Showing 105001 words to 108000 words out of 171161 words

Chapter 36 - MATAN AREWA BOOK TWO COMPLETE PDF .txt

ta tambayata ina basu amsa cikin raha da sakin fuska, har izuwa lokacin da Hajiya babba ta shigo ita ma muka ɗaura da ita zancenta ɗaya biyu sai ta sako yanda yaya Amin da su Nawwara suka girmama da kuma Mr Saif tsabar sanya musu ido da tayi har gwadawa su Abba tayi yansa ya rusuna da zai gaishe yanda take yi ɗin ya sanya mu kwashewa da dariyar da ta jawo mana daƙuwa daga wajen Baba.
Wayarsa yaya Majid ya zaro daga aljihunsa ya fara nuna musu hotonan da muka yi ɗazu idan wannan ya gani sai ya miƙawa wani ya gani har su Abba sai da suka gani kowa yana mana san barka da fatan alkhairi cikin karatun mu da yanzu ma muka sanya ƙafa, ƙurawa wayar idanu Umman su Salma tayi sosai kafin ta miƙawa yaya Majid yana taɓe baki gami da furzo zancen dake cikinta"ikon Allah wai yanzu Na'ima ke ce tsakanin garadan mazan nan majiya ƙarfi wai da sunan hoto?, ina mutunci da maluntan gidan nan kika tarkasu kika ajiye? da wanni ɗan firit ɗin hijabin da ko Jidda ta sanya shi ba zai kai mata gwiwa ba wai wannan ne suturar da kuke sawa kuna yawo dashi a cikin makarantar goɗai-goɗai daku?".


AYI MANEJI DA WANNAN SANNAN INA BARAN ADDU'O'IN KU DAGA BAKUNAN KU MASU ALBARKA ANYI MANA RASHI ALLAH YA JIƘANSHI DA RAHAMA YA SANYA MUTUWA TA ZAMTO HUTU A GARE SHI, YA BA WA IYALINSA HAƘURI DA JURIYA.


-07038908713-


MATAN AREWA


(Book two)


©Maimunah Tijjani Iyam


________________________________




Page 9⃣3⃣




Tsif falon ya ɗauki shuru babu wanda ya tanka mata har ta gama zancenta ta dire sannan yaya Majid ya ce da ita"to ai ƙa'idan department ɗin kenan dole sai da wannan uniform ɗin, kuma idan kin lura kin kallin hoton da kyau za ki ga ai duk hijabi ne a jikinsu su mata kuma suturar jikinsu bata bayyanar da suturan jikin su ba".
Sai da ta ƙare masa kallon tsaf tana taɓe baki ta ce"ai kuwa daman ai shi laifi tudu ne mussamman idan son zuciya tayi wa zuciyar mutum kanta sai ya sanya ƙafa ya take nashi yana hangen na wani".


"Ke Zainabu tashi ki koma ɗakinki kiyi zamanki ba za ki tada mana da hankali daga shan ruwan mu ba, wai meye haka ne sai haushe za'a zauna ba ki tsiro da wani fitina daga dinginki ba?". Furcin Baba kenan cikin ƙololuwar ɓacin ran da ya bayyana ɓaro-ɓaro a cikin furcinsa da ya sanya Umman su Anty Kubra yin shuru da bakinta tana cigaba da harare-hararen da take yi.


"Ku tashi ku bamu waje kuma ku tabbatar kowa ya tashi sallan tahajjud akan lokaci".


Abba ya faɗa cikin bada umarni cikin rawar jiki duk muka miƙe muka fice daga falon bayan mun yi musu a kwan lafiya, Nurain da ya fara bacci a kan cinyata na saɓa shi a kafaɗarta muka fice har cikin ɗakinsu na kai shi sannan na wuce na Ummata Anty Zakiyya sashin Hajiya Babba zata kwan domin ɗakin su da ya rage saura ita kaɗai a cikin sa'anninta da basu yi aure ba bayan komawarta wajen Goggo Suwaiba, Salma ke tsegunta mini cewar an ba wa su Ikilima, Falmata da Firdausi yanzu suke kwana a cikinsa.


