Showing 132001 words to 135000 words out of 171161 words

Chapter 45 - MATAN AREWA BOOK TWO COMPLETE PDF .txt

sai kin zama tamkar wawiya ko kuma wacce bata san abinda take yi ba a gaban sa don ki fahimci abinda yake ɓoyewa ko kuma wannan ɓoyayyen manufan nasan. Kiyi masa biyayya iyakar iyawar ki kar kiyi la'akari da cewar bakya son su hakan ya sanya ki yin abinda bai dace ba, a ko wani yanayi ki sama mai amfani da irin tarbiyan da iyayen mu suka ɗaura mu a kai Salma. Maganar kusanta ta baya kuwa ku ƙara zama dashi ki nusar dashi haramcin hakan a addinance da kuma illansa ga lafiyarku gabaɗaya kiyi haƙuri kinji".
Kanta kawai ta ɗaga mini wasu hawaye sirara suna zirara daga idaniyarta suna wanke mata fuska, musgutawa nayi na riƙo hannunta ina fuskantan ta sosai nake faɗin"kiyi haƙuri ki ƙara haƙuri Salma yanzu ko wani aure akwai nashi irin ƙalubalen, koma ko wacce mace kika gani zaune cikin gidan aurenta to wallahi ita kaɗai ta san irin matsalar da take fuskanta domim mai ɗaki shi yasan inda yake masa yoyo".
Ajiyan numfashi kawai take sauƙewa hawayen suna cigaba da kwaranyowa daga koramar idaniyarta, lallashinta na cigaba da yi har ta tsagaita da hawayen tare da bata wasu shawarwari kafin na baro gidan sai ta kuma roƙana akan na riƙe mata sirrinta kar na gayawa kowa koda kuwa Ummata ne nayi masa wannan alƙawarin, har kusan zaure tayi mini rakiya sannan muka yi sallama ina tafe ina tinanin wani irin lamari ne malam Mamman da Umman Salma suke ɓoyewa har muka isa gida tinanin da nake ta yi kenan.


Zaune yake a ofishin likitan ya gama karanta sakamakon gwajin kenan da ya sanya aka ƙara yiwa Ummin, shafa gefen sumarsa ya yi yana miƙewa tare da miƙawa likitan hannu suka yi musabaha ya ɗauki takardan sakamakon da kuma na sallaman da aka basu a yau ya fice daga ofishin. Ɗakinta na nufa ya iske Farouk har ya gama shirya komai shi kawai suke jira su tafi sai da ya sanya takardan a aljihunsa sannan ya iso ya miƙawa Ummin hannunsa ta riƙe ta tashi tsaye da kansa ya sanya mata hijabi a jikinta sannan suka fara tafiya a bayan motan ya zaunar da ita Farouk ya zauna a kujeran ɗan zaman banzan shi kuma ya yi driving ɗin motar. Sai da suka tsaya a hanya suka yi siyayyan fruit sosai sannan suka wuce gidan, ɗakinta suka wuce da ita Farouk ya haɗa mata ruwan wanka ta shiga, da kanshi Saif ya ciro mata wasu kayan da duk abinda zata buƙata ya ajiye mata akan gado sannan suka fice izuwa ɗakunan wanka suka yi suka sauya shiga sai da ya biya ta kitchen ya haɗo mata coffe tare da ɗauko goron ruwa sannan ya wuce ɗakin, zaune ya iske su da Farouk ya sanya ta a gaba sai zuba mata suturu yake yi babu abinda take ce masa illa mishi da ido da take ko sai kuma murmushin ta take yi masa.


Ajiye mata coffen ya yi sannan ya ɗauko maganinta ya ɓalla mata ya miƙa mata tare da ruwan, karɓa tayi ta sha kana ya miƙa mata coffen murmushi kawai ta sakar masa ta fara kurɓa a hankali tana faɗin"idan kayo aure Allah ya baka mace ta gari kaga duk wanna ɗawainiyyar ita zata na yin shi, kai ma zaka sama ishashshen lokaci a ganka Saifuddeen".


