Showing 111001 words to 114000 words out of 171161 words

Chapter 38 - MATAN AREWA BOOK TWO COMPLETE PDF .txt

kamar yanda ya faɗa hakan Mahmud ya aiwatar da umarnin nasan ba tare da ya kuskurewa wani abun. Su na isa gidan ya shige ɗaki ya kwanta yana maida numfashi a wahale ji yake yi tamkar ya sanya hannunsa a kai ya yi ta kurma ihu ko zai ji sausacin raɗaɗi da ƙunar da yake ji cikin ransa, kai tsaye shi dai kam ba zai ce an yi masa auren dole ba sai dai ya yi auren biyayya ga Anty Binta a matsayinta na uwa da uba a gare su. Sosai ƙirjina yake yi masa zafin tamkar ana watsa masa garwashin wuta ƙarfin hali da taurin zuciya gami da jarumtar da ya bashi damar amsa sunan cikakken namiji shi ne kawai ya ke sanya shi danne abinda yake jin yana barazanar tarwatsa mata allon ƙirjin. Allah ya san nufin sa kuma shi ne kaɗai masanin abinda ke taskace cikin tsokar naman zuciyansa baya jin zai iya ba wa kowacce iriyar mace lokacinsa balle har a kai ga batun soyayya ta gilma tsakanin su, macen ma wai Aishan da sam bai hangi nutsuwa ba balle kunyar ɗiya mace a tattare da ita baya son ya zamto azzalumi a zaman su da ita domin yana da tabbacin cewar bayan ci, sha, sutura da magance laluran rashin lafiyan da kan iya tasowa babu wani buƙatarta da zai iya biya mata a auratance, zai iya shiga haƙƙinta da yake tsoron tsayawa gaban ubangijinsa da wannan haƙƙin a gaban dukkan halittun duniya.


A hankali ya saki ɓoyayyan ajiyan zuciya mai ƙarfin gaske, yana mirginawa ya dafe kansa da yake sarawa kamar zai tsage gida biyu tunda aka zo masa da batun auren in ya zauna bashi da wani aiki sai na tunani da hashashen yanda rayuwar auren nasun zai kasance. Da ya rufe idanunsa hoton Na'ima ne ke yo masa gizo rabuwar su yanzu an doshi kusan watannin takwas amma ya rasa dalili ɗaya da ya sanya har yanzu ya kasa mancewa da ita duk da yana da yaƙinin cewar ba zai ƙara mallakanta ba. Babu shiri ya tashi zaune yana sanya dukkan hannayensa biyu ya dafe goshinsa, idanunsa suna lumshe yake faɗin"rabbi inni anzalta alaihir min khayrin faƙir ya Rabbi ka dubi lamarina ka kawo min sauƙi da sausauci ta hanyar da banyi zato ba balle tsammani. Ka cire min wannan baiwar takan daga cikin raina da tinanin da take zuwa a ko yaushe ya sauya min da abin da yafi zama alkhairi a gare ni".
Ya daɗe zaune cikin ɗakin shi ɗaya don Mahmud ma yana kawo shi ƙofar gidan ya sallame shi ya ce ya juya abin sa, jeranta ƙiran da ake yi masa cikin wayar salulansa dake yashe akan katifar wani na bin wani shi ya tilasta masa buɗe marafan idanunsa da suka yi masa nauyin gaske ya zube su akan wayarsa da sunan Yaya Auwal yake yawo cikin screen ɗin wayar har ya tsinke bai ɗaga ba, ƙiran Anty Binta ya kuma shigowa shima bai ɗaga ba sai da ta sake ƙira a karo na biyu sannan ya jawo wayar a sakalance ya ɗaga ƙiran tare da sanya ta a handsfree ya bar ta a wajen.
Muryanta ne suka dirarwa kunnuwansa dake nuna tsantsar fusatan da tayi akan rashin ɗaga ƙiran da bai yi ba da ake ta fama yin masa"sai yanzu kaga daman ɗaga ƙiran?, Yusuf ba fa zan juri rashin mutuncinka da wannan ɗiban albarkan ba tun wuri ka dawo dai-dai ɗinka kafin mu sanya ƙafan wando ɗaya da kai. Tun ɗazu iyayen yarinyan nan suke kawo kayanta za'a je ayi jere ana ƙiran wayarka a sanar maka ka kwashe naka kayan dake ɗakin su jere mata nata, amma ka maishe da mutane ƴan iska to duk inda kake kazo yanzu ina jiranka kuma ka tabbatar ka kwashe naka kayan domin gasu nan zuwa gidan da Mahmud".


