Showing 90001 words to 93000 words out of 171161 words
Chapter 31 - MATAN AREWA BOOK TWO COMPLETE PDF .txt
gaisawa.
Muna zaune ƙarƙashin sololin da wajen yake ƙarancin hayaniya muna karatun, kamar an ce mini Na'ima ɗaga kan ki ai kuwa ina ɗagowan da zan yi idanuna suka sauƙa akan mutumin dake tafe yana waya duk da daga nisa idanuna suke gane mini shi amma ina da tabbaci da yaƙinin shi ɗin ba zai yi mini gizo a bisa idaniyata ba. Zumbur na miƙe tamkar wacce aka tsikarawa matsilli ina nuna shi da hannuna da yake rawa kamar mazari na buɗe baki da nufin furta sunansa hayaniyar da suka yi wa ƙofofin kunnuwana diran mikiya da yake kusanto wajen da muke ya rufe mini baki.
Duk kai duban mu muka ga ina hayaniyar take tashi juyawan da nayi ya ɓace mini ɓar a idaniyana waige na fara yi da nufin ko zan ƙara ganinsa sai dai babu shi balle alamunsa ko mai kama dashi ban gani. Caraf Nazifa ta riƙo hannuna muka fara tafiya inda mutane suka cika ta cikinsu muke kutsawa har sai da muka iso gaba securities damƙe a wajen wani dattijo a cikin su da ya fi musu girman shekaru kamar yanda yanayinsa ya nuna ya fara magana cikin tsantsan takaicin da yake bayyane a cikin muryansa"Innalillahi wa inna ilahiri raji'un wannan wani iriyar musifa ce take ƙoƙarin cinye mana al'umma?, iyayenku sun turo ku domin su sama ilmi su sama wasu abun da zaku iya taimakon rayuwarku har da wanda yake kusa daku amma sakayyar da zaku yi musu kenan da daɗi da babu daɗi zasu hana bakunan su cin mai daɗi su turo muku ku ku ci amma duk hakan bai isa ya sanya tausayinsu yaɗuwa a cikin zuƙatanku ba, ke yanzu me kuke yi a cikin daren nan kuma a wannan wajen?".
Sai a lokacin idanuna suka sauƙa akan matashiyar budurwan da e yashe a ƙasa cikin zungumemen hijabin da ya rufe mata dukkan jikinta sai dai ya zame daga kanta da hakan ya bayyanar da tulin gashin kantin da aka yarfa mata ƙananun kitso dashi, gefe guda kuwa wani saurayi ne riƙe a hannun ragowar securities ɗin rigarsa a hannunsa jikinsa gabaɗaya rawa yake ga hawayen da yake yi shame-shame da ko ita macen ba ta yi shi ba domin idanunta ƙar kamar na soyayyar kifi.
"Ba tambayan ku ake yi ba meye kuke yi a cikin nan?".
Wani daga cikin securities ɗin ya kuma doka musu tsawa, a dake ba tare da wani tsoro va ta ce"hira muke yi".
"Hirar ce ba zaku yi ta da rana ba sai cikin wannan daren kuma ku rabewa jama'a ku zo nan? ke ba akansa aka same ki ba?". Ba ta ce komai ba sai ma juyar da kanta da tayi jinjina kansa security ɗin ya yi yana kuma faɗin"tunda naga ba ki da kunya za mu miƙa ku ga hukumar makaranta a ƙira iyayenki a sanar dasu abinda kike yi".
Zubewa saurayin ya yi tare da riƙo da ƙafar security ɗin cikin kuka yake faɗin"Don Allah kuyi haƙuri wallahi ni kam ban taɓa yi ba ita ta jawo ni ita ta koya min a kanta na fara yi, kuyi min afuwa ku barni nayi tafiya ta wallahi maraya ne ni ni kaɗai ne a wajen uwa jin wannan mummunan zancen zai iya yin sanadinyar raba ruhinta da gangar jikinta don Allah kuyi min rai".
