Showing 33001 words to 36000 words out of 322641 words
Chapter 12 - DEEN Complete Hausa Novels By Arewa Novels.txt
tayi su sumee dake bayanta sukayi Saurin tareta.
Dagowa sukayi baki sake suna kallonshi kowannensu ya kasa gasgata abinda yafaru yanzu
Riqe Kanshi dake barazanar rabewa gida biyu yayi da hannu biyu yana groaning
Dago rinnanun idanunshi dasukayi mugun runewa yayi ya watsamasu nan take jikin kowaccensu yafara 6ari
Ganin ya nufosu gadan2 yasasu Saurin duqewa suna curewa wuri guda suna sakin qara
Naushi yakaima iccen wurin yana sake wani gurnanin, nan da nan hannun yafara jini
Sake dafe kai yayi da dayan hannun marar ciwo yanajin hajijiya na dibarshi, duk jijjiyoyinshi sun tashi rudu2 gasunan kana gani 6aro2.
Dagowa zee tayi tana kallonshi tana maida numfashi da sauri2
Juyawa yayi yafara tafiya cikin hada hanya kamar dan maye, hannunshi kau izuwa yanzu yariga ya wanke da jini
Beyi nisaba wani mugun jiri ya kwasheshi ya zube a wajen.
Wata iriyar qara nurr ta kwala ta tashi ta nufeshi dagudu.
Cikin kuka ta birkitoshi tana kwala kiranshi amma ko motsawa beyi ba
"shikenan, kin kasheshi! Kin kasheshi da mugun halinki!" inji nurr cikin kuka
Tana zaune a wajen takasa motsi sai kallonsu datake kamar doluwa, everything just happened so fast that takasa figuring a mafarki take ko zahiri.
Tana nan inda take taga mutane sun taho wajenshi da alamu su sumee suka kirasu.
Tana kallo aka daukeshi suka wuce dashi duk akabar wajen aka barta ita kadai in her sitting position kamar statue
ππππππππππ
"Daughter!!" taji hakan kamar daga sama ana girgizata
Firgigit tayi ta dawo daga duniyar tunanin data lula ta dago tana kallon daddy dake kusada ita da alamu shine ya girgizata sai takuma maida kan mummy da itama tayimata quri tana kallo.
"Wai lfyarki lau kuwa Daughter?" inji daddy yana kallonta keenly
Lumshe idanu tayi ta bude kawai sannan ta dauki fork dinta data ajiye tundazu don tama manta a dining take tariga ta lula duniyar tunanin da tasaba a yan kwanakinnan.
"magana fa ake miki" inji mummy tana kafeta da idanu
Dagowa tasakeyi Wannan karon idanunta sun duri ruwa
Ganin hakan yasa daddy Saurin kamo hannunta yana cewa
"ya sallam! Wai Daughter meke damunki ne ko haryanzu jikin ne?"
Dagamashi kai tayi ahankali hawaye na sakkomata
"To gaskiya hospital zamu koma, ace fever haryanzu bata sauka ba? Tunfa ranar wednesday kika dawo haka amma haryanzu babu sauqi dukda magungunan da kikesha? Gaskiya we have to do something" yafada yana zaro wayarshi
Sunajinshi ya kira family doctor dinsu yana mashi complaining akan haryanzu dai jiya iyau zee fa bata warwareba, basu ji me akace ba a dayan bangaren sukaji yace gobe kawai zasu zo tunda yanzu dare yayi yafison suje hospital din ayimata aune2 tunda treatment din gida yaqiya.
Da haka sukayi sallama akan goben insha Allah suna nan tafe.
Itadai zee zagaye abincinta take da fork tana saurarenshi hakama mummy wadda bata tofa komaiba don ita tasan Wannan ba fever bane akwai dai abinda ke damunta bayan Wannan.
Cigaba da kwantarmata da hankali daddy yayi akan insha Allah gobe koma meke damunta za'a gano kuma za'a maganceshi insha Allah.
Batace komaiba sai narkemashi datayi a kafada tana 6ata fuska ashagwa6e.
Wurin barci ma yau kamar yan kwanakinnan neman barcin tayi ta rasa, juye juye kawai take tarasa abinda ke mata dadi.
Abubbuwa ne suka taru sukayi mata cinkis a rai
Nafarko baqincikin faduwar da zatayi a assignment wanda hakan na nufin ta rasa 50% na marks idan aka hada da wancan 30% din na attendance
Na biyu 6acin ran Marin da Deen ya wankamata wancan ranar just because ta nunamashi 6acin ranta akan 6arnar da yayimata, a dakeka a hanaka kuka? Ita yayi mawa amma shi yafi reacting?
