Showing 6001 words to 9000 words out of 322641 words

Chapter 3 - DEEN Complete Hausa Novels By Arewa Novels.txt

27 Nov 2025

6127

shigowar mummy falon

Fadin tashin hankalin da akayi a ranar 6ata bakine don mummy liss tayimata ko daga kasawa tayi, shikuma daddy yana dawowa ya tarar da abinda yafaru yahau masifa

Ta inda yake shiga batanan yake fita ba, ranshi yayi mugun 6aci munsanman dayaga yadda jikin zainab din yayi rudu2 jikinta yayi rau alamun zazza6i, abinka da yar hutu

Duk banbamin dayayi qin tankamashi mummy tayi haryayi ya gaji, hakan ba qaramin sake 6atamashi rai yayi ba hakan yasashi korar yar aikin da abin yafaru saboda ita

Wannan abun ba qaramin 6ata ran mummy yayiba amma saitaqi tankawa saidai tasa aranta babu gudu babu ja da baya duk sanda zainab tayi ba daidai ba saita tsawatar mata saidai duk abinda zai faru ya faru don bazata zuba ido diyarta kwara daya duniya da lahira ta lallaceba


Tun daga lokacin zainab tafara tsoron mummy, duk rawar kanta bata yarda tayi gabanta, sosai taja baya daita hakan yasa babu irin Wannan shaquwar ta d'a da uwa atsakaninsu

Hakan na damun mummy amma hakan take dannewa don tasan idan ta sake mata dayawa abin gaba zaici

Haka rayuwa taita gangarawa har zainab tagama primary aka sata wata secondary itama ta masu kudi

Shiganta secondary school yasake ta6ar6are al'ammura don a S.S1 ta hadu da wasu qawaye suma masu jida kudi da Wulaqanci

Kan kace me? Suka qulle kasancewar duk kanwar jace kowacce na taqama da arziqi

Awajensu qawayen ta koyi shigar banza wanda su a wajensu fashion ne

Cikin dan qanqanin lokaci itama ta koya, tayi slim fitting din top din uniform dinta takuma gutsure skirt din yakoma guntun don dakyar yake rufe gwiyagu

Takoma saka dammamun kaya acikin gida sa6anin gowns datake sawa ada


Saida tajima tanayin haka sannan mummy ta ganota kasancewar duk abinda zatayi da taku takeyi saboda mummy yar da eyes don duk wani movement dinta tana qoqarin ganin tasani

Amma dayake zainab 'A' ce saita gwadamata ita yar zamani ce

Idan zata school saita sassauto da skirt din qasa yadda zai zama normal ta dora cardigan akan uniform din yadda baza'aga matsewar rigar ba, dataje school kuma ta cire cardigan din ta maida skirt din yadda yake, agida kuma bata yarda takamata da shigar diban albarkar datake idan tasan zasu hadu saita dora after dress

Ranar da mummy tagano ba qaramin bugu taciba don Wannan karonma saida tayi mata liss dukda daddy nanan kasa qwatarta yayi, haka ta tisata gaba taje ta watso kayan closet dinta ta daukesu

Wannan abin ba qaramin 6ata ran zainab yayi ba shiyasa taqara jan baya daita don aganinta bata sonta kullum burinta ta takuramata, bayan ba haka akema friends dinta ba don su asalin free life sukeyi babu takurawa dukda su sunada yayye da qanne ba kamar ita ba, gani take ita dake ita kadai Awajensu kamata yayi ace ita tasamu kwatankwaci koko fiyeda gatan dasuke samu

Hakan yasata yankewa aranta cewa mummy bata qaunarta don itama wani sa'in tantanmar anya ita ta haifeta kau


Dole tabar shigar banzan agida don anchanza mata closet inda aka tulamata gowns gowns masu kyau da tsada saidai ita bata ganin wani kyaunsu kawai sawa take, uniform ma mummy tasa aka dinka mata wasu kuma duk sadda zata fita zuwa school saita bincikata sannan ta tafi


Ana haka har suka shiga S.S3, anan ne fa suka tsara wai su a qasar waje zasuyi higher institution.

