Showing 45001 words to 48000 words out of 171161 words
Chapter 16 - MATAN AREWA BOOK TWO COMPLETE PDF .txt
ta fara mantawa da komai to ina roƙonka da kayi nisa da ita domin makaranta zata koma kaga nan sakamakon jarabawar waec da neco ɗinta ne in sha Allah Na'ima makaranta zata koma tayi nisa da garin ma gabaɗaya da kuma baƙin cikin dake cikinsa kuma wallahi ka ƙara neman Na'ima da wata maganar hukuma ce zata shiga tsakanin mu da kai".
Yana ƙare faɗin hakan ya yi wucewarsa da kallon yaya Yusuf ya raka shi dashi har ya ɓacewa ganinsa, saurin dafe goshinsa ya yi saboda barazanar da kansa yake masa da rabewa gida biyu.
"Rabbi inni lima anzalta alaiya min kharin faƙir".
Shine kalmar da ya yi nasarar furtawa yayin da ƙafafunsa suke rawa da shirin zubar dashi a ƙasa, runtse idanunsa ya yi da matuƙar ƙarfi yana mai cigaba da sauraran canzuwa bugun da ƙirjinsa ya yi cikin daƙiƙun da basu haura biyu zuwa uku ba.
Makaranta kenan Na'ima zata koma to ma wani makarantar kenan cikin jerin makarantu huɗu da ya cike mata yayin ragistan jam, tinawa ya yi da wata tautaunawar su a wancan lokacin da take bayyanar masa da tsakanin son ta ga zaɓi na farkon. Cike da ƙarfin gwiwa zuciyarsa da take bugawa a raunane take raya masa tabbas zaɓin farkon zata bi tunda makin ɗinta na jamb yakai yanda suke buƙata daga dukkan wani ɗalibi mai sha'awar karantar harkan jarida babu shakkar can zata.
Bai ji ƙarisowar sa wajen ba balle tsayiwar da ya yi a kusa dashi illa muryarsa da yaji sun bugi dodon kunnuwansa. "Yusuf lafiya kuwa, kake tsaye a nan?".
Sai da ya jawo numfashinsa ya fesar da ƙarfi kafin ya watsa masa idanunsa yana faɗin"makaranta Na'ima zata koma Hashim nima dole na bita duk inda zata je wallahi".
Fuskarsa da maɗaukakiyar mamaki Hashim yake binsa da kallo cikin ransa yana ƙara jinjina ƙarfin haukar Yusuf, kafin ya ce dashi"duk inda taje sai ka bita fa ka ce Yusuf?, wai nikam meyasa ba zaka rungumi wannan ƙaddarar bane?. meyasa kake wahalar da zuciyarka akan abinda kasan cewar ba zata taɓa samun sa ba mallakinka bane? dan Allah ka manta da yarinyar nan kuma da kake faɗin zaka bita kana ji ina makaranta zata koma to kaje kayi meye kai kuma a can?".
"Abinda zai kai ta nima shi zai kaini karatu, sai dai ni da manufa biyu zani bayan karatu da kuma son ganinta. Dole naje Hashim don wallahi ba zan taɓa samun sukuni ba matuƙar ban gano yanda lamarin nan ya afku ba dole naje duk makarantar da zata je nima zani na ƙaro karatu zanyi degree na biyu".
Sosai Hashim yake kallonsa don yanzu ya daina bashi haushi sai ma tasauyinsa da yake ji matuƙar yanda yake neman zaucewa.
"Zan wuce gida don ba zan iya zama a nan ba, tun daga yanzu zan fara binciken makarantar da Na'ima zata je nima na nemi gurbin karatu a can".
Iya abinda ya faɗa kenan ya wuce ya bar Hashim tsaye a wajen riƙe da ƙugunsa yama rasa meye zai ce masa ya dakatar dashi domin tabbas baya cikin cikakken nutsuwarsa da zai iya kai kansa gida. Ganin ya riga da ya fice daga cikin makarantar akan mashin ɗinsa y sanya Hashim gaggawan ƙiran yaya Auwal ya sanar dashi halin da ake ciki.
Mashin ɗin ce take sarrafa kanta domin bin ta kawai yake yi tamkar raƙumi da alaka, rurin da wayarsa ta soma yi ya sanya shi faka mashin ɗin a gefen titi tare da zaro wayar daga aljihunsa tagwayen ajiyar numfashi ya sauƙe tare da ɗaga ƙiran ya kara a kunnensa.
