Showing 120001 words to 123000 words out of 171161 words

Chapter 41 - MATAN AREWA BOOK TWO COMPLETE PDF .txt

da sassafiyar nan Kulu?, ai nayi tinanin amintar dake tsakanin mu ya kai munzalin da idan naga Aisha tana aikata ba dai-dai ko a gidan wani na tsawatar mata balle kuma Yusuf take aure. Ko kuma a zantukan da ta labarta mikin ba haɗo miki da irin rashin kunya ta yi min cikin laffuzanta da kuma wanda naga tayi shi ƙuru-ƙuru akan idona ba?".


"Duk wannan bai dame ni domin da ba ki jan ƙafafunki ki je har cikin gidanta ba, babu yanda za'a kiga duk abinda kika furta tare da alƙanta hakan da rashin kunya".


Tsabar mamaki da ya tsaya mata a rai, shi ya hana Anty Binta cewa komai har ta katse ƙiran ba ta ce da ita komai ba. Sam ta kasa komawa baccin domin ko kaɗan bata tinanin akwai ranar da Hajiya Kulun da duk cikin ƙawayen ta fi kowa sanin sirrinta sama da kowa za ta yi mata haka ba, ta yi tinanin haɗa auren da tayi tsakanin Yusuf da Aisha sai dai ma ya ƙara hauhawa girmanta da kimarta a idonun Hajiya Kulun ba zai farashin sa ya yi faɗuwar tasa ba. Wunin ranar sukuku tayi shi da an taɓo ta sai bala'i da masifa ta ƙuduri niyyar koyawa Hajiya Kulu da Aisha hankali ta hanyar ba da su taɓa tsammanin sa balle zato.


Bayan sallan magrib ta ƙira Yusuf, zaune yake a gaban ta ta tisa shi a gaba tana bin shi da kallon da har zai da ya tsargo da kansa a nutse ya furta"lafiya kuwa Anty ko akwai wata matsalar ce?". Ƙatuwar numfashi ta sauƙe kana ta ce"ina kuwa lafiya Yusuf mahaifiyar Aisha ta ƙira ni tayi min tas tare da keta min rigar rashin mutunci, duk dai akan wannan abun da ya faru wancan zuwan nawab gidanka shiyasa na yanke shawaran na ƙira na faɗa maka cewar ko baka ganni a cikin gidanka ba ko kar kayi tinanin wani abu ne. Dole naja girmana a matsayina na babba in ce dai sai naje ai balle har tayi min rashin kunya ko kuma na gani a aikatace ko?, to ba zan ƙara taka ƙafata ko da ƙofar gidanku bane ku je can kuyi rayuwar auren ku cikin farin-ciki ku huta da takurar da aka ikirarin cewar ina yi muku".


"Haba Anty ai wannan hukuncin bai kamata ba, banyi tinanin cewar akwai wani maganar da zata zo a faɗa miki har ki janye daga zuwa inda muke ba Anty. Don Allah kar wannan zancen ya sanya ki yanke wannan hukuncin in sha Allah zan yiwa tufkan hanci tun da wuri ina mai ba ki haƙuri".


A faƙaice ta saki yalwatacciyar ɓoyayyiyar ajiyar zuciyar cikin burinta, a zahiri kuwa ƙara marairacewa ta yi tana faɗin"shikenan duk yanda ka ce". Haƙuri ya cigaba da bada har ta nuna mishi ya wuce da wayo ta riƙe shi har ƙarfe goman dare, sallan isha'i kawai ya fita ya yi ya kuma dawowa suka zauna da Mahmud suna hira kafin ya tafi.


A ƙofar gida ya iske yaya Auwal zai shiga hango sa da ya yi ya sanya shi dakatawa suka shigo tare, maman Hanan kawai suka iske a tsakar gidan tana karatun littafi ga wayarta da ta kunna ƙira'ar karatun al-qur'ani yana tashi sallamar da suka yi ya sanya ta dakatawa tare da ajiye littafin dake hannunta gefe guda ta miƙe tana yi musu barka da dawowa. Haɗe baki suka wajen amsa mata sai da suka zauna ta gabatar musu da abinci tare suka fara ci, yaya Auwal ya ɗan waiga haɗi da faɗin"ina take ita kuma?".


