Showing 162001 words to 165000 words out of 171161 words
Chapter 55 - MATAN AREWA BOOK TWO COMPLETE PDF .txt
murya ya furta sunana na amsa masa a sanyaye ya ce na matso gabansa na ja jikina na matso gab dashi.
"Uwata menene matsayina a wajen ki?".
Cike da rashin fahimta na ce"Abba kai mahaifina ne".
"Kin yarda soyayyar da nake miki ba zai taɓa sanya ni na miki mummunan zaɓi ba a rayuwarki?". Kaina na ɗaga masa domin gabaɗaya jikina ya gama mutuwa murus.
"Mamana ba zamu taɓa cutar dake ba kuma ba zamu taɓa zaɓar miki abinda zai cutar dake ba. Ke matar aure ce yau kuma yanzu za'a kai ki ɗakin mijinki". Ban ƙara fahimtar komai ba daga tarin zantukan da suka ɗaura dashi, ban motsa daga inda nake ba har Baba ƙarami ya taso ya kamo hannuna gami da miƙar danj tsaye ya ɗaura mini alkabba akan hijabin dake jikina tare da dafa goshina bakinsa na ƙurawa ido cike da son fahimtar abinda yake furtawa har Goggo Suwaiba ta kamo hannuna muka fita.
Sashinmu muka koma tana riƙe da ni domin na gaza sarrafa kaina bin ta kawai nake yi duk inda tayi dani, ɗakin Ummata ta kai ni nan ma na kasa cewa komai kowa idanunsa a kaina haka aka fice dani aka sanya a motar tare da Goggo Suwaiba da Anty Zakiyya.
A hankali bugun da ƙirjina yake yi a raunane yake ƙara yin ƙasa, zuciyata tana yi mini wani irin zafi mai soya tsayiwar motar ya yi dai-dai da tsayiwae bugun ƙirjina na wucen gadi numfashina ya fita da wani irin sauri. Hannuna suka kamo suka fito dani daga cikin motar kamar gawa bana jiya komai basu dire ni ko ina sai cikin ɗaki duk da ina daga zaune amma ina jin jirin da yake kwasa ta kamar zan zube ƙasa.
"Anya zamu tafi mu barta haka kuwa duba da yanayin kiɗimar da take ciki?, wallahi ni kam tsoro nake ji".
Iya abinda kunnuwana suka yi nasarar jiyo mini kenan da na kasa tantance wanda ya yi zancen tsakanin Goggo Suwaiba da kuma Anty Zakiyya. Bana iya cewa komai haka nan na gaza zubar da koda ɗigon hawaye ne daga idona illa bin su da nake yi da ido kamar sukuwa, ji nake yi kamar mafarki nake yi bacci nake yi ko kuma a farke nake?. Shine abinda na gaza ganewa.
Jin shigowar mutum gidan ya sanya su miƙewa da sauri suna haɗe baki wajen sakin hamdala Goggo Suwaiba ta cike a hanzarce, ita kuma Anty Zakiyya ta dawo ta zauna kusa danj tare da riƙo hannuna gam cikin nata tana zancen da bana fahimtar komai sai dai motsar da leɓɓanta suke yi kawai na ƙurawa idanu. Har Goggo Suwaiba ta dawp ban motsa ba suka fice daga ɗakin Anty Zakiyya tana tare ƙwallar da suka ciko mata ido.
Kamar jira nake yi su fita, suna fita na saki wanj gigitaccen kuka mai uban sauti. Numfashina yana hawa da sauƙa da ƙyar nake iya fesar dashi ƙirjina ya yi mini nauyi tare da harbawa da ƙarfin tamkar zai ɓalle allon ƙirjin ya bayyano waje. Raina yana mini zafi kamar garwashin dake ƙasan tukuban tsire, jin fitar numfashin mutum a hankali ya sani ɗago rikiɗaɗɗun idanun da sauri. Babu shiri na miƙe tsaye ƙam ina nuna shi da ƴatsa cikin rawar baki da na jiki na ce"Yu-yu-yu-yu Yusuf".
Rashin kuzari da ƙarfin da bana ji a jikina da jirin da yake ɗeba na ya sa ni yin baya lu zan faɗi, ya tashi da sauri zai tare ni dafe fuskan gadon da nake kusa dashi nayi na daka matsa tsawa.
