Showing 117001 words to 120000 words out of 171161 words
Chapter 40 - MATAN AREWA BOOK TWO COMPLETE PDF .txt
ce"ban gane kuna makaranta ba kefa waye, hutun ne ba za ki koma gida kiyi shi ba ko meye kike nufi?". Dariya sosai ta bushe dashi sai da ta yi mai isharta kafin ta tsagaita don kanta ta ce"yarinya kenan ai ku yanzu kuka shigo baku san komai ba system ɗin, ni fa kin gani nan ko lokacin da muke 100 level bana hutun ƙarshen zangon karatu a gida. Imfact ni faɗin an bamu hutu ma ba yin shi nake yi ba to ma me zanje nayi a gidan banda ba kwasowa kaina tarin abin baƙin-ciki da takaici gwada nayi zamana inda nake samarwa kaina farin-ciki, Katsina ma ni zan ɗaga idan an koma hutu na dawo". Duk galala muka yi muna kallonta cike da son ƙarin fashib baƙi game da zancen natan.
"Tawan kuna da ƴan-uwa kenan a jahar mu?, shine ba ki tama faɗa min ba".
"Ba dangin iya balle na baba sai dai dangin air". Billy ɗawisu ta faɗa tana miƙe domin ɗaga ƙiran da ya shigo wayata.
Har ta gama amsa wayar ta dawo ta zauna babu wanda ya ce komai a cikin mu, sai da ta zauna ta ɗaura da faɗin"ku dai da kuka ga zaku iya zuwa gidan bismillah". Ƙatuwar ajiyar zuciya na sauƙe ina bin ta da kallo domin ni kam sam ban gaji da kallonta tare da nazarin dukkan zantukanta ɗay bayan ɗaya a cikin raina, ranar bamu kwanta ba kusan biyu da rabi na dare sannan muka kwanta. Muna yin asubahi kuwa muka fara yin shiryeye sai da muka share ɗakinmu tas muka kimtsa komai sannan muka yo wanka muka shirya.
Duk mun fito da akwatinan mu filin hostel ɗin, Nazifa ce kawai yaya Amin ya yi mata alƙawarin zuwa ya ɗauke ta amma ni da Nawwara tasha zamu muje mu hau mota don Yaya Majid da kawu Musa ba zasu sama damar zuwa ba. Ƙarfe goma saura mintuna yaya Amin ya ƙira Nazifa yana shaida mata cewar ya iso cikin makarantar tare muka isa inda ya ce yana yake cikin jami'ar. Muka gaisa cikin sakin fuska sannan ya ce mu shiga ya sauƙe mu a tasha, hakan kuwa aka yi ya dire mu a tasha tare da biya mana kuɗin mota godiya muka yi masa sosai sannan muka rungumi juna da nazifa babu ruwan mu da inda muke da yake cike da cincirundon jama'a muka fara sakin kukan rabuwa.
Tun yaya Amin nayi mana dariya har ya soma lallashin mu da ƙyar muka rabu kowacce ta shiga motar da zai yi garin su. Muna hawa titi na ƙira yaya Majid na sanar dashi cewar na taso muna tafe ina ta juyayin zancen Billy ɗawisu cikin raina da gasken take fa ba inda zata je hutun zangon nan don duk mun watse mun barta a hostel ita kaɗai ta ce zuwa yamma wai cikas ɗinta zai zo ya ɗauke ta su ɗaga zuwa katsina.
Wani wawan numfashi na fesar mai nauyin gaske irin wannan lamarin laifin na iyayen ko kuwa na ƴaƴan?, na jefawa kaina tambayar da na gaza samun amsarta sai dai zuciyata tafi bada ƙarfi ga bangaren iyayen nayin wasarere ta fannin bibiyar lamuran ƴaƴansu da suka turo jami'a dole ya sama yawaita ire-iren Billy da yawa, matuƙar iyaye zasu na sakarwa ƴaƴansu dukkan ɗawainiyyar da ya kamata ace sunyi musu idan ba ayi dace da samun ɗan da ya ƙoshi da tarbiya ba sai ya sauƙe hanya. Zancen da iska ya kwaso ya dire shi a kunnuwana suka sanya ni dawowa hayyacina daga zancen zuciya da nake saƙawa da warwa.