"Tana ɗaki wataƙil ta gaji ne shiyasa ta shige da wuri".


Sosai ran shi ya kuma ɓaci da ita don ya lura tun farkon zuwan ta gidan ba ta zama da maman Hanan ɗin, a zahiri take nuna kamar ƙyamar ta take yi dole ya dakatar da ita tun kafin wanki hula ya kai shi dare, sai da suka gama cin abincin ya yi musu sai da safe ya wuce nasu ɗakin.


Babu kowa a falon don haka kai tsaye ya nufi uwar ɗaka, kwance ya hange ta akan gado cikin shigar kayan bacci masu santsin da ko kaɗan basu taimaka wajen suturta jikinta ba, ƙafarta ɗaya kan ɗaya tana danna wayarta tare da sakin dariya har da riƙe ciki ko tantama babu ya san cewa chart take yi, da ko lokacin salla ne ya ratso tana wannan chart ɗin to sai ta kammala sannan ta tashi.


Sai da ya yi mata kallon tsaf ya tabbatar da cewar ba san da shigowar sa ɗakin ba balle tsayiwar da ya yi a kanta. Kansa ya jijjiga tare da wuce banɗaki wanka ya yo ya fito ɗaure da towel a jikinsa a wannan sa'ilin zaune ya tarar da ita tana wayar da suna haɗa ido ta birkice tare da kashe wayar bai ce da ita komai ba illa kayansa da ya zaro ya sanya, zama ya yi bisa kujera yana fuskantan ta.
Sai da ya cije leɓɓansa sosai kafin ya soma faɗin"kinyi salla ne?".
"Yanzu nake son na tashi nayi".


"Yanzu ƙarfe nawa?, kuma na tabbatar abubuwa wani abun da kika yi mai muhimmanci da ya wuce wannan danne-dannen wayar da har ya mantar da kai gaida ubangijinki. Kin san dai yanzu ke ba yarinya ba ce domin alƙalami ya hau kan ki, tashi kije kiyi kizo zamu yi magana".


Zumɓuro baki tayi tana ƙunƙuni sannan ta miƙe ta shiga banɗaki yana zaune inda ta bar shi ba tare da ya gusa ba, ta iske shi hijabi ta ɗaura akan suturan dake jikinta sannan tada sallan. Ƙuri ya yi yana bin ta har take gabatar da sallan sam ba nutsuwa a cikin ta balle daidaito yin shi take yi son ranta, kamar jira take yi tana yin sallama ta zare hijabin dake jikinta ta yasar gefe tana faɗi"wash ni wahala, ina jinka wani magana ka ce zamu yi don bacci na fara ji".


A dake ya furta"haka aka koya miki yanda ake yin ibada?".


"Ba koya min aka yi a bulayi na tsinci yanda ake yi har na iya". Bai yi mamakin jin furcinta ba domin ya san iya gaskiyarta kenan ta fayyace masa, gyara zaman sa ya yi kafin ya ce"za ki koma islamiyya nima idan ina gida na dunga koya miki wasu abubuwan". Kanta ta ɗaga masa tana lumshe idanu alamar bacci ya fara kawo mata ziyara, lura da hakan ya sanya shi ɗaurawa da"ina so ki zamto mai iya ɓoye sirrinki gidan aurenki ba ko wani abu bane zai faru ki ɗeba ki faɗawa mahaifiyarki, wani abu ni dake zamu iya sasantawa a tsakanin mu. Idan lamarin ya sako da ƴan-uwana a ciki shima babu buƙatar ki sanar da ita idan ba kamawa ya yi ba ko menene ki tunkare ni ki sanar dani in sha Allah zan yi maganin abun. Kuma ba wai ina nufin komai ne bai dace ki sanar da ita ba a'a wasu abubuwan dole ta ji a matsayin ta ta mahaifiya a gare ki, ina fatan kin fahimce ni?".


"Ban fahimci ka ba wani abun aka ce maka na kwasa na faɗa mata?, ko meye shine ban gama ganewa ba?".


"To shikenan duk yanda kika fahimta hakan nake nufi, na hama magana mu kwan lafiya". Duk ragowar zancen da ta ɗaura dashi bai tsaya sauraron ta ba illa ma ficewa da ya yi ya koma falo ya yi kwanciyar sa bata haƙura ba ta biyo shi har nan tana masa hargagi a kai.