Na qarshe kuma halin da aka tafi da Deen ranan, cikin wadannan Abubbuwan Wannan yafi yimata bake2 arai, badon tanajin laifinta ne ba Kawai haka kawai takejin abin ya tsayamata ya tsayamata a kwalwa takasa yakice hakan a kwalwar ta
A cikin yan kwanakinnan, datayi jigim ta fada duniyar tunani to incident din take tunawa, batason ta yarda dacewa ta damu akan hakan, batason ta yarda cewa tanason sanin halinda yake ciki yanzu, dukda kau yadda zuciyarta ke azalzalarta akan haka, gani take ita yaiwa laifi why kuma zata damu dashi? Hakan ba qaramin sake dagula mata lissafi yake ba.
Tashi tayi zaune ta jingina da jikin gadon tareda folding hannayenta a qirji, kafe waje guda tayi da kallo yayinda fuskar Deen a lokacin da ya burkuce tashiga yimata gizo.
_meya faru dashi a Wannan lokacin?_
_fushi yayi? Dama ance masu sanyi basu iya fushi ba ko?_
_meya sashi fushin to? Zagin ko tsawar ko watsamashi coke din datayi?_
_koma wane ne aciki ai hakan be isa har yasa yayi collapsing ba_
_kuma ai duk laifinshi ne, da bai ta6amata kayaba da duk hakan be faruba_
_yanzu a wane hali yake ciki? Is he ok or not_
_meyasa tunaninshi yaqi barin brain dinta, meyasa?_
Haka taita karatun jakinta har barci yayi nasarar saceta can cikin dare.
Washegari kamar yadda daddy yace haka yakaita hospital din dakanshi kasancewar ranar lahadi ne baya fita a ranar.
Asibitin kudi ne data amsa sunanta don ga yanayin zubinta ma kasan bana qananun mutane bane.
Kasancewar dama doctor yasan da zuwansu nan danan ya karbesu yashiga yimata aune2 kamar yadda daddy ya buqata don gano ainahin abinda ke damunta
Duk gwaje2n dayayi be lallubo abu guda dake damunta ba hakan yasashi kawai rubuta musu wasu magunggunan na pain relieve yabasu dakuma basu tabbacin zata warware qila fever dinne be ida sakinta ba
Koda suka fito daga hospital din maimakon suyo gida sai suka wuce yawo inda yaita yawatawa da ita parks parks da wajajen shaqatawa.
Sosai hakan ya taimaka wajen lifting din mood dinta don sosai nauyin datakeji a qirjinta yaragu.
Saida ya tabbatarda tadan warware sannan suka koma gida bayan sunyi sayayyar kayan zaqi dayawa daga parks din
Aranar a kula da zee daddy ya lallace don tare sukayi yinin ranar yana debemata kewa, itadai mummy tazama yar kallo don tunda ta lura dakwai abinda ke damunta tayi2 ta gayamata ta qiya ta shareta. Ta lura zee bata sakin jiki daita kamar yadda 'ya takamata ta saki jiki da uwarta, hakan ba qaramin damunta ba yake amma tarasa yadda zatayi don zee din zumace saida wuta, koyaya ta sake mata zaqalqalewa take bayan haka kuma zee tariga ta Tsorata da ita duk yadda takeson ta dan jawota jiki sai tayi ta baya2 daita don sosai take shaqqarta wanda hakan yasamo asaline daga tsoron dukanta datakeyi don zee bata qaunar abinda zai ta6amata lfyar jiki hakan yasa take baya2 daita babu shakuwar nan ta uwa da 'ya atsakaninsu.
*WASHEGARI*
Yau monday kuma tayi shirin zuwa school wanda tun wancan wednesday din bata sake zuwaba
Jiki a sanyaye tayi shirinta inda tunnanika kala2 ke kai kawo a brain dinta saidai wanda yafi kowanne rinjaye shine nashi, dukda batason gasgata hakan tasan babban dalilinta na zuwa school din shine azalzalarta da zuciyarta keyi nason sanin halinda Deen ke ciki.
Abin har mammaki yake bata na yadda ta damu dashi dubada yadda takeda I don't care mana nata ta6a zaton zata ta6a damuwa da mutum irin Deen ba.