Har ta ƙare zancen bai ce komai ba ya kashe wayar yana sauƙe ƙatuwar ajiyar numfashi, tare da zube idanunsa akan agogon wayar da yake nuni da ƙarfe biyun rana saura. Zumbur ya miƙe don ko ƙiran sallan zuhr bai ji ba balle ya yi ta, fitowa ya yi ya shiga banɗaki a gurguje yayo wanka sannan ya fito ya ɗaura alwala a gida ya yi sallan sannan ya soma shiryawa ruwan sararin samaniyan shaddan da suka yi anko da yaya Auwal da kuma Mahmud ya saka yana ɗaura agogo a tsintsinyar hannunsa ƙiran Mahmud ya shigo wayarsa bai damu da ɗagawa ba domin ya jin dirin tsayawar mota a ƙofar gidan da yake tabbatar masa da cewar sun iso, sai da ya gama shirinsa tsaf sannan ya haɗe jakan kayansa waje guda da ya dawo dasu daga makaranta. Fitowarsa daga ɗakin ya yi dai-dai da shigowar Mahmud cikin gidan yana faɗin"Yaya ina ta ƙiran wayanka daman sun iso ne zasu yi jere".
Kansa ya jinjina masa yana faɗin"su shigo katifan ciki kuma sai ku jiyo dashi ka ɗauka kana amfani dashi". Daga haka ya fice yaje suka gaisa da matan sannan ya wuce gidan Anty Binta cike da mata ya iske gidan ana ta hayaniyar da tun daga zaure yake jiyo ta yana shigowa kuwa ya tarar rikici ake yi tsakanin Anty Bintan da wasu matan da daga furcinsu ya gano wacce dangin mahaifin Husna ne. Yaya Auwal shi ke ta bata baki amma tana ƙara bijirewa ga wasu ƙawayenta da suke ƙara zugo ta, kansa ya jijjiga sa'ilin da idanunsa suka sauƙa akan Husna dake takure gefe guda tana sakin kukan da baya bayyanar da sauti illa fuskarta da tayi jajir da hawayen da suke ambali saman fatan fuskan.


Kansa tsaye ya nufa inda take durƙushe ya miƙa mata hannunsa ta riƙo ta miƙe, ficewa ya yi da ita daga cikim gidan suka shige ɗakin da Amir da Mahmud suke kwana dake zauren gidan bakin tabarmar dake malale cikin ɗakin ya yi mata nuni da idonunsa akan ta zauna. Zama tayi kamar yanda ya umarce ta sannan shima ya zauna yana fuskanto ta har yanzun yana iya jiyo ajiyar zuciyan kukan da take yi a hankali.


"Menene ya faru a cikin gidan?".


A sakalance kamar mai ciwon baki ko kuma wanda aka yi wa dole ya jefa mata tambayar, sai da ta zuƙe majinar kukan da yazo mata kafin cikin muryanta da take rawa ta soma faɗin"dangin Abba ne suka zo daga ƙauye shine suka ƙira ni suke yi min nasiha, cikin nasihar suka sanyo da cewar kar na biyo halin uwata in ba haka ba zaman auren ma sai ya gagare ni. Shine wata ƙawar Umma taje ta tsegumta mata ta fito suka fara wannan hayaniyar". Numfashi mai zafi ya furzar daga bakinsa tare da sauƙe ajiyar zuciya a lokaci guda kana ya ce"ki daina damuwa da ire-iren waɗannan abubuwan, nasihar su kuma ki ɗauke ta ki sanya ta cikin aiyukanki matuƙar basu kaucewa koyarwa addinin islama ba. Husna ki sa ni wata rayuwa ce yanzu za ki soma sabuwa wataƙil kuma ta zo miki da tarin ƙalubale amma ko yaushe ki sanya a ranki cewar aure bautar ubangijin ne kuma hanyar samun aljannarki ce, ki bi mijinki ki bi mijinki Husna kiyi biyayya a gare shi domin yanzu babu wanda yake da iko akan ki saman da mijinki ki kyautata masa iyakar iyawar ki. Sanna ki sanya haƙuri cikin dukkan lamuranki za kiji duk nasihar da za'a yi miki za'a ce kiyi haƙuri to ɗauki hakan dole sai kin zamto mai kauda kai ga wasu abubuwan, ki riƙe iyayen mijin tamkar naki haka nan ma ƴan-uwansa".


