Showing 165001 words to 168000 words out of 171161 words

Chapter 56 - MATAN AREWA BOOK TWO COMPLETE PDF .txt

yanzu zai dawo ban tanka masa ba illan gyaɗa kaina da nayi.
Na ɗauro alwala nazo na gabatar da nawa salla kan sallayan na zauna ina juyayin yanda ƙaddara tazo mini ta yanda ban taɓa zato ba, a kai-a kai nake sauƙe numfashi tamkar wacce tayi gudun ceton rai ina kallon kaina da mamakin kasancewata a matsayin matar Yusuf a wannan lokacin. Ɗago idon da zan yi idanuna suka sauƙa akan sa yana tsaye a ƙofar ɗakin ya naɗe hannayensa a ƙirjinsa tare da ƙura mini ido, saurin kawar da nawa gefe nayi ina gyara hijabi ɗin na rufe jikina. Har gaba na ya tako ya zauna kana ya ce"tinanin meye kike yi?".


"Babu". Na amsa mishi a gajarce ya gyara zamansa yana naɗe ƙafafunsa wajen guda ya ce"na san ni laifi ne a wajen ki Na'ima, kuma zan cigaba da neman afuwanki har zuwa lokacin da kike jin cewar zuciyarki ta aminta dani ta yafe min". Shuru nayi masa hakan ya bashi daman ɗaurawa da"na san dole ki dunga ganin abun wani iri sai dai ina mai neman afuwanki yafe min ko nima zan samu zuciyata ta yafe min akan lafin cutar dake da nayi, na gane ba zan iya rayuwa babu ke ba ko na rayu ma to tabbas zan zamto marar amfanin da ko kaina ba zan iya taɓukawa komai ba, ki tausashi zuciyarki ta yafe min laifukan da na aikata mata". A raunane ya ƙare zancen muryarsa yana rawa kamar mai shirin yin kuka a karom farko a tsakanin jiya da yau da na kalli tsakiyar idanunsa kenan na tsawon wasu mintoti.
A hankali na ce"na yafe maka Yusuf ban taɓa riƙe ka a raina ba, sai dai tarin darrusa da ka koyar dani game da rayuwa suna nan a zuciyan...". Ban ƙarisa ba naji hannunsa caraf a cikin nawa ya riƙe gam duk zafin da zazzaɓin da nake ji ya haifar mini sai naji nashi zafin jikin ya ɗara nawa sau babu adadi.


"Na'ima ki bani dama zan sa ki manta da komai don Allah ki bani wannan damar". Take naji wasu hawaye sun ƙaryo mini da ƙyar na iya furta"an umarce ni da yi maka biyayya akan komai matuƙar bai kaucewa hanyar koyarwa addini ba, don haka na baka wannan damar". Ina iya jiyo sakakken ajiyar zuciyan da ya saka yana ƙara ƙarfin riƙon da ya yi wa hannuna ya ce"na gode na gode matata".


"Ance kayi ƙara aure ina matar take?". Na faɗa ina haɗiye wani miyau mai ɗaci daga maƙoshina.
"Mun rabu". Idanuna na ware a kansa"meya raba ku?". Ɗage kafaɗarsa ya yi cikin ko in kula ya ce"ai dama ramin ƙarya ƙurarren ne Anty Binta ce ta haɗa auren kuma ita ta raba". Ban kuma cewa komai sai can ya ce"ba zamu daɗe a nan ba zan saki hayan gidan nan zamu koma garin su Anty Zakiyya saboda makarantanki da kuma nawa".


Ƙatuwar ajiyar zuci na saka tsabar tashin hankalin da na tsunguma ciki gabaɗaya ma na manta da wani batun karatun duk soyayyar dake tsakani na dashi. Shi kaɗai yake kiɗansa kuma yake rawansa domin shi yake zancen kuma yake ba wa kansa amsa, a haka har aka yi ƙiran sallan magrib ya fita masallaci bai dawo da wuri ba sai da aka yi isha'i ya shigo da ledodi niƙi-niƙi a hannunsa ya ajiye su yana bani haƙurin bari na ni ɗaya da ya yi taƙaitaccen murmushi kawai na sakar masa.


