Showing 102001 words to 105000 words out of 171161 words

Chapter 35 - MATAN AREWA BOOK TWO COMPLETE PDF .txt

ban cire kaina ba wataƙil shine na ƙarshen da zasu gani a rayuwarsu sai dai wannan ilmin Allah ya bar wa kansa sanin sa babu wanda ya san gawan fari a cikin mu sai dai muyi fatan cikawa muna masu imani kuma akan turba mai kyau. Da yawan lecturer sun rufe lectures da zaran mun yin gwaji suke rufe lectures ɗin su sai kuma zuma bayan sallan da babu jimawa zamu fara jarabawa.


Duk zafin rana da azumin da muke tsaka dashi hakan bai hana da yawa daga cikin mu yin shirin matriculation ɗin mu ba da ya rage saura kwanaki biyar za muyi shi a yinin da zamu kai azumi ashirin da bakwai cas. Mu dai ƴan kallo muka zama domin ba ma ko wani shiri illa na tafiya gida a ranar da zaran an gama tsaf muka yi wankin mu tare da goge su kuma kimtsa su waje guda, cikin kwanakin nan sosai muka mayar da hankali ga ibadan da muka saka a gaba gadan-gadan babu kama hannun yaro.


Zo kuka murna a fuskokin mu sa'ilin da na ƙira gida nake shaida musu ranar da aka sayar a matsayin na rantsar damu da tabbatar damu a matsayin cikakkun ɗaliban jami'ar suka tabbatar mini da cewar zasu, haka nan ma yaya Amin ɗin Nazifa ya ce zai zo daga nan su koma gida tare kawun Nawwara ma ya bamu tabbacin ba za ayi babu shi ba.


Ranar alhamis ranar da ta kasance za'a yi taron namun da yawa basu runtsa ba a hostel sai hira ake ta yi ga kuma rabuwar da za'a yi a ranar sai kuma Allah ya kai mu bayan salla mun dawo. Tun faran safiya suka tashi muka gabatar da dukkan aiyukan mu muka yi girkin mu har rana wanda zai ishe mu har da ƴan gidan da zasu zo mana kayan mu kuwa sun daɗe a cikin jaka sai da muka gyare ɗakin mu tsaf muka fito. Dukkanin ƴan mass communication department uniform ɗin mu muka sanya maza da mata sannan muka ɗaura gown ɗin mu a sama muka nufi hall ɗin sai da aka ƙara jaddada mana yanda zamu gudanar da komai har yanda zamu shigo cikin tsari department by department sai da aka ƙara biya mana.


Ƙarfe tara da ƴan mintuna lokacin ana dab da farawa don sai ƙarfe goma za'a fara yaya Amin ya iso ya ƙira wayan Nazifa ta ɗaga ya shaida mata ya iso muka je muka same shi tare yake da wata matashiyar budurwan da ba zata wuce Nazifan ba da suka rungumi juna cike da murnar ganin junan su da suka yi.


"Anty Nazifa kinga wani kyaun da kika yi kuwa".


Ta faɗa tana bin ta da idanu murmushi Nazifan tayi kafin ta furta"Munira bana son zolaya wani kyau nayi kin dai faɗa ne don ki ji daɗin bakinki".


"Wallahi Anty Nazifa kin yi kyau don Allah yaya Amin ka ganta fa bata canja ba?".


Murmusawa ya yi yana gyara tsayiwar sa da ya yi jikin motarsa ya ce"wannan kuma tsakanin ku ne ba zan shiga anjima kaɗan ku bani kunya ba". Dariya duk muka saka muka gaishe shi ya amsa mana sannan budurwan ma ta gaishe mu Nazifa ta dafe kai haɗi da faɗin"oh sorry ban gabatar muku da ita ba ƙanwar yaya Amin ce Munira, Munira ga ƙawayena Na'ima da Nawwara".


Gaisawa muka ƙara yi cikin faran-faran dai-dai sa'ilin da wayata ta soma ruri ganin lambar yaya Majid ya bayyanar cikin screen ɗin wayar ya sanya ni saurin ɗagawa maimakon naji muryansa sai naji muryar Hajiya Babba nayo sololo a wajen ba tare da na ce komai ba har ta gama labarta mini cewar sun iso cikin makarantar gasu a bakin gate ban motsa daga inda nake ba.