Dakyar dai tasamu tagama shiryawa tafito tashiga dakin mummy don yimata bankwana
Saida mummy ta tabbatar da taci abinci sannan tayimata addu'ar dawowa lfy bayan ta kashemata warning din data gama abinda takeyi ta kamo hanyar gida
A harabar gidan ta iske bala wanda ganinta yasashi Saurin budemata kofa tazo tashiga yamaida yarufe sannan ya zagaya nashi mazaunin ya zauna, cikin yan sakkani motar ta halba kan kwalta.
***
Fitowa tayi daga motar bayan yagama gyara tsayuwarshi a parking space din, sanya shade dinta tayi ta rataye handbag dinta sannan tabi hanyar dazai sadata da department dinta cikin tafiyar ta daya riga ya zamarmata jiki.
Kasancewar sunada lecture din safe kuma sauran yan mintuna afara yasata nufar class direct.
Koda tashiga students kadan ta iske kuma duk ciki babu wanda takema magana hakan yasata samun mazauni ta zauna.
Zaro wayarta tayi tana danne2 saidai ko za'a shaqeta bazata iya fadin abinda takeyi da wayar ba don hankalinta kwata2 ba tareda ita yake ba yalula can inda yasaba lulawa a yan kwanakinnan.
Ahakan ne taji an dafa kafadarta, dagowa tayi taga su sumee ne tsaitsaye kanta hakan yasata dan yatsine fuska irinta basarwa tana gyara zama
Duk samun wuri sukayi kusada ita suka zazzauna sai alokacin ta lura da yadda class din yadan qara cika.
"barka zee, yau agari inji maqi baqo" inji deeya
Qara dan yatsine fuska tayi kamar bazatayi magana ba saikuma tace
"humm"
"kwana dayawa zee harmun fara tunanin zuwa duboki ga layyukanki duk basa shiga" inji sumee
"uhm am not available ne" ganin yadda take amsamusu a daqile yasasu jan bakinsu sukayi shiru don sun lura yau yan wulaqancin na bisa kai
Ita dama nurr bata tankaba don haryanzu tanajin zafin abinda zee tayiwa Deen dukda taso barin zee tafita daga cikinsu saikuma taji bata iyawa don zama da zee babban alhairi ne don zee din tayi ta fannuka da dama, barta da wulaqancin ta da rashin kunya amma a bangaren bude hannu da facaka da qawaye ba'a magana, gashi tarayya daita yasa ta chanza sosai ta koyi abubbuwa da dama na classic girls inda yanzu a unguwarsu batajin akwai wanda yafita gayu da suna, wadannan abubbuwan yasata jin bata iya rabuwa daita yanzu dukda kau mugun haushinta dake danqare a zuciyarta.
Ba'a jimaba lecturer din dazaiyi basu darasi yashigo yafara abinda yakawoshi
Saida sukayi 40mins a lecture din sannan suka fito kowanne yakama gabanshi yayinda su zee suka nufi mazauninsu.
Tana jinsu sunata labaransu taqi tankawa kowa acikinsu dukda suna dan sanyota aciki, burinta kawai suyi magana akanshi ko zata dan samu haske akan abinda zuciyarta ke mintsininta akai, amma kamar sun sani babu wanda ya dauko zancenshi hakan yasata jin ranta yaqara jagulewa
Ana haka taji deeya tace
"zee bakizo ranar friday ba bayan kinsan ranar mutuminki zai raba assignment"
Ranta ne yaqara 6aci saidai ko Dagowa batayi ba bare ta nuna alamun taji
"To anraba saidai be bada nakiba wai idan kinzo kizo kisameshi a office"
Sai a sannan ta dago ta kalleta, kamar zatayi magana saikuma tafasa ta maida kanta ga phone dinta datake huce haushi akanta ta hanyar danna.
Ganin haka yasa suma suka fita batunta suka shiga discussing din marks dasuka samu inda duk babu wanda marks dinshi yakai goma dga mai 2 sai 5 sai 4, nurr cema tasamu 7.
Nan sukaita labarin su suna zazzaginshi wai ai dama baso yake suciba shiyasa ya sakamasu mugunta don wlh ba don yahada da mugunta da sunci
Itadai zee jinsu take yayinda take tunanin nata makomar, ko tantama babu gani yayi haukan yayi yawa shiyasa yakeson tazo har office dinshi yaci mata mutunci yadda yaga dama, yakuma yimata gori akan yadda tacika baki a wancan karon gashi ba'aje koina ba tafara sacewa.
Ana haka wani saurayi yazo wajen yayi musu sallama.
