan tsakani Farouk ya shigo yake shaidawa Anty Zakiyyan ɗan aiken da yaya Saifuddeen ya aiko yana falo yana jira. Ruwa ta ce dani na kai mishi kafin ta ɗauko masa takardun ɗauka na sanya akan tray na fita kai masa.


Yana tsaye ya juya bayansa ya zubawa hoton Anty Zakiyya da ba yaya Saifuddeen ɗin da suka ɗauka tare cikin murmushi an maƙala jikin bangon falon idanu, sallamar da nayi ya sanya sa waigowa da sauri.


Dam-dam ƙirjina ya buga da ƙarfi babu shiri ba saki tray ɗin dake hannuna ya faɗi nan take ya tarwatse. Mirtsike idanuna na soma yi tare da son tabbatarwa kaina a farke nake ko kuma cikin bacci nake saboda abunda nayi tozali dashi tsaye a gabana.






MATAN AREWA


(Book two)


© Maimunah Tijjani Iyam


_________________________________________




Page 1⃣1⃣9⃣


Kallon kallo muka shiga yiwa junanmu ba tare da mun yi wani kwakwkwaran motsi ba balle furta abinda ke ranka da tsantsar mamaki da kaɗuwa ya danne shi. Har Anty Zakiyya da Farouk suka shigo falon a tare suna tambayar lafiya?, ƙaƙarewa zancen ya yi a bakin Anty Zakiyya ba tare da ta gama furzo shi waje ba ta sauya da faɗin"Yusuf Yusuf kai ne?".
Dai-dai sanda na zube akan gwiwoyina ina jin wani irin azababben kukan da ban san dalilinsa zuwan sa ba a wannan lokacin yana turniƙe mini rai.


"Anty daman kin san shi ne? shine wanda yaya Saif ya aiko ya karɓa masa takardun".


"Na san shi Farouk". Ta faɗa a gajarce tana miƙa masa takardun ya bashi, hannunta ta kama ta miƙar dani tsaye muka bar cikin falon. Ɗakinta muka zarce muna isa na zube akan gwiwoyina ina sakin kukan da ban sama damar yin sa ba, da dukkan ƙarfina nake yi jikina gabaɗaya yana yin wani irin rawa tamkar ana jona mini wutar lantarki. Idanu ta zuba mini tallafe da kuncinta a haka har wasu mintoti suka shuɗe kafin ta furta cikin ƙarfin hali da sauƙe numfashi"Na'ima kiyi haƙuri na san wannan kukan da kike yi baya rasa nasaba da tino irin rayuwarki da kika yi a gaba a cikin gidan Yusuf, ki manta da komai ki tunkari rayuwarki ta gaba kinji?". Kaina kawai na ɗaga mata don na gaza bata amsa da baka ta tare da zuciyata ta yarda da zantukanta akan zan iya mancewa da irin rayuwar da nayi da yaya Yusuf ba. Har izuwa ranar da numfashi zai yi bankwana da gangar jikina a kaini kushewa ba zan taɓa mancewa da yaya Yusuf a cikin rayuwata ba.


Lallashina ta cigaba tayi har na tsagaita na tashi na shiga toilet ɗinta na wanke fuskana, tare muka kuma kitchen ɗin bayan na gyara falon muka kammala girkin. Ranar ba zan ce makaranta ba don haka nayi zama na a ɗaki ina ta fama saƙa da warwara cikin raina, a haka Anty Zakiyya tazo ta tarda ni ta ɗaura da tisar tilawar lallashin da tayi mini tare da labarta mini cewar yaya Saif ya ƙira yana tambayar meya faru don shima Yusuf ɗin ya koma masa a yanayin da ya kasa ganewa amma ta ce dashi babu komai sai ya dawo kawai.