Sai da Nawwara ta jefa mini tambayar lafiya? sannan ya fesar da numfashin mamakin da ya sarƙafe mini ruhi na jawo hannunta na ce"Nazy bari muje mu shigo da su yaya Majid sun iso". Kanta ta ɗaga mini muka wuce muka bar wajen muka nufi bakin gate ɗin ban gama gaskata abinda kunnuwa suka ji ye mini da na gandanta hakan da matsalar network ba sai da muka isa naga Hajiya Babba tsaye gam a zahiri a gabana ai ban san sanda na saki hannun Nawwara na ɗebi sauri naje na rungume ta ba ina hawayen farin-cikin da ba zan iya misalta shi ba a wannan lokacin. Ita ma rungume ni tayi sosai a jikinta tsawon wasu daƙiƙu sannan ta ɗago ni tana share mini hawayen fuskana sai a sannan na lura da Anty Zakiyya, Salma da Yaya Majid da suke tsaye suma a wajen Salma na jawo jikina kafin kuma na hankaɗe ta ina banka mata harara na ce"sai yau kika yi niyyan zuwa inda nake ke kuma?".


Murmushi ta saka kafin ta furta"afuwan ranki ya daɗe Allah ne bai yi ba yau da Allah ya nufa ai gani kin ganni ba zato ba tsammani".


"Kar kiyi mini wani zaƙin baki malama kin ci sa'a dai na yafe miki".


Dariya duk muka saka sannan muka haɗe baki wajen gaida Hajiya Babba, Anty Zakiyya da kuma yaya Majid duk suka amsa mana cikin sakin fuska. Hannuna riƙe cikin na Hajiya Babba muka ɗauki hanyar inda muka bar su Nazifa nan ɗim muka iske su yaya Majid da yaya Amin suka yi musaba sannan ya rusuna ya gaishe da Hajiya Babba da bakinta ya gaza rufuwa tunda ta gan shi haka nan ma ƙanwarsa Munira, duk muka gabatar da kowa ga kowa muka tsaya jiran kawun Nawwara da take ta doka masa ƙira yana cewar yana hanya motar su ce ta lalace ganin har an fara haɗuwa a bakin hall ɗin ya sanya mu ɗunguma wajen muma, ƙofar da baki zasu shiga daban yake haka nan ma wanda zamu shige daga cikinsa shima daban ne tun kafin mu shiga su Hajiya Babba suka shige tare dasu Salma da Munira yaya Majid da yaya Amin kuwa suka tsaya yi mana vidoe yayin da muke shigewa a jere department by department ko waɗanne da irin nasu salon shigan amma ba ƴan mass communication.


Haka nan ma wajen zama ko wani department da nasu sai da muka shiga muka zauna kafin Nawwara ta hango shigowar kawu Musa ta ɗaga masa hannu murmushi ya sakar mata kafin ya nema waje ya yi wa kansa mazauni.


Tasowar Mr Saif ya sanya ilahirin hall ɗin ɗaukar ƙara da ihu shi ya buɗe taron da addu'a sannan vice chancellor ya zo ya yi nashi jawabin da ƴan shaware-shawaren da ya bamu kafin lawyer ɗin da zai rantsar damu ya hau stage ɗin duk muka miƙe duk abinda yake rubuce a fefen dake hannun mu yake karantawa ya yi da muke maimaitawa hannunmu na hagu na sama sai da ya karance komai tsaf sannan muka zauna kafin yan aluta tawagar SUG suka soma yi suna gama wa aka ƙarfin sautin kiɗan da aka sanya ya cika hall ɗin bayan ficewar lectures ɗin.


Tunin masu kuzarin da baza jin azumin suka zage dukkan ƙarfin su suna riƙar rawa kamar ba gobe, sosai muka yi hoto da wasu ƴan department ɗin mu sannan muka haɗu muka yi a tare na kama kaina tare da rufe duk wata ƙofar da zai sanya wani namiji raɓo ni balle ya yi mini maganar banza tsakanin na dasu sai dai gaisawa ta mutunci wannan dalilin ya sanya cikin su babu wanda ya yi gigin nufa ta da nufin mu ɗau hoto kamar yanda suke ta yiwa sauran ƴan matan department ɗin nan mun.