Shure sa security ɗin ya yi da ƙafarsa ya faɗi suka hau dukansa ta ko'ina cikin wani irin hanzari, karsashi game da ƙarfin hali budurwan ta miƙe ta fara ture security ɗin tana hana su dukan shi basu kaɗai ba dukkan wani wanda yake tsaye a wajen ya yi mamakinta da kuma irin bushewar da zuciyar dake kwance ƙasan ƙirjinta ya yi, hankaɗe ɗayan tayi cikin maida numfashi take faɗin"ku kyale shi ya ishe ku haka nan ku ya taɓa ko kuma ni?, ince dai inma lalatan ne ai ni ya lalata ko to ku bar m...".
Tsif tayi saboda wani wawan marin da aka sauƙe mata ta gefen ɓarin fuskarta ta hagu da bata tsammani balle zatonsa ba, kowa ya zuba ida cike da zaƙuwar ganin wanda ya yi marin nikam mutuwar tsaye nayi gam ganin malam Yusuf tsaye a wajen take bugun ƙirjina ya tsananta yana harbawa ban gama barin hayyacina ba sai da sautin muryansa suka bugi kunnuwana.
"Shashasha marar hankali ke wacce iriyar mace ce?, ana ƙoƙarin kwato miki ƴancinki, dajararki da kimar ki da Allah ya yi miki na ƴa mace shine har kika ga bakin faɗin wannan maganar. Meyasa za ki watsa da kanki da kuma ɓarar da mutuncin ga wanda da ya gama cin moriyarki zai watsar da ke ko aure zai yi ba zai aure ki za ki sha mamaki idan kika ga kalar macen da zai je ya aura mai kamun kai kuma sai ya tabbatar cewar babu wanda ya taɓa mu'amala da ita kwatankwacin irin mu'amalar da ya yi matan banzan sa, ki nutsu ki san inda rayuwa ta dosa Allah ya yi miki gatan da ba kowacce mace ba ce take samun irinsa kin sama yardan iyayenki sun amince miki sun turo ki neman ilmi amma sakayyar da suka cancanta kenan daga gare ki? Allah wadaran halin irin wannan Allah yasa hukuncin da za'a yi miki ya zamto silar shiriyar ki".
Daga haka ya bar wajen a matuƙar fusace, har ya gama maganar kanta yana ƙasa bata ɗago da ita da saurayin aka tarkata aka wuce dasu students affairs bayan Securities sun gama yi masa nasu nasihar da kuma Amir na MSS da yazo wajen shima.
Kamar wacce aka zarewa laka haka nake tafiyar ba tare da na san inda nake cilla ƙafata ba, a karon farko da na kasa gaska abinda idanuna suka nuna mini akan yaya Yusuf na yarda ba zai yi mini gizo ba sai dai yanzu ina kokonta anya shi ɗin kuwa na gani. A raina na bar abun ba tare da na faɗawa ko su Nawwara ba tun daga lokacin bamu ƙara zuwa area class ba muna yin magrib zamu fita karatun mu a bayan hostel ana yin isha'i kuwa zamu dawo da haka har aka fara azumin watan ramadana.
MATAN AREWA
(Book two)
© Maimunah Tijjani Iyam
___________________________________
Page 8⃣4⃣
Ranar talata ɗaukacin al'umman musulman duk duniya suka tashi da azumin ramada a bakin su, hakan ta kasance ga pan hostel wasu tun kafin goman rana suja fara galabaita nikam zaƙuwa da murnar ganin ƴan gidan mu da suka yi mini alƙawarin zuwa mini yau yana mantar dani azumin balle naji wahalansa. Duk daga gida sai da aka tashe mu da asubahi aka shaida mana da an ga watan ramadan tunda muka yi sahur bamu koma bacci ba muka dukkan aikace-aikacen mu sannan muka yi shirin lecture cikin faɗuwar gaban haɗuwar mu da Mr Suleiman da yake satin da ya gabata bai zo ba tun bayan faruwar lamarin yau ne idan yazo kawai zamu haɗu dashi.
