Showing 153001 words to 156000 words out of 171161 words

Chapter 52 - MATAN AREWA BOOK TWO COMPLETE PDF .txt

ƙariso tunin ya haura ɗakin Ummi juyowan da zai yi ita ma Zakiyyan har ta tashi daga wajen. Kansa ya jinjina tare da sakin miskilin murmushi ya fice.


Ina kishingiɗe a ɗakinmu ban san sanda bacci ya ɗauke ni ba, sai ihun Nawwara da ya ratsa har cikin kwanyata naji da ya sanya ni tashi a birkici ina neman faɗuwa daga kan gadon.


"Na'ima ki fito ki fito gobara".


Tun kafin ta gama tunin na diro daga kan gadon ko ɗankwalina dake gefe ban ɗauka ba balle takalmi haka nayo waje. Wuta ne yake ci bal-bal a cikin hostel ɗin kowa ya yi waje ana tsatstsaye yayin da samarin dake wajen suke ɗeban ƙasa suna watsawa kafin motar ƴan kwana-kwana ta iso wajen lokacin wutan ya gama mamaye ko'ina a hostel ɗin, wani baƙin hayaki ya gauraye wajen gabaɗaya.


Ruwa suka shiga fesawa kafin suka samu suka shiga ciki domin dubawa ko akwai wasu da gobarar ta rutsa dasu a ciki, muna zaune gefe guda mun ƙanƙame jikinmu waje guda dasu Nawwara ƙam-ƙam muka haɗe jikinmu waje guda cikin mu gabaɗa babu mai kallabi a kai balle takalmi doguwar rigar da na kwanta da ita a jikina da ita na bayyano waje su kuwa duk fallen zani da t-shirt ɗin riguna ne a jikin su.


Fitowa aka yi da wata jikinta babu komai dangin sutura, ta bushe gami da wani irin ƙandarewa jikinta ya yi baƙi ƙirin ya daddare. Da sauri duk muka runtse idanunmu wajen gabaɗaya ya kuma rikicewa da ihu da kukuruwa, motar clinic da ta iso wajen aka shigar da ita, leccatorin duk sun bayyana a wajen har da cancellor da vice ɗin sa.
Sai da wuta ya fara mutuwa sannan aka fara jiyo kukan jariri a wahalce, ma'aikatan fire service ɗin ne suka ƙara komawa ciki sun ɗau lokaci kafin suka fito ɗauke da jariri sabon haihun da ko cibiya ba'a yanke masa ba. A wahale yake sakin kukan da muryarsa bata fita da kyau numfashinsa yana hawa da sauƙa na fahimci hakan ta yanda ƙirjinsa yake tashi.


Shima motar clinic ɗin aka shiga dashi, ta tagan motar nake hangen yanda likitotin suka rufu a kanta tare da maƙala masa robar numfashi ta oxygen kafin suka figi motar suka fice daga cikin makarantan.
Ficewar motar daga cikin makarantar ya yi dai-dai da shigowar sa cikin makarantar, ko kashe motar bai yi ba ya fito ya nufo inda mutane suka dandazo kutsawa ya yi ta cikin su. Har ya hango Abdul-aziz da wasu malaman tsaye ya nufi wajen su tare da jefa musu tambayar lafiyar?.


"Fire outbreak aka samu a female hostel lamarin har ya runtsa da wata student da kuma jariri an wuce dasu hospital".


"Jariri kuma? jaririn waye?". Ɗage kafaɗarsa Abdul-aziz ya yi alamar bai sa ni ba shima, kama waist ɗinsa ya yi da hannunsa ɗaya yayin da ɗayan kuma ya dafe goshinsa dashi yana taune leɓɓansa kafin ya riƙo hannun Abdul-aziz ɗin suka isa ga ma'aikatan fire services ɗin da suke wajen. Cikin wani irin kiɗima yake faɗin"apart from jariri da wannan student ɗin akwai wasu da lamarin ya rutsa dasu".


