Showing 12001 words to 15000 words out of 171161 words

Chapter 5 - MATAN AREWA BOOK TWO COMPLETE PDF .txt

kalli fuskar yaya Yusuf amma ina dannewa. A ƙoƙarin cika alƙawarin da nayi wa kaina na cewar zan fige so da ƙaunarsa gabaɗaya daga raina. "Abba kai tsaye ba zan ce ga wani laifin da Na'ima ta aikata min ba, zama ne kawai ya ƙare dole a rabu kamar yanda bahaushe yake cewa koda so in zama ya ƙare za'a rabu".
Ya ƙar ya ƙare zancen domin ji yake yi zuciyarsa tana ɗillin-ɗillin, zantukan da Anty Binta ta kimtsa masa kafin tahowar su suka shiga masa yawo a kai. Baba ƙarami ya karɓe zancen da cewar"Kar ka mayar damu mutanen banza kamar yaya zaka ce babu dalili kenan haka siddan ka danƙara mata saki har uku ba tare da wani ƙarƙarfan dalili ba, wannan ai maganar banzan ce".


"Malam Nuhu kuyi haƙuri a bi abin nan a sannu".


Furcin ƙanin mahaifin su yaya Yusuf kenan take naji raina ya ƙara tuntsura da babu ko kunya ya kalli idon iyayena ya furta musu bashi da wani dalili na saki na, muryar Anty Binta ta katse mini hanzari.


"Idan iyakar abinda zaku faɗa kenan mu zamu tafi".


Tsananin fusata hajiya Babba tayi a kufule ta ce"Dan Allah ki rufe mana baki muyi abinda ya tara mu a nan".
Shuru ya ɗan ratsa falon na wuce gadi wanda ina da tabbacin haushi furcin na san ne yake nuƙurƙusan su. Sai can Abba ya yi gyaran murya kana ya ce"Shikenan mun ji wannan amma in ce kuna da masaniyar cikin dake cikinta?".


Shuru gabaɗayan su suka yi hakan ya sanya numfashina cushewa a karo ba adadi kaina yana fitar da hayaƙi tamkar garwatsin da aka sanyawa tureran wuta yana tashin hayaƙi. Sai da Abba ya ƙara maimata maganar kafin yaya Yusuf da tun ɗazu yake kokuwa da numfashinsa ya cira kai ya ce"ni na san da zaman cikin dake cikinta kuma na amshe shi domin nawa ne".
Wani irin wawan tsalle zuciyar Anty Binta dake dakan lugudai tayi ta dire mata a ƙirji. Take numfashinta ya cushe tana tirkewa wasu zuffa suka tsatstsafo mata daga dukkan mafitar gashin dake jikinta, ta yaya za'a sako da maganar ciki yanzu, tabbas ta bari suka amshi cikin nan ta gama haɗewa har ganyenta. Na'imar dai da bata son gani da raɓa ita ce take ɗauke da cikin ɗan uwanta.
Innalillahi wa inna ilaihir raji'un bata da shakka ko fargaba akan aikin malamin, ba don haka ba sai ta ce anya aikin da ya yi mata akan ɗaurewa Na'ima mahaifa tsawon shekarun aurensu da Yusuf akan kar ta ɗauki ciki gashi yanzu ciki ya ɓullo. A faƙaice ta share gumin saman goshinta da gefen hijabinta tana ƙoƙarin dai-daita fitan numfashinta.


"Masha Allah tunda kun amsa cikinku, sai ku sani ɗaukar nauyin abinda yake cikinta yana kan ka. Daga yanzu har izuwa lokacin da zata haife shi ta kuma yaye shi daga nan sai ku san yanda zaku yi dashi".


Baba ya furta a zazafe sai a sannan naji muryar yaya Auwal ya furta"ba komai in sha Allah zamu ɗauki nauyinsa muna godiya da karamcin da kuka yi mana".


Da haka tattaunawar ta watse su Abba duk suka fice, yaya Majid ma cike da takaici ya fice yaya Auwal da Baffa suma suka fice Anty Binta ta miƙe da faɗin"sai ka tashi mu tafi tunda ka jawo mu an gama ci mana mutunci".


"Dan Allah Anty kiyi haƙuri ina son ganawa da Na'ima ko na daƙiƙa biyu ne".


