Showing 147001 words to 150000 words out of 171161 words
Chapter 50 - MATAN AREWA BOOK TWO COMPLETE PDF .txt
ya kaimu jibin".
"Amin daman mun tara ku har da ƴaƴanku a kan wannan maganan, domin daƙile zancen cewar iyayen Adamu ne suka kawo wannan kayan da yake yawo a tsakanin ku. Babu wani danginsa da ya zo gidan nan, don haka ku cigaba da shirye-shiryen ku jibi ɗaurin aure babu fashi in mai komai mai kowa ya nufa".
"A'a wallahi da sake wai an ba wa mai kaza kai, wani irin munufurci za'a sanya lokaci biki amma cikin mu gabaɗaya babu wanda ya sa ni sai da abu ya matso gab. Kuma a haka a dubi tsabar idanun a ce damu wai auren ɗiyar mu".
A zafafe Umman su Anty Kubra take zance tamkar mai aman wuta tana wani irin huci, har tayi ta kammala babu wanda ya katseta sai da ta gama Baba ya soma cewar"Zainabu yanzu cikin kalamanki mu ne munafukan kenan?".
"Bakina bai ce haka ba ai ko su waye sun san kan su". Ɓacin ran da ya bayyana akan fuskarsa ya sanya Hajiya Babba hana shi yin wani zancen ta umarci Goggo Jummai da tazo ta buɗe akwatunan kowa ya ganj hakan ta yi ko wanne sai da buɗe shi tare da ɗaga kayayyakin dake cikinsa. Tufarkallah masha Allah wallahi sai dai zuciyar da hassada ta yiwa kanta zai gushe wannan kayan.
Rai a ɓace aka fara ficewa daga falon, ni dai daga nan ɗakin mu na nufa na iske su Nawwara na shigo mana da abinci muka ci muka fara shirin kwanciya. Raina fari ƙal domin ko ba komai Anty Zakiyya ta fita kunya da yawa daga cikin mutanen gidan sai da muka je muka yiwa Umma sai da safe kana muka kwanta. Asubar fari muka tashi muka yi salla, fitowa ta kenan daga banɗaki zan ajiye butar hannu tashin zancen da yake fitowa daga ɗakin Umman su Anty Kubra da nake hange haske tocila ya ɗauraye ɗakin suka yi sallama a ƙofofin kunnuwana.
"Hmm ai ba komai Allah ya kaimu jibin mu sha kallo, wataƙil ma sadakan ta aka bayar a masallaci shiyasa ake ta rufa-rufa da zancen ba'a son a sa ni in ba hakan ba ma wani mai hankalin ne zai yi sha'awar auren Zakiyya. Yarinyar da ta gama gantalewa a titi ta tsufe a cikin gida duk matan duniyar nan ta malikiyo muddin bai ga kowa ba sai ita, a dai kawai lauje cikin naɗi".
Ƙatuwar ajiyar zuci mai nauyi na sauƙe ina jin ƙafana yana rawa, bana ƙaunar jin ragowar zancen kamar yanda bana buƙatar jin da wanda take zancen don haka na ja ƙafafuna na koma ɗakin. Ranar tun kafin sallan zuhr yara suka fara ihu ga Goggo Suwaiba ga Goggo duk muka bayyano waje na rungume Anty Zakiyya tsam a jikina muka yi ɗaki, riƙe baki nayi yabon kyau da sheƙin da fatarta tayi kamar wani sabon halitta haka matan gidan da ƴaƴan su suka kai ta shigowa kallon Anty Zakiyyan da har wani ƙiba tayi ta fuskanta. Umma Salma da ta kasa riƙe abunda ke ranta sai da ta fallaso shi waje ta ce"Hmm ayi dai mu gani duk wannan gyare-gyaren da aka yi zaman gindin murhu na haɗa itace ma kaɗai ya isa ya ƙonar da fatan da aka gama jemewa".
Bayab sallan zuhr dangin Umma suka iso daga geidam haka nan ma gayyan Hajiya Babba mutan maiguduri, su yayun mata ma duk sun zo ko ba don Allah ba don kashe ƙwarƙwatan idanun su haka nan ma Abasiyya, Salma da Balkisu duk sun zo. Da yamma aka fesawa amarya ƙunshi kasancewar yawancin ƴan matan da suka zo daga dangin Umma sun iya.
