Showing 138001 words to 141000 words out of 171161 words
Chapter 47 - MATAN AREWA BOOK TWO COMPLETE PDF .txt
da Anty Zakiyya take zaune na faɗa jikinta tare da ƙanƙame ta tsam a jikina, na rasa wani kalan murna zan yi dariyan zan tayi ko kuwa kuka?, domin bayyanar da zallan farin-cikin da ya mamaye mini ƙalbina.
"Alhamdulillah alhamdulillah nayi farin-ciki wallahi sosai Allah ya tabbatar da alkhairin dake ciki".
Amin suka haɗe baki wajen faɗi, suturai kawai nake yi barkatai na ma rasa me zan yi Umma da yaya Majid suna ta yi mini dariya har yamma muna zaune a ɗakin muna tattauna gabatowan magrib ya sanya yaya Majid ficewa.
Sai da nayi sallan magrib ina zaune akan sallayana ina tasbihi da yatsun hannuna, zancen yaya Majid na ɗazu ya faɗo mini a rai tamkar faɗuwar aradu. A bayyane na maimata sunan da ya ambata da a lokacin tsabar farin-cikin da na tsunguma ya mantar dani komai.
"Saifuddeen".
Kamar wacce aka tsigarawa matsilla haka na tashi a miƙe na shafa addu'ar, na nufi ɗakin Umma Anty Zakiyya kawai na tarar tana karatun alƙur'ani tana kai ayan ƙarshen a suratul Maryama ta kallo ni tare da yi mini alama da ido akan lafiya?.
Kaina na jijjiga mata da hakan ya sanya ajiye alƙur'anin a gefe ta ce"menene?".
"Wai ɗazu wani Saifuddeen ɗin yaya Majid yake faɗa ne?".
Sai da ta gama kalle ni kafin ta ce"waye kike tinani?". Cike da zaƙuwa na ce"don Allah ki sanar dani in ina tinanin wani ai ba zan ma zo na tambaye ki ba".
"Saifuddeen ɗin malamin ku na jami'ar wanda suka zo gidan nan ɗazu". Baki da hanci na buɗe gabaɗaya ina kallonta kafin na sauƙe wani ƙaton numfashin da naji ya tokare mini ƙirji na ce"Mr Saif?". Ta ɗaga mini kanta cike da tabbatarwa ban kuma cewa komai ba don na gama yin zurfi cikin tinanin da na faɗa.
"Ke tinanin me kike yi ko wani matsalan kika hango?". Wani ajiyan zuciyan a karo na biyu ba saka ina musgutawa daga inda nake zaune na ce"babu wata matsalan da na hango tattare da hakan, ko a makaranta an masa kyakykyawan shaida sai dai abunda yake taskace cikin tsokar zuciya ne sanin sa sai mai shi da kuma maƙaginta, zan taya ki da addu'a in sha Allah".
Ina iya jiyo sakakken ajiyan numfashi da ta saka a bayyane ta ce"na gode". Daga haka ta cigaba da karatunta ɗakin mu da yanzu ya kasance babu kowa a cikin sa face ni kaɗai na koma na yi zaman ƴan bori dirsham a ƙasa ina tinane-tinane.
Me yaja hankalin shi zuwa ga Anty Zakiyya?, ina tsoron ya yi irin auren da ake yiwa laƙani da auren ɗanɗane ko kuma irin auren da suke ganin cewar kuɗi sanya suka sayo ki hakan ya saka ba zasu kanga da mutunci ba balle kayi kima a idanunsu. Da wannan tinanin na ƙarar dagowan wannan wunin tas ba tare da na taɓuka wani abun ba.
Sai dab da magrib suka koma hotel ɗin tsabar ciwon da kansa yake yi masa har ganin abubuwa yake yi double double, riƙe da goshinsa ya ƙarisa cikin ɗakinsa akan bed ya zube yana kallon rufin ɗakin da ya samo masa shamaki tsakanin sa da sararin samaniya. Ya ɗau tsawon mintoti a haka kafin ya tashi ya shiga bathroom ya sakewa kanaa shower sai da ya ɗauro alwala kana ya fito bai tsaya shafa komai a fatarsa ba ya zura doguwar rigar jallabiya a jikinsa, ya fice izuwa ɗakin Farouk tsaye a gaban dreesing mirror ya hango shi ɗaure da towel a waist ɗin sa a nutse ya rako ya tsaya ta bayan sa hannunsa ya kama ya ja shi zuwa bakin gadon ya zaunar dashi ya ɗauko kumb ya gyara masa sumarsa da ya barbaza su sama-sama ya murza masa mai a fatarsa da take da haske fiye da nashi domin shi duk kammanin Ummi ya ɗebo har hasken fatanta saɓanin shi da ya yo mahaifinsu.
