Showing 93001 words to 96000 words out of 171161 words

Chapter 32 - MATAN AREWA BOOK TWO COMPLETE PDF .txt

ba, ba zai taɓa mance sallamar ƙarshe da suka yi ba kafin ya yi tafiyar da ta zamto ajalinsa.


Tafiyar da ta sauya akalar rayuwar su gabaɗaya tare da jijjige dukkan sassan da dashen bishiyar farin cikin da ta baza cikin rayuwar su, ta turbuɗe hasken tauraron da ke haske rayuwar su tare da bari su suna lalume a cikin duhu.


Ajiyar numfashi ya sauƙe a karo na barkatai ina cije lips ɗinsa tare da addu'ar Allahu ya ƙara masa ƙarfin gwiwan iya tunkaran dukkan ƙalubalen rayuwarsa da kuma wanda zai ci karo dasu a nan gaba. Ya kawo masa hanyar mafita ya kuma warware masa ƙullin da ya shige masa duhu. Jin numfashin mutum dab kusa da kusa dashi ya sanya shi saurin kai dubansa ga ɓangaren musgutawa ya yi yana ajiye wayar gefensa tare da jingina bayansa jikin kujerar da yake zaune ƙafafunsa ya miƙar akan teburin gilashin dake gabansa idanunsa suna kallon ceiling ɗin falon da ya zamto masa shamaki tsakaninsa da sararin samaniya bai damu da cewa komai ga Abdul-aziz ɗin da ya zuba masa idanu ba illa alama da ya yi masa da hannu akan lafiya.


"Saifuddeen".


Rashin amsawarsa bai dame sa ba sai ma ɗaurawa da ya yi da"Saifuddeen what is wrong with you?, a sanin da nayi maka ban sanka da wasa da aikinka ba but now it almost about two weeks baka shigo school ba menene yake faruwa i call your phone but you refuse to pick ko jikin Hajiyan ne?".


A taƙaice ya furta"Abdul da kazo gaka alamar wani abun ne?, ai lafiya shike ɓoye mutum in da wani abun i will let you known thanks for your caring about me".
Murmushi Abdul-aziz ya saka yana ƙara fuskanto shi da kyau ya ce"Saif kenan hawaye fa na tarar da kai kana yi amma kake ce min babu komai?, bana son takura maka amma sai nake ganin bai kamata muke ɓoyewa junanmu wani abun ba idan sai lokacin da muke cikin farin-ciki kawai za muna kasancewa tare lokacin baƙin-ciki kuma kowa ya yi nasa shi kaɗai ai babu amfanin abokan dake tsakanin mu sannan zaman tare bai yi mana rana ba, don Allah ka sanar dani matsalarka menene yake damun ka Saifuddeen?".


Gauruwan ajiyar numfashi ya fesar yana jin zuciyarsa tamkar zata faso fata da namarsa ta fito waje ta taka rawa tsabar bugawan da take yi masa da ƙarfi-ƙarfi, tauee lips ɗinsa yake yi da ƙarfin gaske tamkar ba jikinsa ba tare da dafe kansa dake matuƙar sarawa. Ko shi ma kansa yana ƙaunar ya ga yana faɗin matsalolinsa koda kuwa ga gudan jininsa ɗaya tilo ne sai dai kash hakan ya gagare shi ga Umminsa kaɗai yake iya buɗe zuciyarsa yake kuma iya zubda hawayensa sosai har ya ji sauƙi a cikin ransa, cikin wani irin zafin nama da kuzari ya cafko hannun Abdul-aziz ya ɗaura a ƙirjinsa dai-dai da yake bugun famfalaƙi muryarsa a shaƙe ya soma faɗin"Abdul-aziz cikin ƙirjin nan nawan akwai damuwa kala daban daban da kalmomin baki sun gaza wajen furta su, indai da gaske ka damu da rayuwata Abdul to kawai ka taya ni da addu'a shi kaɗai nafi buƙata".


Tsoro ne sosai ya dabaibaye Abdul-aziz kansa kawai ya ɗaga masa ya ce" ina yi maka Saif sai dai na ƙara". Sakar masa hannu ya yi ya koma ya jingina da kujeran kansa na kallon sama, sai da ya nutsa ya ce"daman nazo ne muyi magana akan iftila'in da ya faru a gidan gonan ka sai nake ga kamar bai kamata a zubawa abun ido ya tafi a haka kawai ba ba tare da an gudanar da binciki game da faruwar lamarin ba".


