Showing 15001 words to 18000 words out of 171161 words
Chapter 6 - MATAN AREWA BOOK TWO COMPLETE PDF .txt
dakan lugudai rawar da ƙafafuna suke yi suka tsananta. Naji wani ƙulli ya zarge mini a ƙasan ƙirjina duk sanyin da nake ji yana ɗan shiga na kasancewar wanka da nayi amma yanzu wani tiririn zafi nake ji, babu shiri na saki bokatin dake hannuna da hakan ya jawo hankulan su Daada izuwa gare ni.
Kamar wacce ake jawo ta da mayen ƙarfe haka naji ƙafafuna suna fizga na, basu dakata a ko'ina ba sai a gaban Daada da Umman su Anty Kubra. Hannuna na ɗaga ina nuna su dashi cikin tsantsar ɓacin rai da baƙin-cikin da ya sanya ni makancewa har na manta da su ɗin su waye ne, matar mahaifina ce da kuma matar ƙanin Abbana. Cikin rawar ciki da sarƙafewar harshe na shiga faɗin"Mushirika fa kika ce mushirika fa Daada Umman tawan?".
Yanda nayi maganar kamar bana cikin hayyacina don na hangi tsoro a cikin idanunsu kwance. Kafin Daada da jikinta ya ɗan fara rawa ta dake ta furta mini"e ita ɗin ko za ki dakan ne?". Cije leɓena nayi ina jijjiga kaina kafin na ƙara matsowa dab da ita sosai ina fitar da wani hucin ɓacin rai na ce"na gode Allah tawa uwar iya haka ta tsaya, domin ba a taɓa kama ta tana halin ɓeraye ba balle har ta kunyata a idanun jama'a. Kuma alhamdulillahi mu ƴaƴanta bamu taɓa jefa ta cikin wani rigimar da ta kasa fita da kanta ba ko a hakan ma mun godewa Allah". Ba don naso ba na tsayar da zancen sai saboda raguwar da suka maƙale mini a maƙoshi, nayi ƙwafa ina barin wajen bayan na gama cilla musu wani kallo. Na wuce ɗaki kamar zan kife domin ban san inda nake cilla ƙafata ba, ina jiyo ihun da Daada ta saka tana faɗin har da kukanta wai nayi mata rashin kunya na zage ta. Idona har wani dishi-dishi suke kallo mini abubuwan da suke gabana. Rigana doguwa na saka na kwanta ina jin duk raina a jagule ina jin zaman gidan ya gundure ni tamkar ta zabura na fita daga gidan a guje ko zan sama sukuni da salamar ruhi. Ina daga kwancen nake jiyo hayaniyar da ya ɓarke a tsakar gidan da kururuwan Daada tafi duk raguwar maganganun tashi. Daga hayaniyar da suke ratsa kunnuwana suka tabbatar mini da anyi ca a tsakar gidan kowa ya fito, kamar daga sama Asma'u, Falmata da Jalila suka faɗo ɗakin kamar an jefo su wanda suke gabaɗaya ƴan ɗakin su Anty Kubra ban da Asma'u da take ƙanwar Salma. Kallon ɗaɗɗaya na jefo musu kafin na ce"meya shigo mini daku ɗaki?".
Cikin wani jijjiga Falmata ta ce"za ki ga abinda ya kawo mu yanzu". A zabure na tashi zaune ganin sun nufo kaina gadan-gadan da zummar rufe ni da duka. Mamakin ya hana ni taɓukawa kaina komai balle samun zarafin cewa dasu wani abun.
Duk suka zame ɗan kwalayen kansu suka ɗaure ƙugunsu kallo na tsura musu da son ganin gudun ruwan su. Suka nufo ni gadan-gadan cike da son tabbatar mini da furcin su, shigowar yaya Majid ɗakin ya dakatar dasu na lura da ɓacin ran da ya kwanta luf a saman fuskansa. Cikin azama da zafin nama ya ɗauke Jalila da wani gigitaccen marin da ya sa ta zaman ƴan bori dirsham tana ɓare baki da sakin wani ƙarƙarfan ƙara kafin ya kuma kan Asma'u kafin yazo ga Falmata tayi saurin zillewa ta fice. Gidan ya ƙara rikicewa sosai banda hayaniya da ife-ife babu abinda kake ji wani kukan baƙin-ciki na tuntsire da shi da taƙaicin da ya yi mini dabaibayi. Yaya Majid ya kamo hannuna ya kai ni ɗakin Umma ya ce na zauna kar na fito idan akwai wacce take jin rashin kunyarta ya bunƙasa to ta shigo har ɗaki ta same ni, duk sababin da matan gidan suke yi kamar zasu cinye shi ɗanya bai tanka musu ba ya fice daga sashin gabaɗaya.