Rigar da ya gani akan gado ya ciro ya taimaka masa ya saka, sannan ya kuma riƙo hannunsa suka fice daga ɗakin yana tina rayuwar su ta baya lokacin da shi yake yi masa komai wanka shiri da dukkan sauran abubuwan, yayin da Ummi take fita yawon bin gidaje neman aikin aikatau domin samo musu abinda zasu ci. Da sauri ya kai bayan hannunsa ya tare ƙwallan da suke shirin tsiyayo masa ba tare da sanin sa ba, a shirye suka iske Abdul-aziz suka wuce masallacin dake bakin hotel ɗin sai da suka gabatar da sallan isha'i. Daga nan wajen cin abincin dake ciki suka wuce suka ci abinci tun safe sai yanzu ya sanya wani abu a cikin cikinsa da tashin hankalin da yake ciki ya mantar dashi ma wani yunwa. Gobe suke son su bar cikin potiskum su wuce kano wajen Anty Fauza daga nan kuma su wuce gida.
MATAN AREWA
(Book two)
© Maimunah Tijjani Iyam
______________________________________________
Page 1⃣1⃣1⃣
A karo na barkatai ya saki wani numfashi mai ƙarfi tare da fesar da zazzafan iska mai ɗumi daga bakinsa, tun daren jiya da ya kammala zana jarabawan sa na ƙarshe yake jin matsanancin faɗuwar gaban da bai san dalilin sa ba. Kalmar hasbiyallahu wa ni'iman wakil kawai yake ta maimatawa a bisa harshensa, har motar ta dire a cikin garin potiskum adaidaita ya hau izuwa gidan Anty Binta domin tun jiyan take sanar dashi cewar a gidanta zai sauƙe, su maman Hanan ma duk nan zasu zo su haɗu.
Har ƙofar gidan ya sauƙe shi ya sallame shi ya tafi, sai da ya kuma sakin wani gwauron ajiyan zuci kana ya saɓa jakan kayansa a kafaɗarsa ya tura ƙofar gidan sai da ya kusa ƙure zauren kana ya furta siririyar sallamar da ta tsaya iya kan leɓɓansa.
Amsawa suka yi a tare da zubo masa idanunsu gabaɗayan su suna kallon sa, a hankali yake ɗaga ƙafarsa tamkar mai tsoron taka ƙasan ya fara nufo inda suke. Tsayawar sa ya yi dai-dai da tsayiwar harbawan da ƙirjinsa yake yi a raunane, rasa abu guda ɗaya takamamme da zai aiwatar a lokacin ya yi, har izuwa lokacin da ta fara zance cikin sheshsheƙar kukan da ta soma nan take a lokacin.
"Sai yanzu ka dawo sanyi idaniyata, nayi kukan rashin ka kusa dani sau babu adadi ni kam ba zan iya juran rashin ka ko na daƙiƙa ba".
Shuru wajen ya kuma ɗauko tamkar babu wasu halittun masu numfashi da motsi da suke zaune a wajen, runtse idanunsa ya yi da matuƙar ƙarfin kafin ya sanya hannunsa ɗaya ya raba ta da jikinsa. Bai yarda sun haɗa ido da kowa ba ya yiwa kansa mazauni a kusa da yaya Auwal. Kamar mai ciwon haƙori ya furta"ina kwananku na same ku lafiya?".
Iyee ba shakka lalle Aisha fitsaran takin ta kai kin kuma bunƙara, akan idanunmu za ki yi wannan iya shegen tsabar rashin ta ido da lalata irin na ƴaƴan wannan zamanin. Hmm ba komai zan yi maganin ki Aisha da ni kike zancen".