"Mun gama maganar nan duk ma'aikatana na yarda dasu mun ɗau tsawon shekaru muma aiki tare bana tinanin wani daga cikin zai ci amanata balle har yaso ganin na tafka babban asara irin wannan".


"Hmm Saifuddeen kenan kana kallon rayuwar mutane ne a bisa yanda taka rayuwar take, don kai ka kasance mutumin kirki kuma na ƙwarai ba kowa bane yake a haka da yawan mutanen da zasu raɓe ka ko kuma su nuna maka tsantsar soyayya da zaka juya baya sune farkon waɗanda zasu fara kawo maka sara babu yarda yanzu balle riƙon amanan da farashinsa ya yi tsadan da ba kowa ne yake iya mallakansa ba".


Sai ce komai ba sai da ya miƙe tsaye ya ce"ni dai na gama maganan nan na barwa Allah komai, zan hau sama na watsa ruwa Umar ya kusa dawowa daga asibiti muyi iftar mu koma wajen Ummi".
Daga haka ya haye upstair ɗin da zai sada shi da ɗakinsa da kallon tausayinsa da ya daɗe a ƙalbinsa Abdul-aziz ya bishi yana jinjina kansa yana juyowa idanunsa suka sauƙa akan Farouk dake tsaye a ƙofar falon yanayin fuskarsa kaɗai ya isa ya tabbatar masa da cewar ya daɗe tsaye a wajen komai ya ji duk abunda suke zantawa. Sai da ya haɗiye miyau kafin ya ce"Farouk yaushe ka iso?".


"Yaya Abdul tun ɗazu na shigo". Ya furta yana ƙarisa shigowa cikin falon kusa dashi ya zauna ya gaishe shi sannan cikin raunanniyar murya ya soma faɗin"naji duk abinda kuka tattauna da yaya Saif nima nayi iya ƙoƙarin akan ya bari a gudanar da bincike amma yana nuna cewar ya barwa Allah komai kuma duk cikin ma'aikatan baya zargin kowa da zai iya cutar da dukiyarsa. Wallahi hankali bai kwanta da cewar wai haka kawai lamarin nan ya faru ba tabbas akwai lauje a cikin naɗin da bamu san dashi ba. Ka taimaka min mu gano wannan gaskiyar tare ba tare da yaya Saif ya san abinda muke ciki ba".


Sosai tausayinsa ya ƙara yin kane-kane cikin zuciyar Abdul-aziz riƙo hannunsa ya yi cikin bashi cikakken tabbaci ya furta"in sha Allah Farouk zamu gano ko menene da iznin Allah kai dai kawai ka cigaba da addu'a".


"Na gode".


Cikin son canja masa yanayin da yake cikin ya ce"akwai kayan iftar da Amira ta haɗo na taho mana dashi yana mota muje mu shigo dashi kafin ya sauƙo".


Tare suka miƙe suka fito suka shigo da kayan suka jere shi a falon kasancewar basu fiye cin abinci akan dinning ba shima Farouk ɗin wanka ya shiga ya yi ya fito a gurguje saboda lokacin salla da ya gabato, Koda Saif ɗin ya fito da niyyar dafa musu tea ya fito don mai aikin Ummi ta daina kwana sai dai tazo ta gyara gidan da safe ta tafi ganin kayan iftar jere ya sanya shi kai duban sa ga Abdul-aziz domin ya san wannan aikin ba na kowa bane face shi, sai dai bai yarda sun haɗa ido ba illa ma maida hankalinsa da ya yi kan latsa wayarsa da suke chart da Farouk duk da suna zaun wajen ɗaya akan yanda zasu ɓullowa lamarin, dabino da fruit kawai suka sha da aak yi ƙiran sallan suka fice sallan magrib.


Basu dawo ba sai da suka jira aka yi sallan tarawi sannan suka dawo gidan, hannu baka hannu ƙwarya Farouk yake cin abincin kamar zai ƙware da hakan ya sanya Saif ɗin da yake juya cokalin a cikin plate ɗin abincin dake gabansa dubansa sosai kafin ya ce"meye haka ne?".
Langwaɓar da kai ya yi ya ce"Yaya Saif wallahi azumin yau ya bani wahala ka kaso kaji yanda nake ji yanzun nan" Bai ce masa komai illa ajiye cokalin hannunsa da ya yi ya motsa ya ɗaura hannunsa saman goshinsa zafi gau miƙewa ya yi ya nufi ɗakinsa ya ɗauko masa maganin zazzaɓi ya dawo sai da ya ɓalla masa sannan ya miƙa masa tare da cup ɗin ruwa. Rau-rau da ido ya yi yana faɗin"ni fa bana jin komai kawai gajiya ne amma babu inda yake min ciwo a jiki ka yarda da ni yaya Saif".