Tare da friends dinta suka yanke cewa uk zasu cigaba da karatu har suna cewa zainab acan zatafi sakewa tayi living free life dinta babu takurar mummy

Jin haka Yasata Jin dadi sosai tana hasaso yadda zatayi rayuwarta mai cike da yanci

Nan suka shiga tsare tsarensu suna planning yadda zasuyi rayuwarsu as classic ladies


Koda zainab ta tunkari daddy da maganar kasa musawa yayi kamar yadda yasaba sabida gudun 6acin ranta

Hakan yasa shi amince mata farat daya, sosai zainab taji dadi takuma qagara suyi final exams dinsu Wato w.a.e.c

Alhamdullilah sunyi exam din cikin aminci sun gama inda suke saka ran samun results mai kyau don sosai suka dage a exams din musanmman zainab dake doqin wucewa abroad, batason result dinta yakawo mata cikas shi yasa ta dage gashi dama tubarkallah zee din badai kwalwa ba

Koda result din yafito taji dadi sosai ganin yadda yayi kyau saidai murna ce takoma ciki jin daddy ya sauya maganarshi ta tafiyarta abroad

Lokacin saida tayi dan qaramin hauka don rudewa tayi ta giggice banda kuka da ihu babu abinda takeyi

Qarin abinda yabata haushi shine jin cewa mummy ce tasa daddy yafasa, baqinciki yasata kulle kanta a daki na kwana daya

As usual daddy ne yashiga damuwa, yayi yayi ta bude kofar taqiya, haka shima yawuni bakin kofar ta yana rarrashi don shima hankalinshi be kwanta da tafiyar ba dama tun farko amsa mata yayi amma ansar bata kai ciki ba saigashi mummy tazo taqara zugeshi inda taita lissafomashi illolin dake tattare da barinta tafiyar

A bangaren mummy kau ko ajikinta, tana ganin yadda daddy yaqi tsaye yaqi zaune sabida fushin zainab din tayi kamar batasan sunayi ba don acewarta wannan shirmen bada itaba

Saida tagaji da fushin ta ta fito don dole jin yunwa zata kassarata, saidai tun Lokacin batada walwala kullum cikin qunci take

Ahaka har Lokacin zana jamb yayi, don tabasu haushi taje taqiyin komai a jarabawar acewarta meye amfaninta bayan ba abroad zataba kuma ita Allah yasani batayin school anan

Koda result yafito daddy beji dadi ba sam don ba haka yasoba itakau mummy tana ganin result din ta6e baki tayi tace idan bazatayi karatunba ai sai ayimata aure tunda ta ita, abu cikin sauqi

Sosai ran zainab yaqara 6aci don dama don taba mummy haushi tayi amma taga alamun bata damuba saima sa6on datayi, wai aure

Ca6! Aikau beyiwuwa, duka nawa take zatayi aure kuma ita ai haryanzu bataga wanda yayimata ba don haryanzu bataga taste dinta ba don ita yana daya daga cikin burikanta ta auri handsome multi-millionaira guy, mai ji da kyau da gayu dakuma naira wanda idan yashiga taro dolene asan da wanzuwarshi

Wannan burin nata yasa bata sauraron kowa don kallon yan jagaliya take musu wadanda basukai level dinta ba

Zainab tanada wani hali na downgrading din mutane musanmman na qasa da ita, tanada halin jin kai da taqama da isa shiyasa ba'a cika shigemata ba saboda halinta don samarin ma masu qarfin hali ke tunkararta wanda daga qarshe dai wulaqanci da cin fuska ke rabasu


Ataqaice dai haka tayi wasting din wannan shekarar wajen xaman gida wanda sam bemata dadi ba saboda takurawar mummy don cikin shekara dayannan saida ta tilastamata iya girki don tisa qeyarta take su shiga kitchen tare

Hakan yasa shekara na zagayowa ta kwantar da hankalinta ta zana jamb din dakyau don sosai mummy kemata barazana da kalmar aure kuma tasan halin mummy tana iya sawa ayimata din

Sai gashi result din yafito mai kyau, daddy yaji dadi sosai, beyi wata2 ba ya sama mata gurbi a jami'ar Umar Musa Yar'adua


Haka dai tafara zuwa school din badon tasoba sai don tasan shine kadai maslaha agareta


Farkon zuwanta school din kamar tayi kuka don takaici, haka dai ta haqura tacigaba da zuwa saidai kwata2 bata qaunar school din