"Anty don Allah mu bar wannan zancen wannan ba abinda ya kamata kina sanya kanki bane a ciki. Lamarin auren yaran nan dole sai kina kau da kai akan wasu abubuwan ko don tsira da mutunci da kimarki a idanunsu, da kuma gudun lalacewar zumuncin dake tsakani". Furcin yaya Auwal kenan da ya sanya Yusuf sauƙe numfashi, gabaɗaya da-na-sa-nin dawowa yake yi sau dubu zaman makarantar yafi masa ammam babu yanda ya iya. Wuni suka yi a gidan zum sai bayan sallan isha'i suka koma gida, bayan ya kammala komai da zai yi ya yi zaman sa a falo yana kallo a zahiri idanunsa suna kan tvn amma da zaka yi masa kallon ƙurilla zaka fahimci tunun ya yi nisa a duniyar tinanin da ya zurma cikinta.
Babu shiri ya yi sauƙar mutum a jikinsa da sauri ya kai idanunsa gare ta, yana ƙara buɗe manyan idanunsa a kan ta kafin ya furta"lafiya?". Kamar jira take yi ta fashe da kuka har da sheshsheƙa tana faɗin"meye nayi maka don Allah kake yi min wannan wulaƙancin Yusuf?, ya ya kake so nayi da raina?. Kwananka nawa baka cikin gidan nan amma yau ɗaya da ka dawo ba zaka iya bani lokacinka ba, da na san haka auren yake ma da na cigaba da zamana tare da Ummata".
Tunda ta fara zancen natan bai ce da ita ko kanzil ba har ta dire shi, illa kallonta da yake yi da gefen idonshi yana jin warin man bleaching ɗin da take using da shi yana hawa masa kai tare da tayar masa da zuciya. Musgutawa ya yi yana janyen nasa jikin haɗi da faɗin"bana son warin wannan man da kike amfani dashi". Kallo shi tayi kafin ta yi ƙasa da idanunsa tana shinshinan jikinta ta ce"amma babu wani warin da yake fita daga jikina".
"Ba lalle ke kiji shi ba kawai ni dai bana so".
Kanta kawai ta jinjina masa tana jin wani ɗaci a cikin ranta yana bin cikin jininta yana gudana, fahimtar sauyawan yanayin natan ya sanya shi jawo ta jikinta gabaɗaya ya rasa abinda yake masa daɗi a gidan duniya.
Yau ta kasance ranar da Anty Zakiyya da Goggo Suwaiba zasu koma nguru tafiyar sassafe suke son yi duk da ba wani nisa bane har na azo a gani tsakanin mu. Lambar Goggo Suwaiba su Abba suka lamince yaya Majid ya ba wa Mr Saif domin zance da Anty Zakiyyan da har yanzu babu wayar salula a tare da ita, domin a cewar ta babu amfanin da zata yi da ita. Sai da muka je gidan Salma da ita suka yi sallama kafin suka tafi.
Sati na zagayowa nima na koma makaranta zango na biyu da muka koma, na iske Nawwara da Nazifa duk sun riga ni dawowa don na haka na tarar da sun gyare mana ɗakin tas komai tsaf.
Bamu fara lecture a satin ba sai na gabansa, ina so na sanar dasu zancen Anty Zakiyya da Mr Saif amma tsoro ya hana ni bisa ga yanda Umma ta ce damu zancen ya tsaya a iya tsakanin mu ya mu ya mu, hakan ya sanya ni yiwa bakina sakata naja na kulle. Ranar mun dawo daga lecture ɗin ƙarfe huɗu a matuƙar gajiye duk zubewa muka yi akan katifunmu muna mayar da numfashi.
"Nifa wallahi yau ko ruwan zafi ba zan iya dafawa ba balle kuma abinci, don haka kowa ya kama cikinsa sai da safe".
Furcin Nazifa kenan da yake ranar girkinta ne, hararo ta Nawwara tayi daga inda take kwance kana ta ce"ai kuwa ba ki isa ba yarinya don ni kam ba zan iya kwanan yunwa ba, alhali ga kayan abincin muna dashi sai dai ki san yanda za ki yi damu".
"Shikenan sai muje wajen Mama Marry mu saya masa muci mu kwanta".