Ni da su Nawwara ma aka zanzara mana tare da yi mana kitso, kusan rabin kwana muka yi muna hira abin gwanin ban sha'awa. Wannan ne karon farko da aka fara auran da mutum ɗaya a gidan mu ba tare da an haɗa da yawa ba amma yawan jama'an na daban ne.
Washe gari tun asuha su Abba suka aiko ƙiran Anty Zakiyya nasiha suka haɗu suka yi mata mai kashe dukkan gaɓoɓin jiki, Hajiya Babba, yaya Majid da su Goggo duk sun yi mata hakan ma Umma. Ummu-Abiha ƴar ɗiyar ƙanwar Umma ita tayi wa Anty Zakiyya kwalliya da tayi shigar shuɗin leshi mai zane-zane ruwan zuma ɗas ta fito kamar ba ita kwalliyyar ta zauna mata sosai a fuska, dai-dai sauƙowa daga sallan juma'a da ya yi ɗai-dai da ƙarfe biyun rana lasifikan masallacin dake kusa da gidan mu aka yi shelan sanar da aurin auren Zakiyya Muhammad Kabir da angon ta Saifuddeen.
Zamewar da Anty Zakiyya tayi daga tsayiwar da tayi izuwa ƙasa shi ya jawo hankalina izuwa gare ta, na isa wajen da sauri tare da jan hannunta muka yi ɗakin mu da yake da sauƙin mutane, a ruɗe na ke jeranta mata tambayoyi.
"Lafiya meye ya faru?, wani abun ne ya faru Anty Zakiyya?". Har na ƙare bata amsa mini ko ɗaya ba sai can ta ce"Na'ima bacci nake yi ko bacci nake yi nake mafarkin an ɗaura min aure ko?, don Allah ki tashe ni ki tashe ni". Ban san san da hawaye suka ziraro daga idaniyata ba sai jin sanyin su nayi. Sai da na aro jarumta na yaɓa cikin son bata ƙarfafa mata gwiwa na soma faɗin"Anty Zakiyya ba bacci kike yi ba kuma ba mafarki bane a zahiri komai suke wakana, yau ake ɗaurin aurenki kema za ki tafi gidan mijinki za ki tafi ɗakin ki domin neman aljannanki. Ki daina wannan kukan ai shi mai rai baya taɓa cire tsammani daga rahaman Allah kuma aure lokaci matuƙar ya yi dole ayi shi ko da shiri ko babu".
Har yanzu hawaye bai bar gudana a fuskarta wanda nasan ko bata furta mini da baka ba, zubar su yana da nasaba da abinda zuciyata take tinano na gori, tsangwaman, ƙage da ƙarafin da ta fuskata a dalilin jinkirin auren da ya faɗo a tsagin ƙaddararta. Sai da ta saki sakakken ajiyan zuci kana ta ce"tabbas komai lokaci kuma dukkanin jinkiri alkhairi ne ga wanda ya yarda cewa hakan daga Allah yake yi, zancen ki gare ni kenan a ko yaushe idanuna suka zubar da ƙwallan baƙin-ciki sai gashi yau suna zubar da na farin-ciki". Hannunta gam na damƙe cikin nawa ina goge mata hawayen da ya yi kwance a fuskarta.
MATAN AREWA
(Book two)
© Maimunah Tijjani Iyam
___________________________________
Page 1⃣1⃣5⃣
Habaici, gogar zana da shaguɓe ranar babu irin wanda ba'a yi ba, ƙarara wasu suke bayyanar da baƙin-ciki da haddasa gami da ƙyashi a fili ba tare da su sakaya shi ba. Bamu mayar da hankalin mu gare su domin nasihar da Umma ta yi mana akan mu gani mu ƙi gani mu ji muyi kamar bamu ji ba. Mun sha hotuna domin masu ɗaukar hoto har biyu aka ɗauko, su Anty Maimuna da sauran yayun mu duk a gida suka kwana haka nan ma su Abasiyya Salma ce kaɗai ta koma gidanta. Sai washe gari za'a kai ta don haka ranar ma baccin mu ragagge ne, Goggo Suwaiba, Goggo Jummai, Umma Talatu ƙanwar Umman mu da kuma Hajiya da su za'a tafi. Duk yanda Umman Salma ta zo zuwa gami da dagewa Hajiya Babba akan ta sanya sunanta cikin masu zuwa hakan bai yiyu ba.