Kafin ƙarfe takwas gabaɗayan mu hallara cikin hall ɗin muna jiransa, sai da muka shafe mintuna goma zaune kafin yazo shi koda yazo bai ce damu komai ba don mun bi shawarar yaya Majid bamu zauna waje ɗaya ba duk mun zauna waje daban daban. Taƙaitaccen lecture ya yi mana tare da bada group assigment a matsayin second C.A ɗinsa ya yi ficewarsa. Hamdala muka yi don ganin bai ƙara yi mana zancen ba muna tinanin ko ya mance ko kuma ya watsar da kashin mu wataƙil ya fahimci cewar ba zai sama yanda yake so daga gare mu bane. Muna fita daga nan muka wuce next lecture bamu fito ba sai ƙarfe sha biyu muka wuce hostek muka yi salla ina raka'an ƙarshe wayata ta soma ruri Nazifa ce ta ɗaga tare da gaisuwa sannan ta ce"har kun iso to gamu nan fitowa".
Ina shafa addu'ar da nayi na miƙe na ce"yaya Majid ne?".
"Shine uwar zumuɗi". Ta furta tana sakar mini dariya miƙewa suka yi muka fice bayan mun jawo ƙofar ɗakin, can wajen old hostel muka hange su suna tsaye babu abinda ya sha mini kai balle lura da ɗumbin jama'ar dake kai komo a wajen na zuga a guje na isa ga ina suke tsaye na ƙanƙame Anty Zakiyya tsam a jikina kamar za'a ƙwace mini ita.
Ita ɗin rungume ni tayi sosai cikin murnar ganin juna da muka shafe satikai masu yawa bamu ga junan mu ba, mun daɗe a haka har sai da su Nawwara suka iso wajen kafin na sake ta ina gaishar da Goggo Suwaiba da yaya Majid da suke tsaye sun ƙura mana na mujiya suna kallonmu.
"Sai yanzu kika gan mu to bama son gaisuwa riƙe abin ki, na ƴan-uwanki kaɗai ya ishe mu tunda su sun gamu".
Furcin Goggo Suwaiba kenan cikin raha kwaɓe fuska nayi na ce"Ayya Goggo kuma fa na ganku". Naɗe mini kafaɗa tayi alamar oho mini da hakan ya sanya ni rungumo ta ita ma murmushi mai sauti ta saka kafin ta ce"ƴata ya makarantar?".
"Alhamdulillah wallahi sai tarin kewarku".
Ɗago ni tayi ta dubab su Nawwara ta furta"in ce dai kuna karatun sosai ko?". A tare muka haɗe baki muka amsa da kalmar e ta kuma ɗaura da faɗin"to Allah ya taimaka ya baku sa'a gashi kuwa duk sun rame".
Sai da muka dara kafin muka amsa da amin, na kamo hannun Anty Zakiyya na ce"Ga Anty Zakiyyan da nake faɗa muku ɗin to duk da ma kun ganta a hoto to yau ga ta a gabanku a zahiri".
"Ayya ai kuwa ga kama nan kuna yi wallahi, duk da dama ta fiki kyau".
Harara na cillawa Nazifa da tayi zancen tare da juya mata idanu na ce"sai dai in makancewa kika yi yarinya". Dariya Nawwara tayi tana cewa"ai kuwa dai gaskiya Nazifa ta faɗa miki ko ni na hangi nisan da tayi miki a fagen kyau to yaya Majid da yake namiji ma ba ki gama ƙafarsa ba balle Anty Zakiyya".
Duka na kai mata tayi saurin kaucewa na kwalalo ido waje haɗi da faɗin"wallahi sai dai in sharrinku ne ya motsa ehe, yaya Majid ɗin ne ya fi ni kyau lalle ma".
Caraf naji ya cafke mini kunne yana matsewa na toshe bakina saboda ihun dake shirin kubce mini"watau gani mummuna ko ban fi ki kyau ba".
Kaina kawai nake jijjiga masa ina yarfa hannuna saboda zafin da nake jin yana ratsa ni, Goggo Suwaiba ta kwace ni daga hannunsa akan rest bench ɗin da suke wajen suka zauna yaya Majid ya kallo ni da nake ta zuba suturu a Goggo Suwaiba da Anty Zakiyya ina tambayar su mutan gida kamar an kunna ni ya ce"ke Na'ima anya kina azumin nan kuwa?". Fari nayi masa da idanuna na ce"sosai ma kuwa". Bai ce komai illa murmushin da ya yi yana danna wayarsa ya ƙira Abba ya miƙo mini wayar karɓa nayi tare da yin sallama ya amsa kafin na gaishe shi yana ta jera mini tambayoyin lafiya, ya makarantar, ya kuma azumi babu wani matsalar ko?.