"Yanzu kika yi magana yarinya". Nawwara ta faɗa tana tashi zaune daga kwanciyar da tayi ta dawo da duban ta gare ni ta ce"Nimcy tashi ki fara shiga wank....". Uwar hararan da na watsa mata ya sanya ta haɗiye ragowar zantukan, ta sa ni sarai bana son wannan sabon sunan da ta fara ƙira na dashi tun dawowar mu amma bata ji ba. Ƙwafa nayi na tashi na fita sai da naji jira don na tarar da mutum a banɗakin kana na shiga na fito suma suka shiga suka yi, kaya muka sauya muka sanya hijaban mu muka fita izuwa wajen Mama Marry mai sayar da masa kusa da cafterian dake cikin jami'ar muna tafe muna hiran mu a nutse. Mutane sosai muka tarar a wajen masu jiran ta toya ta sallame su don haka muka zaune a kan benjin dake gefe kaɗan sai da ta gama sallaman su kaf kana ta juyo gare mu.
Haɗe baki muka yi wajen gaishe ta ta amsa masa cikin sakin fuska haɗi da ɗaurawa da faɗin"ƴan matana hutu ya ƙare an dawo ko". Na ce da ita"hutu kam ya ƙare sai dai na gaba Mama gashi har kewar masarki ta sanya mu fitowa da wannan yammacin". Gabaɗayan su murmusawa suka yi kafin ta ce"ai kuwa yanzu ina cire wannan sai na zuba muku, riƙe min babyn nan".
Babu wanda ya ce wani abun illa idanu da muka ɗaura mata har ta yaye lulluɓin dake bayanta ta sinto jaririyar da take goye da ita da dukkan mu sai yanzu muka lura da ita ta miƙa mini ita.
Mayar da dubana nayi ga jaririyar sabuwar haihuwar da ina da yaƙinin ko kwana arba'in bata cika a duniya ba, Nazifa ta yi saurin faɗin"Mama wannan beatiful babyn fa ƴar waye kika samo?".
Murmushi tayi taƙaitacce tana juya masar da ta zuba ta amsa da faɗin"babyna ce".
"Babynki?".
Muka maimata a tare ta ɗaga mana kanta cike da tabbatarwa, da maɗaukakiyar mamaki gami da tantamar zancen natan don bamu taɓa lura da ciki a jikinta ba balle mu tsammata mata haihuwa na furta"yaushe kika haife ta wannan anya ko kwana arba'in ta yi ma kuwa?".
"A cikin hutu na haife ta, jiya satin mu biyu da kwana huɗu".
Mamaki fal a bisa fuskokin mu Nawwara ta ce"sati biyu da ƴan kai shine kika fito da ita nan".
Bata amsa ba sai ta gama cire masan da suka yi ta zuba wasu kafin ta ce"dole ne ta sanya hakan ƴan matana, idan ban fito na nema ba meye zamu ci nida ragowar yarana da kuma mijina?".
"Mijinki shi ma sai kin cinyar dashi, da wannan toyar masan Mama?".
"Hmm ai ku matanku na hausawa suna jin daɗi suna zaune mazajen su zasu fita su nemo su kawo musu, nasu aikin kawai sarrafawa ne. Amma mu ke za ki fita kiyi duk wani buga-buga ki ciyar da iyalinki mijin yana kwance a ɗaki har kije ki dawo, in kin kammala abincin ki tada shi ya ci da za ki yi kuskuren ko ruwan sha ne ba ki kawo ba sai ma ya rufe ki da duka kuma hakan ba shi zai hana gobe ki kuma fita nemowa ba".
A raunane ta ƙare zancen cikin rawar murya da taruwar kwantaccen ƙwalla a cikin idanunta, ajiyan numfashi na sauƙe a hankali ina bin jaririnyar da take baccin ta hankali kwance a hannu da kallo tare da ƙara jinjina zancen na Mama Marry. Zancen da Nazifa ta soma yi shi ya katse mini hanzari.
"Cab ai wallahi ni kam ba zan iya ba kana kwance ina fita na nemo na dafa maka na kawo maka ka ci, sannan kuskure idan nayi ka rufe ni da duka. To wai babu manyan da za akai abun gaban su ne ko meye?".
