Showing 66001 words to 69000 words out of 171161 words
Chapter 23 - MATAN AREWA BOOK TWO COMPLETE PDF .txt
damunsa ba. Koda aka iddar da sallan a masallacin ya yi zamansa yana son ya kunna wayarsa ya ƙira yaya Auwal sai dai sam a yanzu bai shiryawa tarin tambayoyin da zasu yi masa ba musamman ma faɗan Anty Binta da yake da yaƙinin koman daren daɗewa zai ta juye masa ita kwando kwando tunda ya sanya ƙafa ya shure umarninta ya yi tahowarsa ba tare da sanin kowa daga cikin su ba.
MATAN AREWA
(Book two)
© Maimunah Tijjani Iyam
___________________________________
Page 7⃣0⃣
Tunda ya baro cikin makarantar yake zuga gudu akan shimfiɗaɗɗan hanyar da zata sada shi da asibitin da zashi, a kai a kai yake sauƙe ajiyar zuciya mai ƙarfi da kuma sauri yana karanto sunayen mahaliccinsa ɗari ba ɗaya cikin bakinsa a ƙoƙarin dawo da nutsuwarsa da ya fara yin nisan zango da barin gangar jikinsa.
Babu shiri ya gangarar da motar izuwa gefen titi ya faka ta tare da dafe kansa, innalillahi wa inna ilahir raji'un yake ta maimata cikin bakinsa tare da tuntsure idanunsa da suka fara rufewa sama sama yake jin tashin hayaniyar mutanen da suke gefen titin da ya kusa afkawa wani mai saida rake.
Har suka iso wajen motar ya gaza yin koda ƙwaƙwaran motsi ne balle ɓalle murfin motar ya fito waje, illa ajiyar zuciyar da yake sauƙewa babu ƙauƙautawa. Knocking da aka fara yi a gilashin motar ya sanya shi yin ƙoƙarin buɗe idanunsa sai dai hakan ya gagare shi, ƙara dafe goshinsa ya yi a karo na barkatai da yake jinsa tamkar kana zai rabe izuwa gida biyu tsabar sarawan da yake yi masa, duk wata addu'ar da ta zo bakinsa yake yi koda kuwa na mecece yana ƙarawa da addu'ar Allahu ya sanya ba ciwonsa bane zai tashi duk da kuwa dukkanin alamominsa ne suka bayyana yanzu a gare shi. Babu shiri yaji an buɗe ƙofar motar an fizgo shi waje tare da wancakalar dashi gefe guda ya faɗi saboda rashin ƙarfin da yake ji bai da shi balle kuzari.
"Malam mahaukaci ne kai?, zaka nufo kan mutane da wannan irin gudun kamar zaka tashi sama, kuma tsabar rashin sanin darajan ɗan adam irin naku na masu abin duniya shine ka fito ka bada haƙuri ma ya gagare ka hakan ya zamo aiki gagarumi a gare ka. Tunda daman ire-irenku basu san darajan talaka ba wataƙil ma yanzu shaye-shayensa yaje ya yi har ya fita daga hayyacinsa yazo nan yake ƙoƙarin kashe mu a banza da wofi".
Dishi-dishi yake ganin mai maganar da yake yin ta cikin ƙololuwar ɓacin ran da ta bayyana ɓaro-ɓaro a cikin furcinsa, amma baya iya ganin fuskarsa so yake yi ya basu haƙuri sai dai ji ya yi tamkar an sanya masa kirtani an zarge masa bakinsa ta yanda ko kalma ɗaya ba zai iya furtawa ba.
Ajiyar zuciyar ya cigaba da sauƙewa kawai kafin ya yi ƙarfin halin miƙewa akan ƙafafunsa da suke matuƙar rawa, ya haɗe dukkan hannayensa waje guda alamar roƙo cikin tangaɗi kamar zai kife ƙasa ya tako izuwa gaban wanda ya yi maganar ya riƙo hannunsa, ƙudi ya zaro daga aljihunsa ya damƙa masa cikin hannunsa da yake riƙe dashi ya shige motarsa tare da danna masa lock ya kifa kansa akan sitiyarin motar yana kokuwa da numfashinsa dake tsaya masa a iya ƙirji.