"Yusuf duk abinda kake yi ka bari kazo gidan Anty Binta zan nufa can mu haɗu".
Datse ƙiran ya yi ba tare da ya damu da jin raguwar furcin yaya Auwal ɗin ba ya nufi gidan Anty Bintan. Saurin dakatawa yayi tare da lumshe idanunsa ya kuma buɗe su cike da son tabbatar da sahihancin abinda da suke hango masa. Husna ce tsaye da wani matashi a jikin mota hannayensu riƙe cikin na juna suna fuskantar juna tare da sakarwa wani laulausan murmushi ido cikin ido. Da sarsarfa ya iso gare su babu ɓata lokaci ya ɗauke ta da kyawawan marufa biyu a jere reras kafin ya shiga nuna ta da ƴar manuniyar yatsarsa cikin tsananin ɓacin ran da ya gama wanzuwa a fuskarsa yake faɗin"wuce gida kuma na ƙara ganin ki da wannan yaron sai na sassaɓa miki shashasha kawai".
Da kuka ta shige cikin gidan ya rufa mata baya ba tare da ya tsaya bi ta kan matashin ba, faɗawa jikin Anty Binta dake zaune a tsakar gidan Husna tayi tana ƙaurara ƙarfin kukan natan.
"Ke lafiyarki za ki shigo min gida da kuka ke da waye?".
"Kawu Yusuf ne yazo ya same ni tsaye da Safwan muna hira ya tsinka min mari ya koro ni gida".
Sai a lokacin da lura da Yusuf ɗin da yake tsaye ta kai dubanta izuwa gare shi"Yusuf lafiya meye zaka koro ta gida?".
Yarfe hannunsa ya yi kawai tare da cije leɓɓana kamar ba zai ce da ita komai ba sai kuma ya furta"yaron nan bashi da tarbiya kuma idan bamu yi da gaske ba lalata yarinyar nan zai yi bayan ya gama cin moriyar ganga ya yada ƙaurinta, tsaye fa na iske su hannuwansu sarƙafe cikin na juna".
"A'a Yusuf wannan zancen ba zai samu matsuguni a cikin kwanyata ba, Safwan kowa zai shaide sa akan kyawawan hali da nagarta yaro ne ɗan gidan mutunci kuma mai girmama na gaba dashi kuma ni nan na shaida yanda yake son yarinyar nan domin babu wata buƙatar da zata je masa dashi mai biya mata ita ba".
Bai ƙara cewa da ita komai ba saboda zafin furcinta da yaji sa har cikin ransa, ya tabbata cewar duk wacce ta mayar da saurayi mai ɗaukar dukkan ɗawainiyyarta tamkar mijinta shima haka nan wataran ko ba daɗe ko ba jima dole ya nemi ta biya masa buƙata tamkar matarsa. Akan idonsa Anty Binta ta sanya Husna ta miƙe ta wanke fuskarta ta koma wajen Safwan fitarta ya yi dai-dai da shigowar yaya Auwal cikin gidan.
Sai da suka zauna yaya Auwal ya dubi yaya Yusuf da ya yi ƙasa da kansa yana murza hannunsa a hankali ya furta"Yusuf lafiyarka kuwa?".
"Ina kuwa zai ga lafiya ya ɗaurawa kansa damuwar da babu gaira babu dalili ya sanyawa kansa damuwa akan wata can daban, ai shi da lafiya yanzu kuma sun raba sunyi hannun riga".
A fusace Anty Binta ta ƙare zancen da hakan ya sanya yaya Auwal sausauta amon muryasa ya ce"dalilin hakan ne ma ya sanya ni cewa yazo nan muyi magana, munyi magana da Hashim ya sanar dani ka yanke shawaran komawa makaranta domin yin degree na biyu, meye kawo maka wannan tinanin a yanzu?".
Ba tare da tsoro, fargaba ko kuma tinanin abinda kanje ya komo ba ya ce"Na'ima ce zata koma makaranta shiyasa nima dole na bita duk jam'iar da ta samu zan nema gurbin karatu a can".
Wani wawan kallon Anty Binta ta watsa masa tana faɗin"zaka bin ta fa ka ce Yusuf?, anya kana cikin hankalinka kuwa?, to wallahi matuƙar ina da iko akan ku to ban lamince kaje ko'ina ba da sunan bin wannan lalatacciyar yarinyar nan da sunan karatu wallahi ban amince maka ba Yusuf".
