Showing 99001 words to 102000 words out of 171161 words
Chapter 34 - MATAN AREWA BOOK TWO COMPLETE PDF .txt
Abdul-aziz ɗin, idanunsa tunin ya sauya yana faɗin"meye haka Umar meye kuka aikata kenan? cikin ku waye ya yi masa haka na ce waye a cikin ku?".
Riƙe shi Abdul-aziz ya yi yana ƙoƙarin ɓanɓare hannunsa daga kwalar Farouk ɗin da ya riƙe gam ganin ba zai iya ba ya sanya shi soma faɗin"meye haka Saifuddeen? meyasa ba zaka tsaya ka saurari komai daga gare mu ba? meyasa zaka yanke mana hukunci ba tare da bin ba'asi ba?. Habib ɗin da yake yi a kansa Saif butulu ne ya ci amanar yardan da kake dashi a kansa ya cutar da kai cutarwa mafi muni ya zalunce ka ya take halaccin da kayi masa a rayuwa yayin da ya bari son zuciyarsa ya yi masa ringayi har wata soyayyar ƙara ta ruɗe ta ya ci amanar mutumin da ya ɗauki dukkan yarda ya ɗaura a kansa. Saif ka cika shi nayi maka bayanin komai".
Turus ya yi kamar wanda aka zarewa ruhi yana bin Abdul-aziz ɗin da kallo ba tare da ko kiftawa ba ya cika Farouk ɗin ya faɗi gefe guda ya tunkaro Abdul-aziz bakinsa har rawa yake yi domin sam bai iya shiga ruɗu da tashin hankali ba take yake fita fit daga hayyacinsa tun farko abinda Farouk yake tsoro kenan shiyasa ya roƙi Abdul-aziz ɗin da su gudanar da komai a ɓoye har sai komai ya kammala kafin ya sa ni.
"Meye kake faɗi haka Abdul-aziz? ka sanya ni cikin duhu kayi min dalla-dalla yanda zan fahimta don Allah meye kake faɗi akan Habib duk ban gane ba"."ƙwarai kuwa Saif duk abinda kaji na faɗa gaskiya ne Habib ya cuce ka ya zalunce ka wannan abun da ya faru a gidan gona ba haka nan kawai ya faru ba duk shirinsa ne komai shi ya tsara saboda son zuciya irin nasa da kuma manta alkhairi irin na ɗan adam, ka gane na jikin hoton nan?". Ya ƙare zancen yana nuno masa hoton Mina da ya zaro daga aljihunsa kallo ɗaya ya yi hoton ya gano wacece jinjina masa kansa ya yi da hakan ya bashi damar ɗaura da"budurwan Habib ne kuma a sanadinta ya aika maka duk cin amanar da ya yi maka ba tare da sanin cewa ita ɗin ƴar-uwarka ba ce ta jini, ita ta tsara masa komai duk yanda zai yi kuma ta samar masa da fiya-fiyan da ya yi amfani dashi wajen aiwatar da ƙudirin natan tare da yi masa bazaranar rabuwa dashi idan bai aikata hakan ba shi ya zuba musu fiya-fiyan a cikin ruwa duk suka sha suka mutu kuma ya ƙira ka ya faɗa maka tamkar bai san komai ba gashi nan zaka ji komai daga bakinsa Saif".
Tunda Abdul-aziz ɗin ya fara zancen yaji tamkar an zare masa numfashi da ƙyar ya fizgo shi a wahalce yana nuna Habib ɗin da ƴar manuniyar yatsansa sam maganar taƙi fita illa tsaya masa da take yi a maƙoshi.
"Habib ɗin Saif shi ɗin dai ko kana tinanin cewar ba zai iya cutar da kai bane, da farko muma duk haka muka zata sai daga baya muka gano cewar shi maƙiyi ko shekara biyar kayi kana ciyar dashi da hannayenka idan ya sama dama cikin daƙiƙu biyar zai ragargaza rayuwarka".
Taune leɓɓansa ya yi da matuƙar ƙarfi kafin ya juya ga Habib da har yanzun kansa yake ƙasa yana wani irin kuka mai ƙarfi zama ya yi dirshama gabansa yana ƙare masa kallo sosai ya ce"Habib ɗago kanka ka kalle ni ka sanar dani shin abinda Abdul-aziz ya faɗa haka ne?".