Sai da muka gaisa da Baba, baba ƙarami, Ummata da kuma Hajiya Babba da Goggo Jummai na ce a ba wa Salma aka ce mini ta fita ina jin hayaniya fal a cikin gidan namun take kewar rayuwar cikin gidan ya mamaye mini ruhi na ce Goggo Jummai ta ba wa raguwar matan gidan mu gaisa ina ji ta cikin wayar suna cewar ba zasu karɓa ba suna da abin yi Hajiya da Daada ne kawai suka amsa muka gaisa. Sai da zamu yi sallama na miƙawa Nazifa da Nawwara wayar suka gaisa da Umma da take ta faman tambayar su kamar ko yaushe yau ma sai da tayi mana nasiha sosai kafin muka yi sallama na miƙawa yaya Majid wayarsa.
Kayan azumin da suka kawo mini labourers suka kai mana har bakin hostel muka ƙarisa shigar dasu, a waje yaya Majid ya tsaya Goggo Suwaiba da Anty Zakiyya kuwa muka shige tare dasu a ɗakin ƴan kusa sai zuwa suke yi suna gaishe da Goggo Suwaiba kasancewarta mai buɗaɗɗen hannu kayan azumin da ta kawo mana ta ɗauka daga ciki ta ba wa wasun su.
Sai da suka yi sallan asr sannan suka fara shirin tafiya naso su bari sai sun sha ruwa amma suka dage akan zasu tafi don basa son tafiyar dare, tare muka rako su kamar na kurma ihu na ce zan bi su sai dai babu damar yin hakan muna tafe muna ɗan hira da Anty Zakiyya yayin da Nazifa suke hiransu da Goggo Jummai, Nawwara kuwa suke yi da yaya maji da nake kyautata zaton tambayar ta yake yi a game da yanda muka kwashe da Mr Suleiman duk duk da a lokacin mun yi masa bayani a waya. Wani mota ta wuce ta gefen mu a guje kasancewar wajen masallacin maza ne inda suke alwala ya facakalo wa Anty Zakiyya ruwan a fuskanta.
"Subhanallahi".
Goggo Suwaiba ta furta tana waigowa motar bata tsaya ba sai da tayi gaba sosai kafin aka faka ta, idona ƙar akan mamallakin motar naga uban waye ne da ya yi mana wanna wulaƙancin kasa ɗauke idona nayi daga kansa don ganin Mr Saif ya fito daga cikin motar cikin shirgar suit ruwan shuɗi hannunsa ɗaya riƙe da babban roban ruwa ya nufo inda muke, janye idona nayi a faƙaice yayin da yake isowa wajen bakinsa ɗauke da sallamar da yaya Majid ya amsa masa. Sannan muka yi musabaha roban ya miƙawa Anty Zakiyya da ruwan ya ɓata mata fuska a nutse ya ce"am so sorry take this".
Karɓa tayi ta miƙo mini na ɓalle murfin na fara zuba mata tana wanke fuskan natan ya yin da ya juya yana gaishe da Goggo Suwaiba ta amsa masa cikin sakin fuska.
Sai da ta gama tsaf kafin ya kuma faɗin"am so sorry hope kina lafiya?".
"Lafiya ƙalau karka damu babu wani abun ruwa ne fa kawai bawan Allah".
"To alhamdulillah".
Hannu ya kuma miƙawa yaya Majid suka yi musabaha yana cigaba da faɗin"to abokina na gode ina ƙara baku haƙuri".
"A'a ba komai wallahi kar ka ji komai".
Har buɗe bakinsa da nufin cewa wani abun idanunsa da suka sauƙa akan mu ni da su Nawwara da Nazifa da muke tsaye waje guda kallon tsaf ya yi mana kamar mai tinano wani abun kafin ya ce"like those that we meet in staff office ko?". A tare muka ɗaga masa kawunan mu cikinmu yana bada ƙara ƙululu na tsoron bamu shiga lectures ɗinsa ba yau gabaɗaya gashi kuma mun haɗi yanzun.