"Akwai manya sai dai tsarin ne ba zai canju ba, domin wanda za'a kai koken hakan ma gare shin shima hakan yake aikatawa ga iyalinsa kin ga kuwa ai ƙwarya sama ce ke dukan na ƙasa. Ina mamaki a duk lokacin da naji matan hausawa suna complain akan mazajen su idan da ni ce cikin inuwar da suke da ko yankan naman jikina zai dunga yi matuƙar zai ɗauke min ɗawainiyyata da na ƴaƴana zan zauna dashi ba tare da ko wani irin complain ba".
Tagwayen ajiyan zuciya ba saka muna haɗa ido da su Nawwara kowa da irin tinanin da yake saƙawa da tufkewa cikin ransa, tabbas ba zaka taɓa sanin tana inuwa ba sai lokacin da bishiyar da kake shan inuwarta ta guza zaka gane Allah ɗaya ne. Duk tsananin damuwa gami da ƙuncin da MATAN AREWA suke a cikin gidajen auren su da mazajen su ashe nasu nafila ne akan na ƴan kudu. Su da ci, sha, sutura, magani da komai yake kansu alhalin mazajen suna da lafiya da ran su a doron duniya. Cikin ɗanyen jegon da ko arba'in basu fita ta har ta komo bakin sana'arta domin cigaba da ciyar da iyalinta nauyin da ba nata ba. Haƙiƙa da a gidan bahaushe ne komai talaucinsa za'a iske ta cikin kula dai-dai da ƙarfin lalitarsa, sannan abinci sau uku a rana ko babu daɗi sai ta cika tumbinta ta ɗaura da kunun kanwa mai ɗumi a kai.
"Na nawa za'a zuba muku?".
Muryan Mama Marry kenan da suka yiwa ƙofofin kunnuwan mu diran mikiya, ban iya bata amsa ba sai Nawwara ce tayi ƙarfin halin"na ɗari biyar".
Zuba mana ta soma yi na kuɗinmu a leda guda, wanda take bamu kyauta a duk lokacin da muka zo saye shima a leda guda Nazifa ta miƙa mata kuɗi muka miƙe ina faɗin"Mama ko muje da ita hostel zuwa lokacin da za ki gama toyar sai mu kawo miki ita, nan ɗin akwai iska kar ya yi mata illa".
"To ba zai jawo muku matsala ba, ba ku da wani ajin ne da zaku yi a gaba?". Sai da na ƙirƙiro murmushi na yaɓa akan fuskana kafin na amsa mata da"babu matsala Mama kuma lecture ɗin yau mun gama shi gabaɗaya sai kuma gobe".
"To na gode zuwa ƙarfe bakwai na tabbata zai ƙare, sai ku kawo min ita".
"Mama meye sunanta?".
Nawwara ta tambaya tana shafo kan Babyn, sai da ta ɗan murmusa ta ce"ba'a sanya mata suna ba tukunna sai na sama kuɗi za'a bikin sunan zuwa gaba".
Kanmu muka jinjina muka yi mata sallama muka ɗauki hanyar hostel, na sanya ta a cikin hijabina saboda iskan da ake yi har muka ita ɗakin mu cikin mu babu wanda ya ce ko kanzil saboda mutuwar da dukkan gaɓoɓin jikinmu suka yi, a kan katifar Nazifa na kwantar da jaririyar ina kuma bin ta da kallo.
"Cabɗijam wallahi ni fa in nice Mama Marry tun wuri zan kama gabana ba zan iya wannan wahalar ba, tun ƙuruciya bai gama barin jikinka ba duk alamomin tsufa sun gama bayyanowa tsabar wahala".
A zazafe Nawwara take amaryar da zancen cikinta da yake bayyanar da ƙololuwar ɓacin ran da take a ciki, sai da na juyo ina fuskantan ta kafin na ce"Nawwara kenan ba ki ji abinda ta faɗa bane wanda zaka kai lamarin gabansa ma shima cima zaune ne a gidansa, to idan irin wannan ƙaddaran ta faɗa maka yaya zaka yi in ba haƙurin ba? lalle MATAN AREWA su kam suna cikin aljannar duniya idan aka kwatanta da ƴan kudu". Amshe zancen Nazifa tayi da faɗin"ke ai wallahi addinin musulunci ya yi a rayuwa domin shi ya tsara mana yanda zamu yi rayuwar da ta bambamta da na dabbobi, ke musulunci rahama ne Na'ima". Cike da bata amanna da maganar natan muka furta"haka ne kam Allah ya