Ƙasa ya yi da kansa yana murza yatsun hannunsa ya ce"Ummi ba zan taɓa gajiyawa da ɗawainiyyarki ba, sannan ba zan yi wannan auren bane domin na huta da yin ɗawainiyya dake zan yi shine kawai domin kina so don kuma na cika miki burinki".
Shafo kansa tayi"Allah ya muku albarka". Amin suka amsa dashi yana sakin ɓoyayyen ajiyar zuciya a ko yaushe ya zauna sai ya yi tinanin dalilin da Ummi ta dage akan wannan yarinyar, bai sa ni ba ko don a tarihin rayuwarsa bata taɓa ganinsa tsaye da wata mace bane balle har su ɗauko hoto haka oho. Sun daɗe suna hira da Farouk shi kam da ido kawai yake bin su har izuwa lokacin da Abdul-aziz ya ƙira wayansa yana shaida masa cewar yazo shi tare da matarsa suna falon ƙasa. Tare suka sauƙo suka iske su, suka gaishe da Ummi tare da yi mata yaya jiki ta amsa musu cikin tsantsan kulawa, nan suka ƙarishe wunin ranar sai yamma lisi suka tafi. Bai sama lokacin yin magana da Anty Fauziyya ba sai dare komai ya kwashe ya faɗa mata sosai ita ma ta goyi bayan da yaje ya nemi auren yarinya don a shekarunsa ya dace a ce yana da iyali ko don kare mutuncinsa a idanun jama'ar gari.
Ranar muka wayi gari da wani labarin a wajen yaya Majid kan cewar za'a yi baƙi, cefane ya yi mai kyau ya kawo ya ce da ni da Anty Zakiyya muyi girki na musamman duk da bai sanar damu su waye baƙin ba amma daga yanda yake babban shiri wajen karɓan su kaɗai ya isa ya nuna muhimamcin su a gare shi da kuma matsayin sa. Kafin ƙarfe goma tsaf mun kammala komai mun kai sashin su Abba mun jere su, muna dawowa daga sashin muka yi kiciɓus da yaya Majid zai fita.


"Baƙin sun iso kenan?". Anty Zakiyya tayi maganar tana bashi hanya ya ce"e sun iso suna wajen zan shigo dasu su ne". Ya fice mu kuma muka koma cikin gidan na shiga wanka.


MATAN AREWA


(Book two)


© Maimunah Tijjani Iyam


____________________________________


Page 1⃣0⃣8⃣


A falon su Abba suka yada zango yaya Majid ya gabatar musu da girkin da muka yi su fara ci kafin su Abba su shigo, kallon wanda yake zaune kusa da Abdul-aziz yaya Majid ya yi haɗi da faɗin"wannan ban san shi ba amma ƙanin Saifuddeen ne ko?". Dariya Abdul ya yi yana haɗiye yankan kankanan da ya sanya a bakinsa ya ce"tambaya kayi kuma ka ba wa kanka amsa da kanka, ƙaninsa ne". Kansa yaya Majid ya yi"gaskiya kam naga alama ai".


Murmushi kawai Saif ɗin yake sakar musu kansa yana kan wayarsa da yake dannawa lokaci zuwa lokaci, Abdul-aziz da Farouk ne kaɗai suka ci abincin shi kam ruwa kawai ya sha ya yi hamdala duk yanda yaya Majid ya takura shi akan ko kaɗan ne ya ci ƙi yawa ya yi. Hira suka ɗan taɓa har izuwa lokacin da aka fara ƙiran sallan zuhr tare suka fito suka shiga sashin Hajiya Babba suka gaishe ta sosai tayi murna da zuwan su sai tambayar su yaya mai jiki take yi babu ƙauƙatawa balle gajiyawa, masallaci suka nufa suka gabatar da sallan zurh a hanyar dawowa suka haɗu da su Abba suka dawo tare suka zauna a falon su.


"Ya mai jiki?, muna nan muka ji kyakykyawan labarin Allah ya bata lafiya har tana magana munyi murna sosai".


"Jiki alhamdulillah babu abinda zamu cewa Allah sai godiya da kuma ku da kuka zamto sanadi, mun gode mun gode sosai babu abinda zamu iya bi yanku dashi sai dai addu'a".
Cike da jin daɗi Baba ya amsa da"babu komai duk yiwa kaine ai Allah dai ya ƙara mana lafiya gabaɗaya".
Amin duk suka haɗe baki wajen faɗi sun ɗan taɓa hira akan abinda ya danganci rashin lafiyan Ummin tare da basu wasu addu'o'i, har aka yi ƙiran sallan asr tare duk suka je masallaci sannan suka dawo tare yaya Majid ya zarce dasu sashin Hajiya Babba kwaɗon zogalen da yau ta kafe akan shi zata ci da rana ta zubo musu ta ajiye musu a gaban su.