Cikin wani irin kunjin kuka mai toshe hanyar fitar numfashi matar take faɗin"ba zan koma gidansa ba na gwammace na bi duniya duk da bani da inda za ni ban san kowa ba a nan ban kuma san inda zan nufa guɗa ɗaya ba, da na san haka rayuwar aure zata kasance min ba dan yi ta ba da ban bi zantukan mutanen da suke faɗin na ƙi aure nayi zaɓen tumun dare ba". Daga haka ta kuma fashewa da kukan da ya jawo hankulan mafi yawan mutanen motan gare ta, wata da take kusa da ita ita ke ta lallashinta tare da kwantar mata da hankali ta ce"yanzu inda za ki je da kika baro gidan mijinki?, bayan kin ce ba ki san ko'ina ba bayan ƙauyenku da kinyi haƙuri kin koma gidan iyayenki".
"Zan tafi ko'ina ma domin nasan duk inda zan je yafi inda na fito, ko naje gida babu abinda zai sauya zani domin mahaifiyata ta furta min cewar matuƙar na kasho aurena na dawo gida to sai ta tsine min duk da tafi kowa sanin halin ukuban da nake ciki a gidan Hamisu. Ta baya yake kusanta ta ya kan sanya ni a caca idan aka cinye shi wanda ya ci shi yazo ya kwanta dani ba tare da sun san cewar ni matarsa ba ce".
Tsif motar ya ɗauki shuru, wani zuffa ya shiga keto mini kamar anyi ruwa an ɗauke haka yawun bakina ya ɗauke ƙaf tamkar rijiyar da ruwan cikinta ya kafe. Dukkan wani gaɓar jikina ya yi laƙwas ina cigaba da sauraron bayanin da take korawa matar cewa ita ma bata san inda zata je ba kawai ta gaji wannan rayuwar kamar zamanin jahiliya shiyasa ta samawa kanta mafita ta hanyar barin gidan ba tare da ta buƙaci takardan saki daga gare shi ba balle bakin da mahaifiyarta tayi ikirari gare ta ya bi ta, sai a lokacin nayi wa matar kallon tsaf yarinya ce da zamu iya karawa da ita a shekaru amma wahala da tsananin rayuwa ya ɓoye ƙuruciyarta ta ƙarfi ta yaji tare da bayyanar da tsufanta a zahiri. Tare dasu muka sauƙa a potiskum mutanen motar kowa na bata baki tare da yaba ƙoƙarin dattijuwar matar da suka zauna waje ɗaya da ta ce zata kai ta gidanta su sanar da mai unguwa a nemi iyayenta ayi musu bayani a warware auren.
MATAN AREWA
(Book two)
© Maimunah Tijjani Iyam
____________________________________________
Page 1⃣0⃣0⃣
Adaidaita na raka na hau domim nufa gida, bayan tsawon tsayiwar da nayi kan ƙafafuna har sai da adaidaitan da matar suka hau ya ɓacewa ganina, a kai a kai nake sakin ɓoyayyen ajiyan har muka isa na zaro kuɗinsa na miƙa masa.
Firda'usi na iske a ƙofar gida suna tsaye da wasu samari biyu muka haɗa ido da ita, ta iso tana yi mini sannu da zuwa tare da ɗaukar mini akwati kaya sai da muka shigewa gidan samarin suka gaishe ni na amsa bayan na gama yi musu kallon ɗaya ɗaya muka shige, ban iya haƙurin riƙe abinda ke cikina ba sai da na furzo shi waje ga Firdau'sin.
"Su waye waɗannan suke tsaye dasu haka a ƙofar cikin wannan uwar ranar?".
Rausayar da kai tayi kafin ta ce"abokan Ibrahim ne sun zo karɓan list ɗin abubuwan da zamu buƙata na bikin". Da kallo na bi ta na ce"aw amarya amma dai kinsa hakan ya saɓawa tarbiyar da su Abba suka ɗora mu a kai ko?, da ko Nurain kin aiko ai ya kawo musu list". Ba ta tanka mini a zahirance ba sai dai ina iya jiyo ƙunƙunin ƙananun maganar da bana iya tantance abinda take faɗi. Tun kafin mu shiga sashin Hajiya Babba ta sanar mini da cewar taje gaisuwar rasuwa don haka muka zarce izuwa cikin gida bakina ɗauke da sallamar da ta sama amsawar tsirarun mutanen wajen yayin da wasu suka watso mini idanu kamar yau ce ranar farkon da suka fara tozali dani.