"Meya kawo ka nan?, meyasa ba zaka bar rayuwata na huta bane don Allah?. Meyasa ka zamto marar tausayi a gare ni Yusuf?". Na ƙare zancen cikin matuƙar ɗaga murya tare da dafe kaina.
"Na'ima akwai wani dokar da ya hana miji zuwa inda matarsa nake?". Take na wartsake don dole na watsa masa idona kamar wacce ta rasa hankalinta nake faɗin"waye matarka nakan?, wallahi ba zan taɓa iya kuma zaman aure da kai ba nayi a baya kuma na gama. Bana sonka Yusuf wallahi bana sonka idan aka tilasta mini zama da kai zan iya kashe kain...". Ban ƙarisa ba naji takufan hannunsa ya rufe mini bakina ruf, ƙoƙarin ture shi na fara yi amma na kasa saboda bani da ƙarfin yin hakan zaunar dani ya yi amma yana sake ni na kuma miƙewa duk da jirin da nake ji.
"Ki nutsu ki zauna nayi miki bayanin komai".
"Babu wani bayanin da zaka yi mini Yusuf, idan ma kaine mijin da su Abba suka furta mini to wallahi bana sonka bana sonka ba zan zauna da kai ba".
Hawaye na gani a zahiri suna fita daga idanunsa suna wanke masa fuska ya kafe ni da ido, saurin kawar da nawa nayi don bana ma son na kalle shi balle tausayinsa ya shige ni.
"Bakya sona Na'ima kin tabbata?".
Ba tare da tinanin komai ba kaina tsaye na ce"bana sonka kuma ba zan taɓa zaman aure da kai ba gidan mu zan tafi yanzu ba sai gobe ba". Ina gama faɗin hakan na fara ƙoƙarin fita ya tashi da sauri ya tare ture shi na fara yi amma ya riƙe ni gam, ya dawo dani ya zaunar ya riƙe hannuna don kar na miƙe hawayen da suke fita daga idonsa suna sauƙa a saman fuskana ya ce"kiyi haƙuri gobe da kaina zan kai ki gidan kinji?". Maimakon na bashi amsa sai ma wani kukan na tuntsire dashi jikina ya kuma ɗaukar rawa da zafi, sakar mini hannu ya yi ya zare mini alkabban dake jikina.
Cikin kukan da ya ci ƙarfina na ce"kayi alƙawari?". Kansa ya ɗaga mini wasu sabbin hawayen suna ƙara tsiyaya daga idonsa, ban san meyasa ko kaɗan ban ji ɗigon tausayinsa a cikin raina ba balle na rangwamta masa.
MATAN AREWA
(Book two)
© Maimunah Tijjani Iyam
__________________________________________
Page 1⃣2⃣0⃣
Ban runtsa ba har aka yi ƙiran assalatun farkon, ya shigo ɗakin da nufin tashi na ya iske ni zaune bisa gadon fuskarta ta kumbura tsumtum idanuwana kamar zasu faɗo ƙasa tsabar girman da suka yi. Ciwon kan da ya uzira mini har yanzun ya ƙi bari na na huta, a zaune na kwana don ji nake kamar idan na kwanta zai iya shigowa ɗakin abinda bana ƙauna kenan na ganshi kusa dani wani zafi nake ji da ƙuna cikin raina, duk lokacin da na ɗaura idona akan fuskarsa sai na tino rayuwar da muka yi a baya, sai na tino yanda ya damƙa mini takardan sakina a lokacin da ban taɓa tsammani balle zato ba ba laifin tsaye balle na zaune.
"Kina zauna ba ki kwanta ba?". Naji muryarsa da suka yiwa ƙofofin kunnuwana diran mikiya sun katse mini hanzari, kaina kawai na ɗaga masa don gabaɗaya jikina ciwo yake yi mini.
Zama ya yi kusa cikin taushin murya ya ce"Na'ima meyasa kike son cutar da kanki, dubi yanda fuskarki ta koma ki dubi girman Allah ki bani dama nayi miki bayanin komai. Wallahi daren jiya sam ban iya runtsawa ba".