"Ai kwanciya bai kama ka ba malama sai ka tashi ka faɗa min abinda aka ce da kai na faɗawa mahaifiyar tawan da ya kasancen sirrin gidanka". A'uziya kawai yake maimata a cikin ransa da yake tafasa da tunzura shi akan ya tashi ya yi abinda zai iya yin dana sanin sa daga ƙarshe, nan ma bai tanka mata sai ma tashi da ya yi ya koma ɗaki tare da murzawa ƙofar key ya yi kwanciyarsa cike da ƙonar zuci.


MATAN AREWA


(Book two)


© Maimunah Tijjani Iyam


____________________________________________


Page 1⃣0⃣2⃣




Haka lokaci ya cigaba da gudu rayuwa tana juya tare da zuwa da abubuwa da yawa da ya ƙunshi na farin-cikin da na kishiyar hakan. Wasa-wasa auren su ya yi wata guda cif sai dai har izuwa yanzun babu jituwa balle fahimtar juna a tsakanin su, duk yake ƙoƙarin gujewa duk wani abun da zai sanya shi tauye mata haƙƙinta yana yi, abu ɗaya har yanzun ya kasa koda gwada yin sa shine kusantan ta sam ya gaza yin hakan da ya yunƙuro da nufin hakan sai ya ji kamar an zare masa laka a jikinsa.


Zaune yake gaban Anty Binta tare da Aishan da suka zo tare, idanunsa akan kofin ruwan da ta ajiye musu a gaban su ya kasa ɗagowa jinsa yake yi gabaɗaya wani iri da ya kasa kama abu guda da sunan shi yake damunsa, a karo na barkatai ya sauƙe ɓoyayyiyan ajiyan zuciya tare da ɗago kansa ya furta"Anty daman na kawo ta ne ta ba ki haƙuri akan abinda ya faru, sannan ina so na koma makaranta saboda jarabawan da zamu fara".


Musgutawa tayi tana gyara zamansa a bisa tabarman da ya bada damar fuskantar su sosai, kana ta soma cewar"haƙuri game da meye kenan Yusufa?, maganar makaranta kuwa ai bani da ta cewa sai dai nayi maka fatan alkhairi Allah yasa a fara a sa'a kuma a kammala cikin nasara".


"Amin ya Allah, Anty haƙuri mana akan wancan batun da ya shiga tsakanin ku da Aisha, tun lokacin naso zuwa da ita Allah bai nufa ba sai yanzu sharrin sheɗan ne".


Wani murmushi tayi tana tsayar da ƙwayar idonta akan Aishan da tun zuwan su idanunta yake a kan wayarta da take latsawa, a hakimce ta furta"to ina sauraran ta".


"Ki bata haƙuri".


Cikin sauri ta ɗago idanunta ta zube su akan sa cike da son ƙarin bayani ta ce"bangane ba wani haƙuri kenan?".
A dake ya furta"duk abinda na faɗa ba ki ji shi ba kenan?".


"Ko da naji to ina buƙatar ƙarin haske, don ba zai yiyu na sudda kai na bada haƙuri akan abinda ban aikata shi ba never wallahi".


"Na san daman za'a rina wai an saci zanin mahaukaciya ku tashi ku bani waje, duk sanda ta shirya bada haƙurin na gaske ina maraba daku".


Cikin kaurarran murya ya ce"ki bata haƙuri na ce ko?", Idanunta tsaf cikin nashi bada da tsoro ko kuma fargaba ba balle taji kwarjinin da yake yi mata a duk lokacin da tayi yunƙurin kallon cikin idonsa ba ta ce"ƙarya fa da ciwo ba zan iya bada haƙuri akan abinda ban san shi b....". Tsawar da ya kurma mata ita ta tilasta mata haɗiye ragowar zancen da ta ɗauko ba tare da ta dire shi ba, idanunsa a nutse yake faɗin"kar ki tunzura ni nayi abinda ban taɓa aikatawa ba a tahirin rayuwata cikin duniya watau dukan mace, just ki bata haƙuri kawai akan abinda ya shiga tsakanin ku na tsaɓani".