"Babu wasu don ko alamar hakan bamu gani ba, budurwar ce kawai sai kuma jaririn da muka samu a cikin ɗakin da muke da tabbatacin ta nan wutar ta fara, an sanya shi cikin akwatin kaya. Da ransa aka fito dashi amma gaskiya babu tabbacin zai cigaba da rayuwa".
Jinjina kansa ya yi ya koma cikin malaman da suke ta jajanta faruwar lamarin, har yanzu muna takure waje guda da su Nawwara sam mun gaza motsawa daga inda muke tsabar firgicin da muke a ciki. Babu abinda aka fitar daga cikin hostel ɗin komai ya ƙone babu ta yanda za'a iya zama a cikin ta domin hatta rufinsa ya zazzago ƙasa. Dole suka sallame mu akan kowa yaje gida har sai lokacin da suka yi settled ɗin komai. Wani mummunan faɗuwar gaba ne ya ziyarce shi tinawa da ya yi da suma a hostel ɗin suke da zama, waige-waige ya soma yi can idanunsa suka sauƙa a kansu suna zaune ƙasan bishiyan da iska yake kaɗara da matuƙar ƙarfi tamkar zai jijjigeta tun daga jijiyarta da ya bazu a cikin ƙasa. Bayyanannen ajiyan zuciya ya sauƙe yana nufo inda suke, jin takun mutum yana nufo mu ya sanya mu ɗago kawunan mu caraf idanunmu suka sarƙafe cikin na juna.


"Are you ok?".


Babu wanda ya amsa mishi a cikin mu, har ma'aikatan clinic ɗin cikin jami'ar suka fara isowa wajen ana ɗeban ɗaliban domin duba lafiyar su, wani ya yi wa hannu ya ƙarisowa wajen cikin sauri sai da ya miƙe daga tsugunan da ya yi ya ce"take them to clinic a duba lafiya su zauna a nan har sai nazo". Cike da girmamawa ya amsa da"ok sir". Muka tashi muka bi shi, sosai ake duba lafiyan ɗalibai mazauna hostel ɗin wasu tsabar firgicin da suka shiga har ƙarin ruwa aka yi musu. Nan muka zauna cikin mu babu mai cewa komai har yamma ta fara kawo kai wata ma'aikaciyar wajen ta shigo ɗakin da muke ta ajiye ledar da ta shigo da ita a gaban mu haɗi da faɗin"ku tashi ku sauya kayan jikinku da waɗannan yana jiran ku a waje".


Dogoyen rigunan abaya ne a ciki muka sauya na jikin mu dasu, sannan muka fito yana cikin mota muka iske shi muka shiga gidan baya ya tada motar muka fice daga cikin makarantar. Har muka isa waya yake yi akan faruwar lamarin da kwamitin da aka kafa domin binciko musabbabin ɓarkewar wutan da kuma samuwar jaririn mai ɓoyayyiyar uwa.
Ina ganin Anty Zakiyya na fashe da wani irin kuka mai ƙarfin da tun ɗazu nake dakon sa, rungume ni tayi tana bubbuga bayana. Shi ya yi musu bayanin abinda ya faru dalla-dalla duk suma suka shiga tashin hankali sai tambayar mu suke yi babu abinda ya same mu.
Sai da muka yi wanka Anty Zakiyya ta kawo mana abinci amma sam mun kasa ci sai da tayi da gaske kana muka ɗan caccakala, daren ranar bamu yi bacci ba ni kam da na kwanta nake tashi a razane. Washe gari Nawwara ta bada lambar kawu Musa a yaya Saif ya ƙira shi ya shaida masa abinda ya faru haka nan ma Nazifa ta bada lambar yaya Amin.


Zuwa yammaci kuwa kawu Musa da yaya Amin suka bayyana a gida, kuka muka yi sosai da ni dasu Nawwara da zasu tafi. Bayan tafiyar su da wasu awanni yaya Saif yake shaida mana budurwan da jaririn gabaɗaya sun rasu, tunda aka sanar dasu Abba abinda ya faru suka ɗaha hankalin su tare da azalzalan cewar nima na taho gida a ranar da ƙyar yaya Saif ya lallashi tare da kwantar musu da hankali bayan ya yi musu alƙawarin da kansa zai sanya Farouk ya kawo ni har gida washe gari.
Wayewar garin ranar da zan tafi suna zaune muna yin kari tare da yaya Farouk da Ummin su tun zuwana take ta faman kwantar mini da hankali, da su Nawwara suka tafi kuwa cewa tayi na dawo ɗakinta da kwana.
Yaya Saif ya yi sallama amsa masa muka yi cikin haɗin baki ya ƙariso ya zauna, damuwar ƙara-ƙaran fuskarsa fahimtar hakan ya sanya Ummi tambayarsa lafiya?. Sai da ya saki sakakken ajiyan zuciya kafin ya ce"Ummi mahaifiyar wannan jaririn ne ta bayyana kan ta".