Wani kukan mai ƙarfi na kuma fashewa dashi, sakamakon Umma da na hango zaune bakin gadonta ta zagba tagumi da hannu bibiyu da rarrafe na isa gare ta na ɗaura kaina jikin ƙafarta ina mai cigaba da kukan. A hankali take bubbuga bayana tana sauƙe numfashi Anty Zakiyya ta jawo jiki ta riƙe hannuna
A haka muka zauna har lokacin da su Abba suka yi mana ƙiran gaggawa dukkan mu a sashin hajiya Babba a falonta muka zube, tun kafin mu shigo muke jiyo faɗar da Baba yake yi tamkar zai yi aron baki har muka zauna bai lafa ba.
"Ke Na'ima meya faru tsakanin ku?".
Ya faɗa a ɗan zafafe. Duk abinda ya faru na faɗa masa na kuma karɓi kuskurena ba don tsoro ba tun kafin ya faɗa mini, domin nima na san bai dace ba maganar da na faɗawa Daada amma an ce zuciya bata da ƙashi. Abba ya yi gyaran murya yana kallon Daada ya ce"haka ne abinda ta faɗa?".
Cikin kumbar baki ta fara cewar"Ai dole ka tambaye ni tunda ni tsabar lalacewa da watsewar da kimarta tayi a idonka tayi faɗuwar tasa. Duk abinda na faɗa ai baka yarda dashi ba, sai da ta faɗa maka zaka tambaye ni. To ni dai wallahi ba zan ɗauka ba ko kai baka bi min haƙƙina ba, tunda ba juya Allah yayo ni ba ya bani arziki ƴaƴa wallahi sa ƴaƴana sun mata dubun abinda tayi min, ai ko shirwa ya san ƴaƴan kaji kawai yake ɗauka ya kwana lafiya amma ba dai ɗan tsakon jimina b..".
Bata ƙarisa ba cikin zafin nama Abba ya ɗauke da marin da ya sanya bakinta rufuwa kirif, ya nuna da yatsa yana cewar"Halima na gaji da halinki wallahi kin fara kai ni bango. Ni ban tsane ki ba kamar yanda ƙaramar ƙwaƙwalwarki take kimtsa miki, halinki ne dai nake gudu. Ban da zubar da kima ina ke ina tsayawa cacar baki da ƴar-cikinki yarinyar da aka haifa akan idonki".
"Tunda a gaban idonka komai ya faru ai dole ka ɗaura min laifi".
Ta faɗa idonta taf da hawaye, jikina ya ƙara mutuwa tinawa da nayi nice silar faruwar komai. Murya a ƙarye na ce"Dan Allah kuyi haƙuri kuyi haƙuri, Allah ya huci zuciyarka Abba kema Daada ki yafe mini abubuwan da na faɗa cikin ɓacin rai".
"Babu abinda kika yi Na'ima ai uwa ta wuce wasa a gun duk wanda wani ɗan kirki da ya san darajarta. Da can ai ba ki yi mata ba sai da ta taɓo uwarki".
Baba ƙarami ya furta cikin tsananin ɓacin rai kafin Baba da baƙin-ciki ya gama cika ya furta"ke kuma Zainabu ko meye ya faru ai kin san dai Na'ima gaba take dasu Falmata da har za ki umarce su da suje su dake ta, bayan ku san tana ɗauke da juna biyu. wallahi daga ke har ƴaƴanki zaku haɗu da fushina kuka ƙara aikata makamancin irin haka, ku kuma yanzu ku bata haƙuri". Ɗaya bayan ɗaya su Falmata suka fara bani haƙuri na nuna musu ba komai, sai a sannan hajiya Babba ta ce"ni ina ganin kawai Na'ima ta dawo sashina ta zama kafin muga abinda Allah zai yi".
Su Abba gabaɗaya suka aminci hakan, sannan suka sallami kowa bayan sun yiwa kowa zazzafan gargaɗi da kashedi muka watse.
