Showing 114001 words to 117000 words out of 171161 words
Chapter 39 - MATAN AREWA BOOK TWO COMPLETE PDF .txt
gidan nan ba, na dai lura kamar ba mai son shiga jama'a bane ita ɗi....". Harara da ta aika mata ya sanya ta haɗiye ragowar zancen a cikinta ba tare da ta furzo shi waje ba.
"Ban nema kiyi min wani dogon turanci ba tashi kije ki ƙira min ita".
Miƙewa tayi cike da takaici ta nufi ɗakin Aishan taje ta ƙirayo ta, bata tsaya a wajen ba tayi shigewar ta ɗaki tayi zamanta. Kallonta sosai Anty Bintan tayi kafin ya furta"yanzu kika tashi a bacci ne ko meye?".
Ƙara mirtsike idanu tayi ta ce"wallahi Anty jiya bamu kwanta da wuri bane". Jinjina kai tayi ta ce"ba laifi amma ki sa ni bana son wannan sakalcin da kika saba dashi a gidan ku, aure kika zo yi bautan ubangiji ba wai hutu kika zo ki miƙe ƙafa ba, sannan kiyi hankali da wannan matar sosai kar kiga tana janki a jikinta kiyi tinanin wai sonki take yi annabi Musa ne a baki Fir'auna a zuci".
Taɓe baki tayi ta ce"matsalarta ai ni ko kallo ma bata ishe ni ba".
"Ya dai fi kam ina shi mijin nakin?".
"Oh Honey wallahi ya ɗan fita amma ina jin ma yanzu haka yana hanya".
"Yusuf fa nake nufi?".
Dariya ta kwashe dashi kafin ta ce"e ai ni da wannan sunan nake ƙiran shi dashi Honey". Riƙe haɓa tayi tana faɗin"ba shakka tashi muje ɗakin nakin".
Ɗakin suka nufa tunda ta dosara mata ledan pure water ɗaya a gabanta ba tare ƙara waiwayo ta ba, sai ma wayarta da ta ɗauka tana chart da ƙawayenta tare da ƙyalƙyalewa da dariya. Babu jimawa sallamar Yusuf ɗin suka ratsa kunnuwansu, cikin sauri ta dire wayar hannunta ta nufe shi da ɗan saurin ta cikin yauƙi da wani salon tafiya tana turo ƙirji gaba ta isa gare shi ba yi aune ba ya ji ta rungume shi tana cewa"Honey sai yanzu ka dawo ka bar ni ni ɗaya kewarka tana ta addaba na daman Anty tazo tana ɗan taya ni fira".
MATAN AREWA
(Book two)
© Maimunah Tijjani Iyam
_____________________________________
Page 9⃣8⃣
Sakaka Anty Binta ta hangale baki tana bin ta da kallon tsantsan mamaki da girmama halin fitsara da rashin kunyarta a cikin ranta, wani ras yaji ƙirjinsa ya bada yana jin wani abun da ya gaza fasalta shi cikin kalma guda yana bin dukkan gaɓoɓin jikinsa. Saurin ture ta ya yi daga jikinsa cike da takaicin ta ya firzge jikinta tare da jifanta da wani mungun kallo, ji yake yi tamkar ya kauta da mahaukacin duka ko zai huce takaici da zafin abinda tayi gaban Anty Bintan duk bata aika haramun ba a addinance amma bai yi tsammanin rashin kunyarta ya kai har wannan matakin ba. Har ya zauna bai iya ɗago idonsa ya kalli Anty Bintan ba, kansa yana sunkuye a ƙasa ya ce"mun wuni lafiya Anty".
Sai a sa'ilin igiyar mamakin da ya yi mata ɗaurin huhun goro ya sake ta, har ta sama damar jawo numfashinta dake garkewa a ƙirji ta fesar haɗi da cewar" Yusuf rashin kunya da kuke yi kenan a gaban ko wani baƙo idan yazo gidan nakun kenan?".
Shuru ya yi mata yana ƙara yin ƙasa da kansa, bai tsammaci jin komai daga bakin Aisha ba a wannan lokaci amma da mamakin sa sai yaji muryarta ta bugi dodon kunnuwansa da ya tilasta masa saurin watsa masa idanunsa.
