Showing 6001 words to 9000 words out of 171161 words
Chapter 3 - MATAN AREWA BOOK TWO COMPLETE PDF .txt
da ƙirjinta da tun sanda asirin su ya tono yake bugawa da sauri da sauri. Dole taje gidan su Na'ima domin ta gaza samun kwanciyar hankali ko bacci bata taba iya yi gani take yi tamkar zata tona musu asiri.
A gaggauce ta kammala dukkan aiyukanta, tayi shirin fita bata buƙatar da sanar da yaya Auwal balle neman izninsa yayin fita, domin tun dawowar ba wani magana mai tsawo da ta shiga tsakanin su. Biyayyar iyaye ya tirsasa mata dawowa gidansa amma da tayi kanta ne kam ta gama aure dashi har abadan abada domin sanin da tayi mai halin baya canjawa.
Da ƙyar nayi iya tashi wayewar safiyar ranar saboda tsananin zazzaɓi mai haifar da shigar sanyi har cikin gaɓoɓi da ya lulluɓe ni. Na kasa cin komai ga wani kasala da ya sauƙar mini ko kaina bana son ɗagawa, balle buɗe idanuna da nake jin su sun yi mini wani mungun nauyi.
Sashin Hajiya Babba naje na gaishe ta na iske su Abba ma dukkansu sun zo gaishe ta suma na gaishe su, sosai duk suka ƙara yi mini nasiha mai ratsa jiki da har sai da nayi ƙwalla. Baba sai ci mini albarka yake yi. Sashinmu na dawo na tarar da yara zasu tafi makaranta Nurain da ake ta gardama dashi akan ba zai je makarantar ba ya taho da gudu ya rumgume ni.
"Anty Na'ima ki cewa Umma ni ba zan je makarantar ba na gaji, ni na gama makaranta ai ga yaya Majid ma baya zuwa sai dai ya yi ta hutawarsa a gida".
Murmushin dole na ƙirƙiro na dasa a kumburarriyar fuskata kamar kwaɓin fanken da ya tashi fun-fun, na durƙusa a gabansa tare da riƙo hannunsa ina kallon fuskarsa nake faɗin"Nurain ai shi ma yaya Majid ya gama ne shiyasa kake ganinsa a gida, kai ma idan ka dage kwana kaɗan zaka ga ka kama ka zama babban mutum har kayi gemu". Sosai ya sheƙe da dariya yana rufe fuskarsa alamar kunya ya ce"Gemu sai ka ce Baba".
Nima dariyar nayi kafin na ce"e mana".
"Kema yanzu kin dawo gidan Anty Na'ima?".
Kafin na sama zarafin bashi amsa na jiyo muryar Daada tamkar a tsakiyar kaina tayi maganar"Dawowa na dindindin kuwa, ai ita da zaman gidan kam yanzu sai kai ma ka gaji da ganinta tunda ta kaso auren ta dawo". Ta ƙare zancen tana tsirkar da tsaki tare da miƙewa ta fara haɗa kwanukan wanke-wanke. Murmushi kawai nayi wa Nurain na gyara masa maɓallin wuyar rigarsa na raka shi bakin ƙofar fita, ni kuwa na wuce ɗakin Ummata tana zaune bisa gadonta na ƙarfe mai rumfa na iske duk sallamar da nayi bata ji shi ba balle zaman da nayi kusa da ita. Sai da na riƙo hannunta kafin ta kallo ni sai da na sausauta amona na ce"Umma tinanin meye kike yi haka?".
Sai da ta kuma kalle ni sosai kafin ta furta"Na'ima tinanin makomar rayuwarki nake yi da kuma na ƴar-uwarki. Tun jiya Abbanku ya sanya Majid ya ƙira Yusuf amma wayarsa bata tafiya balle muji dalilin sakin". Saurin katse ta nayi da faɗin"Dan Allah Umma kar ki sanyawa ranki damuwa game da wannan, tun muna ciki mala'iku suka rubuta abinda zai wakana a rayuwarmu don haka mu miƙa lamuranmu ga Allah".
Na ƙare maganar ina kwantar da kaina a bisa kafaɗarta, tunin naji hawayen sun ciko mini ƙoramar idanuna ban san meya ke dakatar dani daga sanar da ita cewar ina ɗauke da juna biyu ba. Ambaton sunan yaya Yusuf da tayi suka taimaka wajen ƙara gudun famfalaƙin da zuciyata take yi, lallashina tayi kafin ta fice na kwanta lamau ina jin zazzaɓin yana ƙara shiga ta.