Ƙara tsananta ƙarfin kukan nasan Habib ya yi ba tare da ya ce komai ba ya fara jijjiga kansa sai da ya kuma maimata masa zancen a karo na biyu kafin ya ɗago kansa haɗi da faɗin"yallaɓai babu ƙarya cikin dukkan zancen Abdul-aziz tabbas na kasance butulu mai manta alkhairi da kuma halacci a rayuwa, mun haɗu da Mina watanni bakwai da suka gabata ita ta fara nuna cewar tana sona duk a taran matsayin dake tsakanin mu da ita ta fanni aji da dukiya na amince mata ashe ita da wani ƙullin dake ƙasan ranta a kai na. Munyi soyayya da ita na tsawon wannan watannin ba tare da nasan da cewar kun haɗa wani alaƙa da ita na jini ba ta sha ziyarta ta a gidan gonan ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba har izuwa lokacin da ta fara bayyanar min da ƙudurinta ta fara ne da tusa min hassada akan ka a cikin zuciyata ta hanyar nuni min cewar amfani kawai kake yi wajen gina kanka da zaran ka samu ɗaukaka mantawa zaka yi da duk wani bautar da nayi maka, tabbas yau da gobe ya wuce wasa sannu a hankali zantukanta suka fara samun gurbin zama a cikin kwakwalwata sanda ta zo min da buƙatar na sanya fiya-fiya a ruwan shan su ban amince ba hakan ya sanya ta ficewa daga ofishina cikin matuƙar ɓacin rai da na bi ta har waje amma bata saurare ni. Tayi min barazanar rabuwa dani matuƙar ban aikata son ranta Allah ne shaida ina son Mina matuƙan son da ba zan iya jure rayuwa ba tare da ita ba wannan dalilin ya sanya bayan an tashi daga wajen cikin dare na dawo na sanya musu fiya-fiyan a cikin ruwan shan su".
MATAN AREWA
(Book two)
© Maimunah Tijjani Iyam
______________________________
Page 9⃣0⃣
Tunda ya fara zancen har ya kai aya Saif bai kawar da idanunsa daga kan fuskarsa ba da yake karanta abinda ke taskace cikin ƙirjinsa, wani irin zafi da nauyin ƙirjinsa yake yi masa da yawun bakinsa da ya ɗauke kaf tamkar rijiyar da ruwan cikin ta ya kafe jin idanunsa ya yi sun yi masa nauyin gasken da ko ƙifta su baya ƙaunar yi balle motsa su daga hagu zuwa dama. Sosai kansa yake sarawa tamkar wanda aka yiwa ajiyar wani abun mai nauyin gaske da ƙarfi ya haɗe hannayensa waje guda ya sanya fuskarsa ciki yana sauƙe numfashi a matuƙar wahalce dake bada wani irin sautin gu gu gu da ya jawo hankulan Farouk da Abdul-aziz izuwa gare shi.
Har rige-rigen isa gare shi suke yi cikin sauri Farouk ya jawo shi jikinsa ya rungume tare da riƙo hannunsa ya sanya cikin nasa yana murzawa haɗi da ƙiran sunan shi"yaya Saif! yaya Saif!! yaya Saif ka buɗe idonka don Allah ka amsa min kaji".
Iya abinda yake ta maimatawa kenan yana cigaba da murza hannun nasan dake saƙale cikin nasa, sosai duk suka ruɗe suna ƙiran sunansa tun idanunsa suna a buɗe kaɗan har ya rufe duka dai-dai sa'ilin da Farouk ya ƙara ƙarfin rungumar da ya yi masa yana sakin wani kuka mai ban tausayi da raunana zuciyar mai sauraronsa. Hannu Habib ya sanya zai taɓa shi Farouk ɗin ya yi hanzarin buge masa hannu tare da buɗe rikiɗaɗɗun idanunsa ya buɗe su a kansa cikin kaukausan murya yake faɗin"ka hannunka ya yi ganganci taɓa jikinsa domin ina tabbata maka wannan shi ne kuskure mafi muni da zaka aikata a kaf tarihin rayuwarka".
"Farouk calm down wannan cece kucen ba shi abinda ya kamace mu ba yanzu bari na kawo ruwa a sanya masa".
