Showing 108001 words to 111000 words out of 171161 words

Chapter 37 - MATAN AREWA BOOK TWO COMPLETE PDF .txt

ƙanin Abban su Khalil ya dage akan sai ƴar boko zai aura. Haka nan ya je ya auro wacce take juya shi kamar waina a cikin tanda take jin cewar dai-dai suke dashi tunda boko ne ya yi ita ma ya yi bata ganin kowa da gashi auran bai yi wani nisan zangon ba yazo ƙarshe to meye amfanin wannan abun?".


Sosai tambayar ta da ki birnin zuciyata da ba fara kaskasata kashi-kashi da nufin nemo amsarta, shin da gaske ne hashashen mafi yawan mazan wannan zamanin cewar duk wata macen da tayi zurfi a karatun boko ba iya juya ta?, ko kuma ba'a iya tanƙwarata ko kuma akwai shashi faɗi ne irin na al'ummata?. A take zuciyata ta bani amsa da cewar ke ce za ki zamto misalin da za ki karya wannan igiyar zaton idan har ba ki bari ilminki na boko ya danne na addininki ba.
Dirar mikiyan da amon muryan Anty Hajara suka yi wa ƙofofin kunnuwana suka katse mini tufka da warwaran zancen zucin da nake saƙawa. Cikin sanyin murya ta soma faɗin"hakan ma tana iya faruwa amma ai ba duka aka taru aka zama ɗaya ba mata nawa ne da basu yi bokon ba amma tsiyar da suka shukawa cikin gidajen auransu ko wacce ta ga ƙarshen biro sai haka. Na yarda ilmin boko baya taɓa canja mace ko mai nutsun da tayi a cikinsa sai dai ina zani ce ta tarda muje, daman can tarbiya bata ishe ta ba kuma bata da hali da ɗabi'u na ƙwarai to wannan kam don an ce boko ya sauya ta ba zanyi mamaki ba, amma wallahi ga wacce ta fito daga gidan tarbiya da wuya a sama hakan a gare ta". Taɓe baki Anty Hasina ta kuma yi a karo na biyu.


"Kuma fa haka ne zancen ki Maman Sufya wallahi akwai wani gida a nan kusa dani, duk ƴaƴansa maza ne ɗaya ce mace kuma ita kaɗai tayi karatu. Yanzu da girma ya kama shi ita take ɗaukar duk ɗawainiyyar gidan nan in kinga abin sai son barka wallahi, tun daga lokacin na kwaɗaitu da su Khairat su ma yi karatun zamanin nan".


Furcin bakin Anty Maimuna kenan da ya sanya Hajiya Babba sakin gajeren murmushi kafin ta furta"Allah dai ya sa mu da ce". Duk suka amsa da amin a bayyane ban da ni da na amsa a cikin zuciyata zantukan na Anty Hasina nata yi mini yawo a kaina, duk zantukan da suka ɗaura dashi bana fahimtar abinda suke cewa wani lokacin sai Balkisu ta taɓo ni nake ɗan fizgan maganar.
Ƙiran sallan asr ya tilasta mana tashi muka ɗauro alwala muka gabatar da salla, sashin mu na dawo saboda Ikilima da tazo ta sanar dani cewar wasu dangin Umma sun zo daga geidam na je mu gaisa. Sosai muka gaisa dasu cikin sakin fuska suna ta tambayata makaranta ina amsa musu da alhamdulillah, tare da tambayar yaushe zan je musu nayi musu alƙawarin zuwa idan mun samu hutun ƙarshen zangon mun ɗan taɓa hira dasu kafin na fita na basu waje. Tsakar gidan har yanzu cike da jama'a rarraba ido na soma yi ko zan ga Hajiya amma ban ganta ba hakan ya sa ni shigewa ɗakinta tana kishingiɗe akan gadonta na ƙarfe na iske ta tana ɗan gyangyaɗi a hankali na zauna kusa da ƙafafunta ina ɗan bubbugawa kaɗan kaɗan tare da ƙiran sunanta.