Ban san sanda bacci ya yi nasarar ɗauka ta ba, sai ji naji kamar a mafarki Anty Zakiyya tana ƙiran sunana. Na buɗe idona a hankali tar a kanta.
"Kin yi baƙuwa a waje".
Da kallon mamaki na bita ina ƙoƙarin tashi zauna na ce"wacece?".
"Maman Hanan".
Figigit baccin dake idona suka wartsake sakamakon sunan da naji ta ambata, ta fice tana ƙara jadadda mini na fito tana jira na. A sanyaye na fito na iske ta zaune a barandan ƙofar ɗakin Umma suna zaune har da goggo Jummai kallo ɗaya nayi mata daga haka ban koma gigin kallon inda take zaune ba. ayi wa kaina mazauni kusa da Umma kafin na gaishe ta tayi saurin taran numfashina da faɗin"ina kwana Na'ima".
"Lafiya ya gidan?".
Na faɗa ba tare da na ko kallin inda take ba. Sai dai ina jin idanunta a jikina alamar har yanzu ni take kallo, goggo Jummai ta miƙe haka nan ma Umma ta fara ƙoƙarin tashi ta bamu waje. Ya rage daga ni sai ita ta kuma cewa cikin ƙasa-ƙasa da muryarta"Na'ima nazo ne muyi magana". A gajarce na furta mata"ina jinki tafi kai tsaye ga abinda ya kawo ki".
"Maganar sirri ce zan so mu keɓe sannan muyi ta".
Na ɗan cira kaina ina kallon tsakar gidan, duk matan gidanmu suna zazzaune a ƙofar ɗakunan su sun zubo mana na jiyamun su. Kaina na ɗaga mata kafin na miƙe na shiga ɗakin Umma ta biyo bayana tare da ɗan tura ƙofar. Muka zauna muna fuskantar juna mintuna uku a tsakani babu wanda ya ce komai a tsakanin mu kafin na jiyo sauƙar numfashin da maman Hanan ta sauƙe a ɓoye kafin ta soma cewar"Na'ima na shiga fargaba da tinanin za ki tona min asiri". Ɗaga mata hannu nayi haɗi da faɗin"Yanzun ma kar ki saki jiki akan zan cigaba da rufa miki asiri. Domin ban taɓa tinani za ki aikata irin hakan ba, bayan ina da tabbacin kisan haramcinsa a addinance haka nan kuma cutarwa ne ga lafiyarki". Maimakon ta bani amsa sai kuka ta fashe dashi sosai take kukan da a zamana da ita ban taɓa ganin tayi ko makamancinsa ba ko lokacin rasuwar Hanan kuwa.
Riƙo hannuna tayi"Zan so ki bani lokacinki domin na sanar dake dalilina na aikata wannan abun kafin ki yanke min hukunci". Kaina kawai na ɗaga mata don kukan natan ya gama kashe mini jiki.
"Na'ima kamar yanda na sanar dake yanda aurena ya kasance da Auwal har ma da irin abunda na iske a cikin gidansa bayan auren. To yau zan ƙara faɗaɗa miki labarin Allah ne shaida ban taɓa jin daɗin aure ba har izuwa yanzu da muke wannan maganar dake, Auwal bai san menene aure ba balle sanin haƙƙoƙin mace akan mijinta. Bai damu da bani haƙƙina ba na sha kai kokena gidanmu amma sai a dawo dani da kalmar nan ta haƙuri ba tare da sun saurari damuwata ba, maman Anwar ita ta fara fahimtar yanayin da nake ciki kuma tayi silar shiga ta ƙungiyarmu ta ƴan lesbian da yake ƙunshe da mata masu irin damuwata, a gidanta ko gidana a nan muke ɓarje gumin mu, tun daga lokacin na fita harkan Auwal idan ya neme ni don kansa idan kuwa bai nema ni ba zan wanke ƙafana naje gidan maman Anwar na samarwa kaina nutsuwa. Wanda ina da yaƙinin komai na aikata Auwal ne sila, kinsa dalilin dawowa ta gidan Auwal?".