Ya daɗe cikin wannan halin har izuwa lokacin da ya fara jin sauƙin nauyin da ƙirjinsa ya yi masa, da kuwa cushewar numfashin da yake fama dashi ya ɗago kansa tare da buɗe idanunsa ya zube su akan titin har yanzu ba komai yake gani tar ba, tada motar ya yi tare da cillata akan titi yana jin wani sabon karsashi yana mamaye zuciyarsa mai rauni tina da ya yi da mahaifiyarsa dake can kwance a asibiti rai a hannun Allah da kuma gudan jininsa ɗaya tal. A hankali yake driving ɗin ji yake yi kamar motar ne yake jansa ba shi yake jansa ba.
Ikon Allah ne kawai ya kai shi asibitin tun kafin ya gama dai-daita parking ya kashe motar ya fito yana haɗa hanya kamar ɗan maye, emergency ward ya nufa har yanzu yana riƙe da goshinsa da kansa yake tsananta sarawa ganinsa ya sanya Farouk saurin tasowa ya isa gare shi tare da riƙo shi.
"Yaya Saif meya faru da kai?".
A ruɗe yake yi maganar saboda ganin halin da ɗan uwan nasan yake ciki, murmushi yake son ya ƙaƙalo ya yi masa ko don halin da yaga ya shiga daga ganinsa amma sam ya kasa riƙo hannunsa kawai ya yi ya damƙe tare da fizgo numfashinsa da ƙyar kafin ya sama zarafin furta masa"Ina Ummi?".
"Tana ciki likitoti ne a kanta, jini ake sanya mata amma ana sawa yana fita tun ɗazu suna ciki basu fito b...".
Saurin rungumo shi ya yi ya sanya a jikinsa ya rungume shi gam yana shafa bayansa. Ƙoƙari yake yi ya danne hawayensa da baya iya zubda su a gaban kowa sai a gaban Umminsa.
Bai janye shi daga jikinsa ba haka suka zauna akan kujerun da aka jera su a wajen da bashi da hayaniya ko kaɗan ga tsafta da kuma sanyin AC da ya karaɗe wajen. Cire leɓɓansa ya yi da matuƙar ƙarfi yana shafa sumar Farouk har izuwa bayansa. Bai ɗau lokaci ba ya yi bacci jin sauƙar numfashin da yake fita a hankali ya tabbatar masa da hakan, a hankali ya janye jikinsa daga na Farouk ɗin ya zame tare da kwantar dashi kan kujerun ya tashi ya isa izuwa ɗakin Ummin.
Ta window yake leƙawa yana ganin yanda likitotin suke rufu a kanta suna ƙoƙarin ceto rayuwarta, wani irin datse leɓɓansa ya yi da matuƙar ƙarfin gaske babu shiri ya dafe jikin bango saboda faɗuwar da yake shirin yi. Muryan su Anty Sauda da da Minal ya sanya shi ƙoƙarin miƙewa tsaye tare da boƴe rauninsa da ya fara bayyananuwa.
Idanu Anty Sauda ta tsira masa kamar yanda shima nashi yake kanta, har ta iso wajen ita ta ɗauke nata kafin ta ce"ya mai jikin?".
"Da sauƙi alhamdulillahi jikin ma ya yi sauƙi sosai ba kamar sanda accident ɗin ya faru ba".
A dake ya yi maganar duk da jirin da yake shammatar ƙafafunsa, kallon ta watso masa a razane ya sanya shi ƙara buɗe mata manyan idanunsa akan ta tare da ɗage mata girarsa ɗaya. Bata ce dashi komai ba ta leƙa ta window kamar yanda ya yi kafin ta kwaɓe fuska ta ce"to Allah ya ƙara lafiya daman hanya ce ta biyo damu ta nan muka je bari mu shigo".
Kansa ya jinjina yana kallon Mina da kanta yake kan wayarta tamkar bata ganshi ba yana da yaƙinin ko wacce bai sani ba ce suka haɗu a hanya a irin shekarunsa dole ta bashi girma balle kuma wacce suka haɗa tsatso ɗaya da ita ƴar-uwansa ta jini. Bai bashi mamaki ba hakan domin ya saba da rashin girmamawa daga gare su.
"Shi kuma wannan ba baccin meye yake yi?".
Baya jin zai iya cewa da ita komai don haka kawai ya cigaba da kallonta. Dariya ta fashe dashi kafin ta ce"koda yake tunda zaman banza yake yi babu aiki ai dole ya yi bacci". Daga haka suka fice daga cikin asibitin da kallo ya bisu yana jin wani ƙululun baƙin ciki yana mamaye zuciyarsa. Kusa da Farouk ya zauna ya runtse idanunsa raywuarsu ta baya sun ziyartar kwanyansa tiryan-tiryan.