MATAN AREWA
(Book two)
© Maimunah Tijjani Iyam
_________________________________
Page 4⃣2⃣
Ko da na koma sashin na tarar da maganar bata mutu kamar ma yanzu aka yi ta. Ban ce ko kanzil ba daga ruwan zagin da suke zuba mini na shige ɗaki, cikin ƙunar zuciya nake haɗa kayana nima zan zo haka domin zama cikin su yanzu ba alkhairi bane a gare ni. Ina cikina haɗawa Anty Zakiyya da Umma suka shiga, sai da Umma ta zauna ta kallo ni haɗi da faɗin"Ba tarbiyan da na baku ba kenan Na'ima kuma idan da kiyi min adalci da ba za ki aikata wannan abun ba, ko ba komai Daada kamar uwa take a gare ku tunda tana auran mahaifinku. Yau ko faɗuwa nayi na mutu da ita zaku zauna tunda ko ba rabuwa ai akwai mutuwa kuma tana kan kowa. Na san kina da haƙuri da hau da kai ga abubuwa da dama amma ki ƙara haƙuri dududu rayuwar ma nawa take kwana nawa ne?, ki gama haɗa kayan kije ki same ta ki bata haƙuri".
Tunda ta fara maganar na tsaya da haɗa kayan, nayi ƙasa da kaina da hakan ya ba wa hawayen da suke maƙale cikin idona damar tsiyaya. Kafin nayi magana Anty Zakiyya ta amshe zancen da faɗin"Amma Umma mushirika fa ta ce miki, ni wallahi Na'ima tayi min dai-dai domin dama ni ce a wajen wallahi sai nayi mata abinda har ta koma ga Allah tana jin zafins...". Saurin buge mata baki Umma tayi"kul kar na ƙara ji wannan furcin daga bakinki. Duk wanda yake gaba daku ku bashi girmansa ai bin na gaba bin Allah, don haka maza kije ki bata haƙuri". Kaina kawai na iya ɗaga mata kafin na haɗe kayana tsaf cikin sanyin jiki don bana son dawowa sashin da sunan na mance wani abu nawa.
Sanda na fito haka na tarar da kowa tsayyaye kamar yanda na wuce su, kaina a ƙasa na isa gaban Daada da take zaune ƙasan bishiyan tsamiyar dake dashe a tsakiyar sashin namun ita kaɗai sai huci take yi. Har ƙasa na durƙusa ba tare da na ɗago na kalle fuskarta ba na ce"nazo ne na ƙara ba ki haƙuri akan abinda ya faru, kiyi haƙuri sharrin zuciya ne ki yafe mini".
"Sharrin zuciya ko kuma sharrin uwarki?".
Zuciyata tazo mini har wuya ina jin wani balbalin masifar dake tashi cikin raina, sai da na runtse idona na furta"Allah ya huci zuciyarki".
Ina gama faɗin hakan na miƙe ina jan akwatin kayana ba tare da na tsaya jin raguwar zancen da ta ɗaura dashi ba, Kaina tsaye na wuce sashin Hajiya Babba. Na wuce da akwatina ɗakinta na ajiye sannan na fito falo inda na wuce ta tana zaune, wani tuƙululun baƙin-ciki ya zarge mini raina sakamakon zantukan Daada da suke amsa kuwa a ƙofofin kunnuwana. Muryar hajiya Babba da na jiyo suka dawo dani daga karatun wasiƙar jakin da nake yi.
"Takwara meye kike tinani haka?".
Na saki ajiyan numfashi kafin na ce da ita"Babu komai Hajiya". Ta ƙura mini ido tamkar mai son karantar yanayin fuskana kafin can ta ce"sai haƙuri Na'ima ki dunga haƙuri, shi rayuwar duniya mahaɗinta haƙuri ne da kuma juriya. Matuƙar mutum bai rungume su ba to tilas ba zai rayuwa cikin kwanciyar hankali ba".
Shuru nayi mata da hakan ya bada damar ɗaurawa da"Gobe za'a je ɗebo kayanki in sha Allah, sai ki nutsu ki faɗa abubuwan da ba naki bane wanda dai ya saya da kuɗinsa sai a ware masa kayansa a gefe in anje".
"To".