Ba'a qulla wataba aka san da zamanta a school din, ko tsaddadun shigarta basu da shan qamshinta ba tsiwarta da wulaqancinta zaisa kasanta don bata ragama kowa cin mutunci awajenta ba komai bane

Saida tayi wata uku batada qawa ko daya don bata buqata don aganinta duk ta wuce class dinsu, duk yadda yanmata keson cusa kansu gareta qin basu dama tayi don aganinta tawuce ajinsu

Dakyar su nadeeya suka samu shiga suma don yan gayune sun iya gayu gasu 'ya'yan masu kudi dukda basukai zee ba

Su ukune friends dinta da farko Wato *Nadeeya*, *Ruqayya* da *Nuratu* sai daga baya *Sumayya* tayi joining dinsu

Suna abota sosai don Koda yaushe tare suke saidai hakan be hana tana musu wulaqanci ba saidai basu ta6a nuna sunajin haushi dukda kau suna ji kawai shanyewa suke don ko banza tasasu suma sunyi popular a school din
Duk jikinsu tafi son sumee saboda tafi binta yadda yakamata shiyasa tafi dasawa da Ita saidai batasan dukkansu taciki na ciki

Yanzu haka tana level 200 ne (sorry nayi mistake a page 2 nace watanta 4 da farawa, a min afuwa ina nufin shekararta cikin na biyu kenan)

Tana karatun kadaran kadahar don ba laifi tanada kwalwa saidai duk cikin lectures dinsu tafi tsanar na lissafi plus basu shiri da lecturer din dake subject din he is a no nonsense man, yasha dizgata a aji da korata waje idan tayi laifi kuma cikin ikon Allah takasa maida martani don ba qaramin kwarjini yake mataba, hakan yasa tabar attending din lecture dinshi sai exam ko text daya zama dole shima duk yawanci take samun average dakyar don bata attending class dinshi kuma qawayen ta masu attending din duk masu qwalwar dusa ne


Master kau irin wadannan student dinne marassa jin magana masu neme nemen magana da tada zaune tsaye a school

Asalin sunanshi Murtala amma dayake beson sunan sai kawai ya radama kanshi master wanda yabishi don dayawa basusan ainahin sunanshi ba

Iyayenshi talakawane futuk saidai shi yanada hali don har mota gareshi, mutane sun rasa koina yake samun kudinshi dayake bushasha a school, wasu har cewa suke qila fashi yake ko sata don dama yayi kama da wanda zai aikata saidai azahiri yana samun kudinshi ne ta hanyar huldar kayan chaji (maye) anan yake samun kudinshi kuma yakashe a banzace don beta6a taimakawa Iyayenshi ba dake fama da talauci

Master ya dade a school din don karatun nashi kwan gaba kwan baya yake kasancewar beda man kai, hakan yasa duk aka sanshi a school din don yajima acikinta

Tun farko farkon zuwan zainab school din ya kafa kwakwarshi akanta saidai beta6a tunkararta ba saboda yaga yanayinta yar ji dakai ce kuma zatayi wulaqanci, illai kuwa saigashi hasashenshi ya tabbata hakan yasa yaqi tunkararta amma a kullum da kwadayinta yake kwana yake tashi amma kasancewar shi tattacen dan bariki ne kuma ya dade acikinta yasashi qin tunkararta kai tsaye, shima Alex wanda ainahin sunanshi Aliyu yabashi dama ne kawai ya tunkareta don ganin abinda zatayi saigashi tayi abinda yake tsanmmani din kuma ya tabbata ko shine yaje haka zata mashi

Aliyu (Alex), fahad (gandu), Tajudeen (t.j) da Bashir (bash) abokan jagaliyancin master ne, tare suke duk rashin jinsu shiyasa duk ake tsoransu a makarantar Ana shayin shiga gonarsu don sunsan fada da aljani ba riba, sai gashi yau zainab ta ta6o tsuliyar dodo.... ✍️



No editing πŸ™πŸ»


Masu complaining bana turamasu a group dinsu bayan kuma ina ciki don Allah kuyi hqr, wahalar tayi yawa, shiyasa ma natura link din group din a duk groups danake ciki yadda ko yaya ne wasu members din group din zasuyi joining.

Members din group dina please ku dinga sharing a groups din dakuke don Allah, basai nasha wahala bayan zaman typing inkuma dasa da sharing ba, please do this for me uhn? πŸ™πŸ»β€β™€οΈ?