Sai da nayi wa Umma sai da safe sannan na koma ɗakin mu, turus na iske missed calls ɗin Nawwara da Nazifa a cikin wayata na saki murmushi kana na dunga bin su ɗaya bayan ɗaya ina ƙiran su munsha hira dasu har sai da aka yi mini gargaɗin kuɗin cikin wayar na dab da ƙarewa sannan muka yi sallama.
Ina kwanciya bacci ya sure ni saboda gajiyar da na kwaso na hanya, ƙarfe ɗayan dare gabaɗayan mu ake tashe mu domin gabatar da salla tahajjud masallacin da Abban mu yake limancin muka yi sallan mu a nan sai ƙarfe uku muka dawo gida da yawan mu basu koma bacci ba sai da muka sahur sannan muka kwanta.


Hayaniyar da ya karaɗe dukkan filin tsakar gidan da suka sauƙa a kunnuwana kai tsaye shi ya tilasta mini katse baccin da ke cin idanuna har suna yi mini wani zafi-zafi, tashi nayi zaune dafe da kaina da nake jin yana sara mini sosai kamar zai rabe gida biyu a hankalin nake jin hayaniyar yana ratsawa har cikin kwanyata da ya hana ni sakat dole na diro daga kan gadon na bayyano waje.


Duk matan gidan na iske cirko-cirko sai cin zarafin juna ake yi ta hanyar yaɓawa junan su ɗanyen furcin a idanun ƴaƴansu da suka yi musu ƙawanya, jingina bayana naji jikin bangon ɗakin ina mamakin rashin canjuwan ahalin nawan nayi tinanin ɗan lokacin da na ɗauka bana cikin gidan wasu abubuwan da dama sun sauya ashe angulu tana nan a gidanta na tsamiya.


"Ni fa ba zan laminci wannan abun ba duk an bi an sanyawa ƴaƴana ido a cikin gida nan, nan wanke-wanke ma sai an haɗa da cuta an mayar dasu tamkar jakuna suyi jiya yau ma suyi wallahi da sake wai an ba wa mai kaza kai sam ba zata saɓu ba wai bindiga a ruwa".


Zancen Umman su Balkisu kenan tana karkaɗa kwankwaso da Daada ta amsa mata cikin faɗin"Haba ke kuwa meye abin ta da jijiyar wuya a lamarin nan?, aikin gidan nan dai kowa ya san yaran ne suke yin shi tun ma kafin su kai haka".
"To don su suke yi shine aka ce an mayar min da ƴaƴa iwa jakuna ko bayin da aka sanya sulalla aka sayo su".


Dai-dai sa'ilin da Baba ƙarami ya shigo sashin a fusace tana tafe tamkar zai kife wani irin tausayin su ne gabaɗaya ya soki raina ko yaushe suna cikin ƙoƙari damu amma har kawo yanzun mun gaza samun cikakken hankalin da zamu yi wa kan mu karatun ta nutsu mun san cewar Annabi fa ya faƙu da har su ma zasu sama nutsuwar ruhi su huta. Tambayar ba'asi ya soma yi Daada tayi masa dalla-dalla da komai wai Firdau'si ta sanya tayi mata wanke-wanke shi ne Ummanta ta fito ta ce ba zata yi ba jiya ma ita tayi ba za'a maishe mata da ƴaƴa bayi ba. Cikin zafin rai ya ke faɗin"ban sab wani irin hankali bane ku kam gare ku?, komai abin hayaniya ce a wajen ku ku dinga kai zuciyoyinku nisa fa duk yawan mutawan nan da ake yi ku bai ishe ku ku rungumi junan ku ba?. Wataran duk mutuwa zamu yi zaku nema ganin junan ma amma hakan ya gagara, aiki kuma daga yau na kafa sharaɗin kowacce mata tayi abin ta tunda haka kuke so".


Tsif wajen ya ɗauki shuru tamkar babu wasu halittu masu motsi da numfashi a wajen har ya yi ya ƙare zancen babu wacce ta kuma cewa uffan ya fice daga sashin, ɗaya bayan ɗaya kowa ya fara watse daga wajen ganin hakan nima ya sanya ni komawa ɗaki na saka hijabina na fito na fara haɗa wanke-wanken da Firdau'si ta fara ta bari da sauri Daada ta dakatar dani da faɗin"a'a Na'ima bar shi kawai zan yi abi na kin dai ji abinda Babanku yanzu ya gama faɗa a nan".


