Showing 75001 words to 78000 words out of 171161 words

Chapter 26 - MATAN AREWA BOOK TWO COMPLETE PDF .txt

babu abinda bai ji ba wayar akan sa ne da ake tsara yanda za'a yi maganinsa a cikin jami'ar, ba yau ya saba jin irin wannan ba don haka wannan ma bai bashi mamaki ba. Sallama ya yi ciki ciki tun kafin ya amsa ya bashi iznin shigowa ya ƙarisa shiga cikin ofishin.


Da kansa ya ja kujera ya zauna tare da harɗe ƙafarsa ɗaya kan ɗaya yana ɗan murza zoben dake saƙale a yatsarsa ta tsakiya dake hannunsa na hagu, shuru ya ɗauki cikin ofishin na tsawon daƙiƙun da ba zasu gaza biyu ba cikinsu babu wanda ya yi magana, sai dai ta gefen idonsa yake ganin hararan da malam Daudan yake banka masa a faƙaice kafin ya saki tsaki mai dogon zango ya ce"meya kawo ka nan ko akwai wani abun da baka faɗa min bane ka dawo yanzun ka faɗa min?"


Shafa sajensa ya yi da ya yi wa tsukakkiyar fuskarsa ƙawanya ya ce"yeah bayan ka tafi ne na canja shawara, no problem ka turo min yarinyar tomorrow evening".


Ya ƙare zancen yana miƙewa tare da zura dukkan hannayensa a cikin aljihun wandon suit ɗin jikinsa, har sai da ya kai ƙofar ficewa muryar malam Dauda suka sanya shi dakatawa.


"Kayi farar dabara ka kuma taimaki kanka, i will send her to you".


Cire leɓɓansa ya yi kawai ya fice ransa yana masa wani irin zafi, zuciyarsa tana sanar dashi hakan da ya yi shine dai-dai ta wani ɓangaren maslaha ga rayuwar yarinyar da bai san wacece ba ce bai kuma san irin ta ba, sai dai ya san tunda ta haɗa hanya dasu malam Dauda da shekarunsa da furfuran da suka mamaye baƙin gashin fuskarsa basu hana sa bayyana maitarsa a fili ba balle sakaya wani abun to ita ma ɗin duk kanwar ja ce, kuma kwaryar sama ce ke dukan na ƙasa.


A gurguje ya haɗe duk abinda zai buƙata ya rufe office ɗin ya nufi motarsa ya fice daga cikin makarantar, a hankali yake driving ɗin wayarsa da ya ke dialing lambar da ya yi saving da gudan jini ke ta fama ruri ba'a ɗaga ba, sai da ƙiran ya kusa katsewa sannan aka ɗaga shuru ya yi bai ce komai ba sai daga ɗayan ɓangaren aka ce"Yaya Saif".


"Yes bloody ya jikin Ummin bayan tahowa na?".


Cikin danne abinda ke taso masa a rai Farouk ya ce"da sauƙi alhamdulillah, amma da ka wuce gida kayi wanka ka huta before ka taho hospital ɗin".
Kamar mai jin baccin ya amsa da"hankalina ba zai kwanta ba idan ban zo yanzu na ganta ba i'm on my way in less than ten mins zan iso take care".


Yana ƙare faɗin hakan ya datse ƙira tare da ƙara speed ɗin motar, yana isa ya wuce ofishin likitan dake duba Ummi gaisawa suka yi ya fara amayo mishi da tarin tambayoyin dake ransa.


"Doctor har yanzu ba wani cigaba?".


"I'm sorry to say amma har yanzu babu wani abunda muke gani yana damunta koda kuwa scanning aka yi mata, kuyi mata addu'a kawai zuwa next week idan bamu ga wani haske ba zamu ba ku sallama kawai aje a gwada yi mata na gargajiya mussamman rubutun addu'o'i".


Ɓoyayyen ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauƙe tare da jingina kansa jikin kujerar da yake zaune, ji yake yi duniyar gabaɗaya ya yi masa zafi ya rasa inda zai sanya ransa ya ji ɗan dama-dama. Ciwon iyaye akwai raɗaɗi a zuciya mussamman irin wannan mai ɗauke kai.


"Thanks".