Da kansa ya ɗauko plate ya yanka fruit ɗin da ya shigo dasu, sannan ya tsiyaya yogut ɗin a kofina tare da buɗe ledar kazan ya kallo ni cikin kulawa ya ce"ki sauƙo ki ci abinci ki sha magani".


"Bana jin yunwa". Bai ce komai ba ya ɗauko plate ɗin har kan gadon da nake zaune ya yago kazar ya ce na buɗe bakina, kaina na jijjiga masa ya ce"buɗe ko na buɗe miki da kaina na sanya miki bayan na tattauna miki shi, ta yanda da na saka miki haɗiye kawai za ki yi". Ba don naso na buɗe na karɓa na fara ci sai don bana ƙaunar yawan magana, sai da naci sosai ya bani maganin zazzaɓi nasha ya haɗa mini ruwan wanka na shiga nayi nazo na kwanta.
Haka kwanaki biyu suka shuɗa komai shi yake yi a cikin gidan yana bani kulawa kamar kwai ko motsi nayi sai ya ji dalili da tambaya lafiyata. Sai har yanzu ban gama sakewa dashi ba daga gidan mu babu wanda yazo mini shima daga nashi dangin babu wanda yazo har yanzu. Gashi babu waya a hannuna balle na ƙira su, sai da muka cika sati biyu ya ce jibi zamu koma makaranta har ya sanya wani abokinsa dake can ya kama mana hayan gidan da zamu zauna, don haka gobe zamu je gidanmu da gidan yaya Auwal da Anty Binta muyi musu sallama.


Da fargaban abinda zan je na tarar da gidan Anty Bintan na kwana har muka wayi gari muka sauƙa a gidan yaya Auwal. Sosai nake kallon gidan da tino rayuwar da nayi a cikin a lokacin baya da ya shuɗe maman Hanan ta fito cike da murnan ganina ta rungume ni kamar jira muke yi duk muka fashe da kuka. Su yaya Auwal suna ta yi mana dariya tabarma ta shimfiɗa mana tare da gabata mana da ruwan sha sannan muka gaisa.


Jin motsin takun mutum daga bayana ya sani waigawa caraf idanuna suka sauƙa akan fuskar Husna da fitowar ta daga bayi kenan, butar hannunta ta saka ita ma tana bi na da kallo kamar yanda na kafe da ido.


"Husna".


Na furta cike da son tabbatar da ingancin idanuna don gani nayi gabaɗaya ta canja mini, tayi mungun sauyawa daga Husnan da nayi a zamanin baya. Ta rame tare yin duhu ga cikin da ya fara bayyana a jikinta.




MATAN AREWA


(Book two)


© Maimunah Tijjani Iyam


____________________________________________




Page 1⃣2⃣1⃣


Ganin hawayen da suke gudun akan fuskarta ya sanya nima nawa fara kwaranya, ta iso kan tabarman da nake zaune ta durƙushe a gabana tare da kifa kanta akan gwiwoyina. Na gaza cewa da ita komai domin nima na kasa tsayar da ruwan ƙwallan da suke shawagi a bisa fuskana.


"Ya isa haka". Na faɗa ina ɗago fuskarta da ya jiƙe jigif da ruwan hawaye, murmushi na ƙaƙalo na jefa mata na ce"ashe kin yi aure Allah ya sanya alkhairi". Ƙara ƙarfin kukan natan kamar zata shiɗe ta ce"don Allah ki yafe min abubuwan da na aikata miki Anty Na'ima, wallahi tun daga yanzu Allah ya fara nuna min sakayya". Sai da na sanya hannu ina share mata hawayen idonunta na furta"ba ki aikata mini komai ba Husna in ma ki yi mini to na daɗe da yafe miki".