Ni da su Nawwara ma su Abba cewa suka yi mu bi su mu koma makaranta tunda gari ɗaya ne muna gama karin kumallo muka shirya. Shiryar ruwab madaran liffaya Anty Zakiyya tayi da tayi mata matuƙar kyawu gami da amsar jikinta ya yi mata ɗas, sashin su Abba aka fara kai ta suka ƙara yi mata nasiha sosai sannan aka wuce da ita sashin Hajiya Babba ita nasihar ta ƙara yi mata da umarnin yiwa mijinta biyayya akan komai matuƙar bai saɓawa hanyar Allah da manzonsa ba, daga nan sashin mu aka dawo da ita wajen Umma ita ma ta ƙara tisa masa tilawar nasihohin da su Abba suka yi mata.
Kafin aka fito da ita zuwa ɗakunan matan gidan, ni da Daada muke riƙe da hannayenta don liffayan ta sauƙo ta rufe mata fuskarta gabaɗaya. Ɗakin Umman su Anty Kubra muka fara shiga Daada ta zaunar da ita haɗi da faɗin"to ga amarya fa za'a wuce da ita kuyi mata nasiha da kuma shawarwari".
Taɓe baki tayi gami da kawar da kanta gefe guda kana ta furta"yo wani nasiha kuwa zan mata menene sabo gare ta namijin ne bata sani ba ko menene?, uhmm Allah ya tsare hanya ya bada zaman lafiya".
Wani abu naji mai zafi ya dira dai-dai ƙahon zuciyana yana sukar ta danne zuciyar da take yi mini dingwal-dingwal nayi ba tare da na ɗago kaina ba, ina cije lebbana da matuƙar ƙarfi tare da ƙara ƙarfin riƙon da nayi wa hannun Anty Zakiyya da yake cikin nawa.
A sama naji Daada na faɗin"ashsha haba ke kuwa wannan wani irin magana ne?, ko da yake ai kin gama komai da kika ce Allah ya basu zaman lafiya daman shi suke nema tashi mu tafi Zakiyya".
"Kayyar banza gayyar tsintsiya babu shara".
Umma su Anty Kubra ta faɗa tana rako mu da tsaki yayin da muke ficewa daga ɗakin, duk ɗakunan da muka shiga ire-iren zantukan Umma su Anty Kubra suke yaɓowa hakan ya ƙara ƙarfin kukan da Anty Zakiyya take da tun tana yin sa a ɓoye har ya bayyana.
Isowar mototin ɗaukar amarya ya sanya aka fito da Anty Zakiyya dake ɗakin Umma ta kifa kanta akan gwiwar Umman tana sakin wani kukan mai narkan da zuciyar mai sauraron ta, duk mutanen suka fito baranda suka bar su su kaɗai dangin Umma ne suka fito da ita bayan ɓanɓaro ta da ƙyar daga jikin Umma aka sanya ta a cikin motan.
Mototi uku ne suka zo ɗaya amarya da Goggo Jummai da Hajiya suna a ciki, ɗaya kuwa ni da su Nawwara sai ɗayan kuma Goggo Suwaiba da Umma talatu sai Nurain da ya kafa ya tsare akan zai je Hajiya Babba ta ce ake dashi.
Har muka isa muna hira sai da naji motar ta tsaya yana danna horn sannan na ɗago kaina tare da sauƙe idona akan gate ɗin da aka fara buɗewa ta ciki, har ya dai-daita parking ina bin farfajiyar gidan da kallo ba wani girma ne dashi ba sai dai ya tsaru iya tsaruwa dai-dai misali babu ƙarya da ƙarairayi.
Wasu mata ne suka fito tarban mu cikin fara'a da tsantsan murnar da ya bayyana a bisa fuskokin su, tare da nufar inda Anty Zakiyya take. Kalmar masha Allah kawai suke ta maimatawa har muka isa cikin wani falo muka zauna muka gaigaisa da juna, wata farar dattijuwar mace mai cikar haiba ta furta"ƴata tazo nan ki zauna".
