Showing 27001 words to 30000 words out of 322641 words
Chapter 10 - DEEN Complete Hausa Novels By Arewa Novels.txt
fada
"O'O! Banason wadannan idanun!" yafada yana yamutse fuska
Dan Wara idanu zee tayi tace
"baka sonsu? To saika kwakulesu yadda zansan baka sonsu" tafada cikin quluwa
Yamutse fuska yasakeyi yace
"uhun, ni bazan iyaba besides idan na kwakule zaki koma skull with ugly forhead"
Dariyar dasu sumee keta dannewa tundazu tafito fili suka shiga kyakyatawa
"ni kake cewa ugly skull with forhead?!" tafada a qule
Kauda kai yayi bece komaiba sai hura hanci dayakeyi
Kwafa tayi tana kada kai
Ganin bata qara tanka mashi ba yasashi cewa
"intafi? Munada class in the next 15mins" yafada yana kallon yar agogonshi dake maqale da hannunshi
"eh tafi din" tafada cikin gatse tana harararshi
Dadi yaji ya kamashi yayi saurin juyawa zai tafi
"au tafiyar zakayi?!" tafada a fusace
Kasancewar tayi maganar a tsawace yasashi Saurin Juyowa a tsorace yana cewa
"O'O!"
"O'O! Nabi O'O dagudu, wai tsaya wama yasaka a university bayan ga kindergaten nan birjik a gari? Meye ma sunanka wai?" tafada tana Girgiza kasancewar ta tunda tafara ta miqe
Banza yayi ya kyaleta yana kumburi
"ok bazaka fadi ba? Sumee bani wayata inkira kawu"
"Deen..." yafada a kumbure
"mene?" tafada tana yatsina fuska
"I said Deen!" ya fada da dan qarfi
"kutt... Ni kakewa tsawa?" tafada tana nuna kanta cikin zare ido
Banza yayi ya kyaleta sai hucin dayake
"Dakyau! Amshi kaje ka siyomin ruwa" tafada tana miqa mashi 1k
Juyowa yayi ya dan kalleta sannan ya amshi kudin yajuya yana cika da batsewa
Su rukky da cikinsu harya fara ciwo don dariya ta kalla taja guntun tsaki sannan ta zauna tana huci
"Allah dai zee, wlh you guys are so funny!" inji rukky
"I swear, wlh kunfi tom & jerry ma" inji nurr itama cikin Dariya
Tsaki tasake ja tace
"kuke ganin funniness dinshi, mtcheew! he's so annoying"
"Bawan Allah, I wonder how handsome guy kamar shi yake haka, gaskiya solu6ancinshi ba qaramin qwararshi yaiba" inji sumee
"wlh kau, dama ance mutum tara yake be cika goma ba, shi nashi tawayan kenan" inji deeya
Zee bata sake tankamasu ba tacigaba da danne dannenta a waya
Deeya ce ta ta6o sumee tana gwada mata Deen daya taho kinkime da ledar pure wata daya
Wara idanu sumee tayi tana toshe baki sannan ta ta6o nurr dake kusada ita ta gwada mata itama waro ido tayi tana qumshe Dariya, dama rukky tunda deeya ta ta6o sumee itama ta ankare
Zee batasan wainar da ake toyawa ba don hankalinta nakan wayarta harya qaraso sai jitayi ya dire mata ledar pure water din agabanta yana miqomata chanji
Bin ledar pure water din tayi da kallo sannan ta maido Kanshi cikin alamun rashin fahimta
"ga chanjin" yafada yana miqamata
Qara maida kallonta tayi ga ledar ruwan tace
"meye Wannan?"
"pure water din dakikace asiyo mana" yafada yana hade gira
"ni nace ka siyomin Wannan? Wannan ne pure water? How is it pure kana ganin abu kamar ruwan toilet? Nufinka ni zansha Wannan?" injita tana kallon ruwan a wulaqance
"but you said I should buy you water, wane ruwane kuma bayan Wannan" yafada cikin qosawa
"ce maka akayi kowama nashan qazantar dakuke sha ne? Swan water nake nufi, dummy!" tafada tana harararshi
Gani tayi beko motsaba hakan yasata qara cewa
"kafa dauke Wannan abin daga gabana ka kawomin abinda nace"
Bece komaiba sai duqawa dayayi ya dauki ledar ruwan ya wuce yana kumbura fuska
Binshi da kallo sukayi suna Dariya qasa2
"ayyah? Ni wlh harya fara bani tausayi" inji nurr
"nima wlh, the guy is so cool yanada hqr" inji deeya
"karma yayi haqurin, ba ya iya jefa mutum Mud ba?" zee tafada tana kwafa
"Allah sarki, gashinan ya dawo" inji sumee
Duk Juyawa sukayi suka kalleshi suka ganshi ya taho ruqe da swan water daya
Ta6e baki zee tayi ta Kauda kai tana taunar chewing gum din bakinta
Koda yazo miqamata yayi yanzun ma yana turo baki
Dagowa tayi tayi mashi kallon up & down sannan tace
"meye Wannan kuma?"