Cikin raha take faɗin"ga abunda yafi nama daɗi bismillanku". Dariya sosai yaya Majid ya yi har sai da idonsa suka kawo ƙwalla kafin ya ce"lalle wannan tsohuwar anya kin kuwa san daɗin nama?, mussamman kika sama gashin shago ai sai kin manta da wani abu wai shi zogale in gaya miki gaskiya".


Harara ta watsa masa kafin ta ce"ai kuwa ni nasan daɗin nama tunda har na sunanka ni nan na ci shi". Izuwa yanzu har Abdul-aziz da Farouk sai da suka murmusa Farouk ya soma faɗin"Hajiya gaskiya fa nama na daban ne kowanne dai da matsayinsa".


"Har kaima sheƙiyancin zaka yi min kenan?".
Cikin dariya ya ce"a'a akwai na bambamce miki su ne".
A karon farko tun bayan shigowar su sashin da ya yi magana kenan ya furta"mun gode Hajiya sannu da ƙoƙari kamar kin san na daɗe ban ci zogale ba".


"Yauwa ɗan nan kai dai Allah ya taro albarka ya lafka maka a kai". Tuntsirewa gabaɗaya suka yi da dariya banda Saif ɗin da ya yi fuska ya jawo ruwan da ta ajiye tare da kwanon zogalen ya wanke hannunsa ya fara ci yana jin su suna hiran su ko sau ɗaya bai tsoma baki ba. Sai da ya cinye zogalen tas ya wanke hannunsa yana hamdala ga ubangiji, Hajiya Babba ta kallo shi tare da faɗin"gaskiya na yarda kana som zogale da yawa, da zanga matarka da na bata satan amsa akan a duk sanda ta yi maka wani abun to kawai ta yi maka kwaɗon zogale". Taƙaitaccen murmushi ya saka ya na rusunar da kansa ƙasa, Abdul-aziz da yake sakin dariya babu ƙauƙatawa ya ce"to ai kuwa ba ki canka dai-dai ba domin wannan ƙaton tuzuru ne zaune a gabanki ko tsayayya bai dashi balle zancen aure, dama ni kika gama wataƙil ki da ce".


"Haba dai? to ai shi aure lokaci in lokaci ya yi dole zai yi shi ko yana so ko baya so, amma dai ya kamata a nema".


Jinjina kai Abdul-aziz ya yi"lokaci ne kam wataƙil in an muyi tafiyar cikin sa'a ma lokacin ne ya yi".
Sosai suka ci gaba da hira da Hajiya baba kafin suka shigo sashin mu bisa jagorancin yaya Majid domin su gaida iyayenmu mata


Muna zaune a tsakar gidan bisa tabarma da Abasiyya da bata daɗe da zuwa ba, ƴarta ta biyu da ake ƙira da Nabila ina ware mata kintson kanta jifa-jifa muke maidawa juna zance domin tun zuwan ta auren su Salma na fahimci wasu tarin sauye-sauyen ɗabi'a daga gare ta, sai wani jin ƙamshi take yi da kallon gani-gani ga kowa, gefe guda kuwa su Daada suna zazzaune. Muka jiyo sallama a tare muka zuba na jiyamun mu a hanyar shigowa sashin tare da kafe mutanen da suke shigowa wani bayan wani da kallo.


Gyaran murya yaya Majid ya yi da shi ya fara shigowa yana faɗin"ku gyara ga baƙi zasu shigo". Ɗan-kwalina na ware na lulluɓa daga kaina zuwa kafaɗata tabarman da muke zaune tare da Abasiyya suka zauna cikin ladabi duk suka gaishe da matan sannan mu yara muka haɗe baki muka gaishe su a tare suka amsa mana.


Gabana yana dukan uku-uku na gaishe su raina cike da mamakin wannan zuwan nasun ma a karo na biyu cikin gidan mu, na jefawa kaina tambaya ko sune baƙin da yaya Majid yake ta tsimayi tun farar safiya?, ban kai ga cimma tambayoyin ba muryar Umma da suka dirarwa na'uran tantance mini sautika ya katse mini hanzari.