Bai kuma cewa komai ba illa shafa sumarsa da ya yi yana cije lips ɗinsa yana duban Goggo Suwaiba cikin girmamawa yake faɗin"Anty naga kamar tafiya ne zaku yi i can help you ko hanya ne na rage muku".
"A'a ɗan nan kar mu wahalar da kai mun gode kayo tafiyarka".
Never mind it Anty babu wahalar da kai a ciki ni da nayi muku laifi na watsa mata ruwan datti a fuska ba komai kar ku damu malami ne ni a jami'ar nan ina ne za ku?" Na lura sai yanzun hankalinsu ya ɗan kwanta suka sa ki jiki dashi yaya Majid ya ce ya bari amma ya dade ala dole suka shiga motarsa bayan mun gama sallama dasu nikam har da kukana haka suka fice daga cikin makarantar.
Numfashi Nazifa ta sauƙe tana hamdala da Mr Saif ɗin ya rufa mana asiri bai furta gaban su Goggo Suwaiba ba yanayin tsoron da ya gan mun fito dashi daga ofishin Mr Suleiman. Sai da aka sha ruwa na ƙira su naji sun sauƙa lafiya sannan hankalina ya kwanta, duk tesa-tesan mu cikin azumi muka yi su yayin komai ya ƙara tsanani saboda azumi sai bayan mun sha ruwa sannan muke girkin shan ruwa. Randa muka kai azumi uku kawun Nawwara yazo ya kawo mata kayan azumi ana azumi goma kuwa yaya Amin yazo ya kawowa Nazifa ramadan basket sai tsiya muke ta yi mata. Kwanci tashi har muka kai azumi goma sha biyar a bakinmu hankalinmu kwance domin Mr Suleiman bai ƙara yi mana maganar zuwa karɓan script ɗin Nazifa ba, hankalin mu kwance muka ƙara mayar da hankali ga karatunmu da yanzu babu kama hannun yaro.
MATAN AREWA
(Book two)
© Maimunah Tijjani Iyam
_________________________________
Page 8⃣5⃣
Tun shigowar azumi babu sunka ƙa rincaɓewa a gare shi, ga alamar motsarwar ciwonsa da wannan karon bai zo tunda daga farkon bai zo masa da wasa ba da gaske yake jin ciwon a cikin jikinsa da hakan ya sanya baya iya taɓukawa kansa komai ko makaranta baya shiga tunda aka kama azumi. Juriya da ƙarfin hali kawai yake yi ko don kwantarwa da Farouk hankali da tun bayan faruwar lamarin nan na gidan goma har yanzun hankalinsa baya a tare dashi ga kuma jikin Ummin da har kullum babu wani cigaba burin fitar da ita ƙasar ƙetara da yake da ƙudurin yi ya shafe tunda abinda ya dogara hakan gare shi Allah ya zartar da ikonsa a kansa.
Zaune yake a falo shi ɗaya ya ƙurawa hoton mahaifinsu da yake ganin cikin wayarsa idanu, yayin da yake jin wani abun yana zarge masa ransa sosai yake kallon hoton mahaifin nasun da ya ɗauka ba tare da sanin Ummi ba ya ajiye a wajen sa lokaci mai tsawo. Duk wani abun da ya dangance shi ko kuma wani abun da zai tino mata dashi sai ta nisanta su da ita hatta hotunan sa tarkatawa tayi ta ƙone su ƙurmus a sace ya ɗauki wanda yake dashi a waya yanzun.
A hankali yake jin tafiyar ruwan ƙwallar da suka wadaci koramar idanunsa suna sauƙa saman kuncinsa, rayuwar da suka yi tare da mahaifin nasun yana dawo masa cikin kwanyansa duk da an ɗebi shekaru masu tsawon gaske sai dai ba zai taɓa mance wannan yanayin ba har izuwa sanda ƙasa zasu rufe masa nasa idaniyar. Ba zai taɓa mancewa da irin soyayyar da mahaifinsu ya nuna musu ba sanda yake raye, ba zai taɓa mance rayuwar farin-ciki da annashuwan da suka yi tare ba, ba zai taɓa mance yanda yake tattalin su da ƙoƙarin biya musu dukkan buƙatun su na yau da kullum ba, ba zai taɓa mance fuskarsa mai ɗauke da murmushi da fara'a a ko wani yanayi