Shekaru goma sha bakwai ne da rasuwar mahaifinsu tun Farouk yana da shekara shida gashi yanzu har ya kammala bautar ƙasansa, Hajiya Sauda da suke yiwa laƙabi da Maama ita ce matar mahaifinsu ta farko da take da ƴaƴa bakwai dashi biyar mata biyu maza, su kuwa su biyu ne a wajen mahaifiyarsa Hajiya Hafsat da suke ƙira da Ummi daga shi sai Farouk.
Mahaifinsu hamshaƙin ɗan kasuwa ne da sunansa ya karaɗe ƙashashen africa ta kugu domin ya yi shura sosai, Mina da Sultan kawai ya girma duk sauran sun girme masa Farouk kuwa shine ƙarami a maza Mina kawai ya girmewa.
Basu zauna wajen guda ba tare da Maama hasalima ba a gari ɗaya suke ba hakan ya sanya basu san juna ba har sai bayan da rasuwar mahaifinsu da yazo da abubuwa da yawa masu rikitar da tinanin dukkan mai tinani, Maama ta juna sam bata san yana da wata mata da ƴaƴa ba bayan ita da ƴaƴanta bakwai. Akwai maƙiya ne suka turo su domin anga mijinta ya mutu shine ake son aci gado Ummi tayi kuka sosai duk waɗanda suka je neman aurenta suma sun musanta hakan. Har kotu aka je da magana amma shima alkalin an saye sa sai kuma abinda aka kimtsa musu suke zartarwa ala dole suka haƙura saboda ƙarancin ƙarfi da suke dashi da rangwamen gatan da basu da wanda zai tsaya musu.
Tun daga lokaci Ummi bata ƙara wani auren ba duk da matsin lambar da take fuskanta daga iyayen natan, sun cigaba da samu barazana daga Maama akan rayuwarsu dole suka ɓoye gaskiyar da suke da ita suka nisanta kansu da dukkan wani abunda zai alaƙanta su da marigayin.
Shekara ɗaya a tsakanin mahaifin Ummi Allah ya yi masa rasuwa, rayuwa ta ƙara tsananta ƙunci a gare su har abinda zasu ci ya gagare su kamar alamajirai suke yawon bara gida gida domin biɗar abinda zasu sanya a bakin salati.
Wata makwabciyarsu ta sanar dasu tallafin da ake ba wa marayu ta ƙarƙashin ƙungiyar HAJIYA FAUZIYYA D SULEIMAN, watau CREATIVE HELPING NEEDY FOUNDATION.Tayi musu vidoe ta aika mata duk da ita a cikin garin kano take amma alkhairinta da na ƙungiyarta ta game ko'ina cikin ikon Allah suka sama wanda ya ɗauki nauyin karatunsu da kuma na abincin da su ci da muhalli saboda yanda ruwa ya rushe rabin gidan.
A haka suka cigaba da gudanar da rayuwarsu, da kuma karatun da babu ko sisinsu duk ƙarƙashin ƙungiyar creative helping needy foundation a cewar shugabar ƙungiyar Hajiya Fauziyya D Suleiman wani bawan Allah ne ya ɗauki nauyinsu wanda ya buƙaci a ɓoye sunansa, a haka ya gama secondary school lokacin mahaifiyar Ummi ita ma ta rasu, suka dawo rayuwa su kaɗai.
Alkhairin Hajiya Fauziyya D Suleiman ga rayuwarsu ba zasu taɓa mancewa dashi ba, domin ita ta taimaka musu a lokacin da suka rasa komai nasu, ta yaye musu ƙunci da baƙin-cikinsa da ya yi kane-kane a cikin rayuwarsu ta wanzar da dariya a saman fuskokinsu. Ta zame musu hasken fitillan da ta yaye musu duhun da ya mamaye rayuwarsu, bayan Ummi ita ce mata ta biyu a rayuwarsa da take da matuƙar muhimammanci fiye da komai da kowa a gare shi.