"Yaya mai jiki fa?".


Abdul-aziz ya amsa da"jiki alhamdulillah da sauƙi sosai".
"Masha Allah, Allah ya ƙara sauƙi". Amin suka amsa dashi a tare suka yi musu sallama har sun miƙe ɗayan da ban sunansa ba ya sunkuyo ya amshi Nabila daga hannuna yana mata wasa suka fice tare da ita, sallama suka shiga suka yiwa Hajiya Babba dasu Abba gabaɗaya suka fito inda suka yo parking motar.


Gaba Abdul-aziz da Farouk da yake ta faman yabon Nabila da faɗin ta burge shi suka yi, riƙo hannun yaya Majid Saif ya yj suka shiga cikin motan suka zauna a kujeran baya suna fuskantan juna Saif ɗin ya fara faɗin"wani magana nake son muyi da kai".


"Ina jinka menene?".


Dogon numfashi yaja ya fesar kana ya ce"ƙanwarka Zakiyya tun a ganin farko da nayi mata na yaba da hankali da nutsuwarta, bayan mun zo gidanku kuma na ƙara tabbatar da tarbiya irin na gidanku wannan dalilin ya sanya min kwaɗayin son haɗa iri da ku. Munyi magana da mahaifiya da kuma makusanta na kuma duk na sama goyan bayan su na fara yin maganan da kai domin naji ko anyi mata miji domin nema cikin nema haramun ne".


Tunda ya fara zancen yaya Majid ya gaza ɗauke idonsa daga kansa wani irin farin-ciki na mussamman ne ya mamaye masa dukkan ruhinsa, jin furcin Saif ɗin na ƙarshe godiya ya shiga yi ga ubangijin da ya sanya komai a tsari kuma daki-daki mai ɗauke da lokaci, tunin ya ji wani ruwa ya wadaci kurmin idaniyansa ya ce"ba ayi wa Zakiyya miji ba hasalima babu wanda take tsayiwa dashi".


Ɓoyayyan ajiyar zuciya Saif ya saka"alhamdulillah na gode Allah ina son maganan ya isa gasu Abba, don in so samu ne ina son a tsayar da magana kafin mun bar garin nan zuwa nan da kwana biyu na sama iznin zance da ita daga manya".


"In sha Allah zanyi wa su Abba maganan sannan zasu so zama da kai domin jin wasu bayanai daga gare ka, da zai taimaka musu waje gudanar da bincike mun gode da wannna karamcin".
Guntun murmushi ya yi"ni ne da godiya duk yanda ake ciki sai muyi magana a waya, zamu wuce masauƙin mu hotel". Musabaha suka yi da juna yaya Majid ya ɓalle murfin motar ya fice sai da suka yi sallama da su Abdul-aziz da Farouk ya amshi Nabila daga hannunsa tare da damƙa mata dubu biyu a hannu ta sayi alewa.


Mazaunin driver Abdul-aziz ya shiga Farouk ya zauna a kujeran maj zaman banza, waigowa Abdul-aziz ɗin ga yi yana duban sa da ya jinginar da kansa jikin kujeran ya lumshe idanunsa ya furta"yaya dai what's up ya kuka yi dashi?".


Shuru ya yi masa ba tare da ya tanka masa ba, sai da ya cire rai da zai amsa ya fara ƙoƙarin tada motar ya ji ya soma cewa"we're lucky ba'a yi mata miji ba". A tare suka sauƙe ajiyar zuciya mai nauyi cike da farin-cikin jin wannan zancen, daga nan hotel ɗin gollaka dake cikin garin potiskum suka nufa domin a can zasu sauƙa har zuwa sanda zasu tafi.
Rasa inda zai sanya kansa don murna yaya Majid ya yi, bai sama zama dasu Abba ba sai bayan sallan magrib tsaf ya zazzage musu komai yanda suka yi da Saif ɗin. Dukkanin su shuru suka yi na wucen gadi sai daga bisa Baba ƙarami ya furta"alhamdulillah! alhamdulillah! alhamdulillah! tabbas komai lokaci ne kuma duk abinda bawa ya sanya haƙuri a cikin sa haƙiƙa wataran zai ci gajiyarsa har ya sha romon sa, nayi matuƙar farin-cikin jin cewar yau wani ya zo mana da buƙatar son auren Zakiyya babu abinda zamu ce sai dai godiya ga Allah".