"Daada shima ɓacin rai ne ya sanya shi yin wannan furcin amma aiki kam ai tunda kuka haifa dole ku huta da wasu abubuwan yanzu, ki bari kawai zan yi shi ma nasan in sha Allah zai huce".


Duk da hakan bata daddara ba sai da ta karɓa soson daga hannuna tana wankewa ina yi mata ɗauraya, muna zancen mu da duk tambayoyi take yi mini game da makaranta ta sai da muka gama tsaf na share wajen sannan nayo wanka na muka gaida Hajiya Babba da su Abba sannan na dawo ɗaki handout ɗina na ɗauko na fara karantawa.


Har izuwa lokacin da Salma ta shigo ɗakin tunda ta shigo take kallona har ta zauna sai da na zargo da kaina na ɗago ina yi mata alama da ido akan lafiya?, murmushi naga ta saka kafin ta ce"lafiya ƙalau kawai burge ni kika yi da na ganki kina wannan karatun mussamman da muke makarantar muka iske ki cikin sauran ɗalibai, sai naji wani alfahari ya mamaye ni da ko a ina zan iya bugan ƙirji na ce ke ɗin jinina ce Na'ima".


Musgutawa nayi daga inda nake zaune da ya gani damar fuskantan ta da kyau kana cikin sanyi na ce"Salma kenan ai shi karatu ko yaya ne yana da daɗi kuma ko ke ma yanzu lokaci bai ƙure miki ba za ki iya komawa ki cigaba tunda yanzu alhamdulillahi su Abba sun fahimci menene karatun boko da kuma alfanunsa saɓanin da da suka ke yi masa wani kallon na daban".
Sai da ta sauƙe ajiyar zuciyar da har kunnuwana suka jiyo mini sautinsa sannan ta furta"Na'ima ai kamar yanda na gaya miki a baya karatu kuma yanzu ai sai dai ƴaƴanmu da zamu haifa su dai zan dage naga sun yi amma ni kam lokaci ya ƙure min. Daman ina so ki huta ne muyi wata magana dake na sama mijin aure har ya turo wajen su Abba wataƙil a haɗa ayi tare da na su Firdau'si".


Sai da na maimaita kalmar alhamdulillahi sau uku cas wani na bin wani sannan na ce"wannan ai abin farin-ciki ne wallahi na taya ki murna Salma Allah ya sanya alkhairi kullum addu'an da nake yi miki kenan waye mijin sannan a ina yake?".


Sai da ta ɗau sakannin kafin ta soma faɗin"Baban su Zaliha ne". Wani wawan kallo na cilla mata har muryata tana shaƙewa nake faɗin"baban su Zalihan dai da na sani Salma ko kuma wani daban ne mai irin sunan sa?". Kanta ta jinjina mini da hakan ya bani damar ɗaura"ke kuwa Salma meya kai ki makancewa kika yi ko kuma meye?, baba su Zalihan da tun muna yara yake zaune akan keken guragu baya iya tafiya saboda tsufa mutumin da ya riga da ya shanye baya iya taimakawa kansa da komai, komai fa sai dai ayi masa a hakan bakinsa bai fasa furzowa matansa baƙaƙen ashariya ba da munanan furci ga ƴaƴansa shi za ki aura Salma me ya yi zafi haka?".


Tunin hawaye suka ambaliya saman dakalin fuskarta cikin kukan take furta mini"to Na'ima yaya zanyi da raina yaya kike so nayi? Umma ta hura min wuta akan lalle sai na aure shi ta tilasta ni amsawa a gaban su Abba akan cewar ina son shi kuma zan iya zaman aure dashi ko yaya yake, tayi min barazanar in har ban amince ba zata tsine min ta kuma cire ni daga sahun ƴaƴan da ta haifa zata ɗauke kai daga dukkan lamurana kuma sai dai na nema wata uwar ba dai ita ba. Na rasa yanda zanyi na rasa mafita da abin yi na rasa wanda zan tunkara da zancen domin ta gargaɗe da kar na gayawa kowa na nunawa kowa cewar ina son shi kuma zan iya zaman aure dashi".