Jijjiga mata kaina nayi ta ɗaura da"Saboda ba zan iya rayuwa ba maman Anwar ba haka nan ƙungiyarmu ba zasu bar ni nayi nisa dasu ba. Don da yawa da suka nemi fita an haukar dasu. Yanzu ki gaya min laifina Na'ima laifina ne ko na Auwal da ya kasa bani haƙƙina?".
MATAN AREWA
(Book two)
© Maimunah Tijjani Iyam
_____________________________________
Page 3⃣7⃣
Sosai jikina ya ƙara sanyaya tamkar kazar da aka jefa da gishiri. Babu abinda yake fita daga idaniyata face hawaye kamar an buɗe burɗaɗɗan famfo wani tausayin halin da ta tsinci kanta suka ƙara narƙar mini da raunananniyar zuciyata. Sosai nima na riƙe hannunta da yake cikin nawa gam kafin nayi ƙarfin halin cira kaina na kalla fuskarta da har yanzu hawaye basu bar gudana ba, saurin kawar da nawa nayi domin wani kifiyar tausayinta da ya sauƙa dai-dai ƙirjina tare da yin nasarar tarwatsa ƙalbina.
"Maman Hanan kiyi haƙuri haƙiƙa yaya Auwal yana da kamasho akan duk halin da kika tsinci kanki a ciki. Amma hakan ba zai zama hujjan da za ki kare kanki dashi ba a gaban ubangiji, kina da damar da za ki kai ƙorafi ga waliyanku a raba auren domin kina cutawa, ko kuma ayi zama a tambaye shi ko bashi da lafiya ne ko kuma matsalar daga gare ki ne. Bai kamata don ya kauce hanya ba kema ki bauɗewa hanyar Allah".
Cikin matsananciyar kukan da ya fara cin ƙarfinta ta watso mini idanunta tare da jarumar furta mini"Na'ima Allah ya sani kuma zai shaide ni nayi iya ƙoƙarin kame kaina daga faɗawa halaka amma abinda yafi ƙarfina, macece ni fa mai lafiya kuma bai buƙata. Nima ba a son raina nake aikata hakan ba shin kin san adadin sandan nake kuka da hawayen idaniyata a duk sanda na aikata wannan abun?. Nayi kuka na roƙi Allah ya yafe min amma sai na ƙara komawa ruwa, ba ruwan Auwal da halin da zan shiga iyayena kuwa na faɗa miki mahaifina Allah ya yi masa rasuwa tun kafin nayi aure mahaifiyata kuwa tsufa ya cim mata komai sai anyi mata ba zan iya tunkaran ta da damuwata ba, sai dai yayuna mata biyu da kuma ƙanin mahaifinmu nasha kai kukan gida amma an gaza saurara balle ƙoƙarin fahimtar halin da nake ciki. Wallahi na rantse miki har da sarkin dake busan numfashi wanda raina yake hannunsa MATAN AREWA da yawa sun zamo karuwai a cikin gidajen aurensu, dalili rashin biyan buƙata daga mazajen na sun. Wasu kuma sun bi irin layin da nayi wasu kuwa hakan tayi sanadin rayuwar su gabaɗaya. Ba ko wasu iyaye bane suke jin damuwoyin ƴaƴansu da yawa sun fi amfani da kalmar haƙuri gare su fiye da zama dasu domin sauraran damuwarsu".
Wani kukan ta kuma fashewa dashi da ƙarfinsa da sautinsa ya zarce na da, babu shiri na runtse idanuna ina jin sautin kukan natan yana ratsawa har cikin kwanyata, kifiyar tausayinta da ya soki ƙalbina yana watsa dafinsa ga ragowar sassan jikina.
Wasu irin al'umma muke rayuwa a cikin su?, wanda babu tinanin mutuwa a rayukansu balle fargaban haɗuwa da mahaliccin su. Meyasa mazan arewa suka taɓarɓare haka suke zamtowa silar faɗawar matansu izuwa halaka?. Bayan sun manta da wannan zancen na fiyayyan halitta da yake faɗin ku zamo kawunan ku daga wuta a wani faɗin Allah maɗaukakin sarki yana cewa ku tarbiyar da ƴaƴanku da matanyen ku hakan zai zamo silar shigar su al'janna ya kuma kishinge su daga faɗa wa jahannama. Muryar maman Hanan suka yi nasarar dawo dani duniyar zahiri daga tafkin kogin da nake linƙaya a cikinsa ruwa yana ƙoƙarin cim mini har wuya.