Da sunan Allah ta buɗe idanunta tare da tashi zaune daga kwanciyan da tayi tana fuskanto ni ta ce"a'a Na'ima ke ce?".
"Ni ce Hajiya ban gan ki a waje ba ne na ce bari na shigo na duba". Sai da ta murmusa alamar taji daɗin shigowan tawan kana ta ce"wallahi gabaɗaya jikina ne ya yi min nauyi ga hayaniya shine na ce bari na shigo ciki na kwanta". Kai na jinjina ta cigaba da cewa"daman kuwa ina son muyi magana dake kafin ki koma makaranta, yaushe za ki koma ne?".


"Ranar lahadi in sha Allah".


"Magana ce game da tsohon mijinki Yusuf da kuma Binta". Dam-dam ƙirjina ya bada sauti mai ƙarfi jin sunayen da ta ambata sunkuyar da kaina ƙasa nayi ban ce komai har ta cigaba da faɗin"Yusuf dai ya bar garin nan tun bayan tafiyarki makaranta babu jimawa bama tare da sanin kowa nashi ba, ga Husna ma naji wai bikinta bayan sallan nan da sati biyu zata auri wani yaro nan cikin unguwansu ɗan kumbon sosa ya ɗauke musu ɗawainiyyar komai da komai, sai dai shaidar da aka bayar a kansa ya nuna ba mutumin kirki bane amma abin hannunsa ya rufewa iyayenta idanu har an bashi ita aure. Wataƙil alhakin ki ne ya soma bibiyar ta tun daga yanzu abin ya juye izuwa kan ƴata ga kuma ƴan-uwanta da yanzu suka fara bijirewa umarninta".
Ƙatuwar ajiyar zuciya na sauƙe"Allah dai ya kyauta ya kuma rufa asiri, amma nikam ban so ba dududu Husnan nawa take?, yarinyar firamari kawai ta gama za'a auran da ita".
"Amin kam aure kam har an sanya lokaci". Kaina na jinjina ina takaicin labarin da kuma juya zancen barin garin yaya Yusuf ɗin duk da ba sau ɗaya ba nasha ganin sa amma ban taɓa gaskatawa cewa shi ɗin bane, mun taɓa hira da ita har sai izuwa lokacin da su Balkisu zasu tafi sannan na fito muka yi sallama duk cikin su babu wacce ta kwana domin faɗin su Abba ne kowacce ta koma ɗakin mijinta.




MATAN AREWA


(Book two)


© Maimunah Tijjani Iyam


__________________________________________


Page 9⃣5⃣


Kafin na koma sai da naje gidajen su Anty Hajara gabaɗayan su har da su Abasiyya da Balkisu. Mun ƙarishe zancen mu da Salma akan aurenta da Baban su Zaliha a yanda take labarta mini cikin zubda hawaye cewar Ummanta ta ƙi sanar da ita ƙwaƙwƙwaran dalilinta guda ɗaya da take son tirsasata auran wanda babu shi a zuciyarta, dukkan lallashin nayi maka tare da nusar da ita riban dake tattare ga biyayya ga uwa. Domin babu wani abun da ɗa zai yi mata ya biya ta kwatankwacin irin ɗawainiyyar da tayi dashi, tun daga ɗaukar ciki har izuwa nishin naƙuda da kuma shayarwa.


Ranar ukun salla muka je geidam wajen dangin Umma wuni muka yi zum, kafin muka dawo potiskum washe gari Goggo Suwaiba da Anty Zakiyya suka koma. Ranar lahadi kuwa na koma makaranta tare da ɗunbin sanyawan albarkan iyayena uku da bani da kamar su balle waɗanda suka fi su, Abba, Baba da kuma Baba ƙarami. Har tasha yaya Majid da Nurain suka yi na hau mota kafin nan mun tattauna dashi sosai ban ɓoye masa komai ba akan gizon da yaya Yusuf yake yi mini a makaranta tun ina ɗauka abin wasa har na fara gaskatawa cewar haƙiƙa shi ɗin ne ba wai gizo ba, gargaɗi ya yi mini mai ratsa kwakwalwa akan kar na kuskura koda da wasa na kula shi ko kuma na bashi fuskar da zai tunkaro ni da wani zancen, makaranta ce dai bamu da ikon hana shi zuwa cikinta tunda waje ne da kazo nazo ya ƙara da zancen da ya gusar mini da annurin fuska. Wai zai ƙira Mr Saif ya shaida masa komai tare da roƙonsa akan ya sanya idanu akan mu, Nawwara na tarar har ta iso sai zuwa yamma yaya Amin ya kawo Nazifa.