Cak numfashina ya ɗauke na wucen gadi sai da nayi da gasken gaske kafin na jawo shi da ƙarfi na fesa, na janyo jikina har gabanta na riƙe dukka hannayensa na sanya cikin nawa cikin sigar kwantar mata da hankali na soma cewa"kiyi haƙuri ki sama lokaci ki zauna da ita kuyi magana na fahimta ki nuna mata cewar bakya son shi, shi kuma zaman aure dole sai da soyayya idan aka yi rashin ta dole a ga ba dai-dai ba na tabbatar zata fahimce ki".


"Na jarraba hakan amma bai yi aiki ba na tambaye ta dalilinta nason aure shi shima ta ce min ba hurumina bane na sani, Na'ima ina cikin damuwa ba zan iya zaman aure da kowani ɗa namiji ba in ba Abdul ba har yanzu zuciyata tana raya min zai dawo gare ni zai dawo muyi rayuwar auren mu kamar da, duk wannan abubuwan da suka faru soyayya ba ta ragu koda da ƙwayan zarra daga cikin ƙirjina ba kullum sabo yake dawowa". Dukkan rarrashi nayi mata tare da yi mata nuni da ta nema zaɓin Allah akan komai ta sanya a gaba a rayuwarta, wani lokacin abinda muke ƙi shine yake zamowa alkhairi a gare mu abinda muke so kuma ya zamto akasin hakan. Wuni nayi ina saƙa da warwaran dalilin da zai sanya Umman Salma tirsasata auran Baban su Zaliha zuciyata tana bani cewar tabbas akwai lauje cikin naɗi kuma akwai sauran rina a kaba. Washe garin ranar Balkisu da Abasiyya suka zo da ƴaƴansu tare muka wuni zum sai yamma suka tafi, a haka har azumi ya tafi kullum sai muyi waya da Nawwara da Nazifa ranar talata aka gudanar da ƙaramar salla kamar kowacce shekaru duk ƴan gidanmu tare muka tafi sallan idi cikin farin ciki da walwala.


MATAN AREWA


(Book two)


© Maimunah Tijjani Iyam


_______________________________




Page 9⃣4⃣




Sai da muka biya gidan wani aminin su Baba da tun muna yara muka taso muka gansu tare sannan muka wuce gida, ranar tare duk aka yi girki masa da miyar alayyahu duk gidanjen dake kusa damu ta ɓangaren hagu da dama sai da muka kai musu abincin salla.


Abasiyya da Bilkisu tunin suka zo da raguwar sauran yayyenmu mata da suke zaune a cikin garin su Anty Maimuna, Anty Hasina, Anty Hajara, Anty Kubra duk sun hallara gefe guda kuwa ga Hanifa da naji daɗin zuwan ta fiye da na kowa. Tabarma aka baje a filin tsakar gidan muka zauna muka ci abinci tare har da yaya Majid da ya shigo cikin raha da annashuwa sai hiranmu muke yi yau dai gwanin ban sha'awa da burgewa. Sosai muka cika gidan don muna yawo ga kuma ƴaƴansu da suka zo dashi ga wanda bai sani ba sai ya zara wani ƙaramin biki ake yi a gidan kamar ko yaushe yaya Majid ya sayo katon katon ɗin drinks aka raba mana bayan an warewa su Baba nasu an kai sashin su. Maƙota da ƴan uwa tunin suka ƙara cika gidan munsha waya da Nawwara da Nazifa a ranar har a Umma da Anty Zakiyya sai da na ba wa suka gaisa kana muka yi sallama, muna zaune a ɗakin Hajiya Babba da su Anty Hasina da su Abasiyya sai Hanifa da nake riƙe da ɗanta mai sunan Baba ƙarami da aka ɓoye masa sunan ake ƙiransa da Adil tunda na ɗauki yaron nake bin duk wani sashin jikinsa da kallo, ba ɗan kaɗan ba yaron ya shige mini har ƙololuwar raina dukka da kasancewarsa zabiya hakan bai hana aihinin kyawun halittan yaron bayyana ba, bashi da hayaniya irin yawan kukan nan na yara. Furcin Hajiya Babba shi ya katse mini hanzari har na ɗauke idona daga gare shi.