Durƙusawa nayi na gaishe da dukka matan gidan mu da suke zaune a wajen har da Umma da goggo Jummai suka amsa mini fuska ba yabo babu fallasa, Umma tana yi mini sannu da zuwa haka nan ma Hajiya da Daada, sannan sauran yaran suma suka yi mini na amsa cikin farin cikin ganin su.
Waigawa nayi na ce"ina kuwa Salma da Nurain kuwa?".
"Sun fita tare da Hajiya Babba gidan su Hassanu da aka yi rasuwa".
"Allah ya jiƙan musulmi".
Na furta suka amsa mini da amin har miƙe zan shige ɗaki saboda gajiyar tafiyar da na kwaso, Ikilima da Zainab tunin suka shigar mini da kayama ɗakin. Maganar da Umman Balkisu ta soma ya sa ni dakatawa akan dole.
"Ƴar boko lalle wannan karatun ya amshe ki, sai wani haske kike yi ga ƙiba ta mussamman meye sirrin ne?".
Cije leɓɓan nayi da ƙarfi ina sunkuyar da kaina kafin na kai ga bada amsa, Hajiya ta amshe zancen cikin faɗin"yo ba dole tayi haske ba ta kuma ƙiba ta rabu da saka ido da masifar tsiya ai dole ta canja, can kuwa hankalinta kwance babu abinda zai dame ta karatunta kawai ta sanya a gaba. Nan kuwa hayaniyarku ma kawai ya isa ya figar da ita wuce kiyi wanka ki zo ki ci abinci don tunda Majid ya sanar da kina tafe na dafa miki taliyar murji na san kina son ai ko?". Kaina na ɗaga mata ina ƙaƙalo murmushin dole na dasa a fuskarta amsar tatan ya sanya bakin Umman Balkisu yin shuru da ma masu ƙudirin yaɓo mini magana irin nata. Ɗakin mu na wuce na zare kayan jikina na ɗauko zani nazo na wuce su na shige banɗaki nayo wanka sai da na fito na ɗauro alwala na sanya kayana na gabatar da kallan zuhr a makare don lokacin har ƙarfe biyu ta gota, Hajiya a aiko Zainab da kwanon taliya buɗewa nayi na ganta cike him na ce ta wanko hannunta tazo muci.
Ina ci ina waya da Nawwara da take shaida mini tunin ta daɗe da huta gajiya ita kam, sai da naji cikina na barazanar fashewa na tashi na wanko hannuna dai-dai nan sallamar Salma da Nurain suka ratso gidan. Har rige-rigen isowa gare ni suke yi muka rungume juna da Salma cikin tsantsar farin-ciki, kafin na zame jikina na ɗaga Nurain sama dariya yake ƙyalƙyalawa sosai na dunga juyi dashi yana cigaba da sakin dariyarsa, har Umman su Anty Kubra ta fito nufo mu tayi kamar zata kife kan hancinta tana cewar"A'a ke sauƙe min yaro ƙasa kafin ki karya shi ki tsugunar dani ko don ba ki san wahalar naƙuda ba kike yi mishi wannan shillin". Duk da naji zafin zancen natan har cikin raina amma ban nuna mata a fuska ba illa ma murmushin da na cigaba nayi na dire shi a ƙasa babu kunya ta kai hannu zata janye shi, ya maƙe kafaɗa yana ƙara shigewa jikina.
"Umman Nurain ki bar shi mana ya zauna cikin ƴan-uwansa".
Salma ta faɗa a kufule alamar ita ma taji zafin zancen natan, wani harara ta raba mana daga ni har ita ta ce"salon ya tashi da ɗabi'ar mata kullum yana cikin su ya fita waje wajen yara maza jinsinsa".