"Babu wani daman da zan baka Yusuf wallahi zama ya ƙare tsakanina da kai, ko da kuwa daga ni sai kai ne muka rage mace da namiji a duniya babu aure a tsakanin mu. Ko ka manta adadin sakin da aka yi mini ne?, ko kuma baka cikin hankalinka ne?".
Bai amsa mini ba illa duƙar da kansa ƙasa da ya yi na wasu mintoti, tsaki na saka a raina ina jin wani takaici na mussamman na kama mini raina.
Ganin har yanzu bai yi magana ba ya sani katse shurun da faɗin"ka cika alƙawarin da kayi mini na mayar dani gida". Sai a sannan ya ɗago idanunsa cike taf da ƙwalla ban yarda mun haɗa ido dashi ba ya ce"ba komai tunda hakan kika zaɓa zan yi yanda kike so ko don farin-cikinki, ki gyara jikinki bari naje salla na dawo sai na kai ki".
Kaina na ɗaga masa wasu sabbin hawayen suna rige-rigen fita daga idona yana fita na kwantar da kaina a kan matashin dake gefena ina reron kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro. Ji nake yi kamar nayi tsuntsuwa na fire na ganni a gidanmu na faɗa jikin Umma ko zan ji sanyi a raina, na kuma sanar dasu ko idanuna suke mini gizo domin malam Yusuf na tarar a matsayin mijin da suka ce dani sun yi mini.
Sosai nayi kukan sai da naji numfashi yana cukurkuɗewa waje guda, na tashi ina dafa gini saboda matsanancin jirin da nake ji na shiga wata ƙofa dake cikin ɗakin da nake kyautata zaton cewar banɗaki ne, da ƙyar na kammala alwalan saboda sanyin ruwan da yake ratsa ni na fito na yi sallan.
Har ya dawo ina zaune a wajen ina ganin sa na miƙe da sauri don na ƙagu na bar gidan, da da lafiyana kuma da kuɗi a hannuna da ba zan tsaya jiran sa ba zan yi tafiyata. Sai da ya kalle ni tsaf ya jinjina kansa ya yi mini alama da hannu akan na fito mu tafi har na riga shi ficewa daga cikin gidan, lokacin da sanyi asubahi don gari bai gama wayewa ba.
Dai-dai isan mu ƙofar gidan dai-dai lokacin ake fitowa daga masallaci, yaya Majid na fara hangowa riƙe da hannh Nurain suna nufo gidan ganin mu ya sanya shi jan baya kafin ya iso da sauri yana tambayar sa lafiya?. Ban tsaya naji amsar da ya bashi ba domin tunin na sauƙa daga kan mashin ɗin na ruga cikin gidan da guda tare da fashewa da wani kukan.
Ƴan bikin da basu gama watsewa ba na iske suna kwashe shimfiɗun da suka yi da suka kwana a waje, duk suka zubo mini na jiyamun su. Anty Maimuna ce ta fara isowa gare ni tare da tambayar dalilin fitowa ta a irin wannan lokacin, maimakon na bata amsa sai ma ƙara ƙarfin kukan da nake yi nayi na faɗa jikinta jikina gabaɗaya yana rawa tamkar ana jona mini mazari.
Jan hannuna tayi ta wuce dani sashin Hajiya Babba da yake da sauƙin mutane Goggo Suwaiba da Goggo Jummai kaɗai muka iske sun iddar da sallan kenan. Suma idonu suka tsura mini suna haɗe baki wajen faɗin lafiya.
Wani kukan na kuma saka kamar zan shiɗe Hajiya Babba gabaɗaya ta gama ruɗewa ta ja hannuna izuwa ɗakinta ta zaunar dani, idanunta a kaina take faɗin"Na'imatu lafiya kika dawo gida a wannan lokacin ina shi mijin nakin?".
