Showing 18001 words to 21000 words out of 322641 words

Chapter 7 - DEEN Complete Hausa Novels By Arewa Novels.txt

27 Nov 2025

6125

wanene

Qarasowa mummy tayi fuska ba yabo ba fallasa ta zauna gefen gado don zainab ta gyara zama ta sauko kaffafuwanta qasa

"sannu mummy" tafada kanta qasa tana jujjuya wayar hannunta cikin rashin sabo don kwata2 bata sakewa daita yadda yakamata 'ya ta sake da uwa

"yauwa, kinyi sallah ne?" inji mummy tana kallonta

"eh nayi" ta amsa mata

"abinci fa.. Kinci?"

"A'a mummy, banajin yunwa?" ta amsa tana dan yamutsa fuska

"meyasa?"

"hakanan, banada apettite ne"

Ido mummy takuramata na wani lokaci wanda hakan yasa zainab Jinta atakure

"meke damunki?" inji mummy

Kallonta zee tayi sannan ta Girgiza kai tace
"babu komai mummy"

"meyasa kika dawo dawuri bayan kincemin 2:00pm zaki dawo?"

Rolling idanu tayi afakaice acikin zuciyarta tana cewa 'da mummy yar jaridace da duk wanda ta tisa gaba da tambaya ya bani'


"mummy banajin dadine" ta amsa asanyaye

"meya sameki?" inji mummy tana kafeta da idanu

"fever da headache" tafada tana kwa6e fuska

Kai hannu mummy tayi ta ta6a wuyanta saidai babu zafi

Janye hannun tayi ta tashi tana cewa
"tashi mutafi kici abinci kisha magani"

Zata musa taga mummy ta tamke fuska hakan yasata tashi badon tasoba tabi bayan mummy tana turo baki

Tisata gaba mummy tayi saida taci abinci tasha magani sannan ta kyaleta takoma saman.

Duk motsin da zatayi saita tuna abinda yafaru dazu kuma duk sadda ta tuna saita tsinci kanta cikin 6acin rai, yanzu shikenan mutuncinta yagama zubewa a idon wadancan kucakan yan school dinsu, tasan yau itace topic of discussion a school din, shikenan sunga wallenta.

Haka taita juyi a daren ranar ta rasa abinda kemata dadi gashi barcin ma yaqi zuwa, babu abinda kemata gizo sai fuskar Wannan gayen, haduwarsu tabiyu kenan duk bata dadi ba, lallai Wannan karon saita mashi rashin mutuncin da bata ta6a yiwa wani mahaluki ba, saita tozartashi fiyeda yadda yayi mata, da wannan alwashin barci barawo ya saceta


*DEEN*


Suna zaune abisa tabarma suna tsintar waken da Deen yasiyo na qosan gobe yana bata labarin abinda yafaru school yau kamar yadda yasaba kullum sai yabata lbrin abinda yafaru dashi idan yafita, idan shawara zata bashi saita bashi, idan yayi ba daidai ba saitayimashi gyara idan kuma yayi daidai saita yabamashi


Saida yagama labarta mata komai yadda yafaru sannan ya dago ya kalleta ta hasken wutar nepan dake akwai yace
"wai kaka laifina ne?" ya tambaya yana turo baki

Murmushi kaka tayi sannan tace
"eh to, gaskiya tafika laifi saboda ita tayi maka tsawa harka saketa, tayiwu kuma batasan bakason tsawaba amma dukda hakan be kamata tayimaba daga taimako"

Dadi yaji sosai cikin ranshi Jin ta goyi bayanshi hakan yasashi cewa
"kuma fa kaka itace bata kallon gabanta, itace taita biyowa hanyata bayan sai kaucemata nake amma saida ta bagajeni" yaqarashe yana turo pink lips dinshi

"Gaskiya bata kyautaba, kamata yayi ace tana kallon gabanta idan tana tafiya don koba yau ba tana iya zuwa ta fadawa wani abu dazai cutar daita kaga ina amfani?"