"Ba zan roƙe ki akan ki rufa min asiri ba yanzu shawara ya rage ga mai shiga rijiya. Roƙo na gare ki bai wuce ki taya ni da addu'a ba Allah ya tsamo ni daga wannan ƙazantacciyar rayuwar da bata da maraba da ta dabbobin da ubangiji bai yi su da lissafi ba, balle bambamce tsakanin mai kyau da marar kyau".
Tagwayen ajiyar zuciyar na sauƙe ina kamo leɓɓena na ƙasa, na ce da ita"Ba zan tona asiri ba waye ma zan tunkara da maganar?, tunda ni kam shan ruwana ya ƙare cikin gidan ina miki addu'a Allah ya yaye miki. kema kuma ki cigaba da addu'a ki kuma yi ƙoƙarin nisanta kanki da maman Anwar, ki kuma ƙara neman kusanci da Allah". Zaro idanu tayi kafin ta ce"kina nufi ko Ummarki ba ki sanar mata ba?".
Kaina na ɗaga mata ina ɗaurawa da"Ban faɗa mata ba domin ban ma sama nutsuwar hakan ba". Ina iya jiyo ajiyar zuciyar da ta sauƙe a jere a jere kafin ta furta"Na gode kuma in sha Allah nayi miki alƙawarin daga rana mai kaman ta yau zan yi ƙoƙarin gyara rayuwata".
"Allah yasa".
"Amin dan Allah Na'ima idan Yusuf yazo gidanku ki saurare shi wallahi wallahi ya yi nadama aihun, idan kika gan shi sai kin tausaya masa a kwanakin nan ba kiga yanda ya lalace ba".
Shuru nayi mata ina kawar da kaina gefe guda, a ƙoƙarin hana ta hango ƙwallar da suka wadaci idaniyata, Allah ya sani yanzu ko sunan yaya Yusuf bana son a ambata mini balle azo mini na maganarsa duk da kuwa idan na ce bana sonsa nayi babbar ƙarya. Amma dole na danne na kuma yi ƙoƙarin fige shi a raina tunda bashi da wani amfani yanzu a gare ni. A raunane cikin rawar murya da sarƙafewar harshe na ce da ita"Dan Allah maman Hanan ki daina yi mini maganarsa wallahi zuciyata tafasa take yi, idan da sanin shi kika zo nan to ko tabbatar masa da cewar babu ni babu shi har abada. Domin shi ya zamto silar datse duk wata alaƙar dake tsakanin mu, ko a hanya ya ganni kar ya yi gigin soma yi mini magana. Ƴarsa ko ɗansa kuma da yake cikina ko yau na haife shi zan damƙa masa abinsa idan ya ga dama ya kai jeji ya yasar ruwansa ne". Na ƙarƙare zancen ina haɗe hannayena biyu alamar roƙo, haƙuri ta bani tare dayi mini alƙawarin ba zata ƙara zuwar mini da maganar ba, sai da tayi sallan zuhr kana ta tafi iya ƙofar sashinmu nayi mata rakiya na koma.
Daren ranar gabaɗaya ban runtsa ba sai faman juyi nake yi ban san sanda hawaye ya fara sauƙo mini ba sai jin ɗumin su nayi suna gudana bisa kuncina na saka hannu na kawar dasu. Ganin baccin yaƙi ziyarta ta ya sani tashi nayo alwala nazo na tada salla, na daɗe ina sallan har sai da naji ƙafafuna sun yi sanyi laƙwas na sallame. Na shiga jera kirari ga ubangijina kafin na fara nemawa kaina sauƙi daga ƙuncin da na tsinci kaina a ciki. Washe gari da yammaci Hajiya ta dawo daga tafiyar da nayi a bakin Anty Zakiyya naji tana faɗa wai taje biki gidansu. Ina zaune a ɗakin Umma ta aiko ƙira na, na tashi naje tana ɗakinta tana fuskantar ƙofar shigowa na zauna tare da gaishe ta bata amsa ba illa kallon da take bina dashi har sai da na tsargu da kaina sai can ta ce"Na'ima yanzu nake sintar zance wai aurenki ya mutu?".