"Hajiya Babba wallahi ba zan iya zama dashi ba, Yusuf ne fa Yusuf ɗin da ya yi min saki uku kuke son na koma gare shi". Da mamakina sai na ga ta saki murmushi saɓanin ruɗun da nake zaton zai ƙara mamaye ta. Sai da ta riƙo hannuna ta ce"Na'imatu har yanzu akwai aure tsakanin ku da Yusuf". Kallo na watsa mata da ya sanya ta ɗaurawa da"ki share hawayenki kafin iyayenku maza su shigo za ki ji bayanin komai". Ba don na yarda da abinda ta faɗa ba nayi shuru ina sauƙe numfashi dai-dai lokacin da Umma ta shigo ɗakin kamar an jefo ta. Idanuna taf da wasu ƙwalla na tashi na faɗa jikinta a hankali take bugguga bayana cikin sigar rarrashi da lallashi yayin da Hajiya Babba take yi mata bayanin komai kamar yanda nayi mata. Nauyayyan ajiyan zuciya ta sauƙe daman ta san za'a rina wai an sace zanin mahaukaciya wannan dalilin ya sanya tun farko ba ta kasa yin mubaya'a akan ƙudurin su Abba na cewar sai bayan an gama komai za'a sanar mata.
Da ƙyar ta lallashe ni na tsagaita da kukan ta ce dani naje nayi kwanta, nayi tare da sauya wasu kayan ta bani maganin zazzaɓi na sha na kwanta. Ina jin muryar Anty Zakiyya a falon Hajiya Babban zata shigo ɗakin nayi maza na runtse idanuna kamar mai bacci don bana ƙaunar ganin kowa yanzu balle yin wasu maganganun, kwakwalwata ya ɗauki zafi kaina yana juya mini zuciyata tana harbawa fiye da kima a kimiyyance. Raina cike da tinanin dalilin rashin tsintar firgici da zallan mamaki akan fuskokin Hajiya Babba da Umma, sanda suka ji cewar Yusuf ne mijina a yanzu. Haka ta ƙarishi zaman ta ta fice ina jin wasu baƙin son ganin kwakwaf suna shigowa yiwa Hajiya Babba sallaman zasu tafi tare da tambayarta lafiya amaryar da aka kai ta ɗakin miji a daren jiya wayewar gari ta dawo gida.
Sai da rana ta fito tar Goggo Jummai ta shigo ta ajiye mini abinci, sai da ta matsa mini nayi cokali biyu na ture kwanon gefe. Muna zaune tare da ita Goggo Suwaiba ta ɗago labule ta ce nazo su Abba na buƙatar gani na, sai da ta jira ni na sanya hijabina ta riƙe ni har cikin falon saboda har yanzun da na miƙe nake jin wani jiri na walagigi dani.
Can gefe na takure ta gefen ido nake ƙarewa duk mutanen falon kallo, Abba, Baba ƙarami da kawun malam Yusuf kawu Gambo ne zaune a kujera guda gefen su kuwa Hajiya Babba ce sai kuma Ummata da su Goggo da muka shigo tare dasu. Daga gefen su yaya Majid ne zaune da Yusuf ɗin da ya sunkuyar da kansa sai kuma Yaya Saifuddeen, malam Abdul-aziz da kuma Farouk da suka miƙe zasu fice Hajiya Babba ta komar dasu da cewar suma yanzu sun zama ƴan gida.
"Mamana shin ashe ni ban isa dake ba balle nayi miki umarni ki bi shi?". Furcin Abba kenan da suka daki kwanyata na jijjiga masa kaina alamar a'a wasu hawayen suna ƙoƙarin zirarowa daga idaniyata. Ya ɗaura da faɗin"to meyasa kika kasa yi mana biyayya akan wannan?, meyasa kika tadawa mijinki hankali a daren farko da kika koma ɗakinsa?, ina tarbiyyan da muka ba ki Na'imatu?".
"Abba Yusuf ya sake ni fa saki uku". Na faɗa hawayen suna sauƙa daga idona a hankali murmushi ya yi cikin taushin murya ya fara warware mini zare da abawa. Ji nayi numfashina ya tsaya na wucen gadi idanuna suka kafe akan malam Yusuf ba tare da na tina da cewar ina gaban su Abba, hawayen da nake yi ma suka gagare ni yanzu na shiga kokuwa da numfashina da ya koma garkewa a ƙirji.
Sai da Goggo Jummai ta ɗebo ruwa ta shafa mini a fuska sannan na saki wani gauron ajiyan zuciya mai matuƙar ƙarfi gami da sauti.