"ruwan" yafada yana dan Wara mata oily idanunshi
"guda daya nacemaka kasiyo? Ko nikadai ke anan dazaka siyo guda koko cemaka sukayi azumi suke" tafada cikeda gadara tana enjoying moment din
"zee mana" inji nurr tana kya6e fuska don honestly yafara bata tausayi
Wani kallo tayimata ta dauke kai ta maida kan Deen dayake turo baki still
"ko bakaji ba?"
Sake cinno baki yayi yace
"but you said swan water" yafada yana kallonta da innocent face dinshi
"yes amma ai ba daya nace ba"
"To nawa?"
"mu nawa ne nan?"
"5"
"To 5 zaka siyo"
"but munada lecture saura 5mins ashiga" yafada yana duba agogo
"kaje ka dawo in 3mins sai katafi"
Ba don ranshi yasoba yajuya yatafi qarowa a qasan zuciyarshi yana cewa _I don't like her_
Bayan tafiyarshi nurr tace
"ayyah, zee adinga dai tausayawa"
Dan harararta tayi tace
"banason irin Wannan nurr, duka me nayi mashi? Shifa a ruwan chakwali ya jefani yasani nazama abin Dariya wanda a sannadiyar hakan yasani zaman gida na sati daya ina jinyar qarya, nikuma daga fara ramawa yau sai kice wani abu?"
"kuma fa, kawai nidai yanayinshi kebani tausayi, he's so timid" inji nurr
"shi ai be ba Kanshi tausayi, bakiji abinda yacemin dazu ba? Wai ugly skull with forhead"
Dariya duk suka Fashe dashi sumee tace
"ai ke kikace ya kwakule maki idanu shiyasa yagayamaki yadda zaki koma"
"ba Dole ince ya kwakulesu ba tunda yace baya sonsu? Mtcheew dani yake zancan wlh" tafada tana maida kanta akan wayarta
Cigaba da firarshi sukayi itadai zee bata qara tankamasu ba harya sake dawowa da robar ruwa hudu dik ya hada gumi saboda zirga2.
Ajiye masu yayi duk suka dauki guda guda sannan ya miqama zee chanjinta yana kumburi
Saida ta watsamashi harara sannan ta amsa tace yatafi zata nemeshi idan tana buqatarshi
Cikin Jin dadi ya juya yafara tafiya da sauri don gab ake da shiga class sai jiyayi ankira sunanshi kuma
Juyowa yayi yana 6ata rai alamun menene kuma?
Nurr data kirashi ta nunamashi robar ruwan hannunta alamun yazo ya amsa
Girgiza mata kai yayi kawai alamun baya buqata sannan yajuya yabar wajen da sauri don karma a qara tsaidashi
Dariya duk suka sa rukky na cema Nurr maganinta kenan, Murmushi kawai tayi ta daga kafadu suka cigaba da firarsu.
A bangaren mr ibrahim kau Kanshi ne yadau zafi, yarasa hanyar dazaibi wajen aiwatar da qudurinshi na kada zee
Yasan idan ya tsaurara dayawa ba zee kadai ba zata fadi harda dayawa acikin class din wanda shi ba haka yakeso ba, ita kadai da unserious elements irin qawayenta yakeso su fadi amma tayaya? Yasan ba laifi kan zee na ja fiyeda wasu dake attending lecture dinshi, idan zai kadata ta hanyar tsaurara questions yasan dayawa cikin students dinshi suma zasu fadi tareda ita, To yanzu ina mafita??.... ✍️
No editing 🙏🏻
Kuyi hqr jiya ban samu chajiba sai da marece gashi ina azumi inajin wuyan typing, kar inje insaki layi🥴
Ummin fasihu 🧚🏻♀?