Ya faɗa yana miƙa masa hannu kafin ya fice daga ofishin, ya nufi ɗakin Ummin tana kwance tamkar gawa bata motsa ko wani gaɓa daga jikinta numfashin da yake fitar mata shine kawai ya bambamta ta da gawar dake kwance cikin kushewa.
Idanu ya tsura mata kamar yau ya fara sanya ta cikin ƙwayar idonsa, yayin da kifiyar tausayinta yake ragargaza masa raunananniyar ruhinsa. Saurin mayar da ƙwallar da suka ciko masa idanu ya yi tare da sauƙe idanunsa daga kanta ya maida shi kan Farouk da yake salla a cikin ɗakin. Jan ƙafafunsa da suka yi sanyi ƙalau ya yi ya shige banɗakin dake cikin ɗakin shima ya ɗauro alwalan sallan magrib ya fito ya yi kusa da Farouk sai da iddar sannan ya koma kusa da Umminsun.


Duk kallonta suke yi yanda fuskarta tayi fayau da ita ta rame sosai sai dai ta ƙara wani hasken da ba lalle mutum ya gane ba sai ya ƙura mata ido, riƙon hannunta ya yi ya haɗo da na Farouk duk ya sanya su duk cikin nasa.


"Allah ya ba ki lafiya Ummi, Allah ya tashi kafaɗunki ya sanya wannan jinyar ya zamto kaffara ga zunubanki. Ya ba ki tsawon ran da za ki ga jininmu".


"Amin amin ya Allah".


Faruok ya amsa dashi murya a raunane, suka cigaba da zuba mata idanu cikin rashin sanin makama da abin yi akan lamarin da yake ƙoƙarin girmewa kwanyarsu. Sosai ya yi zurfi cikin tafkin tunanin da yake iyo a cikinsa kafin muryar Farouk suka dawo dashi cikin zahirin hayyacinsa.


"Yaya Saif wataƙil da yanzu muna da uba, ƴan-uwa da kuma makusantan dangi da sun kasance a tare damu a wannan lokacin, da sun kasance mana majinginar da zamu jingina a irin wannan lokacin da sun zamo mana farin-ciki da mafi kyawun abinda idanuwanmu kan iya gani. Sai dai ƙaddara ta riga fata bamu tashi da uban ba balle kuma ƴan-uwan a maimakon hakan sai ma nisanta kansu da suka yi da damu da yin fatali da alaƙar dake tsakanin mu. Bamu da wani gata sai Allah, kai sai kuma Anty Fauziyya kai ne koman mu ci, sha, sutura, rashin lafiya da komai bani da burin da ya wuce yanzu na sama aiki ko yaya yake koda kuwa dubu biyar za'a dunga biya na at end of every month ina so na rage maka wani abun ɗawainiyya sun yi maka yaw...".


A karon farko da ya sa ki murmushi tun bayan faruwar hatsarin da Ummi tayi, yana ɗaura ɗan yatsarsa a kan lips ɗinsa yana fuskantar sa sosai da hawaye suke zarya a tudun fuskarsa a nutse yake faɗin"Ba zan taɓa gajiyawa da ɗawaniyyarku ba Umar bani da wanda suka kai ko balle su fi ku, idan ban yi muku ba a waye zanyi wa?, maganar aiki kuma ka barwa Allah komai bai mance da kai ba bloody".


Kifa kansa Farouk ya yi kana cinyarsa yana goge hawayen da suka ɓata masa fuska a hankali Saif yake shama sumar kansa. Basu bar cikin asibitin ba sai goma sha ɗayan dare kamar yanda suka saba Farouk ya haɗa masa tea ya kai masa sannan ya kwanta.


Saƙon da manajansa na gidan kajin da yake dashi ga turo masa yake dubawa, yana ji a ransa can kawai Farouk zai fara zuwa kafin Allah ya kawo masa wani aikin.




Haka nan yau na tashi sam bani da wani kuzari a jikina kamar wacce aka zarewa laka haka nake gudanar da komai, magana ma ban son yinsa nake yi tun bayan wayan da muka da Abba ya ba wa Hajiya Babba da Umma muka gaisa. Na koma nayi kwanciyata Nawwara tana wajen yana wanki ita kuma Nazifa ana yi mata kitso saboda zuwan yaya Amin tun farar safiya take ta gyare-gyare da kallo kawai nake bin ta duk da abin natan yakan bani dariya.