Na faɗa ina jin faɗuwar gaban da ban san dalilin sa ba, matsowa tayi tare ɗaura hannunta saman nawa haɗi da faɗin"Na'imatu ki cire wannan tinanin daga ranki, ko wani bawa da irin ƙaddaransa a rayuwa don haka ki rungumi naki hannu bibiyu duk yanda yazo miki". Kaina kawai na ɗaga mata tayi ta yi mini nasihohi tana kwantar mini da hankali.
Ba kamar kullum ba yau dai na sama bacci kai ɗaya na farka, daga haka ban kuma komawa ba har aka yi assalatu na tada hajiya Babba tayi sallan ita ma. Share ɗakin nayi tsaf haka nan ma falo na wanke banɗaki ina niyyar share tsakar gidan. Hanifa ta shigo har ƙasa ta tsuguna ta gaishe ni na amsa mata fuskana fal da fara'ar da ta kasa ɓoyiwa, Allah ya sani duk cikin ƙannena babu wanda nake jin so da ƙaunar su ya dame na kowa kamar Nurain da Hanifa sun kwanta mini a rai. Karɓan sharan tayi ta fara yi ni kuwa na koma ɗakin wajen hajiya Babba na fara karatun alqur'ani.
Ɗaya bayan ɗaya yaran gidan suka fara zuwa gaishe da hajiya Babban wasun su sanye da kayan makaranta. Sai daga baya matan gidan suma suka zo gaishe ta sai a sannan na gaishe da Umma don Allah ya sani sam bana marmarin koda leƙawa sashin namun ne, ina jin hajiya Babba tana faɗawa Umma maganar zuwa ɗebar kayan ta ce sun yi ma maganar da Abba jiya, yaya Majid, Goggo Jummai da Salma su zasu je. Hajiya Babba tayi na'am da hakan sanda zasu tafi yaya Majid yazo ya sanar da hajiya Babba. Har ƙofar falo ta rako shi tana roƙonsa da har su yarda suyi wani fitinar ko Anty Binta ta cakale su da hakan suyi mata kunnen uwar shegu.
Ranar gabaɗaya wunina a ɗakin hajiya Babba nayi sa daga kwanciya sai karatun al-qur'ani sai kuma tinanin da na kasa yakice shi daga raina. Sai bayan sallan zuhr su yaya Majid suka dawo, a sashin Hajiya Babba aka zube kayan cikin ɗakinta na da kafin ayi mata wannan ciki da falon. Ko fitowa kallon kayan ban yi ba don haɗa ido dasu ma ƙara tina mini abinda zai sanya ni wani tinanin zai yi don haka na shafawa kaina lafiya nayi zama a ɗaki.
Sai da aka yi sallan magrib Salma ta shigo ina zaune kan sallayan da nayi sallan ina lazimi ta zauna har na gama. A kallo ɗayan da nayi mata na lura cike take da zaƙuwan fesa mini abinda yake cikin bakinta.
"Lafiya?".
Na faɗa ina naɗe sallayan da naki sallan, ta gyara zama kafin ta furta"Ke dai zauna tukunna maganar ba ta tsayiwa ba ce". Zaman nayi kamar yanda ta ce kana ta ajiye mini wata doguwar farar takarda akan cinya haɗi da cewar"Saƙo ne aka ban na ba ki".
"Saƙo kuma daga waye?".
"Ki karanta mana ke kuwa".
Buɗe takardan nayi na fara karantawa kamar haka.
" ```Na'ima tun bayan rabuwar mu dake nake cikin tashin hankali, na kasa samun nutsuwa komai nawa ya lalace hatta aikina yana watangalili komai nawa ya tsay cak. Na gane rashin ki kusa dani babban illa ne ga rayuwata hakan na nufin koda zan cigaba da numfashi to zan yi rayuwa ce da ban da maraba da gawa, domin ba zan iya amfanar kaina ba balle ba amfani wani na kusa dani. Bana buƙatar sai an faɗa min domin nima kaina na san ban kyauta miki ba, kuma ina tsoron Allah ya kama ni da laifin saka ki cikin wani hali don haka nake roƙon yafiyar ki. Don Allah ki yafe min Na'ima ko zan samu sallama, nayi farin-cikin jin kina ɗauke da jinina dan Allah ki bani dama ɗaya na samu ganin ki koda kuwa shine alfarma ta ƙarshe da za ki yi min a rayuwa".