Furcin Abdul-aziz kenan yana miƙewa ya fice daga cikin ɗakin da sauri ruwa ya ɗebo ya dawo ya sunkuya ya shafawa Saifuddeen ɗin a fuskarsa ko motsi bai yi ba balle su sanya rai ga buɗe idanunsa sai da ya ƙara shafa masa ruwan a karo na huɗu sannan ya saki wata shirgegiyar ajiyar zuciyar da ta sanya su sakin hamdala a tare suna jadadda godiyar su ga Allahn da ya dawo masa da numfashinsa ga gangan jikinsa bayan ɗaukewan sa na tsawon mintoti.
Dafe kansa ya yi da jijiyoyin kansa suka shimfiɗa raɗau-raɗau a saman goshinsa, a hankali ya jawo numfashinsa da ƙarfi ya fesar ta bakinsa yana ƙoƙarin tara jikinsa da na Farouk tare da ƙarewa ɗakin kallo da nufin gano abinda ya haifar masa da suman da abubuwan da suka faru gabannin hakan. Ajiyan zuciya kawai yake sauƙewa a kai a kai tare da runtse idanunsa yana jin wani irin zafi a cikin ƙirjinsa dake bugawa da ƙarfin gudun da ya wuce ƙa'ida da kuma misali.
"Yaya Saif kana lafiya kuwa ko asibiti zamu je?".
Kansa kawai ya jinjina masa alamar cewar he's ok, ba don ya yarda ba Farouk ɗin ya ja bakinsa ya tsuke sai don gudun ƙara tayar masa da hankali bayan wanda yake cikin sa a yanzu, sannu Abdul-aziz yake ta jera masa haɗi da faɗin"ko mu kai ka gida Saif ka huta? daga bayan sai mu gama wannan maganar".
Sai a sannan ya buɗe idanunsa tar akan fuskar Abdul-aziz ɗin bai ce dashi komai illa miƙewan da ya yi cikin haɗa hanya kamar wanda ya shawo ya yi tatil ya iso gaban Habib da ya duƙar da kansa ƙasa ya zauna dirsham tare da riƙo hannunsa ya sanya cikin nasa ya riƙe sosai yana kallon fuskarsa da yake tinano masa da abubuwa da yawa da shuɗe cikin har da yanda ƙaddara ta haɗa su. Sai da ya sauƙe ajiyar zuciya sannan ya sama zarafin soma faɗin"Habib zuciyata ba zata taɓa yarda da cewar zaka iya zubawa wani ido ya cutar da ni ba balle kuma ace kai da kanka ne zaka aikata hakan a gare ni wallahi ba zan taɓa yarda ba koda kuwa dukka jikina kunnuwana amma sai gashi ka furta min hakan da bakinka. Da kanka kake warware min komai yanda ka tsara ka shirya kuma ka aiwatar dashi a aikace, ka bani kunya ka ci amanar yarda da yaƙinin da nake dashi a kanka ka watsa min ƙasa a ido mai cike da tsaku ka budulcewa alkhairin da nayi maka a rayuwa ta hanyar da ban taɓa tsammanin sa ba balle zato. Habib ƴar uwata ce Mina ita ɗin jinina ce domin ba'a canjawa tuwa suna duk inda yaje amma da ita ka haɗa kai ka cutar dani ka cutar da dukiyata ka ruguza min komai nawa wannan gidan gonan shi ne kaɗai gare ni Habib da shi nake riƙe maraicin mu da kuma namu yardan da nayi da kai ya sanya na zaɓe ka sama da kowa cikin kuwa har da gudan jinina Umar na ɗaura a wannan matsayin na bar maka ragamar komai ba tare da nayi maka iyaka da komai nawa ba".
Daga haka ya dakata saboda nauyin da ƙirjinsa ya yi masa ya dafe goshinsa da ƙarfi kafin ya ɗaura da"tabbas na ƙara yarda da ƙarfi da tasirin soyayya domin yana gusarwa da mai yinsa hankali har ya ingiza shi aikata abinda daga baya zai dawp yana cizon ɗan yatsa a yayin da lokaci ya riga ya ƙure masa, Habib kaje na yafe maka na yafe maka sai dai ina roƙonka da ka nisanta kanka da ni bana son ganin ka darasin da ka bar min a rayuwa kaɗai ya isa sanya zuciyata jinyan tsawon lokaci".