"Gaskiya kam sai dai mu godewa Allah zamu zauna da Hajiya Babba da kuma Amina mu tattauna maganan".


Furcin Abba kenan da ya zamto abu na ƙarshe da suka tattauna a zaman da suka yi, washe gari bayan sallan asubahi Abba ya aiko ƙiran Umma lokaci kowa yana farke an iddar da salla ba'a koma ɗakuna ba da kallo aka rakata sanda take ficewa kafin Umman Balkisu ta saki wani shewa tana miƙewa ta furta"ko menene in ya yi tsami ma jiyo warin sa". Tana dasa aya ta shige ɗakinta ido muka haɗa da Anty Zakiyya take zaune kusa dani sannan muka saki ajiyan zuciya a tare kowa da abinda yake tinanin cikin ransa.


Har Hajiya Babba, Goggo Suwaiba da Goggo Jummai da kuma yaya Majid ta iske a falon bayan su Abba, sai ta zauna kafin Baba ya yi musu bayanin komai don hatta Hajiya Babba sai yanzun take jin labarin.


"Wannan dalilin shi ya sanya muka taru a nan, ya nuna yana buƙatar aurenta tare da neman iznin fara zance da ita daga gare mu Hajiya hukuncinki shine abunda duk zamu tsaya a kai".


Sai da tayi godiya ga ubangiji kana ta furta"babu abinda zan ce ga Allah sai godiya da ya nuna min wannan ranar ina cikin rayayyu kuma cikin ƙoshin lafiya, tabbas tun zuwan su nan na farko na yaba da hankalin yaron sai dai hakan bashi zai hana ayi bincike a kansa ba kafin ya fara tsayiwa da ita".


"Haka ne Majid sai ka sanar dashi yazo muna son ganin sa yau".


Cike da girmama yaya Majid ya amsa da"to in sha Alla...". Bai ƙarisa ba sakamakon sheshsheƙar kukan Umma da ya tilasta mishi haɗiye ragowar zancen dukkan su ido suka ƙura mata, kafin Goggo Suwaiba ta ce"ashsha haba Aminatu meye abin kuka kuma?, ai kamata ya yi ki ɗaga hannu ki godewa Allah da ya nuna miki wannan ranar".


Jinjina kanta kawai Umma tayi tare da sanya hannu ta share ragowar hawayen idanunta, ficewa Hajiya Babba tayi su goggo suna rufa mata da ɗaɗɗaya duk suka watsa ya rage daga ita sai Abba rarrashinta yake yi sosai cikin faɗin"kinga ikon Allah ko Aminatu?, shiyasa bawa kar ya yanke ƙauna daga rahamar Allah, yau wacce aka ɗebi shekaru ana yi mata gorin aure ita ce wani ya tako ƙafa da ƙafa don neman auren ta". Ajiyan zuciya kawai Umma ta sauka don ita kai tsaye ba zata iya fasalta abinda take ji cikin zuciyarta ba, da ta kasa rabewa tsakanin farin-ciki da mamaki wanne take yi.


MATAN AREWA

(Book two)


© Maimunah Tijjani Iyam


________________________________


Page 1⃣0⃣9⃣




Sai da safiya ta soma yi sannan muka koma ɗakin, har wannan lokacin Umma bata dawo sashin ba ɗakinta na soma share mata yayin da Anty Zakiyya ta shiga wanka saboda yau ce ranar da zasu koma nguru tare da goggo Suwaiba. Kamar wacce aka zarewa laka haka take sharar rurin da wayata da na yasar da ita bisa gadon ƙarfen Umma ya sa ni saurin sakin tsintsiyan hannuna na ɗauki wayar, haka nan kawai na tsinci kaina da sakin murmushi ganin Nazifa ce mai ƙiran. Sai da na zauna bakin gadon sannan na ɗaga ƙiran ko gaisawa bamu yi ta hau ni da masifar wai bani da kirki, dariya kawai nake yi ina bata haƙuri tana cijewa sai da na yi mata zancen yaya Amin kafin naji ta saki wani dariya mai ƙarfi tana haɗawa da faɗin"shikenan na haƙuri amma wallahi ki yarda Na'ima na fiki kirki, ya gida ya su Umma?".


"Na yarda ranki ya daɗe amarya kuma uwar gida a gidan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login