Yaya Auwal ne ke labarta mini abinda ya faru da Husna da kuma halin da yanzu take a ciki. Sosai naji kifiyan tausayinta ya caki zuciyana tare da tarwatsa shi into piece, tabbas dole ta shiga damuwa kuma ta lalace duba da ƙarancin shekarunta da kuma girman jarabawan da Allah ya jarabce ta dashi.
Har muka baro gida bakinta bai gushe daga neman afuwana ba kamar yanda nake sanar da ita bata aikata mini komai ba. Daga nan gidan Anty Binta muka nufa babu abinda ya sauya a gidan yana nan kamar yanda na san shi a baya, sai da muka jera sallama baki uku reras kafin aka amsa hakan ya bamu lasisin kutsa kai ciki. Da Amir muka fara yin arba ganin mu ya sanya shi saurin faɗi"Aah kawu ku ne kuke ta tafka sallama haka?, tare kuke kenan da Antyn namun daman naji labari bakin kawu cewar ta dawo, kaga yanda nayi murna kuwa ranar har wani ɗan akuya da yake kai kawo a layin nan nayi wuf dashi, muka danna masa wuƙa muka yi party da jama'ana".


"Kai dai Amir Allah ya shirye ka ina Anty Bintan take?". Furcin malam Yusuf kenan yana ware mana tabarmar dake yashe filin tsakar gidan sai da muka zauna kana Amir ya ce"tana ɗaka walaƙil bacci take yi, Antynmu sannu da zuwa fa". Murmushi na sakar masa ina mamakin girman yaron da kuma canzuwan da ya yi, sak ya koma cikakken ɗan daba-daba da a kallon farko zaka fahimci hakan, shirgar ƙauraye ne a jikinta ko magana zai yi sai ya juya bakinsa gefe.


"Sannu Amir ya kake?". Sai da ya murmusa ya amsa mini da cewar"to lafiyan dai za'a ce". Rufe bakinsa ya yi dai-dai da fitowar Anty Binta daga ɗaki cak ta tsaya tana ƙare mana kallon tsaf.
"Ƙariso mana Umma ko dai ba ki gane ta bane?". Furcin Amir kenan da ya sanya ta watsa masa wata uwar harara tana ƙarisowa ta zauna shi ya fara gaishe ta sannan nima na gaida ta ta amsa yana yatsina fuska.


"Daman mun zo yi miki sallama ne gobe in sha Allah zamu bar garin".
Cikin ko in kula ta ce"Allah ya kaimu". Muka amsa da amin yayin da Amir ya saki shewa tare da faɗin"Wayyo ni shegiya duniya mai koyawa ko wani ɗan iska zama wanda ba'a haifa ba ma tana jiran zuwan sa balle wanda yake cikinta. Ummata Ummata kenan uwata ta kaina ashe shi gama ma da gamonsa wai aljani ya daka wuta".


"Tashi ka fice min daga ita tun kafin na sassaɓa maka". A harsale tayi zancen kamar zata kai masa duka da hakan ya sanya sa miƙewa yana cewa"Allah ya ba ki haƙuri Hajiyata, kawu na barki lafiya Allah ya sauƙe ku lafiya ni kunga tafiyata".


Yana dasa aya nan ya fice cikin tafiyarsa na cikakkun ƴan daba, tana fito har ya fita. Ɓoyayyar ajiyar zuciya na sauƙe ina tausayin rayuwarsa matashi kamar sa da ya dace ace yana makaranta ko kuma wajen sana'a amma hakan ya gagara. Ban mu ƙara minti biyar masu kyau ba muka yi mata sallama muka fice raina cike taf da mamakin nata sauyawan ita ma wataƙil hakan baya rasa nasaba da furcin da Kawu Gambo ya yi akan ya yi mata gargaɗi ficewa daga lamuran gidajen su.


Daga nan gidanmu muka wuce tare dashi muka shiga sashin Hajiya Babba muka gaida ita, sosai fuskarta ya kasa ɓoye bayyanannen farin-cikin da take ciki na ganin mu haka. Nasiha ta ɗan yi mana kafin na tashi na shiga sashin mu sai da na shiga ko wani ɗaki na gaishe su sannan na shiga ɗakin Ummata, tayi farin-cikin ganin na kwantar da hankalina tare da mance komai. A nan muka yi sallan zuhr har da asr domin sai da muka jira dawowar su Abba muka yi musu sallama.
Wani nasihar suka ƙara yi mini na mussamman akan na katse mutuncin kaina da na igiyoyin auren dake kaina, idan na koma makarantar haka muka bar garin cike da kewar ƴan-uwana.