"Mahaifiyarsa? a ina take me ya kawo jaririn cikin makarantar?".


Kansa ya jinjina kafin ya ɗaura da"ƙwarai kuwa mahaifiyarsa ɗalibar makarantar ce. Da ta yi rainon cikin a cikin hostel ɗin ba tare da kowa ya sani ba har ta haife shi a cikin room ɗin su, ta sanya shi cikin akwatin kayanta ta kunnu wutan ta gudu ba tare da kowa ya gan ta ba sai da taji labarin ya rasu shine tazo ta bayyana kant..". Cak maganan ya tsaya masa saboda zafin da ransa yake yi masa, salati duk muka saka cike da jimamin da al'ajabin lamarin kafin Ummi ta ce"innalillahi wai uwar da ta ɗauki nauyin cikin wata tara a jikinta tayi wahalar naƙuda ne zata aikatawa jaririn da ya faso jikinta ya fito haka?. tabbas duniya tazo ƙarshe".


"Duniyar ta fara bani tsoro Ummi, idan kika ga yarinya za ki yi tsammanin ko ɗan yatsa kika sanya mata a baki ba zata iya taunawa ba balle har ta aikata hakan. Domin ita ce take riƙe da muƙamin Amira ta mssc na jami'ar".


Cikin wani irin yanayin da ya wuce a ƙira shi da na tsoro ko firgici na ce"Sister Sadiya Umar Malik?".
Kansa ya ɗaga mini cike da tabbatarwa yana miƙewa ya haye sama riƙe da kansa da jijiyoyin kan suka bayyana ɓarau-ɓarau bisa goshin sa, da ido Ummi tayi wa Anty Zakiyya alama akan ta bi shi ta tashi ta rufa masa baya.


Gaurayen ajiyar zuciya na sauƙe ina jin abun kamar a mafarki wai Sadiya Umar Malik ɗin da na sani ita ce da aikata wannan aika-aikan. Innalillahi wa inna ilaihir raji'un na furta a cikin raina, duk jami'ar kowa zai shaide ta akan kyawawan halayya da kuma kame mutuncinta a matsayinta ta ɗiya mace. Ƙaryan mutum ya ce ya ganta da shirgar banza kullum cikin dogayen hijabi take har ƙasa da niƙabi ga karatun al-qur'ani a bakinta kamar meye idan ta fara rero shi abin gwanin ban sha'awa da burgewa. Amma wai ita ce da haifan cikin da ba'a san ubansa ba har da yunƙurin kashe rai jaririn da bai san komai ba?. tabbas Allah shine kaɗai masanin abinda yake taskace cikin zuciyoyi.




MATAN AREWA


(Book two)


© Maimunah Tijjani Iyam


_______________________________________________




Page 1⃣1⃣8⃣




Har ƙofar gida ya kai ni ya fito suka gaisa da su Abba da kuma Hajiya Babba, ina shiga sashin mu duk wanda ya tambaye ni abunda da ya faru sai kuka a haka Umma ta fito daga ɗaki ta iske ni. Muka shiga ɗaki rarrashina tayi sosai kafin na tsagaita da kukan da nake yi, daga ni sai suturan dake jikina da kuma wasu da yaya Saif ya saya mini sai hijaban da Anty Zakiyya ta bani su kenan na taho dasu domin komai nawa sun ƙone a gobaran ban tsira da komai ba.
Jin abunda ya faru ya sanya hankaluna mutanen gidan mu gabaɗaya tashi mussamman jin mussabbabin tashin wutar, Umma sosai ta ruɗe da jin zancen haka nan ma Hajiya Babba dasu Abba.


"Yanzu kam ai sai a saduda a gane cewar Annabi ya ƙafu, tun ba'a yi nisa an fara samun irin wannan matsalar ai shi kaɗai ma ya isa zamowa darasi ga mai hankali domin hausawa sun ce gani ga wane ya isa wane tsoron Allah. Wannan bokon tunda ba aikin Allah bane babu lada babu zunubi a haƙura shi haka nan kafin wataran ita ma Na'imar ta ɗauko mana wani abun maganan da ya fi na wannan. Ƴaƴa mata nawa ne wanda suka fi ta nutsuwa da kamewa amma sanadin boko suka zamto watsatstsu ni dai kam ban ga amfanin wannan ilmin nasaran ba".