Ya furta a raunane da hakan ya ƙara tsananta fushinta"Wai kai meyasa shashasha ne dukkan wannan wulaƙancin da suka yi maka bai ishe ka ba?, tana neman zantawa da ƴarsu to tayi maka uwar meye kar ka manta fa yanzu babu aure a tsakanin ku".
A harsale hajiya Babba ta amshe zancen da faɗin"yo ai mu ma bamu yi lalacewar da zamu yarjewa ƴar mu sauraransa ba, tunda yanzu babu sauran wani abu a tsakani babu kare bin damo".




MATAN AREWA


(Book two)


© Maimunah Tijjani Iyam
_________________________________________




Page 4⃣0⃣


Rawar da jikina ya ɗauka ya sanya ni tashi da niyyar ficewa daga falon ina ɗagowa idanuna suka sauƙa cikin idanun yaya Yusuf kasa ɗaukewa muka yi daga cikin na juna tsawon daƙiƙun da ba zasu gaza biyu. Ba hawaye ne taf cike da idanunsa, haka nan nima nawa idanuna suke a cike bayan hawaye tabbas na hange wasu abubuwan bayan hawaye kwance a cikin idanunsa, sai da nayi kokuwa da zuciyata da take harbawa fiye da kima kafin na runtse idona nayi ƙasa dasu, kunyar Ummata da hajiya Babba da suke waje ya kama ni. Ban san yaya aka yi na iya kawo kaina izuwa sashinmu ba domin ni kaina ban san inda nake jefa ƙafata ba.
Ban san dalilin sauƙar hawayen da naji suna wanke mini fuskana, kaina ya sara a karo na barkatai na zauna tallafe da kuncina abin duniya duk ya isha shi. Soyayyar yaya Yusuf tana azalzalan zuciyata da hakan ya tilasta mini sauƙe wani gauron ajiyan numfashin da ban shirya masa ba. Kallon idanun yaya Yusuf da nayi yanzu suka ƙara fama mini raunin dake cikin zuciyata, kamar yanda na sha faɗawa zuciyata a duk lokacin da tayi mini rashin adalci ta hanyar busawa gawar gangar jikin soyayyar yaya Yusuf a raina cewar babu amfanin wannan soyayyar gare ni domin lokaci ya ƙure dole na ɗaura aniyar yaƙi da zuciyata kan lamarin.


Wani irin azababben ciwo kai nake ji ta gefe ɗaya kuma duk jikina ya yi mini nauyi zuciyata tana hura sosai, dafe goshi nayi cike da tausayin kaina. Na daɗe zaune a wajen cikin ciwo sai da aka yi ƙiran magrib Umma ta shigo bata ce dani komai ba ta ɗauki abinda ya shigo da ita ta fice.


Daren ranar ban iya cin komai ba sallan kawai nayi na wuce ɗakinmu na kwanta ina jin wani zazzaɓi mai zafi da haddasa shigar sanyi jikin ɗan adam yana ƙara ratsa cikin ƙashi da ɓargona. Salma ce ke ta aikin lallashi na amma duk yanda ta nuna damuwarta akan halin da nake cikin hakan bai sanya na tsagaita ba, raina a cunkushe kunnunwa suna tariyo mini furcin yaya Yusuf da nake ƙoƙarin yaficewa daga raina na faɗi da ya yi babu laifin tsaye balle na zaune da na aikata masa zama ne ya ƙare tsakanin mu. Kamar ko wani dare yau ma ban iya runtsawa ba saboda ciwon kan da ya ƙi barina. Duk yanda naso miƙewa akan ƙafafuna da suke rawa hakan ya gagara ni saboda jirin da yake kwasa ta da ko nayi yunƙurin miƙewa yake mayar dani babu shiri, ƙanƙame jikina nayi waje guda jikina gabaɗaya yana rawa tamkar kazar da ruwan saman ya yi mata mungun kamu ko kuma wacce ke mashashshara.


Tun bayan fitar su daga gidan Baffa yake ta surfawa Anty Binta faɗa, wacce ita kam hankali da tinaninta ma basa gare shi balle har ta sama nutsuwar sauran abinda yake faɗi har ya kai ga ta iya tantance su, tunin tayi nisan da bata ji ƙira cikin duniyar tinanin da zurma. Har ya yi ya gama ba ta ce dashi uffan ba balle ya saka ran samun amsarta. A hanya suka rabo da Baffa su kuwa suka wuce gidan Anty Bintan basu shiga ba saboda ƙiran sallan magrib ɗin da aka keyi suka wuce masallaci. Ita kuma ta shige tagumi ta zagba tana zaune bakin gadonta.