8/2/21, 9:32 PM - Buhainat😝: *🙍🏻♂️DEEN 🙍🏻♂?*
*011*
"zee kiyi hqr, nasan yadda kikeji ahalin yanzu, kiyi mashi uzuri da yanayinshi nasan da normal yake da beyi maki haka ba" inji nurr tana kallon zee dake zaune hannuwa harde da qirji lip dinta naqasa acikin bakinta tana tauna ahankali
Kallo daya zakamata ka hango tsantsan 6acin ran datake ciki
"Dole fa abin ya bada takaici, bansan solu6ancin gayen nan harya kai ya watsa ma mai kareshi qasa a ido ba, Wannan ai gaulanci ne" inji sumee
Haka kawai nurr taji maganarta tamata zafi hakan yasata cemata
"sumee karki manta kowanne dan adam da tawayar da Allah yayimashi don dukkanmu tara muke babu wanda yacika goma, ke da kike taqama kina normal idan an bincika akwai abubuwa da dama da wannan bawan Allahn yafiki dashi, kowanne dan adam da irin baiwar da Allah yabashi don haka a dinga sanin abinda za'ace don inhar kana raye To bazakace ka gama lfy ba"
"ikon Allah, daga magana sai cibi yazama qari, wai nurr meye tsakaninki da guy dinnan? Naga sai wani zaqalqalewa kike akanshi, danace yana solu6anci ba solu6iyon bane? Gayamin! Inba hakaba wane normal mutum zai aikata abinda ya aikata? Dakuma kike cewa yafini, dame Wannan gaulan zai fini? Saidai da gaulancin amma babu abinda zai iya fina dashi" inji sumee tana harararta
Ran nurr yasake 6aci tace
"ai gwara shi, gaulancinshi abin so ne don baya cutarwa saidai a cutar dashi kuma gaulancinshi be hanashi Tsayawa akan gaskiyarshi ba duk dacinta kau, kuma gaulancinshi be sashi Jin tsoron mutane amadadin Jin tsoron mahallicimshi, tabbas be kyautaba daya dizgata a gaban jama'a amma idan aka duba za'aga akan gaskiyarshi yake, be iya qarya ba kuma tsoron mutum bazai sashi yafaraba, wasu fa? Haka zaka gansu sumi2 kamar na Allah, sululu kasau maciji sari ka noqe, wadanda tsoron mutum zaisa su take gaskiya don farantawa abokin hallitarshi"
Sumee zatayi magana deeya ta katseta da
"wai duk meye hakane? Meya jawo duk Wannan? Haba be kamata kuna behaving immaturely ba haka saboda wani can Deen, idan yayi fiyeda hakan ma ai ba abin mammaki bane tunda dan lokacin da mukayi atare ya isa ya nunamana waye shi, he's a straight-forward man, yana magana ne kai tsaye Batareda damuwa da abinda zai biyo bayaba, kawai zee hqr zakiyi tunda haka Allah yayishi saidai kawai atari gaba" tafada tana kallon zee da haryanzu bata ko daga kai ta kallesu ba tunda suka fara
"aikau dai, kawai sharewa zakiyi kinga gaba idan yaqara shiga irin Wannan halin yaga wanda zai qara qoqarin taimakonshi" inji rukky
"bama zai shiga ba Insha Allahu" inji nurr tana Kauda kai
Hango Deen dasukayi ya nufo wajensu yana kukumbure fuska yasasu zubamashi ido banda zee da batama san da tahowarshi ba
Qarasowa yayi gabansu yaja ya tsaya yana sake hade gira sannan ya miqoma zee ledar juices dinta yana cewa
"gashi"
Saurin dagowa zee da Batasan da isowarshi ba tayi sannan tayi Saurin Kauda kai tana lumshe manyan idanunta
"gashi" yaqara fada yana sake miqomata ledar not minding her reaction
"nurr kicemashi yabar nan kafin inyi something stupid" tafada cikin 6acin rai still bata kalleshi ba
Dan jimm nurr tayi sannan tace
"Deen bani nan" tafada tana miqomashi hannu
Babu musu yaje ya miqamata juices din
"Deen kasan abinda kayi baka kyautaba kuwa?" inji nurr tenderly
Tura baki yayi yaqara hade gira yace
"ni menayi kuma?"