"Rashin kunya kuma Anty? da aka yi meye kenan?. Mijina ne fa shi ni kuwa matarsa ce ta sunna, ai ni a huɗubar aure da aka yi min kafin a kawo ni cikin gidan nan ba a sanar dani cewar idan mace ta tarba mijinta, yayin da ya dawo daga wajen nemo musu halal rashin kunya bane Anty".
A zazafe ya furta"kar na ƙara jin kin furta wata kalmar a nan, tashi ki bamu waje". Zumɓuro baki gaba tayi ta miƙe tana motsa dukkan wasu sashin jikinta ta shige ɗaki, da kallo Anty Binta ta raka ta dashi kafim ta ce"ba shakka Yusuf, hmm ba komai ka cigaba da haƙuri yarinya ne ke damunta yarinya ce ƙarama dududu Aishan ma yaushe aka haife ta girman jikin ne kawai ya riga hankalin zuwa. Amma kayi haƙuri zata daina". Da sauri ya cilla idanunsa cikin nata a karon farko kenan tun bayan shigowarsa cikin falon, fuskarsa ɗauke da maɗaukakiyar mamakin da ta kasa ɓoyiwa sai da ta bayyana ɓaro-ɓaro a bisa fuskarsa, ko kaɗan bai yi tsammanin fitowar ire-iren waɗannan furcin daga bakinta ba domin a sanin da ya yi mata macece mai matuƙar girmama al'ada a wani sa'ilin har ta kan fifita shi tare da sanya sama da addini. Tana da tsananin riƙo da al'adun baya mussamman ta fannin kunya domin har yanzun bata ƙiran sunan Amir kai tsaye kasancewar ɗanta na fari, tabbas yasan abinda Aishan ta aika bai ci karo da tsarinta ba faɗan da zata yi sai kalaman bakinsa sun kusa ƙarewa wajen bata haƙuri da lallashin ta, domin yasha faruwa ga Maman Hanan ko rakiya ta zo gidan ta iske ta yiwa yaya Auwal wuni zata yi zum tana faɗa har da kumfan baki tare da jingina mata kalmar marar ta ido wato kunya. Baya mancewa hakan ta taɓa faruwa sanda yake tare da Na'ima ta yi ta faɗa.
Har yanzu idanunsa yana kanta ya soma faɗin"Anty meye kike faɗi haka anya ke ce kuwa?, wani irin haƙuri kuma kike magana a kai, a iya sanina duk sanda bisa kuskure irin hakan ta faruwa tsakanin yaya Auwal da maman Hanan faɗa kike yi sosai amma yanzu kuma sai naga kaman kare ta kike ƙoƙarin yi ne bangane ba". Zazzafan harara ta watsa masa kafin ta ce"ka haɗa Habiba da Aisha ne ai ido ba mudi bane amma yasan kima, Habiba da take uwar mata ita kuwa Aishan ma nawa take?. Haƙurin da na ambata dai shi zaka cigaba da yin sa". Bai ce komai illa ajiyan zuciya da ya sauƙe mai nauyin gaske, har ta ƙare zancen da ta ɗaura dashi bai ce da ita ko kanzil ba ƙiran sallan zuhr ya sanya shi tashi ya fice masallaci.
Kamar jira take yi ya fice ta faɗa cikin uwar ɗakan ta iske Aishan da ta gama cika ta kam da tsabar tsagwaron takaici, ta faɗa ɗakin tana muzurai can ƙuriyar ɗakin ta hange ta. Da sarsarfa ta isa gare ta sai abinda ta yi tozali dashi ya tilasta mata ja ta tsaya babu shiri tare da ƙare ware idanunta akan ƙullin ledodi da wasu kwalaye masu ɗauke da hotunan jinsi biyu mace da na miji kwance a jiki.
Haɓa ta riƙe ta ce"na shige su ni Binta me idona yake gane min haka, Aisha meye waɗannan?". Ɗagowa tayi ta jefa mata wani kallo kafin ta mayar da dubanta ga abinda take yi, a dake ta furta"maganin mata ne da wasu sirran riƙe miji gam a tafin hannunka". Galalo idanu Anty Binta tayi numfashinta har yana fizga take faɗin"maganin mata kuma Aisha meye haɗa ki dasu?".