"Mama lafiya kuwa?".


Muryar Husna suka katse mata hanzari, a harsale ta ɗago kanta tana fitar da wani hucin ɓacin rai ta ce"ubanki ne kin ji ƴar iska marar hankali".


"To Allah ya ba ki haƙuri, bani na kar zomon ba rataya aka bani wanda ya taɓo ki daban wanda za ki sauƙe fushinki a kansa daban".


Ta faɗa cikin ƙunƙunin rashin kunya kafin ta fice daga ɗakin tana banko ƙofar, ƙwafa Anty Binta tayi ta miƙe tare da zare hijabin dake kanta ta fito da nufin yin alawa.


Cak ta tsaya sakamakon zazzagan gargaɗin da malaminta ya yi mata akan har ta kuskura tayi wani ibada har sai bayan kwanaki goma da yin aikin, a wahale ta sauƙe numfashi domin dududu yau kwana huɗu ne da barowanta gidansa. Komawa ɗaki tayi ta kasa zaune balle tsaye ranta fal tinanin abinda zai fishsheta take yi game da cikin nan, ta daɗe tana zarya a ɗakin kafin zuciyarta ta tsayar mata da matsayar da take tinanin shine mafita gare ta. Fito tayi dai-dai sanda yaya Auwal da yaya Yusuf suke shigowa bakunan su ɗauke da sallama ciki-ciki ta amsa kafin ta umarta Amir ya shimfiɗa musu tabarma.


Sai da suka zauna tana daga gefe su kuwa suna jere a gabanta tamkar suyi mata sujjada don biyyaya da girman da suke bata. Gyaran murya tayi tana kallon Yusuf da yake murzar zoben azurfan dake saƙale a hannunsa a hankali, ta furta"Yusuf magana nake mu yi".


Ba tare da ya ɗago kansa ba ya ce"ina jinki".


"Magana ce akan cikin da iyayen Na'ima suka ce tana ɗauke dashi, da suka dangata shi da cewar naka ne. Nayi mamaki da ka amshi hakan bayan na san tunda ta ƙwallafawa ranta ga wannan bokon ba ma wani samun kanta kake yi ba".


Taune leɓɓensa ya yi yana ɗan shafa gefen sumar kansa kafin ya ce"ban da abin ki Anty Na'iman nan fa matata ce na tsawon shekarun uku da rabi kafin ƙaddara ta raba mu, to meye abinda zai ba ki mamaki don an ce tana ɗauke da cikin ɗana ko ƴata a jikinta?. Balle ma ni na daɗe da sanin hakan".


Sosai gabanta ya faɗi don bata yi tsammani amsar da zai futo daga bakinsa ba kenan, a ɓoye ta sauƙe tagwayen ajiyan zuciya ya tari numfashinta da faɗin"Idan wannan ce iyakar maganar ta kin to ni ina gani zan wuce gida ina da aiyuka".


Kalle shi tayi tsaf tana son su haɗa ido amma sam ya kaucewa faruwar hakan. Domin ya fara zargin wani abu duk lokacin da zasu yi wani magana matuƙar idanunsu suka haɗu waje guda baya iya faɗin ra'ayinsa haka nan baya iya ja da abinda ta faɗa. Koda kuwa ya san ba akan dai-dai take ba balle samun ƙarfin gwiwan yi mata nasiha.


Har ya miƙe furcinta suka dakatar dashi daga ficewa daga cikin gidan.
"Ba shakka Yusuf yau ni Binta kake kallon cikin idona kana gaya min hakan?, Allah ya jiƙan Baffa da Inna da suna raya na tabbatar duk hakan ba zai faru ba daman ni ai ba ganin mutumcin kake yi ba". Sosai ya runtse idonsa domin jin ta ambaci iyayensu da suka daɗe a cikin ƙasa, ba tare da ya buɗe idonsa ba ya ce"Ban faɗa miki wani abunda za ki auna hakan a matsayin rashin kunya ko kuma rashin ba ki girmanki a matsayinki ta wacce kike sama dani ba, balle har kiyi zargin bana ganin ki da mutumci. Allah ne shaida tun bayan rasuwa su Baffa mun ɗauke a matsayin uwa da uba gare mu kuma bamu taɓa kuskure wasiyyar su ba komai zamu aiwatar sai mun nema shawararki kamar yanda suka umarce mu, Allah ya ba ki haƙuri idan na ɓata miki".