```
Wata ƙatuwar ajiyan zuciya na sauƙe dai-dai sanda na gama karanta kalmar ƙarshe ta wasiƙar. Ƙwalla tana ciko mini idaniya na ɗauko idona na zube su akan Salma. Ita ma ɗin ni take kallo ta ce"malam Yusuf ne ya bani da muje ɗebo kayanki, wallahi Na'ima sai kin gan shi abin tausayi duk ya rame ya yi duhu, kai ni kam da ba saki uku ya yi miki ba wallahi da sai nayi ruwa da tsaki kin koma gidansa don har yanzu yana sonki".
Taɓe baki nayi ina jin zancen na ƙarshe suna sauƙa a kunnuwana tamkar busar sarewa wai yana sona. Tuƙuiƙuye takardan nayi na ce"ai ba ranar da soyayyar tayi mana tunda hakan bai hana mu rabuwa da juna ba kin ga kuwa ba amfanin ta".
"Naji amma dan Allah ya roƙe ni da na sanar dake ki kunna wayarki, don ya sha ƙira a kashe kuma na tabbatar masa da zan sanar dake".
"To kin yi ƙoƙari tunda kin cika alƙawari, sai dai ni ba zan kunna wayata saboda wannan dalilin ba". Na faɗa a harsale domin na lura so yake ya raina mini hankali, ta yaya zai yi mini saki uku babu laifin tsaye balle na zaune kuma ya ce wai baya cikin nutsuwa ai ko shaye-shaye ya yi sai haka.
Cikin zafin rai na ce"Salma idan kina son mu zauna lafiya kar ki ƙara zuwar mini da wannan maganar". Sai da nayi maganar naji kunya ta kama ni domin yanda jikinta ya yi sanyi sai dai na dake. Haƙuri ta bani kuma canja hira gani nan dai a gaban ta amma sam hankali da nutsuwata sun yi ƙaura daga gangar jikina.
Ban kunna wayar ba da tunda nazo gida na kashe ta. Domin gujewa duk wata hanyar da zata haɗa ni da yaya Yusuf, Allah ya sani ko muryarsa bana son ji balle kallonsa ido cikin ido. Washe gari hajiya Babba ta shiga makwabta barkan haihuwa, ni kaɗai ne zaune a sashin ɗago kan da zan yi naga Abasiyya tsaye a kaina tana faman jijjiga ƙugu da kallo mai bayyanar da maɗaukakiyar mamakin dake kwance a fuskana nake bin ta. Kafin ta furzo mini zance da suka sanya mamakina ƙara girmama, wai tazo ɗaukawa Daada fansar rashin kunyar da nayi mata tunda uwa bata fi uwa ba.
Zuciyata ta shiga sarƙa mini me take nufi kenan?, me zata aikata mini?, ban kai ga cimma amsar ba naji ta finciko ni izuwa ƙofar falon nayi mata wani kallo idanuna cike da hawaye"Abasiyya ni kika wancakalo haka ni Abasiyya?".
Tsaki tayi ta ce"ke ɗin Na'ima na ce ke ɗin". A hankali na miƙe wallahi ta ci darajan turtsetsen cikin dake cikinta da haihuwa ko yau ko gobe, ba don hakan babu abinda zai hana ni ajiye girman ta da nake gani muyi abinda take so. Ɗaga hannu tayi da nufi sauƙe mini mari nayi saurin runtse idona tabbas ban ji hannunta saman kuncina ba amma naji ƙara ɗauke mutum da mari tas da aka yi kafin ihun Abasiyya ya cika wajen.
MATAN AREWA
(Book two)
© Maimunah Tijjani Iyam
___________________________________
Page 4⃣3⃣
Yaya Majid ne tsaye yana wani irin huci tamkar saniya zata kai bugu, cikin ƙololuwar ɓacin ran da ya bayyana ɓaro-ɓaro a saman fuskarsa yake nuna Abasiyya da ƴar manuniyar yatsarsa yake faɗin"wallahi ki kiyaye ni Abasiyya ki fita idona daga ke har uwarki, in ce dai an kashe maganar nan amma shine za ki ɗauko ƙafa tunda gidan mijinki ki taho".
Bata iya bashi ba sakamakon wani irin gigitaccen ƙaran da ta kuma