"abinda kayi yanzu mana, ka yarfa zee alhalin kai take taimako" inji nurr din
"ni ban yarfata ba, cewa nayi abinda tafada ba gaskiya bane ba kuma babu kyau qarya shiyasa na gayamata" yafada cikin son kare Kanshi
"amma saboda wa tayi qaryar? Saboda kai nefa, lokacin datazo mutane ne cike a wajen amma babu wanda ya iya cewa komai sai ita ta dauki risk din shigarmaka, kace qarya take basu mareka ba kanada tabbacin da bata tankaba daidai Wannan lokacin bazasu yima abinda yafi marinba? Atleast saikayi shiru kabari sai mun ke6e sannan kace qarya take amma ba gaban kowaba can, ka kunyatata gaban mutanen suji kamar su keda gaskiya" tafada cikin kulawa
Shiru yayi kawai amma shima sai yaji badadi kuma yaji beyi daidai ba
"sorry" yafada ahankali yana tura baki idanunshi aqasa
"bani zaka cemawa ba, ita zakaje kaba hqrin" tafada tana nuna zee da tundazu taqi kallon 6arinsu
Kallon zee din data nuna yayi ya 6ata fuska yace
"she'll shout"
"she'll not, just go apologize, shikenan" tafada affirmably
Kamar bazai tafi din ba sai kuma yatafi yana qara 6ata fuska
Agabanta yaja ya tsaya yana huhuro hanci da tura baki, ganin ko nuna tasan dashi batayiba yasashi qara 6ata rai yace
"sorry"
Bata ko motsaba bare ta dago hakan yasashi sake cewa
"am sorry"
Ganin kamar jine batayi ba don yanzu ma bata motsaba yasashi duqowa saitin kunnenta yace
"I said am sorry!" da qarfi
Dagowa tayi Saurin yi tana watsa mashi wani kallo hakan yasashi ja baya yana turo baki yace
"O'O!"
"Duk anubuwan da kayimin bai isheka ba saika hada da dodemin kunne?" tafada tana harararshi
"O'O! Nazaci bakiji bane inata cewa sorry" yafada yana yamutse fuska
"eh ga kurma ba? Ai dole kace banjiba... Kuma sorry din me zakayi mun? Ni ai na saya da kaina, ina zaman zamana rukky tazomana da zancen gaka can ankusan kashe ka, banma ida jiba na tashi kamar wata mahaukaciya na nufo wajen aguje, dama na sani da cewa nayi suqarama suyima liss" tafada cikin hargowa
Dariya su sumee sukayi shikuma ya Kauda kai yana kumburi
"dama Wannan ba shine na farko daka kunyatani ba, na farko ka jefani a Mud agaban mutane yanzu ma ka qara tsinkani agabansu daga taimako!"
"yanzu dai kiyi hqr tunda yabaki hqr" inji nurr tana Dariya
"hqrinshi na banza? Me xanci dashi? Kuma wlh ka qarawa kanka, da nafara hucewa amma yanzu ka da6a don haka yanzu muka fara wasan wlh"
Bata fuska yayi yace "O'O! Ni menayi kuma?"
"baka san abinda kayi ba? Zaka sanine, bari kaga.." tafada tana bude jakkar littatafan ta tana bincike
Wani littafi ta zaro irin mai hard cover dinnan da handout daya ta miqamashi
"Gashi, badai aiken ne bakaso ba? Fine, amshi nan"
Amsa yayi yana jujjuya littatafan a hannu
"wait ma ina littatafan ka inga ya jangos writing dinka yake?" tafada tana zaro daya daga cikin littatafan shi dake aje can gefe tafara dubawa
Ajikin bangon littafin tafara cin karo da sunanshi daya rubuta cikin wani unique handwriting
_*KAMALDEEN MUHAMMAD*_
dan tsurawa sunan ido tayi tana sake nanata sunan a zuciyarta, _dama Kamal sunanshi?_ abinda ta tambayi kanta kenan.
Kauda tunanin tayi a ranta ta bude littafin
Sake buda manyan idanunta tayi akan super unique handwriting din littafin wanda beyi kamada wanda hannu ya rubuta ba, Bin rubutun tayi da kallon shagala, ahankali ta cigaba da bude pages din littafin tana kallon the same unique handwriting wanda kallo daya zakamashi kaji ka kamu da sonshi
Dagowa tayi ta kalleshi taga haryanzu kumburi yake
_ya shi ya handwriting dinshi_ inji wani 6arin zuciyarta
Saurin Kauda hakan tayi a ranta ta rufe littafin tana yatsune fuska tace
"ba laifi, yanzu kaje da wannan littafin da handout dinnan kayi copying abin handout din daga page 15 inason zuwa gobe dazan amsa kayi pages biyar, understand? Thats your purnishment for embarassing me in public" tafada cikin isa kamar irin tana magana da danta ko qannenta
Bece komaiba sai sake pouting din baki dayayi, nurr ce tace
"haba zee, this is too much, ki dinga tausayawa condition dinshi mana"
Kallon wutsiyar ido tayimata tace
"atleast ya godewa Allah nama bashi aikin yi, da yayta zuwa school abanza yakoma a wofi" tafada tana juya idanu
"aikaudai zee, nima ga nawa kinga idan yayi naki yau ni sai yaimun gobe" inji sumee
Tare nurr da zee suka watsamata wani irin kallo
"akan me? Nima ai da dalili nasashi afterall he's mine dama, baxaiyi ba ai ba Bawan kowa bane" inji zee cikin jin haushi
Jin hakan yasa nurr dan sakin ranta don harga Allah batajin dadin abinda ake mashi kwata2 yanzu
"you can go" tafada tana kallonshi
Kallonta ya danyi sannan ya dauki littatafan shi ya hada da wadda tabashi ya wucewarshi.