Saida sukayi mashi kallon up & down sannan suka amsa adage itakau zee ko Dagowa batayi ba abin da ya dameta ya dameta
Saurayin da shima bada son ranshi ba yazo wajen yayi facing din zainab da haryanzu kanta ke kan wayarta yace
"Zainab Farouq Dan faranshi, mr ibrahim yace nace kizo"
Sai a sannan zee ta dago tana kallon saurayin a dage kamar yadda sauran sukayi mashi saikuma ta watsar
"dake nake mallama" yafada yana jin haushin kallon dasuke binshi dashi, dama idan ba qaddaraba mexai kawoka majalissarsu duk abinda sukayi maka kai ka siya.
"mallam tunda ka isar da saqonka ai sai kaqara gaba ko? Tajika ai" inji deeya tana yatsina
Kallonta yayi yace
"ai nasan da haka mallama, cewa yayi nazo qafata qafarta"
Sai a sannan zee taqara Dagowa ta kalleshi, zatayi magana saikuma tafasa haka kawai yau taji magana ma wuya take mata don damuwa da baqin ciki dasuka taru sukayi mata katutu arai.
Batace komaiba ta miqe ta rataya jakkarta sannan tayi gaba, ganin haka ya take mata baya don cika umarnin mr ibrahim.
Rakasu da kallo sukayi sannan suka kalli juna suna ta6e baki
"antafi amsar zero over kunnuwa" inji deeya tana Dariya
"kedai bari, ai shiyasa tundazu take wani cicin magani, tasan abinda ta taka ai" inji rukky tana ta6e baki
"ai dama Allah ba azzalumin kowa bane, gashi ta gina ramin mugunta ta zurma aciki, shiyasa akace ka kiyayi mutum especially ire iren Deen don baka ta6asu ka wanye lfy, gashi yanzu tafara gani ai" inji nurr
"Zata dai fara gani, ai wlh naji dadin yadda Deen ya kashe yar banza da mari rannan, bawan Allah ko yaya jikinshi?" inji sumee
"da sauqi ai ko yau kafin na shiga class saida nabiya department dinshi na tambayi Wannan friend din nashi yace min da sauqi sosai maybe ma cikin week dinnan yadawo school" inji nurr
"To Allah ya sawwake kuma Allah yasaka mashi" inji deeya
Da amin duk suka amsa haushin zee daqare da zuciyarsu, dama yaya lfyar giwa?
Da sallama tashiga office din saurayin na biye daita.
Amsawa yayi Batareda ya dago daga abinda yakeyi ba sannan ya sallami saurayin akan yana iya tafiya.
Juyawa yayi ya fita hakan yasa mr ibrahim Dagowa ya kalleta sannan ya nuna mata seat alamun ta zauna.
Kamar bazata zauna ba sai kuma taja kujerar tazauna a dosane tanajin kamar ta cire zuciyarta ta yar ta huta da nauyin datayi mata.
"nasa agayamaki idan kinzo kizo ina nemanki, saqon ya isa gareta?" injishi yana yan rubuce2
Dagowa tayi ta kalleshi saikuma ta Kauda kai ganin shima na shirin Dagowa
"A'a" tafada a taqaice
Jingina kai yayi sannan ya turomata wata folded takarda a gabanta yana komawa ya jingina da kujera yana dan jujjuyawa
Kallon takardar tayi sannan ta kalleshi zuciyarta na qara quntata
Nuna mata takardar yayi da idanu alamun ta bude, ganin tayi jimm tana kallon takardar yasashi cewa
"open mana"
Hadiye wani yawu mai daci tayi sannan ta miqa hannu tafara warware takardar, zuciyarta na bugawa har wani jiri2 take gani, tasan ta fadi amma ganin abinda taci din ba qaramin affecting dinta zaiyi ba, taso kawai atafi ahaka Batareda tasan me taci dinba ko ba komai tayi preventing kanta from heart attack.
Ida warware tayi cikin qarfin hali tana jan numfashi ahankali sannan ta kalli takardar.
Ahankali manyan idanunta suka fara qara girma harta ida kwalalosu akan takardar tana kallon takardar with greatest shock rubuce a fuskarta.
Dagowa tayi ta kalleshi sannan takuma maida akan takardar tana jin jikinta na tsuma don shock
"waye yai miki?" taji muryar mr ibrahim kamar daga sama
Hakan yasata qara Saurin dagowa tana kallonshi
"yes, ni dake munsan ba ke kikayishi ba, tell me who helped you?"