Bai kula shi ba sai ma tsatstsare shi da ido da ya yi yana miƙa masa maganin, kallon Abdul-aziz ya yi da yake murmushi da nufin ya yi masa magana ya ɗage masa kafaɗa alamar babu ruwansa babu yanda ya iya ya karɓa maganin ya sha yana yamutsa fuska.


Suna gama cin abincin suka gyare wajen tare da zuba kwanunkan a motar Abdul-aziz, suka nufi asibiti wajen Ummi tare kamar kp yaushe haka nan suka tarar da ita kwance babu motsi an maƙala mata roban numfashi a hancinta. Sai da suka shafe kusan mintin talatin kafin suka baro asitibin Abdul-aziz ya wuce gidansa kuma suka wuce gidan. Taya mafi tsayin daren su suka yi suna addu'ar samun sauƙi ga Ummin na sun dake kwance ita ba rayayyiya ba ita ba matacciya ba.


MATAN AREWA


(Book two)


© Maimunah Tijjani Iyam


_______________________________




Page 8⃣7⃣


Washe gari kasancewar ranar ƙarshen mako ne bashi da lecture don haka tun safe ya yi shiri suka wuce asibiti wajen Ummin su, sai da ya fara biyawa ta ofishin likitan ya ƙara yi masa bayanin yanayin jikin natan da kullum jiya iya yau babu wani cigaba duk da ruwan rubutun da Anty Fauziyya ta aiko musu tun daga kano ana bata amma babu abinda ya sauya zani.
Tsaf-tsaf ɗakin yake ɗauke da ni'imantaccen ƙamshi mai tafiyar da zuciya da samarwa ruhi nutsuwa, sai dai gare su abin ba hakan yake ba domin sam hakan bai taimakawa wajen sausauta gudun famfalaƙin da zuciyoyin su suke yi.


A tare suka sauƙe gigitaccen ajiyar zuciya mai nauyin gaske, suna sarƙafe hannayensu cikin na juna a haka suka ƙarisa cikin ɗakin kamar ko yaushe suka zauna kusa da ita suna bin ta da kallo sun daɗe a haka kafin Saif ya tashi ya ɗauko ruwan rubutun dake adane cikin ɗan madaidaicin freezern dake cikin ɗakin ya shafa mata a dukkan jikinta yana yi yana jin wani irin zafi a cikin ransa tabbas duk wanda Allah ya ba wa lafiya haƙiƙa ya bashi babban arzikin da kuɗi ba zasu saya masa ita ba koda kuwa zai ƙarar da duk abinda ya mallaka wajen neman ta sai wanda Allah ya ga damar ba wa yake ba wa baka sanin daɗinta har sai kaje kaga waɗanda suke da ƙarancinta.


Lokaci zuwa lokaci Farouk yake duba agogon dake ɗaure a tsintsiyan hannunsa yana ɗan jijjiga ƙafarsa, duk wani motsinsa yana kan idon Saif da yake bim sautin ƙira'an karatun Sheik Muhammad afif da ya karaɗe ɗakin cikin zazzaƙan muryarsa da yake fitar da haƙƙin kowacce kalma yana karato suratul Juma'a.


"Lafiyanka Farouk?".


Saurin sunkuyar da kansa ya yi don gujewa kansa fallasuwar asirinsa kafin ya ce"lafiya ƙalau yaya Saif". Yana rufe bakinsa sallamar Abdul-aziz tana sauƙa a kunnensa ɓoyayyan ajiyar zuciya ya sauƙe yana miƙewa ya bashi kujerar da yake zaune a kai ya koma kusa da Saif ya zauna.
Gaisawa suka yi tare da tambayar su yaya mai jikin?, suka haɗe baki wajen amsa mishi da alhamdulillah, fatan samun ingataccen lafiya mai amfani ya yi mata kafin ya kallo Saif ɗin ya ce"ina son a ƙara min Farouk zai raka ni wani waje".