Bisa tilastawan ta na fito na wuce ɗakin Ummi don izuwa lokacin na tabbatar ta tashi daga baccin da ta kwanta bayan mun gama kari, tausa na fara yi mata a hankali muna ɗan hira har lokaci ya ja.
Sai gab da magrib yaya Saif ya dawo tare sa Farouk suka shigo sannu da zuwa nayi musu ina miƙewa izuwa ɗakin da aka mallaka mini a cikin gidan.
Bayan sallan isha'i muna zaune muna cin abinci mu dukka, yaya Saif ya yi gyaran murya tare da cewa"ɗazu me ya faru a gidan nan?".


Ɗage masa ido ɗaya Anty Zakiyya tayi alamar yaushe, muryarsa a kaushashe ya ce"ɗan aiken da na aiko ya kuma min cikin wani yanayin da ban gane masa ba, ya ƙi kuma bani damar da zan tambaye shi".


"Nima na fahimta hakan Yaya Saif domin kamar sun san juna da Na'ima".


Farouk ya faɗa yana tsayar da idanunsa a kaina, ban ɗago kaina ba sai ma ƙara ƙasa da nayi dashi ina jin Ummi tana cewa"wani baƙo aka yi a gidan?". Farouk ɗin ya yi mata bayanin komai duk idanu suka tsura mini cike da son ƙarin bayani, na gaza cewa komai kamar yanda na gaza samun ƙarfin gwiwar ɗago kaina.


Sai Anty Zakiyya ce tayi musu bayanin komai dalla-dalla game da yaya Yusuf ɗin, da alaƙar da ya taɓa shiga tsakanin mu dashi a baya. Bata ɓoye musu komai domin har yanda muka rabu da yanda hukuma suka shiga tsakaninmu babu su babu mu sai da ta sanar dasu.
Numfashi mai nauyi Ummi ta sauƙe muryarta a karye ta ce"sannu Na'ima tabbas dole kiyi kuka dole kiyi kuka, amma rayuwa ce kuma ko wani mutum da nashi salon jarabawan duk abinda aka sanya haƙuri da juriya a cikin tabbas wataran zai wuce har ya zamto tahiri".


Shuru ya yi yana juya cokalin dake hannunsa cikin plate ɗin abincin, yana nazarin zantukan Anty Zakiyyan daki-daki. A hankali ya furta"saki uku a lokaci guda kuma babu wani dalili?".
Cike da takaici gami da jin ciwon abun ta ce"saki uku wallahi kuma har ranar mai kaman ta yau bai ce damu ga laifi guda ɗaya da tayi masa da ya sanya shi yin sakin ba".


"Ba komai rayuwa ce idan da haƙƙinki a kansa Na'imatu in sha Allah sai Allah ya saka miki tun a nan duniya don haka kar ki sanyawa kanki damuwa".


Furcin Ummi kenan masu cike da tausayawarta gare ni kaina na ɗaga mata ina ƙoƙarin mayar da hawayen da suka wadaci koramar idaniyata. Kafin Murya yaya Saif ɗin suka dira a kunnuwana.
"Ba komai haka Allah ya ƙaddara na san ansha faɗa miki kuma mutane da yawa sun faɗa miki abinda ni ma yanzu zan ce dake. Ki yi haƙuri ki ƙara haƙuri tare da miƙa lamuranki ga sarkin da mulkinsa yake kan komai".


"In sha Allah na-na-nagode".


Na faɗa cikin rawar murya da cushewar numfashin da yake tsaya mini a iya ƙirji, tashi nayi na koma ɗaki na kwanta ina jin wani zazzaɓi mai ƙarfi yana lulluɓe ni da nake jin zafinsa har cikin ƙashi da ɓargona.


Da kallo ya bi ta har ta fice daga falon yana sakin ɓoyayyan ajiyar zuciya, Yusuf ɗalibi ne a jami'ar duk da baya ɗaukar su amma yana handle over courses ɗin wani lecturer da ya tafi ƙarin karatu. A yanzu shike riƙe da course ɗin mutum ne mai hazaƙa da mai da hankali

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login