A ƙoƙarinta gare su ya sama scholarship ya fita ƙasar japan ya yi digirinsa na ɗaya, biyu har da na uku da yanzu yake matsayin prof. Sun taso ne da wannan tabon da dangin uba suka yi musu a rayukansu har kawo girmansu samun aikin da ya yi a wannan jami'ar ya sanya su dawowa cikin garin da har hakan ya sanya Maama da Ummi haɗuwa. Tunda suka dawo garin yake fama da wannan ciwon da aka kasa gane kansa tun yana ɓoye abin dom gudun faɗawar Umminsa da gudan jininsa cikin tashin hankali har ya bayyana. Rasa hankalinsa yake yi gabaɗaya idan ciwon ya motsa masa baya sanin inda yake balle waye akansa baya iya ci balle sha haka nan zai koma tamkar mataccen dake kwance cikin kushewa bugawan da ƙirjinsa yake yi ne kaɗai bambamcin, wannan hatsarin ya faru ne a hanyar dawowar Ummi daga garinsu da taje ziyata duk da iyayen gabaɗaya sun rasu sai dangi abinda yake bashi mamaki yanda aka yi su Maama suka san da labarin hatsarin, asibitin da take har suka so.
MATAN AREWA wallahi ayi hatta akwai mata da yawa masu irin wannan halin na danne haƙƙin kishiyoyinsu da ƴaƴansu bayan mutuwar mijinsu, su kuma rufe bakin kowa ta hanyar ƙarfin sihirin tsafi. Allah ya ƙara mana tsoronsa cikin zuƙatanmu ya saka mufi ƙarfin zuciyoyinmu ya Arhaman rahimin.
MATAN AREWA
(Book two)
© Maimunah Tijjani Iyam
___________________________________
Page 7⃣1⃣
Fitowar likitotin da suke kan Ummi shi ya tilasta mishi miƙewa daga zaman da yake yi a kusa da Farouk da har yanzu yake baccin numfashinsa yana fita a hankali a hankali, da sarsarfa ya isa ga babban likitan da yake yarce maiƙon gumin da ya jiƙa masa goshi ya furta"Doctor ya ake ciki?".
Sai da ya dafa kafaɗarsa cikin sigar son kwantar masa da hankali ya ce"ka same ni a office". Juyowa ya yi ya kallon Farouk dake kwance kafin ya bi likitan office ɗinsa, ido ya zuba mishi ba tare da ya ce dashi komai ba har tsawon wasu daƙiƙu kafin ya maida idanunsa ga files ɗin da suke a gabansa haɗi da sauƙe ƙarƙarfan ajiyar zuciya ya ce"da fari accident ne kawai da kanta ya taɓu sai dai yanzu gabaɗaya ko scanning aka mata ba'a ganin komai a cikinta, da zan baku shawara ku bi to a karɓa mata taimako daga wajen malaman addini domin abin yafi kama da sihiri ko kuma asiri".
Ƙwaƙwƙwaran motsi ma gagaransa ya yi ya daskare a cikin kujerar tare da jinginar da kansa cikin kujerar, wani irin abun da ba zai iya misaltawa bane yake mamaye masa rai da ruhinsa ƙirjinsa yana wani irin nauyi mai ƙarfin gaske.
"Calm down my friend, kowani bawa da irin hanyar da Allah yake jarabtarsa a rayuwa domin gwada ƙarfin imaninsa addu'arku kawai take buƙata a halin yanzu, aikin da aka yi mata a kanta zai iya taɓa kwalkwalwarta if help not taking".
Sama-sama kunnuwansa suke jiye masa zantukan na likitan kafin ya yi jarumtar tashi ya miƙa masa hannu suka yi musahaba ya fice daga cikin office ɗin, muryar likitan ya sanya shi tsayawa cak.
"You can go and see her after two hours from now".
Kansa kawai ya jinjina masa ya fice daga ofishin, sanda ya isa wajen ya tarar da babu Farouk kansa tsaye ya wuce ɗakin domin yasan nan kawai zai tarar dashi, hakan kuwa ya kasance ya hange shi yana zaune kusa da ita ya riƙe hannunta gam cikin na ya zubawa washashshen fuskarta idanu kamar yau ya fara kallonta a kaf rayuwarsa.
Zura dukkan hannayensa ya yi cikin aljihunsa kafin ya soma takawa a hankali har ya iso ina Farouk ɗin yake zaune, ya sanya hannu ya ɗago shi da sauri ya rungume shi a jikinsa, hawayen da suka wadacin idaniyar Farouk ɗin suka sama damar tsiyaya shafa bayansa yake yi a hankali kafin ya ja hannunta suka fice daga ɗakin.