Matsa hannunsa ya yi da yake murzawa sosai kafin ya ce da ita"Anty ban so kika ƙira da wannan sunan ba, domin kema kin haifa kuma gata nan ka gabanki ba ki san irin ƙaddaran da rayuwa tayi mata tanadi ba. Ku gafarce ni domin na riga da na gama yanke hukunci karatu zan ɗaura nima".
Ina dasa aya a nan ya miƙe ya fice, sakakken ajiyar numfashi yaya Auwal ya sauƙe kafin ya soma faɗin"Anty ina ganin mu barshi kawai ka tafi karatun nan, ko zamu samu hankalinsa ya koma dai-dai mu bi shi da addu'a kawai".
"Nifa Auwal wallahi ina tantama anya yarinyar nan da iyayenta basu tsaface Yusuf ba kuwa?".
Taƙaitaccen murmushi yaya Auwal ya yi yana cewar"babu wani asiri Anty tasirin soyayya ce kawai shiyasa na ce muyi masa addu'a kawai".
Sosai ta cika tayi fam ƙiris take jira ta shafa tayi alwashin cewar matuƙar tana numfashi sai ta hana ta jin daɗin zaman duniya kamar yanda ta dalilinta Yusuf yake bujirewa umarninta.
MATAN AREWA
(Book two)
© Maimunah Tijjani Iyam
____________________________________
Page 5⃣9⃣
Haka nan tun safar safiya na sinci kaina cikin matsananciyar fargaba da faɗuwar gabar da ban san dalilin faruwar hakan a gare ni, ina jin tamkar ina dab da rasa wani abu mai muhimamci a rayuwata gabaɗaya. Cikin wannan yanayin nayi sallan zuhr na zauna na zabga uwar tagumin kamar wacce aka aikowa da saƙon rasuwar dukkan ahalinta a lokaci guda. Ajiyan numfashi na sauƙe a karo na barkatai ina shafa goshina da yake tsatstsafo da maiƙon wani zuffan dake tsiyaya daga dukkan mafitar gashin dake jikina, cire leɓɓena nayi ina runtse idona da suke a lumshe da yafi kama da na wanda yake jin bacci ko kuma wanda gajiya tayi wa mungun kamu.
Sallamar da naji sauƙar su tanga raras a na'u'ar dake jiyo mini sautin zantukan mutane shi ya wartsakar dani tare da buɗe idona tar na tsayar dashi a ƙofar ɗakin cike da son tantance mamallakin mai murya don babu shakka cewar muryar ba baƙuwa bace ga kunnuwana. Zumbur na miƙe ina mirtsike idanuna ina jin tamkar mayen ƙarfi ake sanyawa a jikina yake jana domin tafiyar kawai nake yi amma ban san inda nake jefa ƙafafuna na fito daga ɗakin. Turus na tsaya ina dafe bango saboda wata mahaukaciyar jirin dake kwasa ta da ƙoƙarin manna ni da ƙasa saboda mummunan gamun da idanuna suka yi. Anty Binta ce tsaye riƙe da ƙogo tana karkaɗa shi tare da sakin wani huci tamkar mayuwancin zakin da ya shekara ba tare da ya yi tozali da abinda zai yi kalace ba haka take watso mini wani kallo mai sanya kiɗima da firgici a zuciyoyin mafi yawan mutane musamman masu raunin zuciya iri na.
"Daman tafiyar naki ne".
Ta furta tana nufo inda nake tsaye, dai-dai lokacin da Umman Salma, Umman Ikilima da kuma Daada suka fito filin tsakar gidan Salma dake banɗaki ma ta shiga wanka ta fito ɗaure da zani a jikinta ta ƙura mini ido tana ajiye bokatin ƙarfen dake hannunta.
"Baiwar Allah lafiya?, za ki shigo mana gida babu neman izni?".
Furcin Umman Ikilima kenan da ya sanya Anty Binta kai dubanta gare ta tare da yi mata kallon tsaf kana ta ce"ba wajen ki nazo ba malama don haka ki tsagirta min, domin ba take naje yi ba yanzu don haka kiyi wa bakinki linzami ta hakan ne kawai za ki kuɓuta daga rashin mutuncina da nake tafe dasu buhu-buhu da zan juye su a gidan nan".