Cafewa Deen da duk dadi yakamashi don kaka tanuna bashi da laifi yayi dacewa
"kuma kaka kodayaushe a fusace take, itace fa Wannan dana cemiki tamin tsawa dana cire gyallen ta a bracelet dina, wancan karon ma haka tamin tsawa kuma na gayamata babu kyau zai cutar daita amma kuma taqara kuma fa na gayamata idan tana fushi tayi inhaling tasbih tayi exhaling tahlil amma kinga batayi ba... "

Murmushi kaka tayi tana qara Jin qaunar shi acikin zuciyarta, he's so innocent, maganarshi ma irin ta yarace, idan mutum yaji maganarshi sai yayi tunanin irin wadanda basuda lafiyar kwakwalwa ne amma rass yake kawai halitarshi ce hakan, haka Allah yayishi shiyasa yake bata tausayi don tasan ba qaramin qalubale yake fuskanta awajen mutanen waje ba don suna iya cutar dashi cikin sauqi don Deen mutum ne da duk wanda ya washe mashi baki to masoyinshi ne, yanada sanyi fiyeda yadda akeso kuma tasan hakan ba qaramin raini zai jamashi awurin jama'a ba musanmman a school, qila ma shiyasa yarinyar tayimashi tsawa, wama yasan adadin masu yimashi tsawan?

Wannan tunanin yakawo kwalla a idanunta tayi hanzarin maidasu don tasan daya gansu to an banu don barci na iya gagararshi tasan halinshi sarai, maida hankalinta tayi gareshi don tundazu zuba yake taji yana cewa

"... Kuma idan adrenaline hormones din mutum yaqara gudu yana iya yin abu Batareda yasani ba ko yayi abinda ya girmi tunaninshi amma taqi ganewa" yafada yana 6ata fuska

Murmushi kaka tayi tace
"ai wasu dama basa ganewa, yanzu dai gobe idan Allah yakaimu idan kaje kuka hade kabata haquri kakuma yimata bayyanin kai bada gangan kayiba, kakuma gayamata bakason tsawa, Tsorata kakeyi saigaka ta fahimceka itama ta baka haquri wataqila batasan bakason tsawa bane"

Kada kai yayi cikin gamsuwa yana cewa
"insha Allah kaka"

Haka sukaita firarsu har suka gama sukayi tatar qullun kokon gobe duk suka kai suka adana suka daura alwalla suka yiwa juna saida safe kaka na jaddada mashi yayi addua idan zai kwanta

Kowannensu saida yayi shafa'i da wutri sannan ya kwanta bayan sunyi addu'ar barci


*WASHEGARI*


Tun bayan sallar asuba suka fito suka fara kiciniyar daura koko da qosai
Deen ne ke hura wuta yayunda kaka ke surfa waken kosai

Saida wutar takama sosai sannan ya dauko qatuwar tukunyar dasuke amfani daita wajen yin kokon ya dauraye ya dora yazuba ruwa aciki

Itakuma kaka ta wanke waken ta cire duka hancin yayi tass, tasa a bokiti tasa watsa taruggu da albasa aciki taba Deen dake jiranta don yakai markade

Kafin yadawo harta tsiyaya ruwan qullun ta daddama acikin bokitai plastic ta rurrufe sannan tashiga hura wutar qosai

Wutar bata ida Kamawa ba yadawo, shi ya amshi hura wutar Itakuma tashiga hada qullun qosan.

Saida wutar takama sannan ya dauko kaskon tuyar qosan ya dora ya bulbula mai aciki ya tsugguna tsakankanin wutan biyu yana gyara duk wadda ta ije

Saida kaka tagama buga qullun qosan ya bugu sosai sannan ta dauki kujera yar tsugguno ta zauna gaban murhun qosai lokacin har man yayi zafi tashiga debar kullun da cokali tana sakawa a man

Ruwan kokon na tafasa Deen ya maido bokitan plastic din kusa2 yasake motsasu da miciya wanda suke amfani daita sannan yashiga sheqa kokon.