Sai da ya tsagirta kana ya ɗaura da"kar kiga a nan Ummanki na ɗagawa Abbanku murya kiyi tinanin kwatantan hakan a naki gidan auren, hakan babban kuskure ɗaga murya tafi na mijinki yayin da suke magana. Husna kar naji kar na gani kar ki kuskura ace wani matsala ta ɓullo daga wajenki don wallahi ba za ki ji da daɗi ba".


Kuka mai ƙarfi ta fashe mishi da shi, ya cigaba da yi mata nasihar da yake ratsa dukkan gaɓoɓin jikinta. Ya daɗe yana yi mata har Yaya Auwal shima ya shigo ya ɗaura daga inda ya tsaya, su da kansu suka kai ta har cikin mota suka sanya ta aka kai ta gidan aurenta.
Ranar yasha masifar Anty Binta kamar zata yi aron baki akan cewar bai je yaga Aisha ba bayan ɗaura aure, bai ce da ita komai ba har tayi ta gaji ya tashi ya bata waje. Wani fargaba na mussamman ne ya yi masa mamaya sanda ya tunkaro ɗakin da aka kawo Aishan take a ciki. Cak numfashinsa ya ɗauke na wucen gadi kafin ya dawo dukkan addu'an da ta fara zuwa bakinsa yake karantowa kafin ya yi ƙarfin halin ɗaga ƙafarsa ɗaya tare da ɗaga labulen ɗakin ya shiga bakinsa ɗauke da siririyar sallamar da ta tsaya iyakan leɓɓansa. Tana zaune akan gadon jeren da aka yo mata fuskarsa lulluɓe da mayafi kamar kowacce amarya zama ya yi a bakin gado idanunsa suna kallon sabuwar ledan da aka shimfiɗa a gabaɗaya ɗakin, sosai yake ƙoƙarin danne dukkan abinda yake ji yana taso masa a cikin ransa hannayensa ya haɗe waje guda kansa yana ƙasa ya furta"buɗe fuskanki".


"Kowacce amarya a irin wannan lokacin angonta shine buɗe mata lulluɓinta yayin da aka kawo ta cikin gidansa ranar farko. Zan so nima na sama wannan gatan daga gare ka mijina".




MATAN AREWA


© Maimunah Tijjani Iyam


_______________________________________




Page 9⃣7⃣


Sosai zantukan natan suka daki zuciyarsa, haka nan yake jin wani tuƙuƙun baƙin ciki na taso masa tare da yi masa dabaibayi a cikin ruhinsa. Bai ɗauko kansa ya kalle ta balle ta saka rai ga samun furcinsa gare ta illa miƙewa da ya yi ya shige banɗaki wanke fuskarsa ya yi yana saki ajiyar zuciya a jere a jere sannan yayo alwala ya fito. Babban rigarsa ta shaddan dake jikinsa ya zare ya ajiye akan kujera sannan ya soma mai yar da maɓallan hannun rigarsa da ya cire su yayin da yake alwalan.


A daƙile ya furta"ki tashi daga wannan zaman kije kiyi alawa kizo muyi salla". Sheshsheƙar kukan da ta soma yi shi ya bashi mamakin da ya sanya shi kai dubansa gare ta bai ce da ita ko kanzil ba duk da hauhauwan ɓacin ran da yake ji a cikin ransa.


"Ba zan zaton hakan a ranata ta farko a cikin gidan aure ba, sannan a yanda ƙawayena da suka riga ni yin aure suka bada labarin yanda ranar su ta farko ta kasance a gidan miji ya sha bambam da ni abinda na tarar".