A sanyaye na ɗaga mata kaina alamar e, ta kuma faɗin"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un daman na san Binta ba zata taɓa barin ki kisha ruwa ba a cikin gidan nan. Barin ki da tayi ma har kika kammala wannan karatun ɗaurin talala tayi miki ta yanda in ta tashi sakar miki nata abin zai gigita ki. Wallahi Binta makira ce ko wannan sakin ma na tabbatar da saka hannunta a ciki domin babu abinda ƴan-uwan nan nata zasu yi ba tare da sun nemi shawararta ba".
"A'a Hajiya kar mu ɗauki alhakinta akan wannan lamarin, saki kam ai bata da ikon sakar musu matansu. Su kaɗai suke da ikon hakan don haka ra'ayin kansa ne kamar ya faɗa ya gaji da zama da ni".
Da sauri na miƙe na fice daga ɗakin ina danne kukan da yake shirin kubce mini. Umma da yaya Majid na iske a ɗakin ko sallama ban yi ba na faɗa kan gado ina sakin kukan da ya turniƙe mini rai, wai daman haka ko wacce macen da ƙaddarar rabuwan aure ya faɗa mata take ji?, ko kuma nawa ne kawai ya bambamta don yazo mini a sa'ilin da ban yi zato ba.
"Tashi ki zauna".
Naji muryar yaya Majid raɗau a masarrafan ji na, ban yi musu na tashi na zauna dai-dai sanda Umma take ficewa daga ɗakin idanunta taf da tarin ƙwalla da kallo na raka ta, ina ƙara girmama tausayi da ƙaunar dake tsakanin ƴa da uwa. yaya Majid ya dawo kusa dani ya zauna kafin ya ce"Har sai yaushe za ki ɗauki ƙaddarar da ta faɗa miki Na'ima?, haka kika fi so kullum Umma na zubda hawaye akan damuwar da kika ƙwallafa a ranki?, akan ki aka fara rabuwar aure ko akan ki za'a ƙare?. Ƙanwata ki yayyafawa zuciyarki ruwan sanyi idan wani ciwon ya same ki yaya zamu yi?.Don kin rasa Yusuf ba hakan ne ke nufin kin rasa soyayya gabaɗaya ba Allah ya canja miki da mafi zamowa alkhairi ga rayuwarki". Can ƙasan maƙoshina na ama da"Amin".
"Ina ta ƙoƙarin neman shi a waya amma bana samun shi, har makaranta naje neman sa aka shaida min baya zuwa yanzu. In sha Allah komai ya kusa zuwa ƙarshe kinji?". Kaina na ɗaga masa ya yi ta lallashina da kalaman kwantar da hankali har nayi sanyi.
Dole ko don damuwar da damuwata take sanya Umma, Abba da ƴan-uwana na rage kukan da nake yi, sai dai ba zan hana kaina yin na zuci ba wanda na kan ji ana faɗin yafi ƙuna da raɗaɗi. Ranar da na cika sati ɗaya cur a gida, na tashi da wani zazzafan zazzaɓi ko idona bana iya buɗewa saboda sarawan da kaina yake yi. Jikina babu kuzari saboda ba wani abincin kirki nake iya ci ba bana samun cikakken baccin da zan sama nutsuwa. Nayi wani irin mummunan rama sai da hajiya Babba tayi mini nasiha sosai. Kullum cin fuska, ba'a da gugan zanan matan gidanmu gare ni ƙaruwa yake yi ba tare da la'akari da halin da nake ciki ba balle su tausaya mini. Da ƙyar na miƙe akan ƙafafuna da suke rawa bisa tilastawa Anty Zakiyya cewar lalle na fito naci abinci sannan na sha magani, tana riƙe dani har muka fito waje take kaina ya fara juya wani jiri ya kwashe ni nayi baya na faɗi babu gaɓɓar dake motsawa a jikina balle alamar numfashi.
MATAN AREWA
(Book two)
© Maimunah Tijjani Iyam
_______________________________________
Page 3⃣8⃣
Ihu da kururuwan da Anty Zakiyya ta tsala, shi ya sanya fitowar su Abba daga sashin su har suna karo da juna haka nan ma Hajiya Babba da goggo Jummai.
"Meke faru?".
Baba ya yi maganar a riɗime nuni Anty Zakiyya tayi masa dani da nake yashe a ƙasa tamkar matacciya, Ummata tana daga ƙofar ɗaki ta kasa ƙarisowa sai goggo