Janye hannuna nayi daga cikin na Nurain na shige ɗakin ba tare da na kuma kallon Umman nasan ba balle na tankawa maganganunsa, hijabi kawai na sako a kaina na fito na wuce sashin Hajiya Babba a can na zauna har yamma bayan sallan magrib su Abba da yaya Majid suka dawo naje na gaishe su mun sha hira dasu har sai da aka yi ƙiran sallan isha'i sannan suka tashi suka tafi masallacin na dawo sashin mu.
Har mun kwanta Salma ta tashi mirtsike idanuna nayi ina bin ta da kallon da hasken tocilan da ta kunna a ɗakin yake bani damar kallon fuskarta da ta jiƙe da hawaye, a ɗan tsorace na furta"Salma lafiya kamar kuka kike yi?".
"Na'ima ba lafiya ba ina cikin damuwa". Fit na nema baccin idanuna na rasa ya washe na ƙura mata ido cike da son ƙarin bayani game da zancen natan. Sai da ta musguta kana ta soma faɗin"akan batun aurena da Baban su Zaliha ne ko kin san a riga da angama magana lokaci kawai ake jira, tare da na Firda'usi, Falmata da Ikilima za a haɗa wata mai makawa".
Sai da na sauƙe ƙatuwar numfashi na dafo kafaɗarta sannan na furta"Salma kiyi haƙuri kiyi ta addu'ar Allah ya san hakan ne mafi zamowa alkhairi a gare ki, wani lokacin abinda kake so ba shine alkhairi a gare ka ba yayin da abunda kake ƙi tare da guje masa yake zamowa alkhairi a gare sa, ki ba wa Allah zaɓi ya yi miki zaɓin alkhairi ga rayuwarki. Ki kwantar da hankalinki don Allah ki ɗauki hakan a matsayin jarabawar da duk cikakken mumuni yake karɓanta hannu bibiyu".
Kanta ta ɗaga mini tare da zamewa ta kwantar da kanta a jikina, haƙuri yanzu shine kalmar da kawai zan iya furta mata bakin alƙalami ya bushe tunda har an yanke rana. Da saurina na furta"amma su nayi mamakin amincewar su Abba game da wannan lamarin".
"Da farko su ma basu amince amma da na amsa cewar ina son shi zan kuma iya zaman aure dashi cikin ko wani yanayi, bisa tirsasawar Ummata a gare ni sai suka saduda tare da yasar da makaman yaƙin su. Na gargaɗe da tattauna maganar da kowa shiyasa ko Hajiya Babba ban tunkara da zancen ba ke kaɗai na faɗawa".
Miɗik na rufe baki cikin raina ina mamakin halin wasu uwayen mata da suke amfani da ƙarfin ikon su cikin rayuwa ƴaƴansu, suke sanya rayuwarsu cikin wani hali. Kamar sauƙar aradu haka nan labarin wannan matashiyar da muka yi zaman mota tare ya diro a raina, labarinta yana kamanceceniya da ta Salma duk uwa ce mafarin lamarin take wani tinani ya ziyarci kwakwalwata da tinanin hanyar da zan fahimtar da al'ummata hatsarin hakan da kuma halin da suke jefa rayuwar ƴaƴan nasun a ciki.
Ruhin son zama marubuciya da ya daɗe da mutuwa cikin ƙirjina shi ya fara numfashi a hankali-hankali, tabbas na yarda marubuta suna taka muhimmiyar rawa wajen kawo sauyi ga rayuwar al'umma ta yau da kullum, sai ina wasi-wasi da samuwar amincewar iyayena game da labarin idan ma sun amince mini ta ina zan fara?, waye zai taimaka mini har na cimma burina?, waye na sa ni da yake da alaƙa da wata ko wani marubucin da zai yi riƙo da hannayena ya nuna mini hanya?.
Da waɗannan tarin jerin gwanon tambayoyin na kwan, sun tsaya mini a rai tamkar ƙayan kifi washe gari sukuku na tashi banda wani cikakken kuzari bayan munyi karin kumallo muka yi wanke-wanke tare da Salma, Hajiya ta aiko ƙira ban ɓata lokaci ba naje na iske ta a ɗakinta.