Muna sauƙa muka wuce gidan da ya kama mana, mai ɗauke da ciki da falo da kuma wani ɗakin sai toilet da kitchen, duk kayana gidan yaya Auwal ɗakina na da aka mayar waɗanda zamu yi amfani dasu kawai muka taho dasu. Tare dashi muka gyare gidan tsaf sannan muka yi wanka tare muka yi girki muka ci da zai fita masallacin sallan magrib ya bani wayarsa ya ce na ƙira su Abba na gaida musu mun iso lafiya.


Sai da nayi nawan sallan sannan na lalumo lambar Abba har ƙiran ya tsinke bai ɗauka ba, haka nan ma lambar Baba ƙarami hakan ya sa ni ƙiran Anty Zakiyya muka sha hiran mu har Ummi na ce ta ba wa mu gaisa ta bata Farouk ne duk yanda naso ya amshi wayar Anty Zakiyya ta ce ya ƙi daga bisani ma wai ficewa ya yi.


Dab da zamu yi sallama wani ƙiran ya shigo wayar tare da katsewa, baƙuwar lamba ce nayi tinanin ko Abba ne ko Baba ƙarami ɗaya daga cikin su ya biyo bayan ƙiran da nayi masa, hakan ya sanya ni danna ƙiran lambar ringing ɗaya aka ɗauka ni na fara yin sallama don haka aka shuru ba tare da ance komai ba, fahimtar da waɗanda nake tinani bane ya sanyi saurin katse ƙiran.


Har zan tashi ƙaran shigowar saƙo cikin wayan ya dakatar dani da lambar da aka ƙira ɗin. Na buɗe na fara karantawa kamar haka.


~_"Yusuf don Allah ko sau ɗaya ne ka bani lokaci mu gana da juna, wallahi ina cikin wani hali. Babu abinda zaka yi min wanda zai sanya na daina bibiyarka, naji ance ka mayar da matarka ni wallahi a hakan ma ina sonka kuma zan zauna da ke na yarda naje a ta biyu tunda dama ita ka fara aure kafin ni, ina jiran amsa daga gare ka".
_~


Ina gama karantawa na saki gaurayen ajiyar zuciya ko shakka babu matarsa ce da suka rabu wannan bana buƙatar sai an faɗa mini. Gyara zama nayi ina ƙara bin saƙon da kallo da mamakin irin soyayyar da take gwada mishi da ture ajinta na ƴa mace take bibiyarsa bayan sun rabu, tabbas akwai jan aiki a gabana ko dai na tsura ido kwaɓata tayi ruwa ko kuma tunda yanzu na tashi tsaye wajen kula da mijinta tare da manta komai na gwada masa tsantsan soyayya.


Wayar na ɗauka na goge saƙon sannan na tashi na haɗa mana abincin dare kafin ya dawo na kammala komai har na yi kwanta, nazo ina duba kayan da zan sa naci karo da wayar da Farouk ya bani da ko buɗe ta banyi ba numfashi na sauƙe na ajiye ta na ɗauki kayan na saka. Ko da ya dawo ban nuna masa komai kuma ban bari ya fahimci wani abu daga gare ni ba sai dai nayi ƙudurin nuna masa soyayyan da babu algus a cikinsa tare da mantawa da bayan da ko yaushe cikin bani haƙuri yake yi. Washe gari a gidan Anty Zakiyya muka wuni nan take sanar dani zuwan su Nawwara gidan biyu suna tambayar lafiya bana shigowa makaranta take shaida musu abinda yake gudana, har muka baro gidan Farouk bai yarda mun haɗu ba.


Ranar da na fara fita makaranta tare dashi muka je domin shi ma yana da lectures a lokacin, har bakin hall ya raka ni kafin muka yi sallama ina shiga muka rungume juna dasu Nawwara cike da murnar ganin juna sai tsiya suke mini akan abinda ya faru tare da girmama rashin kirkina na ƙin sanar dasu da nayi. Da ƙyar na lallashe su don sun fusata tare da sanar dasu nima kaina ban san komai ba sai da aka gama komai da komai, bayan nan kuma tashin hankalin da na shiga ya mantar dani komai gashi babu waya a hannuna sannan suka haƙura.