Kallon ido cikin ido ya yi masa kamar zai yi magana sai kuma ya yi shuru yana lumshe idanunsa, ganin hakan ya sanya Abdul-aziz ɗaurawa da faɗin"no calm down ba wani nisa zamu yi ba Saif please kar kaje a'a".
Sai a sannan ya buɗe lumshashshun idanunsa tare da sauƙe su akan Farouk ɗin da sam ya ƙi yarda da su haɗa ido sai da ya ɗauki daƙiƙun da ba zasu gaza uku ba sannan ya ce"ba komai kuje".


"Yauwa my man godiya nake irin wannan kullen sai ka ce wata mace?, lokacin da zaka yo aure kuma naga yanda zaka yi Saif".


Bai ce masa komai illa mayar da idanunsa da ya yi ya lumshe su, bai damu da son sanin inda zasu je tunda basu faɗa masa babu dalilin da zai sanya ya tambaye su ya dangata hakan da wani abun da ya shafe su tsakanin su su biyun, baya son shishishigi a rayuwarsa da kuma katsalangan kamar yanda shima yake ƙoƙarin kiyaye kansa daga aikata makamancin irim wannan halayyar ga wani.


Ficewa suka yi daga ɗakin bayan Farouk ya gama yi masa godiya, suna isa farfajiyan asibitin ya sauƙe ajiyan zuciya yana dafe ƙirjinsa hararansa Abdul-aziz ya yi yana faɗin"matsoracin banza".


"A'a yaya Abdul ba tsoro bane kawai dai a kiyaye doka ne a zauna lafiya, ganin yaya Saif nake yo tamkar uba a gare ni shiyasa ko da wasa bana son na tsallake umarnin sa gare ni".


Kallonsa kawai Abdul-aziz ya yi yana jinjina maganar tasan a cikin ransa yayin da suke shigewa cikin motar suka bar cikin asibitin suka nufi gidan gonan sai da suka yi nisa Abdul-aziz ya ce"i hope ka ɗauko keys ɗin ko?".


Kansa ya ɗaga masa tana zaro key ɗin daga aljihunsa yama nuna masa, thump up ya yi masa tana faɗin"good. Har suka isa gidan gonan suna tattauna yanda zasu ɓullowa lamarin da addu'an Allah yasa komai ya tafi yanda suka tsara, babu kowa sai mai gadin da suka iske a waje yana gadi wajen sallama suka yi masa ya amsa musu tare da basu wajen zama basu zauna ba suka ce dashi ciki zasu shiga ganin Farouk da tare dashi da kuma sanin wanene shi ɗin ga Saif ya sanya shi barin su suka shiga wajen tsif babu motsi komai sosai Farouk ya ji zuciyarsa ta karaya tunawa da ya yi yanda wajen yake a da ko yaushe cike wajen yake da mutane masu zuwa siyayya a wajen, ba zaka taɓa zuwa ka tarar da babu mutane ba sai gashi yau kusan kwanaki sama da goma sha biyar ba'a buɗe shi ba tabbas babu wanda ya san mai gobe zata haifar kamar yanda Allah shi kaɗai ua barwa kansa masanin gaibu.


Riƙo hannunsa Abdul-aziz ya yi yana jefan sa da kallon dake cike da ƙarin ƙarfin gwiwa, keys ɗin da ya ɗauko daga ɗakin Saif ɗin suka sanya suka buɗe wajen suka shiga lungu-lungu suke bi suna bincikawa da kuma ofishoshin ma'aikatan wajen sun daɗe suna dube-dube amma basu kai ga samun komai ba. Riƙe kugunsa Farouk ya yi da hannunsa na dama yayin da hagunsa yake yarshe gumin da ya kwanta masa a saman goshi ya ce"yaya Abdul bamu sama komai ba fa".


"Haka ne Farouk amma mu cigaba da dubawa mu duba office ɗin manager".


Turus Farouk ya yi kafin ya furta"Bana jin samu sama komai a office ɗin Habib domim duk wajen nan babu wanda yaya Saif yafi yarda dashi sama dashi komai tare suke yin sa". Dafa kafaɗarsa Abdul-aziz ya yi"Farouk duniyar ta canja wani lokacin ana tunanin wuta a maƙera sai ta kunno kai a masaƙa don haka muje mu duba". Ba don yana da yaƙinin zasu sama wani abun a cikin ofishin ba Farouk ya bi bayan shi cikin keys ɗin suka sama na ofishin suka buɗe suka shiga.