Tsiririyar tsaki ya tsirgar yana naɗe hannayensa a ƙirjinsa duk da baya jin ko burge shi tana yi balle kuma ya ji motsin soyayyarta cikin ransa, baya ƙaunar Allah ya tsayar dashi ranar sakamako da laifin tauye maka haƙƙinta. Hakan ne ya sanya shi fara takowa a hankali har ya iso gaban ta hannu ya sanya ya yaye mata lulluɓin kanta da ya fara jiƙewa da hawayen makirci da kissan da ta soma yi. Caraf ta riƙe hannunsa cikin nata da sauri ya watsa mata idanunsa da babu alamomin wasa a tare dasu babu shiri ta sake shi a bayyane ya yi tsaki yana shafa gefen fuskarsa. Zama ya yi tare da lumshe idanunsa yana jin motsin tashin ta ta shige banɗaki babu jimawa ta fito, ya miƙe ya shimfiɗa sallaya sannan suka gabatar da sallan sai da ya shafa doguwar addu'ar Allah ya bashi ikon cinye wannan jarabawar da ta kunno kai a cikin rayuwarsa sannan ya shafa addu'ar yana naɗe ƙafafunsa wajen guda tare da fuskanto ta da tun ɗazu yake jin idanunta a bisa jikinsa.
Sai da ya yi gyaran murya kafin ya soma faɗin"burinku ya cika an ɗaura wannan auren yanzu kuma ya rage naki kiyi haƙuri da dukkan abinda auren kan iya izuwar miki dashi na tarin ƙalubale, ki cire lissafin ƙawaye daga cikin kanki ki kuma yi farayi da labarurrukan da suke ba ki game da rayuwar gidan aurensu da mazajen su. Kowa da irin hali da yanayinsa sannan abinda wani ya yi aka bashi kuɗi wani idan ya kwaikwaya duka zai sha, ban yi mika alƙawarim samu na yanda kike tsammani ba domin ba zan ɓoye miki ko kuma nayi faɗa miki abinda nima kaina nasan cewar ba haka yake har cikin zuciyata ba, bana jin akwai wata macen da zata iya samun wani matsayi a cikin zuciyata a halin yanzu zan yi iya ƙoƙarin ganin ban cutar da kai a zaman da zamu yi".


Tunda ya fara maganar bata ce dashi komai sai ma bin shi da kallo da take yi, sai da ya ɗage mata ido ɗaya sannan ta ɗauke idonta tana faɗin"ba matsala hakan ma ya yi min".


Miƙewa ya yi yana jin wani jiri mai ƙarfin gaske yana walagigi dashi da ƙafafunsa da suke alamta masa gazawar su ga juran ɗaukar nauyin gangar jikinsa da ya yi sanyi ƙalau, ficewa daga yi daga ɗakin ya koma falo ya zauna yana bin ko'ina da kallo tare da tinanin lokacin da aka yi jeren Na'ima da ya amshi ɗakin ya fara ziyartar kwanyasa ƙarƙarfan ajiyan zuciya ya sauƙe yana godewa Allah ya da ƙaddaro rabuwar su da Na'ima cikin lokacin da dukkan su bashi shiryawa hakan ba.


Tsawon ranar bai runtsa ba kamar dai jiya, tare da yaya Auwal suka je masallacin asubahin da shi yake yin limanci tun kafin tafiyarsa ƙarin karatu. Sosai Yaya Auwal ɗin ya ƙara yi masa nasiha da shawartarsa akan ya nema zaɓin Allah, a gurguje ya yi wanka ya shirya zai fice. Sai da ya ji muryarsa ya tina da cewar ya ajiye mutum mai numfashi a cikin ɗakin.


"Ina zaka je da safiyar nan?".


"Ina tsammanin akwai baƙin da zasu zo kamar yanda yake a al'adance, ko kuma in zauna za ki bani saƙo?". Saurim jijjiga masa kanta tayi tare da sunkuyar da kanta saboda tsare da idanunsa da bata iya jura kallan cikin su kai tsaye da ya yi, ɗaurawa ya yi da faɗin"ga can abinci a falo Maman Hanan ta aiko dashi". Yana dasa aya ya fice daga ɗakin bai iske kowa a tsakar gidan ba don haka kansa tsaye ya sanya zai fice daga cikim gidan muryar maman Hanan da suka sauƙa a ƙofofin kunnuwansa suka tilasta mishi dakatawa.


"A'a ango ina zuwa da safiyar nan?".


Sai da ya gaishe ta ta amsa kafin ya ba fa amsar tambayar cikin faɗin"makaranta nake son na leƙa".