Zaune yake gaban Anty Binta da ta tisa shi gaba da wasu zantukan da baya fahimtar gaban su balle bayan su, kansa ya sadda ƙasa yana murza yatsun hannun a hankali. Sai da ta sauƙe numfashi a karo na ba adadi kafin ta ɗaura da faɗin"wannan shine hukuncin da na yanke Yusuf kuma ba shawara ko kuma ra'ayinka nake son ji ba, wannan umarni ne daga gare ni da nake son ka tabbatar da shi a aikace in dai ni Binta na isa da kai da rayuwarka ina son ka auri Aisha nan da sati biyu a haɗa da na Husna".
Matse yatsun hannayensa da yake murzawa ya yi da ƙarfi har sai da ya bada wani sautin ɗas, tare da cije leɓɓan ji ya yi zuciyarsa tana yi masa wani zafi, raɗaɗi da kuma ɗaci da ƙyar yake jawo numfashinsa da yake fizga kafin ya sama zarafin faɗin"Anty bana son wannan kalmar da kike sanya ta cikin dukkan laffuzanki na ce idan kin isa damu, sanin kanki ne ke ɗin kin isa da mu tunda da kai da kaya ai duk mallakan wuya ne. Sannan ina mai ba ki haƙuri game da wannan auren da kike so nayi bana jin cewar soyayyar wata ƴa mace a yanzun sai iya samun matsuguni a cikin ƙirjina balle har na fara tinanin zaman aure da tara iyali da wata. Ina mai ba ki haƙuri da tausasan laffuza kiyi haƙuri ba zan iya aure ba yanzu mussamman wai Aisha yarinyar da sam ɗabi'unta basu yi dai-dai da irin ɗabi'un da nake da buƙata daga mace ba".


Salati ta rafka tare da sallallami haɗi da riƙe haɓarta tana bin sa da wani irin kallon da yafi kama da na son tabbatar da lafiyar kwakwalwarsa.
"Ba shakka Yusuf, Yusuf kai kake kallon tsabar idanuna kana faɗa min cewar babu wani matsugunin da soyayyar wata ƴa mace zai sama gurbi a cikin zuciyarka?. Yusuf anya an barka haka banza kuwa?, anya kana cikin hayyacinka kuwa?. To wallahi ka ma rubuta a ajiye auranka da Aisha tabbatacce ne matuƙar ina numfashi a bayan ƙasa billahillazi sai ka aure ta, gwara ma tun wuri ka yakice duk wani abunda da yake ranka ka goge soyayyar ko wacece daga ranka domin Aisha ce keda wannan gurbi da matsayin kuma ita zata baza nata sharafin a birnin zuciyarka. Ba zaka koma wannan makarantar ba sai an ɗaura aurenka da Aisha in yaso ka barta a nan kana zuwa lokaci zuwa lokaci".


Ji ya yi ƙirjinsa ya yi masa nauyi sosai taune leɓɓansa kawai ya cigaba da yi yana ɗan lumshe idanunsa a hankali yana buɗewa. Ji ya yi ba zai iya cigaba da sauraran raguwar zantukan natan ba kamar yanda tsananin biyayya da kallon madadin uwa da uban da yake yi mata a gare shi ba zai iya tashi ya barta zaune a wajen ya tafi ba tare da ta gama zancenta ba, tabbas bakinsa bai yi kuskuren bayyano da aihinin abinda ke taskace cikin tsokar zuciyarsa ba. Ya riga da ya gama soyayya tare da mallakawa mace ɗaya dukkan makullan ƙofofin shiga zuciyarsa ba kowa bace face Na'iman da zuciyarsa ke raya masa cewar ba zai ƙara mallakarta ta zama nashi ba.