Duk binshi sukayi da kallo kowa da abinda yake saqawa a ranshi
*MASTER*
Dibar farar powder dake bisa takarda yayi da yatsu biyu manuniya da babbar yatsa yakai hancinshi ya shaqa.
Girgiza kai yayi alamun abin ya shigeshi yana bubbuga kanshi da hannu sannan yakoma jagwab a kujera yana sake jujjuya kai
Sudai su Alex na gefe suna kallonshi ba damar magana don ko mahaukaci ya lalluba yasan Wannan halin bana magana bane
_*ku wadanne irin dabbobi ne!*_
Maganarta tasake dawo mashi a qwanya akaro na ba adadi
_*idan ku a jagaliyanci kukafi qwarewa akai why not kutafi tasha ko dandalin qauraye!*_
_*dama kayi Kama da arnan dajin qarnin farko! So don kayi hakan ba wani abu bane*_
_*saidai zee tafi qarfin a ta6a mata koda tip of akaifanta ne, duk wanda yayi gigin yin haka ya shiryama baquntar lahira!*_
Buga table dinshi yayi da qarfi wanda hakan yasa duk suka miqe tsaye kamar dama akan qaya suke
"master, master kabani izini yanzu yanzunnan inkawomaka ita gabanka, nikuma nayi maka alqawarin kawota har qasan kaffafuwanka boss" inji Alex yana numfarfashin masu nauyi
Dago jajjayen idanunshi master yayi ya saukesu akansu na wani lokaci sannan yafashe da Dariya harda tuntsurawa
Duk binshi da kallo sukayi sunaji ajikinsu ta zee taqare don duk wanda yaji Wannan Dariyar yasan bata alhairi bace
Saida yayi mai isarshi sannan ya gimtse fuska kamar bashi ba yace
"zan gwadamata mu dabbobinne! zan gwadamata mu arnan dajin qarnin farko ne! Zan gwadamata ba iya tip din akaifanta ba kadai zamu ta6a, harta rayuwarta saina tsiyayarmata dashi kuma inzauna lfy! Zan koyamata hankalin da idan ana dawowa duniya akaro na biyu idan ta dawo bazatayi sha'awar ganin kowanne namijiba bare harta daga kai ta kalleshi!" yafada cikin hargowa wanda saida nakusan sakin acawii saboda tsoro🥶
"muna bayanka master! Abinda ya kamata kenan yadda zata zama izina ga duk shege ko shegiyar datayi ko yayi niyyar yin koyi daita" inji gandu shima cikin zazzare idanu
Kakkada kai master yayi yana zagaye la66anshi da harshe sannan ya cije lower lip dinshi da qarfi ya sake kallosu da rinnanun idanunshi
"waye Wannan gayen?" yafada yana kallonsu still
"Gaskiya bamu sanshi ba amma zamu bincikomaka idan kabamu umarnin hakan" inji Bash
Kada kai yayi sannan yakoma ya jingina da kujera yace
"nabaku, ku naimomin komai gameda shi, idan nace komai.. Ina nufin komai ciki harda alaqarsu da ita, banason ragin komai"
"Angama boss!" suka fada atare cikin tabbatarwa
"zamugani, zamu gani idan jarumta ta gaskiya ce, zamu gani idan zaki iya tserewa tarko na!"
Wayyo zee 😭
*WASHEGARI*
Tunda wuri tazo school yau kasancewar yau za'ayi submitting din assignment din mr ibrahim wanda yake amatsayin 20% na jimillan makinsu na subject din.
Dama haka takeyi idan ya bada assignment da kanta zatayi submitting don bai amsar aike saidai tana bashi zata tashi tabar class din kuma be ta6a tankamata akan hakaba.
Qarfe 9am daidai yace musu zai amsa, sanin beda african time ko kadan yasa students din zuwa da wuri don idan har ya rigaka shiga aji to ka lashe
Tun 8:30am ta iso school, direct class ta nufa inda ta tarda aji duk ya hargitse, wadanda basu idaba sai jeka ka dawo suke na ganin sun ida kafin ya shigo.
Bata dade da zamaba su sumee sukayi joining