"Ahayye nanaye to wallahi ko kina cin ƙasa malama ki kiyaye ƙasar shuri, kuma ƙwarya tabi ƙwarya domin idan tabi akwashi sunan ta fashashshiya nima nan da kike ji da gani ba kanwar lasa ba ce ehe".
Wani kallon kawai Anty Bintan ta kuma watsa mata a karo na biyu tare da ɗauke kanta ba tare da ta kuma cewa da ita wani abun ba, ta dawo da duban ta izuwa gare ni haɗi da faɗin"ke ina uwar ki domin kinyi kaɗan nayi dake da ita zanyi idan tana da hankali tayi amfani da abinda zan faɗa mata ko don ta kuɓutar da rayuwarki daga faɗawa tafkin dana sani da nadamar da babu amfani. In kuwa tayi kunnen uwar shegu da maganganuna to duk wanda ya ƙi ji ba zai ƙi gani ba".
"Haba Anty meye haka?, da girmanki kike furta waɗanɗan kalaman da zasu iya yin aiki a ganki ko a koto meye ya yi zafi haka?".
Salma ta furta da ruɗewa fal cikin muryarta da ta soma rawa lokaci guda, sannan ta ƙariso ta riƙe ni nidai idona suna ƙasa jikina yana rawar da ban san dalilin hakan ba sai dai ina jin wani sanyi mai ratsa jijiya da ɓargo yana bin cikin nama tare da gudu cikin magudanar kai jini ga sauran sassan jikina. Shigowar Umma da Hajiya cikin sashin daga sashin Hajiya Babba shi ya sanya Umman Salma haɗiye diri da kwandon masifar da bakinta yake rawa wajen sauƙewa Salma.
"Lafiya kuwa naga kunyi curku-curku?".
Hajiya ta furta yayin da suke ƙarisowa ciki, juyawar da Anty Binta zata yi idanunsu suka haɗe cikin na juna. Dukkanin su tsayawa suka yi juna mayarwa juna kallon da duk muka gaza gano manufar yin hakan, Anty Binta ce ta fara ɗauke idonta Hajiya ta saki guntun murmushi kafin ta furta"meya kawo ki cikin gidan nan?".
"Malama ki tsagirta min kiyi min haƙuri domin ba wajen ki nazo ba ehe, don haka kija gefe ki bani fili". Sai da ta mayar da dubanta ga Umma kafin ta ɗaura da faɗin"wajenki nazo domin nayi miki katsedi ko kuma ma kai tsaye na ƙira hakan da barazana da jan kunne akan ƴarki Na'ima. Kunyi asiri kun asirce min ɗan-uwana don tsabar son zuciya irin naku kun hana shi cigaba a rayuwarshi kun hana sa assala komai komai nasa ya tsaya ƴar biyayyar da yake yi min ma ita ma kun hana yi min. Kun susuta shi kuna ƙoƙarin zautashi da ƙarfin sihiri to wallahi ahir ɗinki hawainiyarku ta kiyayi gonar rama ta kuma kuruwar ɗan uwana kur ɗin ku yasha tabara yasha yasin ya haɗa kuma da rigakafin Allah tsine, zaku tura ƴar ku jami'a ya ce duk inda Na'ima ta tafi a faɗi duniya sai ya bita to shine nazo yi miki gargaɗi tun wuri ku karya asirin da kuka yiwa Yusuf inba haka ba kuwa wallahi idan na tashi yin nawa cikin mu babu wanda zai yiwa daɗi. Inba rashin zuciya ba ma wani irin maita ne wannan yaro ya ce baya sonki yana ƙaunar zama dake ki dinga bibiyar shi".
Saurin ɗago idona nayi tare da yin ƙarfin halin ɗaura su kan Anty Binta, wani irin suka nake ji a cikin ƙirjina tare bugun zuciyata ya yi ƙasa yana bugawa a raunane. Wasu hawaye suka fara fareti a tudon fuskana tare da gangarowa izuwa haɓata ƙafafuna suka ƙara ƙarfin rawar da suke yi mini Salma ta kuma riƙe ni gam a jikinta don babu shakka zan iya zubewa a ƙasa warwas. Maganar da Umma ta soma yi da alamar ɗimuwa a tattare da furcin natan da kuma buƙatar jin ƙarin bayani akan furcin na Anty Binta ta furta"meye kike faɗa haka? asiri kuma?".