Yana gama faɗin haka ya fice ba tare da ya tsaya sauraron maganganun da ta ɗaura dasu ba, ƙarƙarfan ajiyan zuciya yaya Auwal ya sauƙe kafin ya ce"Allah ya kyauta, Anty nima zan wuce a tashi lafiya Allah ya bamu alkhairi". Daga haka ya fice sai dai koda ya fito bai tarar da yaya Yusuf kansa kawai ya jinjina shima ya hau mashin ɗinsa ya wuce gida ransa duk babu daɗi. DZon shima cike yake da tausayin halin da ɗan-uwan nasan ya sinci kansa a ciki.


Bai koma gida ba sai ƙarfe goma sha ɗaya saura na daren don sam in ba dole ba ma ba son zaman gidan yake yi ba, ciki-ciki ya yi sallama da ko kana kusa dashi ba lallekaji ba, yana ƙoƙarin zaro key daga aljihunsa ya buɗe ɗakin muryar maman Hanan ta dakatar dashi.


"Yusuf sai yanzu?".


Kansa kawai ya ɗaga mata ta ajiye butar dake hannunta tare da harɗe su a ƙirji, hasken farin watan da ya game ko'ina shi yake bata damar kallon fuskarsa da ya sunkuyar da kansa ƙasa. Sosai take jin tausayinsa tun bayan faruwar lamarin ya rame sosai ta fuska idanunsa sun ƙara yin can ciki, sai karan hancinsa da ya ƙara fitowa kamar shi ya darawa kansa. Gabaɗaya ya canja canjawa mai yawan gaske duk da dama can shi ba mutum bane mai yawan magana sai dai yana da fara'a da sauƙin kai ga na kusa dashi, amma yanzu ya ƙara komawa shuru sai kayi masa magana sau goma da ƙyar ya amsa maka ɗaya sai dai kawai ya ɗaga maka kansa ko kuma ya jijjiga. Muryarsa da suka bugi dodon kunnenta suka dawo da ita hayyacinta.


"Sai da safe a tashi lafiya". Yana ƙare faɗin hakan ya faɗa ɗakin tare da rufo ƙofar, jingina kansa ya yi jikin ƙofar yana sauƙe numfashi a wahale kafin ya fara bin ɗaki da kallo tamkar yau ya fara shigowa cikinsa. Babu shiri ya runtse idanunsa yana addu'ar Allah yasa duk abubuwan nan da suke faruwa su zamto mafarki ina ma a ce da ya farka daga wannan nauyayyan bacci komai zai dai-daita, ina ma ace yana buɗe idonsa yaga Na'imarsa a gabansa tazo tarban sa da fara'a kamar yanda ta saba masa a duk sa'ilin da ya dawo. Ta kawar masa da gajiyar da ya kwasu da daɗaɗan kalamanta masu cike da sanyi da sanyaya ruhin mai sauraro, ina ma a ce rayuwarsa zata dai-daita ta koma kamar da, ina ma a ce komai zai tafi yanda ya tsara da bai tsinci kansa cikin wannan halin da yake ciki ba.


MATAN AREWA
(Book two)


© Maimunah Tijjani Iyam


__________________________________


Page 4⃣1⃣


Da ƙyar nake iya buɗe idona sanda na miƙe domin yin alwalan sallan asubahi, a zaune nayi sallan domin ko nayi yunƙurin tsayiwa akan ƙafafuna basa bani haɗin kai sai ma butulce mini da suke yi. Lamau na koma na kwanta ina rawar ɗari, Anty Zakiyya ta shigo tana tambayata meke damuna nima kaina ban san abinda yake damuna ba domin idan hakan ta kasancen zan so sanin hakan ni karan kaina. Ganin bani da niyyar tanka mata haɗe da rashin amsa mata ko ɗaya daga cikin jerin gwanon tambayoyin da take yi mini ya sanya fita suka dawo tare da Umma.