Tunin idanunta suka kawo ruwar ƙwallar tsabar takaicin da zafin tsawar da ya yi mata da take ji har cikin ƙololuwar ranta, muryarta a shaƙe ta soma faɗin"kiyi haƙuri Allah ya huci zuciyarki".


Wani murmushin ƙasaita mai ɗauke da ɓoyayyayun manufofi Anty Binta ta saka da har sai haƙwaranta suka bayyana, a hakimce gami da izzan nuna isa da cewar ta kai ta ce"Hmm Aisha kenan wani abu guda da nake so ki gane shi yaro yaro ne kuma ko ya hau tudun dala ba zai hango abinda babba ya hango ba, ba komai ya wuce Allah ya yi muku albarka".


Shi kaɗai ya amsa mata da kalmar amin, banda Aishan da take yarce ƙwalla da gefen gyalenta. Hakan ya bada damar ɗaurawa da"yauwa yaushe zaka tafi makarantar?". Sai da ya gyara zaman sa kana ya ce"wani sati in sha Allah". Jinjina kanta tayi haɗi da faɗin"Allah ya kaimu", ya amsa mata da amin a taƙaice hira suka ɗan taɓa kafin ya yi mata sallama suka koma gida. Tunda ta shiga ɗaki ta yasar da gyale da ɗaurin kallabin dake kanta take ta faman safa da marwa cikin ɗakin riƙe da ƙugunta da take jijjiga shi lokaci zuwa lokaci.
Ajiyan zuciya mai nauyi ta sauƙe tana zama bakin gado tallafe da kuncinta, rurin da wayarta ta soma shi ya dawo da ita hayyacinta da ga tufka da warwaran da take yi a zuciyarta.


Sai da ta kuma sauƙe ƙarƙarfan ajiyan zuciya kana ta ɗaga ƙiran tare da kara wayar a kunnenta, a sanyaye ta ce"ina jin ki shegiyar yaya aka yi ne, meye yaje gudana babu ni?". Shewa aka saka mai matuƙar sauti daga ɗaya ɓangaren kafin aka ce" shegiyar ai ke dai bari kawai, ai ana yi a nan babu ke amma kafin nan ya nake jin muryanki wani iri ko dai ba ki da lafiya ne?". Ajiyar zuciyan ta kuma saka a karo na biyu ta ce"ke dai bari Azima wallahi yau ina cin ɓacin ran da rabon da na shiga makamancinsa har na mance yaushe gamo".


Ashariya ta lailayo ta maka kafin ta ce"lasa min shegiyar meye going ne?".
Cikin wani baƙin-ciki da takaicin da ya bayyana ɓaro-ɓaro a cikin muryarta take cewa"ke dai bari kawai wallahi wannan yayar mijin nawan nan ce ta uzurawa rayuwata ta hana ni sakat ta hana ni rawar gaban hantsi, komai nake yi idanunta suna a kaina ni bata san ma cewar ba mijin bane a gabana ko auren nan ma da nayi. Nayi shi ne domin ya zamto min garkuwa daga ƴan tsegumi da tsurkun da suke yawo dani a cikin gari cewar ina yawon ta zubar, ba cin haka meye na nema na rasa namiji ne ni yanzu ba shi ne a gabana ba don babu irin wanda ban taɓa ɗanɗanawa ba".
Dariya Azima ta saka a karo na biyu haɗi da cewa"wallahi ni ke ce ma kika ɗura min takaicin da ya riƙe min ƙirji, shine kika zauna kika kawo ido kika sanya mata tana yi miki duk cin kashin da ta ga dama kinyin kurum kina kallonta, to ki saurare ni da kunnen basira da fahimta ki fito mata a mutum ki fito mata cikin aihinin suffarki ta Aishan da wannan fuskan da kike yi a gida ba Hajiyata, ai shi ƙarfe baya jin dukan komai sai na ɗan-uwansa ƙarfe don haka tun wuri ki mai da ita kan kashinta ki gyara mata zama kafin linzamin dokin ya suɓɓuce daga hannunki".