Thanks so much, nasan qauna ce tasaku complaining, nima i heart you so very much 😘

Ana together insha Allah 🀝🏻

Ummin fasihuπŸ§šπŸ»β€β™€οΈ?
8/2/21, 9:31 PM - Buhainat😝: *πŸ™πŸ»β€β™‚οΈDEENπŸ™πŸ»β€β™‚οΈ?*



004




*CIGABAN LABARI*


Aranar dai basu koma school din ba don daga siyar wayar suka wuce yawon shopping kamar yadda suka saba yi duk lokacin da yan qalular school din yataso masu


Sai can wajajen 3pm takira drivernta ta gayamashi inda suke yaje ya daukota suka rabu da friends dinta akan sai gobe idan Allah yakaisu


Acan school kau yinin ranar rumours din abinda yafaru tsakanin zee da Alex yaita zagaye school din, inda duk wanda yaji saiya bayyana alhininshi da doqin sanin wane mataki su master zasu dauka akai, duk inda kaga mutane sunyi group suna magana to zancen suke, Allah Allah suke gobe tayi suga me zai biyo baya don sunsan team din master basa yafiya bare mantuwa.


Zee kau Koda suka isa gida a d'ad'arce tashiga gidan tana zullumin yadda haduwarsu da mummy zai kaya

Tadai san yanzu daddy bayanan bare ya taremata hakan yasata aro nutsuwa ta sa

Da sallama tashiga main falo din gidan, sosai taji dadin rashin ganin mummy a falon hakan yasata yin wuff ta haye sama tashige daki

Saida tayi wanka ta chanza kaya zuwa loose kaya nashan iska sannan ta gabatar da sallar asr da batayi ba sannan ta koma kan gado ta zauna tana jingina da kan gadon tareda miqe qaffafunta saman gadon

Remote ta dauka taqara a.c din dakin tana dan jan tsaki

Allah yasani batason irin weather nan ta zafi, jin zafin tsiya gareta kamar wata mai qiba, yanzu kuma lokacin shi ne don lokacin farko farkon damuna ne, ruwan basu sauko ba sosai don duka duka befi sau uku ba da akayi ruwa.

Bata nemi abinci ba don dama saida suka cika cikinsu Awaje, da daddare kuma sawa tayi aka kawomata har dakinta kuma duk Wannan abin tana yine duk don karsu hade da mummy, abinda bata saniba shine mummy tariga ta wuce wajen don batada riqo sam, a lokacin da akayi abu take hawa da adan jima abin zai sire aranta koda zatayi reacting bazaikai yadda zatayi a lokacin da abin yafaru ba



*WASHEGARI*


Yau bata fita school ba dawuri kasancewar yau lecture din bayan sallar juma'a garesu kasancewar yau juma'a

Sai wajajen 2:30pm tafito bayan taje ta gayawa mummy wanda ke qara jaddada mata cewa da angama takamo hanya suyo gida

Da to kawai take amsawa don tasaba da irin Wannan kashedin nata, har mammaki take wani sa'in, yadda kasan tana magana da wata qaramar yarinya da batasan ciwon kanta ba, abin na bata takaici matuqa amma ya ta iya? Haka take binta Dole kodan gudun mazga


Kamar jiya yauma bala ya budemata back seat tashiga ta zauna kamar bataso
Zagayawa yayi ya bude front seat mazaunin driver ya zauna ya tada motar sannan sukazo suka fice

Tafiya suke kan shimfidaddiyar kwalta cikin normal speed, bakajin motsin komai acikin motar Sai dan sautin motar da kuma alamun tafiya suke

Tsaki taja tana dago kai daga wayar hannunta tana yatsine fuska, jitake komai baya mata dadi hakan yasata juya kanta ga window din motar tana kallon abubbuwan dake gudana waje ta tinted glass din motar

Ana haka har suka qaraso school din, samun wuri bala yayi ya parka motar sannan yafito ya budemata murfin kofar

Tun shigowar motar harabar school din idanuwa sukayi caa akanta, dama yawanci ita suke tsimaye don har yanzu sosuke suga yadda zata kaya tsakaninsu da master dukda tundazu suke raba ido suka ko daya daga cikin team din master amma basuganiba da alama dai yau bazasu zoba