Duddubawa suka fara yi ko'ina hatta drawers ɗin dake jikin teburin basu kai ga samun komai ba ko'ina sun hargitsa shi iska mai ɗumi Farouk ya fesar daga bakinsa haɗi da cewar"you see it ko yaya Abdul daman na gaya maka ba zamu sama komai ba a nan, da zamu koma waje mu ƙara dubawa ko Allah zai sa mu da ce".
Shima Abdul-aziz ɗin numfashi ya saka ya ce"mu dai sake dubawa".


Hakan suka cigaba da yi har izuwa lokacin da Farouk ya ci kato da wani ambulan buɗewa ya yi hotunan da suke ciki suka zube ƙasa cak ya tsaya ya kasa gaba balle baya yana nuna hoton Mina dake wajen da hannunsa, fahimtar akwai wani matsalan ya sanya Abdul-aziz isowa wajen ya tsuguna tare da ɗaukar hoton yana kallo cike da son ƙarin bayani yake faɗin"who is she?, meye razana ka?".


"Yaya Abdul Mina ce fa ƴar-uwarmu baka san ta ba yayata ce ta wajen Maama".


"To meya kawo hotunta nan?, sannan meye haɗin ta da Habib da har hotunta ya sama matsuguni a ofishinsa?".


A jere ya jefa masa tambayoyin da tare da bashi damar amsa na farkon ba balle mai biye mata, ɗage masa kafaɗarsa ya yi alamar bai sa ni ba sannan ya ce"zamu zaƙulo wannan daga baya yanzu dai mu gama abinda ya kawo mu tukunna".
Duba ofishin suka ci gaba da yi har sai da suka gaji basu ga komai ba da hakan ya sanya Farouk cewar"yaya Abdul inga muje kawai mu duba wani wajen nan kam dai babu komai".


Har sun kai ga ƙofar ficewa Abdul-aziz ya dawo da baya duk tambayar da Farouk yake yi masa na lafiya bai amsa ba illa ƙara nufar bayan ƙofar da ya yi dustbin ɗin dake wajen ya zazzage ta tas tare da tsugunawa ya ɗauki kwalban da ta faɗo daga cikin ya sanya a hancinsa yana jinjina da sauri ya ja da baya yana ɗan jujjuga kwalban a hannunsa yana karanta rubutun jiki.


"Menene wannan?".


"Fiya fiya ce Farouk".


Ya faɗa yana miƙewa tare da miƙa masa kwalba, jikinsa na ɓari ya karɓa yana karanta rubutun jikin kwalban tabbas fiya fiya ce sai dai meya kawo ta nan kuma waya shigo da ita?. Tambayoyin da bashi da amsar su kenan cikin saurin Abdul-aziz ya jawo shi daga cikin ofishin tare da jawo ƙofar ya rufe da key suka fice daga wajen har suka isa wajen mai gadin da suka baro bai saki hannunsa ba.


Sai da suka zauna akan bencin dake wajen sannan Abdul-aziz ya fuskanto mai gadin haɗi da faɗin"Baba tambaya ce zan maka kuma don Allah ina gama ka da girman wanda rai da rayuwarka yake hannunsa a faɗa min gaskiyar abinda ka sani game da tambayar tawan".


"In sha Allah zan sanar da kai mecece tambayar takan yaro?".


Gyara zamansa kan bencin Abdul-aziz ya yi kafin ya ce"ranar da wannan iftila'in ya faru a cikin gidan gonan nan kaso aiki".


"Tabbas nazo aiki domin har yallaɓai ma ya iso wajen ina nan".


Gyaɗa kansa ya yi ya ce"Good akwai wani baƙon fuskan da ya shigo wajen wanda baka yarda dashi ba, kuma dai ka lura cewar ba siyayya bace ta kawo shi?". Shuru ya yi alamar yana nazarin wani abun sai can ya ce"gaskiya ba zan iya tinawa ba domin ko yaushe wajen nan cike da yake da mutane masu shiga da fita to ba zan iya riƙe fuskokin su ba yaro".


Dafe kansa Farouk da tun ɗazun bai ce komai ba ya yi, da hakan ya sanya Abdul-aziz ɗaura hannunsa akan kafaɗarsa"calm down Farouk".

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login