"Azima makircin matar nan ya wuce tinani da hangenki, domin tun bani da yawo na santa kuma suke aminta da Umma duk wani makirci da ƙulle-ƙulle tare suke shirya shi. So nake na ajiye duk wani alaƙar su da Umma na keta mata rigar mutunci na gasa mata aya a hannu ki bani shawaran hanyar da zan yi don Allah tawan".


"Ai kuwa dai kin kawo kuka ne gidan mutuwa, kayanki ya tsinke a gindi kaba ƙawata, duk da ba mijin bane a gabanki yanzu amma dole ki nuna cewar kina son shi, kulawa da tattaninsa a gabanta ki dunga manne mishi da ƙirƙiro wasu abubuwan a kan idonta. Kar ki bari ta gano lagonki ki fara jarraba hakan domin shi ne plan ɗin mu na farko sannan da ƙissa da kisisina ki san hanyar da kika bi kika tusa soyayyar ki a cikin zuciyarsa kiyi baje-baje ta yanda ko umarni ta bashi akan shi wannan soyayyar zai rufe masa ido ya kasa yi mata biyayya, ƙawata ai ba boka ba malam za ki nuna mata mai laya ya kiyaye mai zamani".
Shuru na wucen gadi Aisha tayi kafin ta bushe da dariya tare da jinjina ƙarfin basira irin na Azima, sallama suka yi tare da zabga mata godiya gami da bata tabbatacin cewar duk abinda ta shawarce ta dashi zata aikata.


Haka nan yau na wayi gari gabaɗaya banda wani cikakken kuzari a jikina a sanyaye nake aiwatar da komai, ina share ɗakin Umma yayin da ita kuma take zaune bakin gado tana tasbihi cike da kulawa ta ce dani"Na'ima yau kuwa lafiyarki?". Sai da na sauƙe ajiyan zuciya na ce"lafiya ƙalau kawai bana jin daɗin jikina ne".
Ina iya jiyo ita ma ajiyar zucin da ta saka kana ta furta"to ki bari kije ki sha magani mana", kaina kawai na ɗaga mata na gama sharan na koma ɗakin mu ina zauna tinanin wannan matashiyat budurwan da zaman mota ya haɗa mu da ita ya shiga addaban rai da ruhina daren jiya har cikin mafarkina na ganta, na gaza gane dalilin da ya sanya tinaninta da na halin da take ciki ya maƙale mini a rai tamkar tsayiwar ƙayar kifi a maƙoshi. Haka na wuni zum da wannan tinanin bayan munyi sallan isha'i su Abba suka ce mu haɗu a sashinsu suna buƙatar ganin kowa da kowa, tunin duk muka hallara a falon har da Hajiya da Goggo Jummai zance ne game da auren Firdau'si, Ikilima sai kuma Salma da ana ambatan sunanta naji ƙirjina ya buda da matuƙar ƙarfi.


Bayani Baba ya gabatar game da bikin da ba a sanya shi dama da nisa ba, sati uku kacal ya rage don su daman angwayen Firdau'si da Ikilima a shirye suke da a son ransu ne ma tun kafin azumi anyi bikin an gama sai dai a lokacin basu kai ga kammala haddan su na littafi mai tsarki ba, tun daga wajen aka fara yi musu nasiha da nusar dasu wasu muhimamman abubuwan bayan nan Baba ya yi musu zazzafan gargaɗin cewar kar ya kuma ganin wata daga cikin su ta leƙa koda ƙofar gida ne indai ba saurayin da zata aura bane ya zo shi su tsaya ta zaure.


"Amma Baba ban raina tinaninku ba game da haɗin auren tsakanin Salma da Malam Mamman ba, amma sai nake kamar ga yarinya ƙarama mai ƙaranci shekaru irin na ta irin wanna auren akan fuskanta manyan ƙalubale".


Furcin yaya Majid kenan da naji su ya faɗe su tar tar tamkar ya tsaga ƙirjina yaga abinda ke ƙunshe cikin tokar naman zuciyana kenan. Shuru ya ratsa falon na wucen gadi kafin ɗaga daga cikin iyayenmu su amsa, doguwar tsaki mai dogon zangon da Umman Salma ta tsirka ya jawo hankulan kowa izuwa gare ta.


Fuskarta a cukurkuɗe take faɗin"bangane akwai manyan ƙalubale ba?, to bakinka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login