"Da alama dai yaron nan ya shige ranki da yawa takwarata". Murmushi nayi har sai da ya bada sauti kafin na ce da ita"ƙwarai kuwa Hajiya wallahi yaron nan akwai shiga rai ina son yaran da babu ruwan su da yawan koke-koken nan".


"Gaskiya kam amma har yanzu ubansa bai san annabi ya faƙu ba, tunda da farko ma direwa ya yi akan cewar ba ɗansa bane sai da aka gudanar da wannan gwajin na zamani DMA yake ko menene?".


"DNA fa Hajiya ake cewa".


Abasiyya ta furta tana dariya, numfashi mai nauyi na sauƙe ina mayar da dubana ga yaron da yake baccinsa hankali kwance, ɗaurawa Hajiya Babba tayi da faɗin"Allah dai ya yi mana jagoranci amma lamarin mazan yanzu sai addu'a, mu a zamaninmu ko da cikin mace ta shiga maka gida yana rufa mata asiri ya kuma raini yaron tamkar jininsa. Balle kuma ace a kai maka matar salin ƙalin kuwa mu'amalan aure da ita har a sama ƙaruwa a haifi yaron ya lashi takobi ka ce ba tsatsonka bane don kawai Allah ya yi shi zabiya ko meye laifinsa oho? Allah dai yasa mu dace".


Haɗe baki muka yi wajen amsawa da amin a raina ina ƙara jinjina zancen na Hajiya Babba tabbas wani abun rashin ilmi ne ke kawo shi, ban da hakan menene laifin Adil don yazo a zabiya da har dalilin hakan zai sanya ubansa ƙaurace masa tun yana cikin jinin haihuwa? menene laifinsa tunda ba'a yi shawara da kowa ba lokacin da ubangiji zai tsara halittansa. Sauƙan zantukan Anty Hasina suka katsar mini da saƙa da warwaran da nake yi a zuciyana.


"Hmm kema da kinyi haƙuri kin zauna a ɗakin mijinki da daɗi da babu, da wataƙil yanzu kema nakin ƴaƴan ne zasu burge wasu har tayi ta marmarin su. Ga su Abasiyya sa'annin ki duk sun ajiye yaya bibiyu Balkisu ma banda cikin baya zama ai da yanzu ta ƙara ajiye wani ita kuwa Salma ƙaddara ta faɗa mata. Ina mamakin yanda hankalinki ya gushe har kika fifita abunda iya duniya zai amfane ki saman da ibadan ubangijinki Na'ima, karatun da anan duniya za ki same shi kuma ki tafi ki bar shi a nan ko meye ya shiga kan su Abba ma har suka ba ki wannan damar oho ni Hasinatu".
Tsif ɗakin ya ɗauki shuru kafin dariyar da Abasiyya take ƙunshewa ya bayyana ban ko ɗaga kaina na kalle ta ba balle na kai ga furta mata wani kalma, duk da kuwa har cikin raina dariyar tatan yafi ƙona mini rai sama da furcin Anty Hasinan cije leɓɓana nayi da ƙarfi kawai ina jijjiga kaina. Anty Hajara ce ta karɓe zancen da faɗin"haba ke kuwa maman Khalil ai idan za a sanya mutuwar auren Salma a layin ƙaddara to Na'ima kuwa dole ta amsa wannan ƙaddaran. Kowa yasan yanda ƙarshen auren Na'ima ya kasance abu ne kamar almara amma tunda shi aure rai ne dashi idan lokakinsa ya yi babu makawa sai an rabu ko da kuwa da soyayya".


Taɓe baki Anty Hasina tayi tana kawar da kanta gefe alamar maganganun Anty Hajaran basu ɗaɗata da ƙasa ba, kafin ta ce"idan da farko an laƙawa ƙaddara to ai gashi yanzu Salma zata yi ko nikam ga ƴa mace dai ma gajeren rayuwar da duk zata yi shi a ƙarƙashin wani ban ga alfanun wannan bokon ba, kwanan nan shi ya yi dalilin mutuwar auren

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login