Sai da muka fito daga hall ɗin muka sama gaisawa da kawu Musa da yake ta faɗin motar da ya hau ne ta lalace a hanya shiyasa bai iso da wuri ba. Gaisawa suka yi da yaya Majid da yaya Amin sannan Hajiya Babba duk muka haɗu aka ɗauke mu a hoto kafin aka yi mana ɗai-ɗai sai da muka yi muka gaji don kan mu da kuma ƙiran sallan zuhr ɗin da aka soma yi sannan muka tafi hostel yayin da su kawu Musa suka wuce masallaci.


Salla muka yi sannan muka yi kwanta muka sauya shiga kafin muka fito da jakkunan mu Salma da Munira ke ta santin ɗakunan hostel ɗin wai ya birge su, ɗaƙi ɗaya bayan ɗaya muke bi muna yin sallama kamar yanda kowa yake yi tare da roƙon yafiya sai kuma an dawo bayan salla.


Inda yaya Amin ya ajiye motar shi muka nufa muna jiran su fito daga masallaci kamar an ce ɗaga kan ki ina ɗagawa idanuna suka sauƙa akan su suna nufo inda muke tare suke da Mr Saif da kuma Malam Abdul-aziz wanda shima lecturer ne a department ɗin mu mamakin ganin su tare ya sanya ni sake baki ina bin su da idanu har suka ƙarisowa wajen. "Afuwa Hajiya mu bar ku kuna ta jira".


Furcin yaya Amin kenan da ya sanya Hajiya Babba washe baki har kunne"ba komai ɗan nan muma bamu jima da fitowa ba".
Da mamakina naga Mr Saif ɗin da Malam Abdul-aziz ɗin sun rusuna sun gaida Hajiya Babba kamar sun santa ta amsa musu wani sashin zuciyana tana ayyana mini wataƙil shekarunta ne ya sanya su bata wannan girman. Maganan da yaya Majid ya soma ya dawo da ni cikin hayyacina daga tinanin da nake yi.


"Zakiyya kin gane wannan kuwa?".


Ya ƙare zancen yana mata nuni da Mr Saif ɗin kanta ta jijjiga masa alamar a'a da hakan ya sanya shi sakin ɗan murmushi kafin ya ce"shine wanda ya watsa miki ruwan alwala kwanakin baya da muka zo tare da Goggo Suwaiba har ya kai mu tasha a motarsa".
Dafe kai tayi tare da yin ƙasa da kanta tana faɗin"wallahi ban gane shi bane ina wuni".


"Lafiya ya ibada".


Ya amsa dashi ta mayar masa da kalmar alhamdulillah da hakan ya bashi damar ɗaura da"a masallaci muka haɗu dasu da suke ce tare kuke na ce bari nazo na ƙara bada haƙuri".


"La ba komai wallahi ni kam ma na daɗe da mancewa". Kansa ya jinjina mata kafin ya kai duban sa gare mu cikin rawar murya ni dasu Nawwara duk muka haɗe baki muka gaida shi kamar ba zai amsa ba sai kuma ya amsa haka nan ma Malam Abdul-aziz ɗin.


Sallama suka yi wa Hajiya Babba zasu tafi yaya Majid ya dakatar dasu da faɗin"dan Allah ko zan iya samu lambar wayanka waɗannan ƙannena kuma ɗalibai ne a makarantar nan basu san kowa zamu daɗi sosai idan ba zamu takura maka ba ka dunga sa mana ido a kan su". Sai da ya yi ɗan jim kafin ya ce"ba komai in sha Allah zan yi hakan". Daga haka ya fara karantowa yaya Majid ɗin lambarsa a take a wajen ya ƙira ya shiga wayarsa sannan yaya Majid ya kuma tambayarsa sunan da zai yi saving dashi.


"SAIFUDDEEN".