Cike da kulawa Umma ta ɗago kaina tare da faɗin"Lafiya Na'ima meke damunki?". Hawaye ne suka ziraro mini masu ɗumi ta gefe da gefen idanu wanda ban san dalilin tsiyayar su ba, ajiyar numfashi kawai nake sauƙewa ina bin su da kallon ɗaɗɗaya. A riɗime Anty Zakiyya ta furta"Mun shiga uku Umma". Tana fashewa da kukan da nake jin sautinsa har cikin ƙoƙuwar kaina, ganin gabaɗaya sun birkice ya sani yin ƙarfin halin faɗin"Lafiya ƙalau Umma kawai ciwon ƙirji ne".


"Sannu Allah ya sauƙe".


Suke furta kusan a tare kafin Anty Zakiyya ta miƙe ta fice da dawo ɗauke da ledar magungunan da aka haɗo ni dashi zuwan mu asibiti na farko. Da kuma kofin ruwa Umma ta tallafo kaina, sa'an nan na sha maganin na komar da kaina na kwanta ina sakar musu da murmushin yaƙe.


"Ki kwanta ki huta Allah ya sauwaƙe, kafin na dama miki kunno ko shi ɗin za ki iya sha, tunda ba wani abun kirki kike iya ci ba".


Umma ta furta tana kwanta da kaina dake kan cinyarta akan matashi. Da Anty Zakiyya muka zauna tare da ƙyar na furta mata"ina son nayi karatu". Da kawo mini al-qur'ani na fara karanta ita kuma ta fice. Na daɗe ina karatun har sai da naji sanyi ya fara ziyartar ruhina da nake ji tamkar ana musayan garwatsin wuta, sallan zuhr ma a zaune nayi shi haka nan asr. Na fito zan yi wanka da taimakon Anty Zakiyya da ta dafa mini ruwan zafi yanda zan fi jin daɗin jikina.


Kamar wacce aka zarewa laka haka na gama wanka, ina jefawa kaina tambayar abinda yake damuna da kuma dalilin faɗawa ta cikin wannan ƙangin damuwar da ƙuncin da ya turbuɗe hasken fitilan dake haska rayuwata. Zanina na ɗaura na saka hijab a kai na fito riƙe da soson wankana da bokatin ƙarfe. Babu shiri naji jiri suna shammata ƙafafuna sakamakon furcin Daada da Umma su Anty Kubra da iska ya kwaso ya sauƙe su a kunnuwana tamkar don naji suka faɗi.


"Zainabu ai wallahi ido kawai na zuba musu domin ganin gudun ruwan su daga ita har malam ɗin, da hajiya Babba da take ɗaure musu gindi suke rashin mutumcinsu son rayin su. Na tabbatar da ƴar wata daga cikin matan gidan nan ne wannan abun ya faɗa a kanta. Wallahi na rantsa har da girman zatin Allah da wani zancen daban ake yi ba wannan ba, balle kuma a ce kana ɗauke da wannan shirgegiyar budurwan da ba'a bambamce ta da matan gidan".


Cike da takaici Umma su Anty Kubra ta furta"ke dai bari waye bai san rashin adalcin hajiya Babba da nuna bambamci tsakanin jikokinta ba, lokacin da Habibu ya yi jinkira turo iyayensa har iyayen samarin su Hajara suka turo wani irin tijara ne ba'a yi min cikin gidan ba. Har cewa aka yi za'a bada ita sadaka a masallacin jumma'a amma ita da yake uwarta matar so ne ai gashi duk sun zuba mata idanu".


"Ai daɗin abin Allah baya bacci kuma komai daren daɗewa za'a haɗu a madakata ya yi wa kowa hisabi. Ai ga sakayya nan sun fara cin karo dashi tun a nan duniya ga Na'iman nan auren ya guntule, ai daman auren asiri baya ƙarko daman ni tun ranar farko da na ɗaura idona akan yaron nan zuciya ta ɗarsu da zargin kyau irin nashi da kuma haiba da cikar kamala irin nasa ya wuce tsaran Na'ima. Ko kallo ba zata ishe shi ba balle har ya furta mata kalmar son da zata kai su ga aure, sai dai aikin asirin kam shirin wannan mushirikan uwar ta tan.


Sanƙarewa nayi a wajen kamar gunki ina kasa gaba balle baya balle kuma na sama damar janye kaina daga wajen. Wasu tulun hawayen suka cika koramar idanuna, zuciya ta shiga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login