"Bangane meye haɗa ni dasu ba?, in ce dai nima macece ko ai kuwa kinga wannan tambayar ma ba ki yi ta a inda ya dace ba. Ai nayi tinanin waɗannan kam duk kin riga da kin waye su farin sa ni, wasun su na mallaka ne wanda nasan ba sabbin abu bane a gare ki tunda duk garin nan babu wanda bai san da cewar gidanki ke ce mijin ba shine matar duk yanda kika so kika dama haka nan ake sha, har sakin ki ya yi amma hakan bai sa kin bar cikin gidan ba kamar yanda shima hakan bai sanya shi dakatawa daga shiga da fice a cikin gidan kamar lokacin da yake ɗauke da igiyoyin aurenki uku ras a kansa ba".
Idanu Anty Binta ta ƙura mata babu ko ƙiftawa da ƙoluluwar mamaki take cigaba da bin ta da kallo, tas ta ɗauke ta marin da ya bada sautin da ya ɗauki dukkan kusurwan ɗakin tunin idanunta suka rufe ɓacin rai ƙara-ƙara shimfiɗe a bisa fuskarta take faɗin"ashe ba ki da mutunci Aisha ban sa ni ba?, ni za ki kalla tsabar idona ki faɗa min waɗannan maganganun. To wallahi ko uwarki wacce take sa'ata tayi tsararo ta furta min wannan zantukan balle kuma ke da aka haife ki bisa idanuna. Tun wuri ki mayar da hankalinki ki kuma shiga taitayinki ki san abunda ya kawo ki cikin gidan nan domin naga kanki yana rawa da fizga, ki koma wajen uwarki ta sanar dake wacece ni da kuma abinda zan iya aikatawa da wanda ba zan iya ba, ki zama mai tina wannan a ko yaushe a cikin ranki cewar alfarma Yusuf ya yi miki ya aure ki ba wai don kin cancanta ba da hakan za'a duba da wallahi babu wani haɗi tsakanin kifi da kaska. Sannan waɗannan abubuwan ki tabbatar da cewar kin watsar dasu ko kuma ki ƙona su gabaɗaya kar ki kuskura na kuma dawowa cikin gidan nan na tarar dasu shashasha kawai wacce bata san inda yake mata ciwo ba".
Dake take da kuncinta da ta sauƙe mata lafiyayyan marin da taji zafin sa har cikin kansa, ga fatar wajen da take yi mata matuƙar raɗaɗi kamar an watsa mata tafashashshen ruwan zafi mai turiri, kuka take yi shaɓe-shaɓe har da shishshiƙa tamkar zata shiɗe, Anty Binta tana haɗe zancen natan da ya ƙare da kashedi mai kaman bada umarni ta fice daga cikin ɗakin a matuƙar fusace kamar kububuwa.
Maman Hanan ta tarar tana kwashe shinkafa da waken da ta gama girkawa kenan, ta fito zata wuce yanda ta sanya kai zata fice shi ya tabbatar mata da cewar bata lura da wanzuwanta a wajen ba hakan ya sanya ta faɗin"Anty har za ki tafi?, da kin tsaya ai kin ci abinci". Ba tare da ta waigo ta ta ce"bar shi kawai Habiba".
A shaƙe ta yi maganar tamkar wacce aka sanya igiyan kirtani aka zargewa maƙoshi, har wani tafasa take jin ranta yana yi mata a tarihin rayuwarta kaf na zaman duniya bata jin an taɓa yi mata cin kashi makamancin wanda Aishan tayi mata yanzu. Bki sake maman Hanan ta raka da kallo sai da ta fice daga cikin gidan ta ɗauke idonta tare da faɗin"Allah ya kyauta".
Zaune yake a cikin ofishinsa yana aiki a cikin laptop ɗin dake gabansa, yau yake sanya rai da dawowan Farouk daga garin kanon da ya tura shi wajen Anty Fauza ya yi salla a can, ko zai rake tinanin da ya kallafawa kansa tun bayan gano cewar duk abinda ya faru shirin Habib ne da Mina. Tun bayan hakan ya ƙara jin soyayya gabaɗaya ya fice masa fit a cikin ransa domin ya yarda cewar wani lokacin takan makantar da mai yin ta ba tare da bashi damar tinanin abinda kan iya zuwa ya dawo ba har ya sauƙa kan turba kamar yanda ta kasance ga Habib.