Baki buɗe Farouk da Abdul-aziz suke kallon shi da son ƙara tabbatar da abinda kunnuwansu suka jiye musu bakinsa ya furta kamar kalmar yafiya ga Habib ɗin.
"Yaya Saif babu yafiya tsakanin mu da wannan mutumin ya cutar damu cutarwa mafi muni da tabon ta ba zai goge daga zuƙatan mu cikin sauƙi ba. Mahaifiyar mu ce take can kwance a asibiti rai a hannun Allah ba ta san inda ganta yake ba balle wanda yake tsaye a kanta da wannan kasuwancin muke komai sai kuma salary ɗinka tunda ni ga yanda nake ke har yanzun babu wani aikin yi amma duk da hakan bai sanya shi tausayin halin da muke ciki ba ya haɗa kai da wata ya cutar damu. Wallahi Yaya Saif ko ka yafe nikam sai munyi shari'a da shi da ita wacce ta sanya shi aikata hakan, har yaushe zamu cigaba da yin wannan haƙurin har sai yaushe na gaji na gaji na gaji yaya Saif ya kamata mu nuna musu iyakar su".
Da hannun Saif ɗin ya yi masa alama akan yazo ya zo kusa dashi ya zauna, sai da ya kalle shi tsaf sannan ya kai hannunsa ya fara share masa ruwan hawayen da suke sauƙowa daga cikin idaniyarsa suna wanke masa fuskarsa a nutse yake faɗin"Umar ko Allahn da ya halicce mu muna yi masa laifi kuma idan mun nema yafiya da afuwarsa ya yafe mana balle kuma mu ƴan adam, mu bar shi da halinsa mu yi masa addu'ar shiriya idan ya nutsu ya tuba don kan sa ka tina furcin nan na Ummi da take cewa duk wanda ya rungumi haƙuri to haƙiƙa ya rungumi babban nasara a rayuwarsa kuma ba....".
"Kuma ba zai taɓa faɗuwa ba a rayuwa".
Saurin ƙarisa masa zancen Farouk ya yi yana fashewa da wani sabon kukan tare da ɗaura kansa kan kafaɗar Saif ɗin, hannunsa ɗaya ya sanya yana bubbuga bayansa a hankali cikin sigar lallashi tare da hura masa iska a fuskarsa.
"Tabbas ban cancanci yafiya ko gafara daga gare ka ba yallaɓai na kasance butulu mai mance alkhairi na ban kyautawa kaina ba banyi wa kaina adalci ba sam kaico na".
"Habib na ce na yafe maka bana son jin ka ƙara cewa komai ba laifin ka bane kai ma soyayya ce ta ja ka ta kuma ruɗe ka don haka ba zan ɗaura maka laifi ba ka nisanta kanka daga inda nake na roƙe ka".
A raunane ya furta zancen dake bayyanar da raunin har cikin ƙalbinsa yake yana rubtse idanunsa dake bada tabbacin gaskiyar abinda ya faɗa na rashin son ganin fuskar Habib ɗin don har yanzu zuciyarsa ƙona take yi masa. Kaɗa kan Habib ɗin Abdul-aziz ya yi ya fitar dashi daga cikin gidan sannan ya dawo inda ya bar su nan ya iske su suna rungume da juna wani iriyar kifiyar tausayin su ne ya caki dai-dai ƙalbinta na irin yanda ƙaddarar rayuwar su take zuwa musu a hagunce a ko yaushe.
Fitowa suka yi daga cikin gidan motar Abdul-aziz suka shiga yayin da suka bar motar Saif ɗin a wajen, shi ya yi driving ɗin su har suka isa gida sosai yake ƙara jinjina ƙarfin hali, juriya, jarumta da kuma tawakkali irin na Saifuddeen ɗin da ace shi ne shi babu abinda zai hana shi maka Habib ɗin da Mina kotu a koya musu hankali sai ya yi shari'a dasu koda hakan na nufin zai rasa dukkanin abinda ya mallaka idan kuwa aka tirsasa mishi ya yafe musu to shakka babu sai ya yi yawo tsirara a hauka ce. Sai gashi shi ya yafe musu da zuciya ɗaya ba tare da ya buƙaci koda ƙarfanfana daga gare su ba, har cikin bedroom ɗinsa suka raka shi suna zaune har ya shiga wanka ya fito idanunsa ya ware akan Abdul-aziz ɗin da yake zaune bashi da niyyar tafiya ya ce"kai baka tafi ba ka san kowa yanzu ƙarfe nawa?".