"Wani irin makaranta kuma Yusuf?, kai da kake sabon ango ai makarantar ma zata haɗa maka ƙafa haba".


"Ba matsala zanje kawai ba daɗewa zanyi ba".


"To abin karin ba da na shigar muku?".


Sai da ya gyara tsayiwarsa kafin ya ce"zan ci inna fita sai na dawo". Daga haka ya fice makarantar ya nufa don tun dawowarsa garin zuwansa bai fi a ƙirga ba saboda tashin hankali da rashin nutsuwar da yake a ciki. Yana isa ya zarce ofishin bai ba wa kansa damar faɗawa tinanin da ya ɗaukarwa kansa alƙawarin ko bai daina gabaɗaya ba zai rage, wasu takardu ya ɗauko ya fara dubawa sannan ya kunna karatun al'ƙur'ani a cikin wayarsa. Shigowar Hashim ya sanya shi ɗauke idonsa daga kan takardun ya zube shi a kansa da yake tsaye yana bin sa da wani irin kallon da yafi kama da na mamaki da al'ajabi. Ɗage masa ido ɗaya ya yi alamar lafiya ya ba ki baki haɗi da cewar"wai mamaki ne ya hana ni magana, angon da aka ɗaura aurensa jiya jiya shine yau ya fito wajen aiki haba Yusuf to ita amaryar fa da wa ka baro ta?".


Murmusawa ya yi yana ɗaura ƙafarsa ɗaya kan ɗaya kafin ya soma cewa"tana gida mana ko so kake na zauna duk baƙon da yazo ya tar da ni, munyi sallama da ita kuma da amincewarta ma na fito".
A harɗe ya ƙare zancen don shi ma kansa yasan cewar ba dai-dai ya faɗa ba, sai dai baya daga cikin irin jerin mutane da suke fitowa ƙiri da muzo su bayyanar tsananin ƙiyayyar su ga matansu ga abokan su, duk da Hashim ya wuce aboki a gare shi kai tsaye sai dai ya ƙira shi da amini amma ba zai iya bayyana masa lamarin da ya shafin zaman aurensa da iyalinsa ba. Babban kuskure ne fitowa kana bayyanar ƙiyayyarka ko kuma tsanarka ga matarka a gaban abokanka yana ɗaga daga cikin abinda suke jawo saurin zubewan mutumcin mutum a idanun jama'a.


"Aw lalle kam masoya".


Taƙaitaccen murmushi ya yi ya ce"in gaji haushi kaima gobe a ɗaura naka auren". Dariya gabaɗayan su suka fashe dashi ranar a makaranta ya wuni da ya tashi ya biya ta gidan Anty Binta kafin ya wuce gida kamar jiya yau ma a falo ya kwana haka nan babu wani dogon zancen da yake shiga tsakanin su, sai dai hakan bai hana shi sanya ido akan ta ba sosai mussamman fannin addinin da ya lura bata da sani a gansa. Kwanci tashi suke shafe kwanaki bakwai cur cikin wannan halin a rana ta takwas ɗin Anty Binta ta zo gidan. Maman Hanan kawai ta iske a tsakar gidan tana gyara kayan miya ganin ta ya sanya ta saurin tashi ta shimfiɗa mata tabarma ta zauna tare da gabatar mata da ruwa sha sannan ta gaishe ta, a daƙile kamar wacce aka yiwa dole ta amsa tana ɗaurawa da "Ina ita Aishan take? ko kuma daga zuwan ta halin nakin kika fara nuna mata na ƙin mutane ki bin baza ƙafa a gida ke ba haihuwa kike yi ba tun daga rasuwar Hanan kin naɗe mararki har yanzu ko ɓatan wata ba ki yi ba, to daman zuwan nan nawa naki ne domin nazo na ja miki kunne na taso ƙafa na ƙafa takanas a kano na zo, kar kiga Aisha yarinya ƙarami ki dunga yi mata shigo-shigo babu zani kina cutar ta da sunan kina janta a jikin ki wallahi zan yi mummunan saɓa miki Habiba. Kamar yanda kike taƙama da nan gidan mijinki ne ita ma haka ne gare ta don haka ki kiyaye ni".


A sanyaye ta furta"Allah ya huci zuciyarki Anty ban taɓa nuna mata wani halin da zai sanya ƙin fitowa filin tsakar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login