Ƙiran sallan zuhr ne ya sanya shi fitowa daga ofishin tare da kulle ta, yana fitowa suka yi kiciɓus da malam Dauda kallon suka shiga mayarwa da junan su ba tare da wani ya ce da wani ko kanzil ba. Limanci ya yi a babban masallacin jami'ar sannan ya wuce wajen motar har ya tada ita ya tina da nauyin dake kansa babu shiri ya dafe goshinsa da yake jin ciwon kai kaɗan kaɗan yana taso masa.
Ɓalle marfin motar ya yi ya fito ya nufi hall ɗin da ƴan 100 level department of mass com suke rubuta exams kasancewar yana da time table ɗin nasun, sai da suka kai sa da lecturers ɗin da suke invigilating kafin ya shiga rarraba idanu.
Kaina duƙe kan booklet ɗin dake gabana ina zuba rubuta, attendance ɗin da wacce ke gabana ta miƙo ya sanya ni ɗago kaina caraf idanuna suka sauƙa a kansa yana tsaye gaban hall ɗin ya zube hannayensa gabaɗaya cikin aljihun wandonsa a faƙaice yake kallon da ba lalle kowa ya gane ba, saurin janye nawa nayi ina saki tsaki ciki-ciki mu kam yaya Majid ya haɗa mu da ƙarfan ƙafa domin tunda muka dawo ya wani sanya mana ido bai taɓa cewa damu uffan ba sai idanunsa da yake kanmu, da muka fara exams kuwa ko yaushe zai ya shigo hall ɗin ya tabbatar da mun zo sannan ya wuce. Attendance ɗin na amsa na sanya sunana da matric number na miƙawa ta bayata na cigaba da rubutuna.
A hankali yake sauƙe ɓoyayyiyar ajiyar zuciya tunda ya tabbatar da cewar sun zo rubuta exams, musabaha suka ƙara yi da lectures ɗin sannan ya fice daga cikin hall ɗin sai da ya fara tsayawa a gida ya yi wanka sannan ya wuce asibiti, Abdul-aziz shi yaje motar park ya ɗauƙo Farouk ya kawo shi asibitin.
Sai da na tashi zanyin submitting na Mr Suleiman yana shigowa hall ɗin wanda exams ɗin course ɗinsa muka yi yau ban yarda mun haɗa ido ba, na fice daga hall ɗin na zauna a waje ina jiran fitowar Nawwara da Nazifa ban jira sosai ba suka fito a tare question ɗin muka tsaya dubawa. Sai da kowa ya fito ana ta maganar sauƙin da question ɗin suka yi wanda babu wanda ya taɓa tinanin Mr Suleiman ɗin ya fitar da irin su. Mun tashi zamu tafi hostel muryar Mr Suleiman ɗin suka dakatar damu da muka ji su a tsakiyar kanmu, cikin wani salon da ya fi kama da na mungunta yake faɗin"kar kuyi murnar ganin waɗannan question ɗin, ku adana handout ɗin ku zai yi muku amfani next year".
MATAN AREWA
(Book two)
© Maimunah Tijjani Iyam
__________________________________________
Page 9⃣9⃣
Duk a ɗimauce muke bin sa da kallo, ya ja baƙin gilashin da ya ɗaga ya ɗasa a saman kansa ya mayar idanunsa ya shige motarsa dake kusa da inda muke tsaye ya fige ta tare da ɓula mana ƙura, da ƙyar muka kai kawunan mu izuwa hostel muna isa muka zarce ɗaki. Nazifa ta ɗaura hannu a ka tana faɗin"mun shiga uku meye wannan bawan Allahn yake nufi damu ne a makarantar nan, meye yake nufi da mu adana handout ɗin mu zai amfane mu next year?".
"Carryover mana Nazifa shi yake nufin mu dashi, kuma duk maganganunsa inda suka dosa kenan. Sai dai wallahi ta Allah ba tashi ba in sha Allah babu abinda ya iya damu sai wanda Allah ya ƙaddara zai faru damu karma ku ɗaga hankulanku".