Bai kuma cewa da ita komai ba har ta ƙare zancen tanan, da faɗin ya bada kuɗin da za'a haɗa mata lefe da sauran abubuwan da ango yake ba wa amarya yayin biki. Bai yi musu ba ya amsa ta akan zai aiko idan ya fita ya ciro kuɗin a POS daga haka ya fice bayan ta gama cewa ya tabbatar yaje gidan su aminiyarta Hajiya Kulun da take mahaifiyar Aisha su gana tsakanin yau ko gobe.
Tunda ya fito daga cikin gidan yake tafiya ba tare da ya zan inda yake zara idanunsa ba tunani kawai yake yi yanda zai fara gina rayuwar aure da wata macen bayan Na'iman da ya mallaka mata dukkan kansa da gindina rayuwarsa gare ta. Sai dai ƙaddarar da ta riga fata ta jijjige dukkan gini da foundation ɗin da ya yi.
Rurin da wayarsa take yi bai hana shi dakatawa daga miƙe layin da yake yi ba, sai ji ihun da yaji an hurma ne ya sanya hankalinsa da ya fara nisan zango da barin gangar jikinsa dawowa gare shi cikin hanzari tare da kai duban sa ga mutanen.


Ture shi da aka yi gefe guda ya sanya shi yin tangal-tangal zai faɗi da ƙyar ya tsaya akan ƙafafunsa tana bin mutanen da kallon son ƙarin bayanin abin ke faru.
"Mahaukacin ina ne kai? kana tafiya a tsakiyar kwalta ana maka horn kana ji kurma ne kai ko kuma gajiya kayi da rayuwar duniyar?. Kake son jaza min masifa da bala'i wawa kawai".


Kallonsa kawai yake yi amma sam ya gaza cewa komai har ya gama maganar yana tsaye akan ƙafafunsa, bai ce komai ba har mutanen suka fara watsewa ya cigaba da tafiyarsa. A gefen wani masallaci ya zauna yana maida wahalallen numfashi sai da ya yi sallan zuhr da asr sannan ya wuce gida, Maman Hanan da Mahmud ya iske a gidan daga gaisuwa bai kuma cewa da ita komai ba illa ɗakin da ya shiga ya ɗauko ATM ɗinsa ya ba wa Mahmud ya ce yaje ya sama Anty Binta ta faɗi kuɗaɗen abubuwan da ake buƙata ya cira ya kai mata.
Duk yanda Yaya Auwal, Maman Hanan da kuma Mahmud suka so ganaaa dashi sam ya ƙi basu wannan damar tunda ya shiga ɗaki ya ture ƙofar bai fito ba sai da aka yi ƙiran sallan magrib, sai da ya jira aka yi isha'i sannan ya dawo ya yi kwanciyarsa. Washe gari da yammaci ya sanya Mahmud raka shi gidan Hajiya Kulu saboda alƙawarin zuwan da ya yi wa Anty Binta, tarba aka yi musu na girma da mutuntawa sosai ya ba wa Hajiya Kulun girmanta don ko kaɗan raina na gaba dashi ba zai kasance ɗaya daga cikin ɗabi'unsa, sun daɗe suna zaman jiran zuwan Aishan da aka labarta musu cewa ta shiga maƙota sai da suka ƙosa sannan ta shigo falon kamar an jefo ta.


Kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauke kansa, domin tun a kallon farko da ya yi mata ta gama faɗuwa a jarabawar don ko kaɗan bai hangi nutsuwa a tattare da ita ba balle kamun kai a matsayinta na ɗiya mace bahaushiya. Kansa yana gefe ya amsa gaisuwar da ta yi masa yana jin wani ɗacin yana gaurayewa da miyau ɗin bakinsa da ƙyar yake jan numfashi saboda ƙarnin man bleaching ɗin da ya gama ƙona mata fata yake fitarwa da ya ɗume ɗakin. Ji ya yi gabaɗaya ya ƙagu da ya bar gidan hakan ya tilasta mata ɗan ɗago kansa haɗi da faɗin"da fatan an yi miki bayanin dalilin zuwana ko?".


"Ƙwarai kuwa ranka ya daɗe".