As usual saida tafara zuro kaffarta ta dama mai sanye da pink hill shoe mai madaurai, sosai takalmin yahau kafarta kasancewarta fara tass

Saida taja yan daqiqu sannan ta ida fitowa bayan ta jefa chewing gum abaki kamar yadda tasaba

Sosai aka qara yayyameta da ido saboda shigar datayi mai tafiya da imanin mutane

Sanye take cikin peach english gowns mai adon pink stones agaba

Rigar tabi jikinta ta zauna wanda hakan yasa shape dinta fitowa sosai, kanta yafe da siririn pink veil Sai purse pink da wayarta dake hannunta.


Bata damu da kallon da mutane kemata ba ta dan kalli bala da wutsiyar ido tace
"kaje kawai, zan nemeka but karkayi nisa" tafada kamar mai ciwon baki

"ok, to afito lfy" bata sake bi takanshi ba tafara tafiya cikin takunta na catwalk wanda yazame mata jiki musanmman idan ta lura idanun mutane na kanta

Batayi nisaba suka hade dasu sumee wadanda dama sun dan jima a school din

Saida suka gaggaisa sannan suka wuce class kasancewar lokacin lecture din yayi

Awa daya sukayi lecture din ya daukesu sannan suka fito, kai tsaye wurin dasuke zama idan suna free suka nufa


Wajen bayan wasu classes ne, wurin is quiet gashi yanada shades din itattuwa hakan yasa wurin keda iska mai dadi ga mazauna wurin

Zazzaunawa sukayi kowa na wash! Kamar wadanda sukayi aiki suka gaji

"guys da alama dai bakusan abinda ke faruwa ba ko?" inji rukky

Duk kallonta sukayi kowa nason jin mezata ce

"Hmm to Mr Ibrahim dai ya tafka mana tsiya, wlh jiya attendance ya dauka na wadanda sukayi attending din lecture dinshi, wai kuma yace attendance din a matsayin 50% ne na exams dinshi"

Duk wara idanu sukayi cikin tsagwaron mammakin maganar ta

"dagaske? Waya fadamiki?" inji Nurr

"Hmm zauna nan, wlh abinda yafaru kenan kije ki tambayi wadanda sukayi attending lecture dinshi kiji" inji rukky

"but this is madness! Tayaya za'ayi attendance kawai yazama 50% din exams? Ina aka Ta6a Wannan?" inji Zee cikin tsagwaron mammaki

"Hmm to ai gashi kinga anyi yanzu, ni wlh hankalina atashe yake" inji rukkyn tana buga tagumi da hannu daya

Duk shiru sukayi suka kasa cewa komai, can sai sumee tace
"kutt! Amma malaminnan akwai dan air, ji wata kalar bazata"

Deeya tace "that means carryover for us don duk tsiyarmu bazamuci kingin 50% dinba kunga failing and carryover is the last option"

"lallai kam, don ni babu abinda nake ganewa a lecture dinshi, kawai nasan yana rubutu yana kuma 6a6atu, nidama can na tsani calculations, bana ganewa sam" inji sumee

"kece baki ganewa ko ni? Dama dakyar nake samun naci 20/60 a exam dinshi sai su assignment din da duk googling dinsu nake wanda yake hadawa da marks din cikin lissafi badon haka ba ai da tuni na fado, kawai dai na yarda soyake muyi carryover din don alamu sun nuna muguntarshi ce ta motsa" inji Nurr

"ca6! Aikau baxai yiwuba wlh, wazai qara repeating 1year a Wannan yar iskar makarantar? Kunga kutashi muje musameshi don bamuga ta zama ba" inji zee tana yunqurin tashi

"ina zaki? Kin manta baya zuwa school ranar friday? Kuma ma idan kinje me zakice mashi? Wannan mai baqar zuciyar kamar arnan farko kinsan ko mutuwa kike kina dawowa bazai chanza qudurinshi ba bare dama ga yadda alaqarku take dashi bakwa hada inuwa daya, kinsan ba sauraronki zayayi ba" inji rukky

Komawa tayi tafasa tashin, ta dafe kai da hannu daya
"wlh nasan saboda ni yayi Wannan abun, dama burinshi inyi failing, yaga duk hanyar dayabi saina


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login