Furcin Nawwara kenan da ya sanya sakin numfashin da nake jin ya taro ya tokare mini ƙirji waje, na sama zarafin faɗin"ai kuwa dole hankalinmu ya tashi don ga duk mai hankali wannan furcin ya isa ya tada masa da hankali, amma kamar yanda kika ce Allah ya fishi kuma addu'a tana gaba da komai. Mun amsa dukkan tambayoyin da ya tambaya a gwaji da jarabawansa in sha Allah ta Allah ba tashi ba".
Wunin ranar dai sukuku muka ƙarisa shi sai dai bamu faɗawa kowa hakan ba. Exams biyu kacal suka yi mana saura daga su mun gama sai kuma wani zangon idan Allah ya ara mana rai, lafiya da numfashi mun kai. Kamar ko wacce safiya tunda muka fara jarabawan sai kawu Musa ya ƙira Nawwara ya yi mata fatan sa'a yau ma hakan ne ta kasance haka nan ma yaya Majid zai ba wa Umma ta yi suburbuɗo mana addu'a, ta fannin yaya Amin kuwa kullum sai ya turowa Nazifa saƙon fatan alkhairi da sa'a shima. Ƙarfe biyu muka rubuta jarabawan yau daga gobe mun gama jibi kuwa da yardan Allah mu kama hanyar gidajenmu, yau ma sai da yazo hall ɗin ya duba mu don dukkan safiya muka yi waya da yaya Majid sai ya yi mini zancensa.
Ƙarfe goma sha ɗayan rana muka zana jarabawar ƙarshe wanda ta kasance course ɗin Mr Saif, cikin nishaɗi kowa ya fito don iya abinda ya koyar damu su ya tambaya babu ragi babh ƙari. Hotuna aka yi sosai kamar ba gobe Nazifa da Nawwara duk suka shiga ni dai ina zaune a gindin bishiya na tallafi hucina ni ba mai tinani ba ni ba wacce nake tare da hankalina ba idanu kawai na zubawa mashigar jami'ar da ake ta shige da fice kamar daga sama naji muryar mutum a kaina.
"Are you ok?".
Ganin sa ya sa ni kiɗimewa ban iya amsa masa da fatan baki ba illa kaina da na ɗaga masa, ya jefo mini wani kallon da ya fi kama da ba tuhuma kafin ya kuma faɗin"how was your examination?".
"Alhamdulillah sir".
Na furta ya jinjina kansa ya ƙarisa wajen motarsa, bai shiga ba sama wayar da ya fara yi da nan take yanayin fuskarsa ya sauya duk da ba wani cika sakin fuskar ya yi ba in dai ba lecturing yake yi ba, wani matashi ne ya ƙariso jikin motar da suke da tsantsar kama dashi kwabo da kwabo ɗauke da jakar laptop a hannunsa ya buɗe motar ya sanya sannan ya zagayo ya mashi key ɗin motar, sai da kuma buɗe masa ƙofar wajen mai zaman banza sannan ya shima ya shiga wajen direba yaja motar, sai da suka ɓacewa ganina sannan na kawar da idona daga kallon motar da nake yi. Dai-dai sa'ilin da Nawwara da Nazifa suka iso wajen harara na watsa musu ina miƙewa na ce"ai wallahi kunyi sa'a da sai dai ku juyo ku ga bana nan", dariya suka yi a tare suna bani haƙuri muka nufi hostel muna tafe muna hirar mu da Nawwara, Nazifa tana daga bayan mu suna biyan fashin wayan da ba yi sosai da yaya Amin tunda muka fara jarabawa. Da yawa yau suka tafi mu kaɗan muka rage bayan sallan isha'i muna zaune a tsakiyar hostel ɗin da muka kunna tocila muka ajiye masu cin abinci nayi masu wanki suma suna ta fama, gefe guda kuwa hira ake yi sosai na rabu don har cewa muka yi ba zamu yi bacci ba yau kowa sai faɗin inda zai je shi hutun wannan zangon yake yi.
"Mu kam ai muna makaranta har kuje ku dawo".
Furcin Billy ɗawisu kenan da ya sanya hankulan mutane karkatowa gare ta, Farida take wanki ta