A nutse Anty Zakiyya ta taro ta kuma jefen ta ta zauna, idanu ta ƙura mata tana cewar"masha Allah, Allah ya baku zaman lafiya ya kaɗe hau a cikin zaman ku".
"Amin".
Muka haɗe baki wajen amsawa, kafin ɗaya daga cikin su ta miƙe tayi mana jagoranci izuwa part ɗin Anty Zakiyya da suke kallon juna kujerunta da tun jiya bayan ɗauri aure motar kayan ta yo gaba sun zauna ɗas a falon, uwar ɗaka muka zarce shima komai an kimtsa shi a matsugunin sa alawala muka shiga banɗakin dake cikin ɗakin muka yi sannan muka yi salla.
Goggo Suwaiba ta ƙira su Abba ta sanar dasu mun iso lafiya, abinci aka kawo mana hula-hula muka ci muka ɗaura da zoɓo. Haka nan ma wayewar gari tun safe aka kawo mana abin kari sannan suka shigo muka gaisa sai da bayan sallan asr da su Goggo zasu koma mu kuma zamu koma makaranta ango ya zo shi suka gaisa tare da yi musu godiya gami da ban gajiya.
Buhun shinkafa, katon ɗin taliya da ƙaramin jakan mai da manja da dubu hamsin a sama aka haɗo su dashi.
Mahaifiyar da ƙaninsa tabbas sun cika mutanen kirki kuma na ƙwarai domin sun yi mana tarba ba mutuntawa gami da girmaman wanda da wuya mu mance dashi, sanda zamu taho Anty Zakiyya har da kukan ta bil-haƙƙi haka muka rabu cike da kewar juna. Suka sauƙe mu a makaranta su kuma suka wuce potiskum domin motar da ta kawo ce zata maida su.
Zaune yake ya tisa kwanon abincin a gaban sa ko cokali ɗaya ya kasa kaiwa bakinsa illa juya cokalin da yake cikin abincin, a karo na barkatai ya saki wasu gwaurayen ajiyan zuci yana lankwashe ƙafafunsa wajen guda sai da ya ajiye cokali kana ya sanya hannayensa ya tallafo kuncinsa tare da faɗawa duniyar tinanin da ya saba.
Tun ɗazun take bin shi da kallo tana daga tsaye a ƙofar ɗakinta, a hankali ta sauƙe numfashi Allah ya sa ni tana son Yusuf har cikin ranta soyayyar da take yi masa ya sanya amincewa da auren sa tare da ajiye duk wasu halayyan da take yi a gefe ta rungumi zama dashi. Matsalarta ɗaya Anty Binta da har yanzun take da ƙudurin koya mata hankali ta hanyar fahimtar da ita karan bana shine dai-dai maganin birin maguzawa.
Takowa tayi ta zauna a kusa dashi cikin kwantar da murya da sausauta amonsa ta soma faɗin"lafiya kuwa? tun ɗazu ko abincin ka kasa ci". Idanunsa da suka fara sauya launi ya ɗago ya zube su akan fuskarta sau da yawa yasha yunƙurowa da nufin sallamar Aisha sai ya fasa bisa dalilin da shima kansa bai sani ba, ɗabi'u da halayyarta yake son ya sauya mata su ta hanyar maishe da ita nagartacciyar mace kafin su rabu.
Sai da ya fesar da iska daga bakinsa yana ɗauke idanunsa daga gare ta kana ya sama damar faɗin"lafiya ƙalau kawai bana jin daɗin yanayin yau ɗin ne".
"Da dai ka daure ka ci ko kaɗan ne". Ta faɗa cikin marairacewa rurin da wayarsa ta soma yi shi ya katse shi daga zancen da yake son yi ya ɗaga ƙiran Anty Bintan.
"To gani nan zuwa" kaɗai ya furta yana katse ƙira yana ɗaurawa da faɗin"ki ajiye shi inna dawo zan gwada ci, zan je Anty Binta na nema na".
Har ya fice ba ta ce dashi komai ba saboda zafin da zuciyarta yake yi mata a duk lokacin da ya ambacin sunan Anty Bintan a gaban ta, ƙwafa tayi tana ɗebe kwanunka ta kai cikin kitchen.