Furcin Umman Balkisu kenan cike ga gatse da ya sanya ni rusunar da kaina ƙasa ina jin bugun da ƙirjina yake da yake ƙara ƙarfi duk juyin daƙiƙa ɗaya na agogo. Gyaran murya Abba ya yi kafin ya ce"Allah ya kiyaye na gaba ku tashi ku tafi".
Duk miƙewa muka yi muka fice na lura hatta Umma ma ta sake da cigaba da karatuna bayan jin faruwar lamarin, hakan ya sanya ni ƙara tsayiwa tsayin daka wajen miƙa kokena ga Allah.


Sai da na cika kwana biyar cur da dawowa ban leƙa ko kofar gida ba ko yaushe ina ɗaki ko sashin Hajiya Babba. A yinin na shidan ina zaune a falon Hajiya Babba Zainab tayo sallama tare da sanar dani cewar Salma ta aiko don Allah naje yanzu tana buƙatar gani na. Haɗa ido muka yi da Hajiya Babba na ce"lafiya kuwa?".
Kafaɗarta ta ɗage mini alamar ita ma bata sani ba ta juya ta fice daga falon.
"Tashi kije ki menene". Hajiya Babba ta furta cikin sigar bada umarni jikina a sanyaye na miƙe na fice izuwa gidan Salman, tun daga zaure nake gwaɗa sallama har na kutso kai cikin gidan amma babu wanda ya amsa mini. Turus nayi ganin kishiyoyinta biyun suna zaune a tsakar gidan da ƴaƴan su amma kamar basu ji ni ba gaishe su nayi ba tare da sanya ran samun amsawa daga gare su ba na faɗa ɗakin Salma.


Tana zaune kan sallaya alamar yanzu ta iddar da salla, ta zagba tagumi da hannuwa biyu da alaman tayi nisa cikin tinanin da ta faɗa. Ko shigowa ta ɗakin bata lura dashi ba sai da na ƙare mata kallon tsaf duk ta rame ta ƙamjame duk da duk jikin mu huɗun daman ita ce marar jiki sosai amma ta ƙara bushewa tare da yin wani baƙin na mussamman.


Sai da nayi wa kaina mazauni kafin na taɓo ta haɗi da furta kalman sunanta, a firgice ta juyo tozali da tayi da ni ya tilasta mata sakin bayyananniyar ajiyar zuci tana cewa"kin iso Na'ima?".
Kaina na ɗaga mata na ce"na iso lafiya dai ko?". Sai da ta sauƙe gigitaccen ajiyan zuci tana fuskanto ni da kyau ta ce"ba lafiya Na'ima wallahi ina cikin gagarumar matsala a cikin gidan nan, na rasa yanda zan yi na rasa inda zan sanya raina naji sanyi".


"Menene ya faru Salma?". Na faɗa a ruɗe sai da ta miƙe ta rufo ƙofar ɗakin kana ta dawo mazauninta ta zauna tare da zuƙe majinar kukan da tazo mata kafin ta sama sararin cewa"Na'ima Umma ta cutar da ni ta cutar da rayuwarta, nayi mata biyayya na auri malam Mamman ashe akwai wani abun tsakanin su da manufa ta tirsasani auren sa ba bisa son raina ba". Tun na gama ruɗewa na cafko hannunta da duk jikinta yake rawa na ce"ke kin ga tafi kai tsaye ki sanar dani abunda ya faru, wallahi ina ƙara sanya ni cikin duhu ne".


"Umma ta tirsasani auren Malam Mamman ne saboda sun ajiye jarjejeniya a tsakanin su. Wai malaman tsubbunsa ne suka bashi tabbacin idan ya auri bazarawa mai aure ɗaya kuma wacce bata haihu ba ta fita wacce gabaɗaya bata haura shekaru ashirin da biyu da haihuwa ba. Arzikinsa zai dawo sai ya yi sunan da duk sanda ake lissafo hamshaƙai sunansa zai ya fito a na ɗaya ko na biyu matuƙar zai tunda mu'amala da ita ta baya kuma yana ɗebar jinin al'adarta yana kai musu suna sun yi wani tsurƙullen dashi burinsa sai ya cika".