"Ƙwarai kuwa abinda kunnanki suka jiye miki shi bakina ya furta, asiri asirin da ke da ƴarki kuka yiwa Yusuf kuke ƙoƙarin zauta shi shi zaku je ku karya shi".
"Binta kinsan dai ni dake kar ta san kar ne, don haaa tun wuri ƙafarki a alfaka ki fice dag cikin gidan nan. Wani asiri kike magana a kai?, sannan yaya aka yi kika san cewar anyi masa asirin?, meye hujjarki na faɗin hakan?, shin kina da hujjar da za ki kare kanki dashi a gaban hukuma?, ke da kika san asirin kuma kike yinsa dole kullum ki zamma cikin tsarguwa da tunanin cewar kowa ma kamanki ne mai hali irin naki".
A matuƙar fusace Hajiya tayi furcin idanunta har sun ƙanƙance.
"Ku dai yi haƙuri abi lamarin nan a sannu". Daada ta furta a karon farko tun bayan fitowarta wajen, so nake yi nayi magana so nake yi faɗawa Anty Binta cewar tayi mana kuskuren fahimta da har ta zarge mu da wannan mummunan zargin mai ciwo a cikin zuciya. Amma sai dai kash ba'a nan gizo ke saƙan ba domin ko kaɗan bakina ya hana ni wannan damar na furta abinda ke raina. Illa karkarwan da jikina ya cigaba da yi Salma cikin hawaye ta ce"Hava asiri kuma?, wallahi Na'ima ba zata taɓa yiwa wani asiri ba balle kuma malam Yusuf".
"Ke Salma ina raba ki, ina raba ki da ɗaukar dala babu gammo. Ta yaya aka yi kika san cewar ba zata iya ba?, ko kuma kinsan abinda ta ɓoye a cikin zuciyarta ne balle har ki bada wannan shaidar a hakan?".
Furcin Umman Salma kenan cikin sigar kashegi ga Salman, izuwa lokacin duk raguwar matan gidab mu sun gama hallara a wajen. Ƴan makaranta ma duk sun fara dawowa suka yi curku-curku a filin tsakar gidan suna ba wa idanun su abinci. Sosai Anty Binta tayi mana tijara da ɗiban albarka kafin ta cika buje ta da iska bayan ta yaɓa mana maganar ƙarshe da suka daki kwanyata sosai har suka sani tanka mata.
"Zan tafi sai dai ku tabbatar kun karya asirin da kuka yiwa Yusuf idan ba haka ba kuwa duk abinda ya sami shamuwa to watan bakwai ne ya ja mata".
Take a lokacin naji wani kuzari yazo mini ina jina tamkar wani ingarman doki na ce"babu wani asirin da muka yiwa Yusuf kuma wallahi ki sani cewar ba zamu yafe miki ba bisa wannan ƙazafin da kika yi mana. Sai Allah ya yi mana sakayya dake a ranar sakamako".
Kamar kububuwa haka tayo kaina da zummar marina Daada ta ce Salma ta jani ɗaki, kuka kawai nake ji amma hawaye baya zuba mini na zuci nake yi wanda ake wa laƙabi da yafi ciwo da raɗaɗi. Salma ke ta bani baki amma ko ta kanta ban bi ba domin nayi mata uzuri da cewar bata san yanda nake ji a cikin zuciyana bane shiyasa. Koda yaya Majid ya dawo daga wajen aiko da aka sanar dashi abinda ya wakana ransa ya yi matuƙar fusata ya ce sai je har gidanta ya yi mata rashin mutuncin da ko da wasa nan gaba ba zata sake gigin zuwa cikin gidan nan. Umma da Hajiya Babba suka hana sa, sai bayan magrib su Abba suka dawo basu san komai ba domin Hajiya Babba ta hana kowa ƙiran waya ya faɗa musu, sai dai daga yanayin da suka shigo cikin gidan rayukan su a ɓace kaɗai ya isa ya tabbatar da cewa labarin tunin ya iske kunnuwansu. Aka tara manya da ƙananan mu a falon Hajiya Babba.
"Tabbas bamu ji daɗin abinda ya faru ba, kuma cikin ku a rasa wanda zai ɗaga waya ya sanar da ɗaya daga cikin mu. Sai da baƙuwar lamba aka turo min saƙo akan abinda yake faruwa muka taho