Cikin mintuna ƙalilan ya isa saboda ƙiran wayan da Anty Bintan take doka masa wani na bin wani, tare da yaya Auwal ya iske su zaune gefe guda kuwa Husna ce durƙushe ta ja hijab ta rufe gefen fuskanta dashi. Sai da ya zauna ya ce"lafiya kuwa?ita kuma wannan meya kawo ta ina mijin natan yake?". Babu wanda ya bashi amsa a cikin su illa kuka mai ƙarfi da Husnan ta tuntsire dashi har jikinta rawa yake yi, a tsawace yaya Auwal ya ce"za ki rufewa mutane baki ko sai na tattaki a nan, yi mana bayanin abinda ya faru".
Sai da ta haɗiye kukan da yake taso mata kana cikin dushashewar murya ta zama damar jawo numfashinta da yake sarƙafewa a ƙirji ta soma cewar"kawu Safwan matan banza yake bi tun yana yi a ɓoye har wataran Allah ya toni asirinsa na kama shi, ya yi min rantsuwa akan ya daina ashe bai daina ba ya kai ya kawo har cikin gida yake kawo su. Su shafe tsawon satikai da na mishi magana sai ya hau duka na ya daina ciyar dani sai dai na ɗauki kwano na fita in bin gidajen ina yin bara tamkar almajira ko marar galihu ya ƙwace wayana ya hana kowa shigo gidan, yawon neman abincin da nake yi ma ya hana ni idan zai fita sai ya sanya makulli ya rufe gidan ta waje sai sanda ya yi ra'ayin dawowa".
Daga haka ta tsagaita saboda kukan da ya ci ƙarfin ta babu wanda ya ce da ita ko kanzil balle kalmar lallashi sai da tayi mai isar ta sannan ta ɗaura da faɗin"bani da iko magana domin ya ce dani da baiwa duk ɗaya ne a wajen shi, tunda kuɗi ya sanya ya sayo ni kuɗi uwata ta gani ta bashi ni don haka duk abinda na ci karo dashi sai na yi kuka da ita. Idan yana son yin mu'amala dani haka zai danne ni kamar dabba ya shaƙe min wuya, jiya ya dawo ya sanar dani cewar daga asibiti yake kuma an tabbatar da yana ɗauke da cuta mai karya garkuwan jiki don haka na haɗo kayana na dawo gida ayi min magana shi ma ya ji da kansa".
"Ya ba ki takardan ki ne?". Yaya Auwal ya yi gaggawan jefa mata tambayar kanta ta jijjiga masa tare da faɗin"A'a". Da damuwa ɓaro-ɓaro akan fuskarsa yake faɗin"innalillahi wa i nna ilaihir raji'un Anty kin ga abinda nake gudu ko?, kin ga irin ranar da nake guje mana zuwan ta ko?, gashi tun ba'a yi nisa abubuwa sun fara gajulewa".
"Haba Auwal kuma sai ka ce ba musulmi ba baka san ƙaddara bane? waye ya isa ya gujewa ƙaddararsa". A cikin wani irin yanayin ta yi zancen da ya fi ƙarfin ruɗewa. Sai a lokacin Yusuf ya ce"ya kamata a sanar da mahaifinta halin da ake ciki".
"Yusuf ba za'a sanar da kowa ba idan ku a matsayin ku na ƴan-uwana ba zaku taru ku rufa min asiri, mu nemawa yarinyar nan lafiya ba sai an sanar da wani to Allah wadaran ƴan-uwantakan". CikeSausauta muryarsa ya yi"Allah ya ba ki haƙuri ba haka nake nufi ba, yanzu ta tashi muje asibiti a gwada ta".
MATAN AREWA
(Book two)
© Maimunah Tijjani Iyam
_________________________
Page 1⃣1⃣6⃣
Tunda suka fice daga gidan Anty Binta take safa da marwa a cikin gidan, babu abinda take yi illa ta kai mari ta kai bango dake zaune a gefe yana bin ta da kallo ya tsirkar da tsakin takaici, cikin ɗacin rai ya soma cewa"to wai Mama duk wannan damuwar na meye ne?, in ce dai lokacin auren nan ke kika fi kowa dagewa da zaƙewa a kai to kuma ai yanzu duk abinda ya faru bai kamata ki wani damu ba".
Kamar kububuwa haka ta juyo da nufin rufe