Sai da nayi mata sannu da hutawa kafin na ce"gani an ce kina nema na". Gyara zama tayi tana ɓantaran guntun goron da za tsinto daga gefen zaninta kana ta furta"daman wata magana nake so muyi kin san cewar Yusuf ya yi aure satikai biyu da suka shuɗe?". Wani ras ras ras ras ras ƙirjina ya bada sautin da har sai da na dafe wajen, ina ɗago kaina muka haɗa ido da Hajiya na yi saurin rusunar da nawa ƙasa cike da kunya sannan na jijjiga mata kaina alamar a'a.
"Ai kuwa dai Yusuf ya ɗaura aure ranar ɗaya da na ɗiyar Binta, hakan ya yi min dai-dai domin nasan ko banza dole zai ga gurbinki bi'izinillahi kuma sai Allah ya bi miki dukkan haƙƙinki da suke tauye shi da Binta".
Cikin wani irin yanayin da nima kaina na gaza gane me ke yi mini yawo a ƙirji na ce"ba komai Hajiya ni kam na yafe musu har cikin zuciyata, aure kuma Allah ya basu zaman lafiya da zuri'a ɗayyaba". Duk da har yanzu idanuna suna ƙasa amma ina ji a jikin idanunta gabaɗaya suna a kaina, ta sauƙe numfashi ta ce"Lalle Na'ima kinyi gado zuciyarki a tsaftace take, in sha Allah ba za ki taɓa tozarta ba kema Allah ya fito miki da miji na gari wanda zai share miki hawaye".
A raune na amsa da amin ina miƙewa na koma ɗakin mu, nayi sa'a ban tarar da Salma a ɗakin ba jagwaf na faɗa kan katifarmu ina sakin wasu siraran hawayen da kai tsaye ba zan iya kama dalili ɗaya na zubar su. Ni dai na san na yaƙi zuciyata game da soyayyar yaya Yusuf da ya yi ka-ka gida a cikinta sai dai abinda ban gane ba yanzu kishinsa nake yi kenan ko kuwa meye, in babu so meya kawo kishi?.
MATAN AREWA
(Book two)
© Maimunah Tijjani Iyam
_______________________________________
Page 1⃣0⃣1⃣
Rurin da wayarta dake ƙasan matashin da take kwance a kai shi ya tilasta mata buɗe marafan idanunta da babu komai a ciki face baccin da ya gama cin ƙarfinta, lalumar wayar tayi ta ɗaga ta kara a kunne ta ba tare da ta tsaya duban mai ƙiran ba. Jin muryar Hajiya Kulu sun sauƙa a ƙofofin kunnuwanta ya sanya ta lafawa daga balbalin masifa gami da bala'in da ta yi niyyar bawaje duk mai ƙiran, yamusha fuska tayi kafin ta ce"wani irin rashin mutunci ne Binta tsawon kwanaki biyu ina ƙiran wayanki a kashe".
"In ce dai kema a garin nan kike zaune ko, kin kuma san matsalar rashin wutar lantarkin da muke fama dashi. Don kin ƙira wayana kin jita a kashe ai bai kamata kiyi ƙorafi ba".
"Ba wannan ne ya sanya ni ƙiran ki ba Binta, Aisha ce ta ƙira cikin kuka tana labarta min cewar inje har gidanta cikin ɗakinta kin ɗauke ta da mari tare da kalaman cin mutunci. Binta menene haka daga auren da ko wata guda mai rufa ba har kin fara sanyawa yarinya ido a gidan mijinta?. To wallahi ni dake kar ta san kar ne duk mulki da ka-ka gidan da kike yi a gidajen ƴan-uwanki tare da san ido akan duk abinda yake gudana tsakanin su da matayen su, ni ba ki isa ki yiwa ƴarta irin hakan ba. Aisha aure take yi a gidan Yusuf kuma shi yake aure ba ke da kike ƴarsa ba don haka ki kama girmanki da mutuncinki sai ita ma ta girmama ki, amma ba zan ɓoye miki har ga Allah banji daɗin abinda kika yi mata haba mari fa a wani dalilin?".
Numfashi Anty Binta ta sauƙe tare da tashi zaune daga kwanciyar da take yi, take baccin idanunta ya wartsake ta soma cewar"yanzu akan wannan dalilin ne za ki yi min ƙira