Ya furta cikin sanyin murya kafin yaya Majid ya gabatar masa da sunayen mu gabaɗaga har da Anty Zakiyya kafin suka yi musabaha suka juya, kuka muke yi bil haƙƙi sanda zamu rabu da Nawwara da Nazifa yaya Amin ne ya kawo mu tasha a motarsa ya sauƙe mu sannan duk muka hau na garuruwan mu mu da Kawu Musa da Nawwara.


-07038908713-


MATAN AREWA


(Book two)


© Maimunah Tijjani Iyam


_________________________________


Page 9⃣2⃣


Tunda muka shiga motar potiskum garina na haihuwa nake sauƙe ɓoyayyen ajiyar zuciya kalaman na yaya Majid da ya yi su ga Mr Saif akan ya dunga kula damu a jami'ar suna ƙara dakan kwanyata. Ban toka komai ba cikin hiran da su Hajiya Babba suke yi a cikin motar da muka ɗauki shatan ta gabaɗaya saboda direwan da Hajiya Babba tayi akan ba zata zauna a takure ko kuma a cika mota numfashinta yana sarƙewa ba ala dole muka ɗauki motar gabaɗaya, suke yi ban ce ko kanzil ba har muka yi nisa sosai sai da muka shiga cikin damaturu sannan Salma dake zaune kusa na lokacin duk sunyi laushi sun kishingiɗe suna bacci ta taɓo ni tare da ɗage mini ido ɗaya alamar lafiya kuwa.


Sai da na sauƙe ƙatuwar numfashin da ban san dalilin yin sa ba kafin na ce da ita a gajarce" me kika gani ke kuma".


"Tun ɗazu ana hira kinyi shuru".


Murmushi kawai nayi mata ban ƙara cewa da ita komai ba sai ma karɓan wayar yaya Majid da nayi ina kallon hotuna da vidoes ɗin da muka yi ɗazu muna isowa cikin garin potiskum ƙarfe biya da rabi saura mintuna ƙalilan lumshe idanuna nayi ina zuƙar iskan garin da soyayyarsa yake ƙara yin dabaibaiyi a cikin raina ji nake yi kamar napep ɗin da muka hau bata sauri ban ƙi ba ya sauƙe ni na zuga a guje naje gida na iske Ummata da raguwar ahalin gidan.


Muna sauƙe da Baba, Abba da kuma Baba ƙarami muka fara cin karo dasu suna fitowa daga cikin gidan da alama masallaci zasu tafi, da sauri na isa gare su na rusuna na gaishe su bakina kamar zai yage suma da maɗaukakiyar murna shimfiɗe akan fuskokinsu suke amsa gaisuwar tawan tare da jera mini tambayoyin yaya makarantar da kuma hanya ina amsawa da kalmar alhamdulillah.


"Ki shiga gida ki huta kafin a sha ruwa idan mun dawo daga masallaci zamu gama gaisawan".


Furcin Baba kenan da ya sa ni ɗaga masa kaina tare da basu hanya suka wuce mu kuma muka shige cikin gidan sashin mu na nufa da ƙishiriwan ganin fuskar Ummata, da ita na fara cin karo tana dama kunu a gindin murha na faɗa kanta tare da kanainayeta ina faɗin"Umma Umma nayi kewar ki sosai wallahi".


Sai da ta ɗago ni kafin ta ce"mu ma nan munyi kewar ki Na'ima". Sai da na saki murmushi kana na gaishe ta amsa mini ina mata sannu da aiki duk yanda naso ta kawo kunun na ƙarishe dama mata ƙi yawa tayi ta ce naje na huta har na miƙe sannan Salma da Anty Zakiyya da suke shige sashin Hajiya Babba da muka shiga suka iso sashin namun. Yaran gidan mu ƙananu suka yi mini ca a kai kamar zasu cinye ni ko kuma yau suka fara ganina naji daɗin ganin su sosai cak raha, annuri, walwala, da fara'an dake mamaye da fuskana suka gushe sa'ilin da ɗanyen furcin da Umman su Anty Kubra ta lailayo ta furzo mini da suka zamto ababaɗen farko na akasin farin-ciki da suka sauƙa a kunnuwana.