Nasiha Kawu Gambo ya ɗaura da yi mini tare da nuna mini halaccin komawa ta gidan malam Yusuf don har yanzun shi mijina ne na sunna, ya kuma bani haƙurin cewae shi ya roƙi su Abba akan kar a sanar dani tun farko haka nan ma a nasu ɓangaren babu wanda ya sani sai yaya Auwal ita ma Bintan sai jiya da aka kai ni yaje takanas ta kano da kansa yake faɗa mata, tare da ƙara jaddada mata ta fita daga harkan gidan Yusuf da Auwal.
"Ki kwantar da hankalinki Mamana ki nema aljannarki a gidan mijinki, ki cire komai daga ranki kiyi masa biyayya dai-dai gwargwadon iyawarki. Bana son na ƙara jin wani abu makamancin abunda ta faru yanzu ya ƙara maimata kansa, ki sani idan kika faranta ran mijinki mutuncinmu ne zai ƙaru a idanunsa kuma mu kika daraja, haka nan a duk lokacin da kika munana masa to za ki sanya masa zargi da wasiwasi akan tarbiyan da muka ba ki da ya kuma fara shakkun wacce ya aura. Ki yiwa mijinki biyayya ki bi mijinki sau da ƙafa kar naji kar na gani ranar da zai kawo ƙaran ki gidan nan".
Zantukan Baba ƙarami kenan da suka ratsa dukkan gaɓoɓin jikina, haka suka cigaba da yi mini nasihohi tare da nusar dano halaccin aurenmu a musulunce. Tabbas nima kaina nasan duk sakin da aka yi shi cikin maye ko kuma wanda ya furta baya cikin hayyacinsa ko kuma aka tilasta sa walau uba ko uwa. To ko ya furta sakin bai inganta ma kuma auren su na nan babu ta inda ya sama tangarɗa.
Numfashina yana fita sama-sama muka koma ɗakin Umma nan muka tarar da Anty Zakiyya ta zagba tagumi, ta bi ni da kallo har na zauna ina dafe goshina da nake jin ciwon kai matsananci.
Dafa kafaɗana Umma tayi tare da sausauta amon muryanta ta soma faɗin"ki yi haƙuri Na'ima ba'a fushi da yin Allah, yanda ya tsara haka kowa zai rungume shi. Ki koma ɗakin mijinki tunda har yanzun yana son ki duba da irin damuwar da ya shiga bayan abinda ya faru tsakanin ku".
"Umma ko yana so Anty Binta ai bata sona kuma basa tsallake umarninta, idan har zata iya sanya shi ya rubuta mini takardan saki bayan ta gusar masa da hankali. To yanzun ma babu amfanin komawa ta don zuciyar da tsana da ƙiyya ya kafu a cikinta zai yi juya wannan tsanar ta rikiɗe ta juya soyayya, ki taya ni roƙon su Abba a ƙarba mini takardana kawai daga wajen Yusuf" .
"Ki yi wa su Abba biyayya ko da kuwa hakan ya saɓawa zabin ranki, Yusuf yana sonki kowa ya shaida hakan domin da Saifuddeen suka fara zantawa kuma shi ya kawo zancen ga su Abba. Wallahi sai kin tausaya masa a lokacin idan kika gan shi soyayyarki ta na neman zautar dashi. Tunda har ya iya faɗin wannan sirrin yanzu kuma kowa ya sani to na tabbatar ita dole ta saduda ta rungumi ƙaddara ko bata so ki ba bata isa ta cutar dake ba, ki manta baya Na'ima". Shuru nayi ina sauraron nasihohin nasun har suka kammala Umma ta kawo mini kunnu sai da ta sanya ni a gaba sannan na sha, su Abba suka je na fito na bi mijina mu tafi duk kunya da kawaicin Umma sai da ta ture shi gefe guda ta ce su bar ni ko zuwa gobe idan na dawo hayyacina sai na koma, amma suka nuna sam basu san zancen ba dole na fito zan tafi tabbas na hange tausayina shimfiɗe a fuskokin dukkan matan gidanmu mussamman Daada da Hajiya da suke ta lallashina. Haka muka koma kamar yanda muka zo muna isa ana ƙiran sallan asr sai da ya buɗe mini gidan na shiga ya ce dani za shi masallaci amma