Ranar bamu da lectures ɗin safe sai na ƙarfe biyu, har Nawwara ta gama wankin ta shigo ta tarar dani yashe inda ta barni ban ko motsa ba.
"Wai ke yau ba za ki tashi bane?".


Juyi nayi"bana jin daɗin jikina ne".


"Ai kuwa ki tashi kiyi wanka, mu gyare ɗakin nan muyi abinda zamu yi kafin mu fita lecture kinsan fa yau zamu karatun test ɗin baƙin mutumin nan Mr Suleiman". Kaina na jinjina mata na diro daga kan gadon na fara tattare mana tsakar ɗakin sannan na share na haɗo wanke wanke na fito dasu zan yi, na tsaya ina kallon Nazifa da ake yarfa mata ƙananun kitso kamar wata amaryar da ake gobe ɗaurin aurenta.


"Sannunki mai kitso lalle za ki sha zaman tsifa, wannan ɗiban kitson kamar ana yi da allura".


Dariya suka yi gabaɗayansu, na wuce nayi wanke-wanken muna yin hira jifa-jifa, Nawwara ce ta yi mana girki muka ci muka tafi lectures awa ɗaya muka fito muka wuce bakin hanya muka sayo kayan miya sannan muka dawo hostel. Nazifa ta gama shiryawa tsaf sai jiran zuwan yaya Amin da take yi tana duba agogo lokaci zuwa lokaci.


Karfe huɗu da kwata na bugawa wayarta ta fara ruri, bata ɗaga ba ta rarumi hijab ta saka ta ce"ku taso muje".
Dariya muka saka nida Nawwara muka miƙe muka rufa mata baya sai tsiya Nawwara take yi mata wai ta cika zumuɗi.


Yana tsaye cikin mota kansa akan wayarsa dake riƙe a hannunsa, ya yi shirga manyan kaya half jamfa mai ruwan toka. Da sallama muka isa wajen da hakan ya sanya shi ɗaukowa ya zubawa Nazifa idanu kamar zai cinye ta ɗanya, sai da tayi gyaran murya sannan ya dawo cikin hayyacinsa har muka sama damar gaishe shi ɗaya bayan ɗaya.


"Yau dai gani ga ƴan hannun daman gimbiya da kullum ake bani labarin su".


Dariya duk muka yi don yana da barkwanci sosai, nikam da na ƙosa na bar wajen na ce"to bari mu bar sarki da sarauniya su zanta a tsakanin su".


Dukan wasa Nazifa ta kawo mini nayi saurin gaucewa tare da riƙo hannun Nawwara muka bar wajen can gefe dasu muka sama bench muka zauna muna jiranta muna kallon masu shige da fita a cikin jami'ar.


Can wata mota ta faka nisa damu kaɗan, idona ne kawai a kanta amma hankalina baya nan gabaɗaya nayi nisa a kewar Ummata da Anty Zakiyya da kuma ragowar ƴan gidanmu. Naji Nawwara ta taɓo ni ta ce"wancan kamar mr Saif".


"May be".


Na amsa mata dashi a gajarce na cigaba da tunanina har izuwa lokacin da idanuna suka hango mini Billy ɗawisu ta nufo ofishin da Nawwara ta ce mr Saif ya shiga.


Kallon juna muka yi kafin ta ce"to meya kawo Billy kuma ofishin mr Saif ko daman ta san shi ne?".




MATAN AREWA


(Book two)


© Maimunah Tijjani Iyam


______________________________________




Page 7⃣6⃣


Ɗage kafaɗata nayi tare da taɓe baki na ce"oho musu ni kuwa ina san sa ni". Shuru tayi kamar ba za ta ce komai ba sai kuma ta furta"Tab lalle kam amma Billy nasan duk inda ta raɓa ba alkhairi bane, kuma duk masu mu'amala da ita to sunyi tarayya akan hali guda ne".


Tsaki na sirtar na ce"matsalarsu ai ni daman duk malaman jami'ar nan wallahi ƙar ƙar nake yi dasu, ko abu ban so ya haɗa ni dasu balle har na taka cikin ofishinsu". Dariya ta saka kafin ta soma cewa"ke dai Na'ima Allah ya yafe miki wannan tsoron naki kamar farar kura".