Kasa amsamashi tayi sai kafeshi da idanu datayi wanda azahiri batama san tayi ba, tunaninta ma tuni yayi qaura daga jikinta ya lula can
"magana nake miss kin tsareni da idanu" yafada yana dan buga table
Hakan yasa tadawo daga duniyar datake shirin dulmiyawa ta kalleshi
"so ta Wannan hanyar kika biyo? Kince zaki iya amma kika nemi taimakon wani? I thought dakanki zaki iya din, Wannan ya nuna gazawarki qarara" yafada yana watsamata kallon raini
Dafe kanta dake mugun saramata tayi ta gangaro da hannayen kan fuskarta ta rufe.
_ya sallam! What have I done?_
_why.. Why.. Why_
Abinda ke yawo aranta kenan
Shi mr ibrahim dayayi tunanin tashiga Wannan halin ne don ganotan dayayi yace
"don haka this paper is on suspense, a qaida dama duk wanda yaci irin marks dinnan musanmman idan ana tantama akan marks din saiya sake yin wani don shafe tantanmar ko kuma ayi cancelling din abin gabadaya... Ke wanne yayi miki? Kin yarda zaki sakeyin wani agabana domin shafe tantama na ko kin yarda kinyi malpractice a cansile?" yafada yana kallonta
Ta dade bata ko motsa ba kuma bata cire hannayenta daga fuska ba hakan yasashi qara cewa
"mallama am talking!"
Sai alokacin tacire hannayenta daga fuskarta, idanuwanta sunyi jawur saidai ko digon hawaye babu a fuskarta
Kallonshi tayi da bloodshot eyes dinta sannan ta lumshe idanu ta bude
Ahankali cikin cracking voice tace
"fix the date, zan.. Chanza wani"
Dama yasan amsar dazata bashi kenan don bata Saurin accepting defeat, ego dinta bazai bariba.
Hakan yasashi cewa
"next week monday, exactly irin wannan lokacin" yafada yana duba agogo
"Thank you" tafada ahankali sannan ta miqe dakyar tanajin haryanzu kanta na sarawa.
Hanyar waje tayi tana dan hada hanya hakan yasata rakata da kallo harta fice sannan ya ta6e baki yana daga kafadu ya cigaba da abinda yakeyi.
Tafiya take Batareda tasan inda take tsoma qafarta ba, jin tafiyar na neman gagararta yasata samun wani icce ta jingina dashi sannan ta sulale ahankali ta zauna qasa.
Ahankali taqara dago takardar tana binta da kallo, ahankali rubutun yafara yimata dishi2 sanadin ruwan daya taru a cikin idanunta, kifa takardar tayi a fuskarta daidai da 6allewar hawayenta... βοΈ
Ummin fasihu π§π»ββοΈ?
8/2/21, 9:32 PM - Buhainatπ: *ππ»ββοΈDEEN ππ»ββοΈ?*
*014*
Batasan tsawon lokacin data dauka ba ahakan sai jitayi an dafata hakan yasata tsagaita kuka marar sautin datake ta dago ahankali.
"ya sallam! Zee lfy?" inji su sumee dama jin shirun yayi yawa yasasu Bin sahu sai ganinta sukayi can jikin wani icce cure wuri guda
"haba zee Wannan ai ba girmanki bane kuka in public ba, idan wani yaganki fa? Hakan ba qaramin zubda m bane" inji deeya tana kamota suka miqar daita tsaye
"komai yayi zafi maganinsa Allah, menene don bakici Wannan ba? Insha Allah zaki fanshe a exam" inji rukky cikin yanayin tausayawa
Dagowa tayi ta kallesu da rinnanun idanunta da sukayi ja sosai saboda kuka, ahankali ta motsa bakinta tace
"ina.. Deen"
Babu wanda yayi magana acikinsu sai kallonta da suke
"tell me please" tafada tana lumshe idonta don ba hawayen dasuka taru damar sauka
"me zakiyi mashi kuma? Kibari ya farfado daga wancan abin da kikayi mashi mana kafin kiyi tunanin dora mashi da wani" inji nurr da dama a wuya take daita akan abinda tayi mashi rannan
Kallonta tayi ta hadiye wani yawu mai daci tace
"where is he? Please" tafada tana kafeta da idanu
Sumee dake bayanta taji tace
"zee, rabon Deen da makarantar nan tun wancan ranar, ashe dama yanada pneumonia, coke din dakika watsamashi ya tado mashi ita, yanzu haka shekaran jiya akayi