Jinjina kansa ya yi"ok bana tinanin zan ƙara zuwa har izuwa lokacin da za'a ɗaura auren don haka ki rubuta abinda zaku iya buƙata yayin bikin ke da ƙawayenki". Sai da ta gyara zama tana fari da idanu kafin ta shiga lissafi cikin yauƙi kamar haka"da farko dai kuɗin entertainment da zamu yi abinci da abin sha, sai kuma ƙauyawa, party da kuma gangakura da zamu yi kuma duk suna buƙata kuɗi. Ga kuma kuɗim gyaran jiki, kitso da kuma ƙunshi ni da ƙawayena". Tun da ta fara zancen yake bin gefen da take da kallon ƙasan ido har ta kai aya iska ya fesar daga bakinsa tare da shafan sumarsa ya ce"kinga ki nutsu duk wannan abubuwan da kika lissafo babu wanda za'a yi, sannan naga kina buƙatar ki koma a ƙara sanar dake wanene Yusuf, ga wannan ina tinanin ya isa wani kitso da ƙunshin".
Yana gama zancen ya ajiye mata dubu goma sha biyar akan kujeran da ya zauna ya miƙe bai ko kallin inda take ba ya fice daga cikin falon, sallama suka yi da Hajiya Kulu suka tafi. Tunda suka baro gidan ya sa rai da ƙiran Anty Binta tare da sille shi tatas akan abinda ya yi, don haka wayarsa gabaɗaya ya kashe babu wanda ya faɗawa batun auren a cikin abokansa. Hashim ne kawai ya san da batun shima yaya Auwal ne da kansa ya nemo shi ya sanar dashi. Bai ƙara zuwa gidan ba har sai ranar da aka aura auren da tsawon daren ranar bai iya runtsawa ba.




MATAN AREWA


(Book two)




© Maimunah Tijjani Iyam


_______________________________________




Page 9⃣6⃣


Duk da aka yi sanarwa an ɗaura aura igiyar aure tsakanin sa da Aishan ya daskare a cikin masallacin, mutanen da suke zuwa domin su yi musabaha su taya shi murna ma ala dole duk suka fice lura da yanayin da yake ciki. Yaya Auwal, Mahmud da Hashim ne suke karɓan gaisuwan sai da aka fara watsewa kafin yaya Auwal ya iso inda yake hannunsa ya kai ya dafo kafaɗansa tare da furta sunansa a nutse"Yusuf lafiyarka kuwa?". Da idanu kawai yake bin sa ba tare da ya furta masa ko da kalma ɗaya ba illa ajiyar numfashin da yake sauƙewa tamkar wanda ya yi gudun ceton rai, dirsham yaya Auwal ya zauna yana fuskantar shi sosai sai da ya kwantar da muryarsa kana ya soma faɗin"Yusuf kayi haƙuri ka taushi zuciyarka ka koya mata yarda da ƙaddara mai kyau ko akasin hakan, ka koya mata karɓan canjin rayuwa ta koya mata karɓan abinda ba ta so idan ya same ta da kuma abinda take so idan ya kufce mata. Idan ka yi haka in sha Allah zaka rayuwa cikin salama da kuma nutsuwar gangar jiki da na ruhi a ko yaushe, kayi addu'ar Allah yasa wannan auren ya zamto alkhairi a gare ka ya baku zaman lafiya dawwamammen da zuri'a ɗayyaba Yusuf. Yanzu ka tashi kaje ku gaisa da mutane ka saki fuskarka".
Bai ko motsa ba dukka da zantukan yaya Auwal ɗin sunyi matuar ratsa shi, sai da ya riƙe hannunsa ya miƙa shi tare da gyara mata zaman hularsa a kansa sannan suka fito waje dole ya saki fuskarsa da annuri ya yi yanka ƙauna gare ta tare da aro murmushin dole ya dasa a fuskarsa yana gaisawa da mutanen da suke yi masa murnan aure, wani kallo ya watsawa Hashim ganin mafi yawan abokan aikinsu a wajen wanda shi dai bai gayyaci kowa ba kawar da kansa Hashim ya yi don baya ma buƙatar su haɗa ido balle ya amsa tuhumar da yake yi masa cikin kallon da yake jefo masa.


Daga nan ƙofar gidan Anty Binta suka koma domin tunin an sanar musu da isowar waliyan Safwan, aka ɗaura nata auren da ya samo halaltan manyan mutane mamallakan manya manyan motoci kasancewar dangin Safwan ɗin hannun su yana cuɗar bayan su. Ganin bashi da wani ishashshen kuzari ya sanya Yaya Auwal umartan Mahmud akan ya ɗauke shi akan mashi ya kai shi gida ya huta zuwa anjima sai ya dawo,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login