Ban kula ta na soma dandanna wayata sai dai sam hankali da nutsuwata basa a gare ta, nayi karkata ga tunanin da ya daddabi raina da kuma tambayoyin da na gaza cimma amshoshinsu meya kai Billy ɗawisu ofishin mr Saif?, meye kuma a tsakanin su?, meye ya sanya su shiga ofishin har da rufe ƙofar?.


Taɓe baki nayi ina sakin tsakin a cikin raina tare da takaicin kaina da na damu da son sanin abinda ke ƙasa a tsakanin si har ya kai ta ga zuwa ofishinsa, wani ɓangaren zuciyata tana ayyana mini cewar nayi musu kyakykyawan zato sai dai sanin halin Billy yake ragaza ƙwarin gwiwan da nake dashi akan hakan.


Jin wayata ta fara ruri ya sani dawowa hayyacina, ganin Nazifa ce ya sani ɗaga ƙiran na kara a kunne daga nata ɓangaren ta ce"kuzo ku gaisa zai wuce".


"Ok".


Kawai na faɗa ina kashe wayar na kallo Nawwara na ce"muje wai zai tafi". Tashi tayi muka isa wajen da muka barsu a tsaye da fara'ar sa yake faɗin"to ni zan wuce sai kuma wani lokacin may be sai cikin azumi, ga amanar Queen dan Allah ku kula min da ita kuma ayi haƙuri da ita".


Murmushi nayi, Nawwara ta ce"kar kaji ka damu in sha Allah za'a kula maka da ita kamar jariri ɗan wata uku cikin zanin goyo".
Kansa ya jinjina tare da yin godiya ya ciro wayarsa ya ce na ɗauka musu hoto karɓa nayi na ɗauka musu guda uku kyawawa, sannan ya ɗauka mana mu ukun dukka yana ƙara yi mana sallama. Tare da zaro damin sabbin kuɗaɗe ƴan dari bibiyu ya miƙa mana muka ce ya barshi.


Ganin ya dage ya sanya ni amsa tare da yi masa godiya, suka yi sallama da Nazifa sannan ya ce mu nema wanda zai shigo mana da kayan buƙatar yau da kullum da ya sauƙe mana daga bayan motarsa, muka nema labourers suka shigar man dashi.


Tunda ya shigo cikin ofishin yake tsaye kusa da taga hannayensa zube cikin aljihun wandonsa, idanunsa a lumshe suke amma hakan bai hana shi zagaye cikin ofishin ba. A hankali ya fara buɗe lumshashshun idanunsa ya zube su akan ta tana zaune akan ɗaya daga cikin kujeru biyun da suke gaban teburin nashin ta ɗaura ƙafarta ɗaya akan ɗaya ƙarar taunar cingam da take yi da yake bada sautin ƙas ƙas shi ya ankarar dashi wanzuwar wani mutum a cikin wajen.


Kallon sama da ƙasa ya yi mata har yanzu bata ɗago idanunta daga danna wayarta ƙirar iphone ɗin da take dannawa ba, wani irin ɗaci ne ya zarge masa ransa ji yake yi kamar ya fizgo ta ya dunga kwalla mata maruka babu ƙau-ƙautawa ji yake kamar ya rufe da mungun duka ko zata dawo cikin hayyacinta har ta fahimcin haɗarin da kan hanyar da ta ɗaura rayuwarta akai da ya fi keken ɓera rashin tabbas.


Matse hannunsa da yake rawa ya yi tare da cije lower lips ɗinsa da matuƙar ƙarfi dole ne ya iya controlling ɗin kansa a irin wannan yanayin da yake son yin gyara.


Mazauninsa ya koma ya zauna ya buɗe laptop ɗinsa ya fara aikinsa na ɗaura test a portal ɗin ɗalibai da ake dab da sake musu result na last semester komai a nutse yake yinsa tamkar bai san da zaman ta a cikin ofishin ba balle ya ɗaga kai ya yi mata kallon arziki.


Ya ɗauki sama da mintuna ashirin yana aikin, kafin ya kai dubansa ga agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa dake nuni da ƙarfe biyar da mintuna goma rufe laptop ɗin ya yi ya fara haɗa wasu file ya sanya a cikin drower ya rufe da key. Wayarsa da key ɗin motarsa ya ɗauka ya isa gaban ɗan madaidaicin fridge ɗin dake cikin ofishina ya buɗe ya ɗauki goran ruwa ya kafa a bakinsa sosai yasha sannan ya mayar da saura ya fara ƙoƙarin ficewa daga cikin ofishin.