"Dalla ku kuma meye hakan? kun wani mamaye ta kamar zaku cinye ta tunda ta sanya ƙafa ta fice daga cikin gidan nan ta taɓa ƙiran waya mussamman ta ce a baku, don kune jarabbu daga ganin ta jikinku ya ɗauki mazari".


Kaina kawai na duƙar ƙasa ina miƙewa daga durƙuson da nayi gaban su hannuna riƙe da na Nuraini da duk hararan da Umman nasun take antayo masa bai yi tasiri a gare shi ya sake mini hannun da ya rige gam ba, da ido Umman mu tayi mini alama akan cewar na shige ɗaki ban ce komai illa buɗe covern wayata da nayi na zaro naira ɗari biyar na ba wa Ikilima na ce taje shagon dake kusa damu ta sayo musu biscuit su raba.


"Haba ke kuwa Zainabu ai dai kya ɗaga mata ƙafa yanzu nan fa sauƙar ta". Furcin Daada kenan da ya sa ni danne duk abinda nake ji a cikin raina na rusuna na gaishe ta ta amsa mini cike da kulawa sannan nayi raguwar matan duk na gaida su babu yabo babu fallasa suke amsa gaisuwar tawan Hajiya ce kawai ban ganta a tsakar gidan ba don haka na bi ta har ɗaki na iske ta tana kishindige muka gaisa kafin na fito na shige ɗakin Umma na cire kayana na watso ruwa ina fitowa daga banɗakin ladanin masallacin dake fuskantar gidan mu yana ƙwala ƙiran salla.


Tunin aka fara buɗa baki manya da ƙanana kowa yana ɗebar ruwan tsirkin da aka haɗa har ɗakin Salma ta shigo mini da ruwa mai sanyin gaske na sha ina sakin hamdala tabbas na ƙara yarda da cewar ruwa shi ya san inda rai yake. Tare muka yi buɗa baki da ita a ɗakin Umma muna ta hiran mu har aka yi ƙiran sallan isha'i muka yi salla muka wuce sashin Hajiya Babba muka yi mata sannu da shan ruwa kana muka yada zango a sashin su Abba muka ɗaura da hiran mu daga inda muka tsaya.


Ɗaya bayan ɗaya matan gidan suke shigowa yi wa su Abba sannu da shan ruwa ban sani ba ko ganin mu a wajen ne ya sanya su suma suka zauna oho, Umma da Daada tare suka shiga suna zama yaya Majid ma ya shigo saɓe da Nurain a kafaɗarsa da sam baya gajiya da yaron duk da irin tashin darajan da Umman su Anty Kubra take yi da fitowa ƙiri da muzo ta nuna bata son tarayyar su hakan bai sanya shi janye jikinsa ba daga gare shi.
Yana ganina ya dire daga jikin yaya Majid ya danno gudu ya faɗa kan cinyata Salma dake kusa na ta zunguri kansa haɗi da cewa"kai dai kam ka shiga uku Nurain sam baka san ka girma ba dube ka fa ƙaro da kai amma har yanzu hankalinka na yara".


Rungumo shi jikina nayi ina haɗin"a'a malama kar ki sanya mishi ido ɗan yaron nan ina batun wani girman da kike ta zuzurawa abinda bai fi a saɓa shi a baya a goye shi da zani ba". Kusan kowa sai dai zancen nawan ya sanya shi murmusawa Abba ya katse mu ta hanyar cewa"Na'ima bamu samu mun zauna ba ya makarantan nakun kuma ya karatun kunyi taro lafiya?". Bakina har kunne na gyara zama na ce"makaranta lafiya ƙalau Abba karatu ma alhamdulillah mun gode Allah".


"Masha Allah haka ake so in ce kuna mayar da hankali sosai ko". Kaina na jinjina masa cike da tabbatarwa kafin Hajiya ta soma faɗin"da azumin nan kuwa yaya kuke yi?".


"Wallahi Hajiya haka nan muke yi ga karatun kuma ga azumin ciki babu wanda za'a fasa".


"Gaskiya kam Allah rai ya mora". Tsiraru ne kaɗai suka taya ni amsa addu'ar ta Hajiya da kalmar amin hiran mu muke yi sosai na yaushe gamo suna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login