Sai da muke hostel muka yi salla Nazifa ta zubo mana abinci nake jin cewar wai Billy ɗawisu tana asibiti sun yi hatsari da wani saurayinta a hanyar su ta zuwa birnin tarayya yawon buɗe ido, tana asibiti rai a hannun Allah. Sosai naji abun ya daƙi ƙirjina na tausayawa halin da take ciki duk da da kalaman baki ake suffanta mini. Hostel ɗin sharau ɗakunan ma ɗaiɗaiku ne da mutane domin tun bayan faruwar wannan lamarin na sister Sadiya Umar Malik da yawan iyaye sun tsorita wasu sun cire ƴaƴansu daga jami'ar wasu kuma anyi musu aure.
Haka muka rabo bayan na kwatanta musu unguwa da gidan suka yi mini alƙawarin gobe zasu zo don bamu da lectures, kwana nayi da zumuɗin zuwan su a raina da misalin ƙarfe goma kuwa sai gasu rasa inda zan sanya su nayi don murna na girka musu abinci muka ci muna ta hiran mu.


Nazifa take shaida mini cewa an sanya bikin su da yaya Amin bayan sallsn layya da sati biyu, sosai nayi mata murna da fatan tabbatuwar alkhairi nan suka wuni tsum kafin su tafi yaya Yusuf ya dawo suka gaisa.


Haka rayuwa ta cigaba da gudana lokaci yana tafiya muna ƙara kusanta mutuwarmu ba tare da mun sani ba, illa ma burikan da suka ƙara cika mana rayuka. A wani daren da ba zan manta dashi ba har mun kwanta yaya Auwal ya ƙira yaya Yusuf yake shaida masa Husna ba lafiya an kai ta asibiti an ce haihuwa ce dole sai dai ayi mata threater a cire ɗan domin gudun kar ya ɗauki cutar. An ƙira mahaifinta ya ƙira ɗaga waya yaya Auwal ne ya rantaɓa hannu akan takardan aka shiga da ita threatern.
Duk bamu iya bacci ba daren don hankulanmu gabaɗaya yana can lokaci bayan lokaci yaya Yusuf yake ƙira ya tambaya ko an fito da ita yake dashi har yanzu suna ciki, sai ƙarfe huɗu ya ƙira ya ce an fito da ita an ciro ɗa namiji duk hamdala muka saka muna godewa Allah. Ya fita masallacin sallan asubahi ina zaune kan sallaya wayarsa da ya bari akan gado ta fara ruri ganin sunan yaya Auwal ya bayyana cikin screen ɗin ya sani sauri ɗagawa tare da karawa a kunnena.
Tambayata ya yi ina Yusuf ɗin na ce dashi ya fita masallaci sai da ya yi jim kafin ya ce"Allah ya yi wa Husna rasuwa yanzu".
Dum naji kunnuwana sun yi mini nauyi na wayar ta sulale ƙasa daga hannuna saboda rawan da jikina ya soma, durƙushewa nayi a wajen na fasa abin yi wani zuciya tana cewa dani ko dai ban ji abinda ya faɗi dai-dai bane ko kuma matsalar network ne. Ban gusa daga wajen ba har yaya Yusuf ya dawo daga masallaci ya iso inda nake tare da tambayar lafiya, cikin ƙarfi hali na ce"yaya Auwal ne ya ƙira ya ce muje potiskum yanzu".


"Yanzu kuma?". Kaina na jinjina masa ya kuma faɗin"lafiya kuwa?". Ban ce dashi komai ba don na rasa ta yanda zan sanar dashi kamar yanda abinda nake tinani bai ƙara tambayata ba ya waiga ya ɗauki wayarsa ya fita daga ɗakin. Jim kaɗan ya dawo dafe da kansa nayi saurin isa gare shi na zaunar dashi, ina tofa masa addu'a a kan nasan.


Sai ƙarfe goma sha ɗaya muka iso cikin potiskum kai tsaye muka zarce gidan Anty Binta, ciki na shi kuwa suka zauna a waje da maman Hanan na fara yin tozali na isa wajen ta na zauna muna yiwa juna gaisuwa,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login