"Malam wajen ka fa aka turo ni".


Cak ya tsaya zai da ya ɗauki tsawon daƙiƙu biyar sannan ya waigo kallon da ya watsa mata ya tilasta mata saurin rusunar da ƙwayoyin idaniyarta da suke a tsatstsefe saboda wani irin kwarjini da cika mata ido da ya yi.


Cikin dakakkiyar muryar da babu alamar wasa da haifarwa mai sauraron nutsuwar dole ya ce"who sent you?".


A wulaƙance ta ce"Malam Dauda level co-ordinator".


Har yanzun idanunsa suka a kanta ya ce"ok you can go back to him ya faɗa miki rule and regulation ɗina nonsense".


Saurin ɗago kanta tayi sai dai ta kasa kallonsa illa gefe ta take kallo muryarta har tana shaƙewa tsabar takaicin da ya gama ɗura mata ta ce"bai sanar dani ba but he told me cewa nazo zaka hayar dani a course ɗinka daka bani carry over a 100 level".


Sai da ya shafo gefen fuskarsa kafn ya furta"ni na ba ki carry over ko kuma ke kika sama abin ki?, before then kin taɓa attending lecture ɗina?".


Shuru tayi don ta rasa abin da zata kuma cewa dashi mussamman da ya tsare da waɗanan idanun nasan tsawar da ya daka mata ya sanya da runtse idanunta da ƙarfi.


"Sauƙe ƙafarki and then kar ki ƙara tauna min cingam irin haka a nan".


Da hanzari ta sauƙe ƙafarta tan tare da haɗiye cingam ɗin da take tauna ɗin, iska ya kai wa duka yana dafe kansa da yake jin kamar zai rabe izuwa gida biyu tsabar sarawan da yake yi masa cikin ƙarfin hali yake yi maganar.


"Menene tsakanin ku da Malam Dauda da har ya turo ki nan?".


Shuru ya koma yi sai ya kuma daka mata tsawa yana maimaita mata tambayar a karo na biyu sannan ta ce"taimakona kawai yake yi".


Ƙara dafe kansa ya yi don a rayuwarsa ya tsani ƙarya ko kaɗan, kuma komai ƙwarewar mutum a fannin ta ƙarya idan ya yi masa a cikin idanunsa yake ganin gaskiyar kwance ɓaro-ɓaro.


"Tambayar ƙarshe zan yi miki idan kinga dama ki faɗa min gaskiya idan kin ga dama ki faɗa min abinda ba shi bane, menene tsakanin ku da malam Dauda level co-ordinator?, ina tambayarki ne kawai ba wai don ba zan iya gano gaskiya ba".


Ya gama cika ta fam da takaicin halinsa na wulaƙancin tsawan da yake doka mata kamar kanta zai tarwatse da kuma jin kansa, ba zata iya tina lokacin ƙarshe da wani ya yi mata irin hakan ba. Ita da malaman jami'ar da kansu suke ribibi akan ta tare da bayyanar da maitar su a fili gare ta wai yau ita ce wani lecture ke faman ɗagawa murya har ya ce mata as bata ce masa kule ba. Sakakken ajiyar zuciya ta sauƙe tare da faɗin"zan zo ka gano ɗin da kanka".


Matse yatsun hannayensa dukka ya yi waje guda da har sai da suka bada wani sautin ɗas kana ta ce"well is allowed then fice min daga office but kafin nan ki sa ni cewar ke macece rayuwarki dukka ƙarama ce da za ki ƙarar da ita kuma a ƙarƙashin wani walau iyaye, miji daga ƙarshe kuma ki koma hannun ƴaƴanki, ruɗu da ƙyale-ƙyalen duniya kar ki bari su ruɗe ki daga ƙarshe su bar ki da cizon ɗan yatsa waɗannan malaman da kike biwa cikin gabaɗaya babu wanda bai ajiye ƴa kamar ki ba wasu daga cikinsu har surukai da jikoki ne dasu. Sun killace nasu ƴaƴan ko ganin su basu ayi balle har ayi abinda suke yi daku da su, idan rayuwar jami'ar da kuke ƙira da rayuwar ƴancin kai ita ce take ruɗar ki to tun wuri ki dawo cikin hayyacinki ban ce malam

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login