"Tafiyan nake son nayi sai dai ban gama yarda da cewar ƙalau kake ba shiyasa na tsaya".
Sai da ya zauna a bakin gado yana fuskantar Abdul-aziz ɗin kana ya ce"lafiyana ƙalau Abdul na gode da kularwaka a gare ni irin yanda kalmomin baki ba zasu iya furtawa, iyalinka tana buƙatar ta a irin wannan lokacin ya kamata kaje gida".
Sai da ya musguta kana ya ce"shikenan tunda ka ce haka take care of your self don Allah". Ya ƙare zancen yana miƙewa tare da hugging ɗinsa murmushi ya sakar masa kafin ya ce"but yaya aka yi ku san duk shirin Habib sannan ta wacce hanya ya shigo hannun ku?, nifa kun bani tsoro?".
Haɗa ido Farouk da Abdul-aziz suka yi suka yi murmushi kafin Farouk ya fayyace masa komai da ya wakana sa'ilin da suka je gidan gona sannan Abdul-aziz ya ɗaura da faɗin"batun shigowan sa hannu kuwa wannan aikina ne domin har ƙofan gidansa na sanya aka ɗauko min shi aka kawo shi inda ka same shi, yaran nan da suka tada hatsaniya har da sare-sare yayin zaɓen SUG su na sanya wannan aikin kuma suka yi yanda na umarce su ba tare da an sama wata matsala ba".
Sosai Saif ɗin ya gwalo idanun sa akan Abdul-aziz saying"meye kayi haka Abdul-aziz?, yaran da nake ta faɗi tashin ganin rayuwar su ta sauya su ka sanya wannan ɗanyen aikin".
"Kwantar da hankalinka ai ko yanzun su shiryu don sai ma da na gama sunanka sannan suka yarda suka yi aikin yanzu dai sai gobe in mu haɗu".
Kansa ya jinjina masa sam ya hana shi raka shi da ya yi niyya sai Farouk ne ya yi masa rakiyar ya dawo, alwala suka yi suka gabatar da sallan nafila raka'a biyu suka sallame ya kai duban sa kan agogon dake manne jiki wall ɗin bedroom ɗin dake nuna ƙarfe ɗaya saura mintuna goma ganin hakan ya sanya shi tisa ƙeyar Farouk izuwa ɗakinsa ya kwanta sai da ya tabbatar ya yi bacci sannan ya dawo nashi ɗakin.
Sam ya gaza runtsawa illa juyin da yake yi akan bed ɗin ya rasa gano manufar Mina na aikata masa hakan kamar yanda na rasa tina abu ɗaya da ya aikata mata a rayuwarta da take bayyanar da tsantsar ƙiyayyarta a gare sa ɓaro-ɓaro, sam bai ga laifin Habib ba balle jin zafin cin amanar da ya yi masa domin idan har ƴar-uwarsa ta jini zata iya aikata hakan a gare sa to ba komai bane don wani bare ya bada nasa gudumawar.
Sai bayan sahur ya sama bacci ranar shi ya wuni a wajen Ummi a asibiti ya ce Farouk ya zauna a gida ya huta, sai a lokacin ya sama damar tsiyayar da ƙwallar da suka turniƙe masa ruhi sosai ya yi kukan da babu mai lallashin sa tamkar shiɗe sai da ya yi don hakan sa ya tsagaita.
YA ALLAH KA RABA MU DA MAƘIYAN DA ZASU SHIGO RAYUWAR MU A SUFFAN MASOYA.
- 07038908713-
MATAN AREWA
(Book two)
© Maimunah Tijjani Iyam
_________________________________
Page 9⃣1⃣
Tsawon kwanaki uku maganar wa'azin da Mr Saif ya yi kawai ake yi abin gwanin ban haushi da takaici, a haka lokaci ya yi ta shuɗawa azumi na ta yi mana ban kwana da wasu da yawa daga cikin mu da