"Ba yanzu ba Farouk ba yanzu ba ka bari ta huta tukunna sai mi shiga".
Kansa ya ɗaga masa suka koma daga waje suna kallonta ta window, tana kwance ita ba rayayyiya ba ita ba sumammiya ba haka nan ita ba matacciya ba. Runtse idanunsa ya yi da matuƙar ƙarfin gaske saboda zafin da yake jin har cikin namar jikinsa tamkar ana hura masa wuta a cikin dukkan sassan jikinsa. Zallar ƙiyayyar da ya hango tsantsa cikin idanun Maama suka ƙara ruguza masa raguwar ƙwarin gwiwan da suka saura masa duk da yana ƙoƙarin ɓoye hakan a gabanta da kuma ƴaƴanta sam baya bayyana rauninsa ko gazawarsa a gaban kowa face Umminsa. Wannan dalilin ya sanya ko hawaye baya iya zubarwa a gaban kowa sai ita ɗin dai ƙwara ɗaya tal, a asibiti suka ƙarar da wunin wannan ranar babu wanda yazo musu domin basu da kowa sai junansu da kansa ya tisa Farouk a gabansa ya bashi abincin da ya fita ya sayo masa shi kam daman cin abinci bai wani dame shi ba ko duniya tana ƙalau ma balle yanzu da yake cikin tashin hankali ga zafin ciwon da yake ji a jikina yana ƙoƙarin dannewa don kwantarwa Farouk hankali.
Sai ƙarfe goma sha biyu saura na dare suka baro asibitin bayan sun shiga sun duba ta suka taho, a ƙa'idan asibitin daman ba'a kwana wajen marar lafiya saboda akwai wadatattun kuma ƙwararrun ma'aikatan da suke kula da kowa.
Farouk ne ya yi driving ɗin motar har gida gate man ya wangale musu gate ɗin ya tura hancin motar ciki, hannayensu sarƙafe cikin na juna suka shiga cikin gidan da babu motsin kowa masu aiki ma duk suna part ɗinsu da yake ta bayan gidan.
"Kaje kayi wanka ka huta".
Kaɗai ya iya furtawa yana hayewa up stair ɗin da zasu sada shi da room ɗinsa, yana shiga ya zube akan bed yana mayar da numfashi a wahale jin jikinsa yake yi kamar ana sassara masa da adda ko kuma wani makami mai ƙarfi da kaifin bala'in da yake ragargaje abu komai ƙarfin sa, ya daɗe a wajen kafin ya yunƙura ya tashi cikin tangaɗi ya wuce bathroom ya sakewa kansa shower ya ɗauko alwala ya fito ɗauke da towel a ƙugunsa da wani ƙarami yana goge sumarsa dashi, dogon rigar jallabiya ya saka ya shimfiɗa sallaya ya daka salla raka'a biyu ya yi ya sallame yana jero addu'a ga mahaliccinsa. Yana shafa addu'ar sallamar da Farouk ya yi suka ratsa kunnuwansa kallo ɗaya ya yi masa ya ɗauke kansa yana tasbihi da gaɓoɓin hannunsa. Ajiye tray ɗin hannunsa da yake ɗauke da coffe mai zafi Farouk ya yi a gabansa tare da zuba masa ido cike da tausayinsa ya ce"coffe na haɗa maka da kaina tun safe baka ci komai ba".
"Bana jin sha'awar cin komai yanzu nafi son kaɗaita da kowa".
"Yaya Saif kaɗaita kanka daga kowa ba shi bane mafita, haƙurin da muka saba dashi shi yamu cigaba da yi da kuma addu'a, na ɗauke ka tamkar uba ne a gare ni wanda nayi rashinsa a lokacin da nafi tsananin buƙatarsa a cikin rayuwata. Rasuwar sa ta ruguje dukkan tubalin ginin farin-cikin da ya gina a rayuwarmu. Yaya Saif sai yaushe haske zai bayyana cikin bahaguwar rayuwarmu?, sai yaushe zamu yi dariya kamar kowa?, sun fincike mu daga dangin ubanmu ta ƙarfi da yaji sun farraƙa mu da ƴan uwanmu na jini amma duk da hakan bai ishe su ba me suke so damu?, idan mun mutu mun bar musu duniyar zasu hutu tunda su dawwama suka zo yi cikinta. Yaya Saif na gaji na gaji da rayuwar nan ga ciwon da kake fama dashi ga nima aiki