Dole ta tsagaita saboda wani kuka maj matuƙar ƙarfin da ya kubce mata da sake shi da sauti sosai, sosai jikina ya gama mutuwa na gaza cewa da ita komai balle furta mata kalaman lallashi. Sai da ta tsaya do kanta kana ta ɗaura da"sun yi jarjejeniya da Umma kan cewar arzikinsa yana dawowa sai bata kaso mai tsoka, ni kuma zai fifita ni a tsakanin matayensa sai kuma sakar min ragamar gidan sai yanda nayi dashi. Duk watan duniya idan zan yi al'ada shi yake sayo min augudan mata ya tilas min cewar idan nayi amfani da ita na sanya a leda na ajiye sai ya shigo ya ɗauka yake ya yasar, ban sani ba ashe amfani yake yi dashi sai jiya da na gama Allah ya toni asirinsa na fahimci ba yasarwa yake yi amfani yake yi dasu, ko da na mishi magana shine ransa ya ɓaci ya hau gaya min maganguna har ya furta min jarjejeniyar dake tsakanin su da Umma, wai ƙashin tsiya gare ni domin malaminsa ya ce matuƙar ya aiwatar da komai dai-dai ko satikai uku ba za'a rufa ba zai ga buɗi amma ni ina nema wata uku babu alamon arziki sai ma talauci da ƙuncin da yake ƙara yi masa dabaibayi".
Daskarewa nayi a wajen numfashina yana fita wani iri zamewa nayi daga zaman da nayi ina miƙar da ƙafafuna da naji sun yi mini sanyin ƙalau. Shuru ya ɗauki ɗakin na tsawon wasu mintoti kafin nayi ƙarfin jawo numfashi da ƙarfi na fesar.


"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un meyasa ita kuwa Umma duk da ta san wannan abun ta sanya ki dole kika aure sa. Ba ta duba yanda makomar rayuwarki zata kasance ba?. Yanzu ke me kika yanda?".


"Na yanke shawaran komawa gida domin ba zan iya cigaba da zama da mushiriki ba wallahi ba zan iya. Zan tafi ko da kuwa hakan na nufin Umma zata yi fushi dani zan sanar da su Baba komai". Sai da sauƙe ajiyar zuci na ce"gaskiya ko ni ba zan ba ki shawaran cigaba da zama dashi ba domin a addini ya haramta hakan a gare ki, don haka ki tashi muje gida ki sanar da su Abba halin da ake ciki".
Bata musa mini ba don ina hangar tsagwaron son barin gidan a cikin idanunta, miƙewa kawai tayi daman da hijabi a kanta muka fito daga ɗakin. Idanunsu gabaɗaya suka maido kanmu ba mu ce dasu ko kanzil ba muka ɗauki hanyar ficewa muryar da aka yi magana da ita a kausashe ya dakatar damu.


"Ke ina za ki kai ta? da kika fito da ita?. Ke kuma in ce dai kin manta dokar malam a cikin gidan nan ko to wallahi kina sanya ƙafa kika fita ba tare da izninsa ba a bakin aurenki ne".
A fusace Salma ta juyo"sai meye don ya sake ni na ce sai meye?, da cigaba da wannan ƙaddararren auren ai gwara sakin ma don Allah in ya dawo ya aiko min takardata gidanmu mai ɗauke da saki saba'in ba uku ba".


Tana dasa aya ta fige hannuna muka fice daga cikin gidan da matuƙar sauti, zumbur Hajiya Babba ta miƙe ganin yanda muka shigo cikin tashin hankali ga hawaye shaɓe-shaɓe a bisa fuskar Salma. Duk tambayar lafiyar da take jeranta mana bamu amsa mata har muka shigo muka zauna Salma ta saki wani kukan tana faɗawa jikin Hajiya Babba.


Ni nayi mata bayanin komai kamar yanda Salman tayi mini, ta ce maza in je in ƙira yaya Majid na ƙira yazo ta ce ya ƙira su Abba ya sanar dasu tana son ganin su yanzu su dawo gida, ya kuwa aiwatar da umarnin natan nan take.


A tare su Abba suka yo sallama falon Hajiya Babba sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login