Izuwa yanzu har anfara shigowa saye, saida yagama ya maida wani ruwan sannan yazo yafara sallamar masu saye yana zubamasu kokon da qosan

Tun masu sayen suna yan tsiraru har sukayi yawa sosai don da an tsame qosai zakaji yaran nata kiran sunanshi, "Yaya Deen na kaza! Yaya Deen ni za'aba! Yaya Deen nine kan layi!"

Shidai saidai yaita Murmushi yana zubamasu kuma be runton layi, yana sane da wanda yariga wani

Ahaka suka saida duka, lokacin har tara takusa, tare suka tsabtacce gidan yashiga wanka agurguje don yanada lecture 10:00am, atsaitsaye yayi break da kokon da suke diba su ajiye Tun tukunyar farko da qosai sannan yayi mata sallama yafice kaka na rakashi da addu'ar dawowa lfy.


Bangaren zee kau qin zuwa school din tayi yau don batasan yadda zatayi facing school din yau ba bayan humuilation din jiya, tasan maidata zasuyi laughing stock susata jin ta muzanta hakan yasata fakewa da batajin dadi taqi zuwa.

Sosai daddy yadamu da rashin lafiyar qaryanta don ranar yafe zuwa company yayi yatsaya ya kula da shalelenshi, itadai mummy zama yar kallo tayi don yabake komai shi keyimata.


A school kau mutane dadama sunzo yau ne don su tunzura *mud queen* kamar yadda suka samata suna

Wasu ma basuda lecture Aranar kawai abinda yakawosu kenan saigashi tabasu gula taqi zuwa makarantar hakan yasa suka fara cewa kunya ya hanata zuwa.

Deen shima dayaje da niyyar bata hqr kamar yadda kaka tace mashi shima yasamu labarin rashin zuwanta, be damu da hakan ba ya cigaba da harkokin gabanshi

A bangaren mr ibrahim kau shima labarin jiya ya riskeshi yadda yaji labarin yasashi sanin abin yafarune bayan fitowarta daga office dinshi, guntun Murmushi yayi acikin zuciyarshi yana cewa somin ta6i kenan, batama ga komai ba yayinda yashiga shiryama yadda zai 6ullomata ya nunamata kowa yaci tuwo dashi miya yasha.


Suma su Alex sun so ganinta yau amma saiji sukayi bata xoba hakan be damesu ba saima cigaba da shiryamata tarkon dasukayi wanda suke fatan ya d'anu kuma tafada tazama prey dinsu (whoo zee baby mai farinjini 😆)


Wasa2 duk kingin ranakun satin an baza idanu an baza kunnuwa babu zee babu alamunta, nanfa akayi concluding cewa taji tsorone wataqila ma bazata qara zuwa school din ba, kunya yasa bazata iya facing kowa ba.

Sosai Alex ya tada hankalinshi dajin Wannan labarin don sosai ya kwallafa ranshi akanta, master ne ya kwantar masu da hankali cewa ko a qarqashin gadon uwarta ne ta 6uya saisun fiddota sunyi abinda sukayi niyya daita babu mahalukin daya isa ya hanasu.

Bangaren zee kau tana gida duk ranakunnan ta fake da ciwon qarya taqi zuwa saidai duk abubbuwan dake faruwa a school din da magangganun da ake akanta tana sane dasu ta hanyar qawayenta Wato su sumee.

Sosai ranta ya6aci, takuma sake daukar alwashin rama abinda gayen nan yayi mata gashi yanzu da mutuncinta da komai ya zubarmata dashi yaja school din ya gagareta zuwa.

Ranar asabar su sumee sukazo har gidansu zee dubiyar qarya

Zuwansu na uku kenan gidan, koda suka iso babu yabo ba fallasa mummy ta tarbesu don ita haryanzu basu kwanta mata ba dukda idan suna gabanta komawa suke salihan gaske amma kwata kwata basuyi mataba

Zee ta sauko qasa ta tarbesu tawuce dasu dakinta daya jiqu da kayan more rayuwa

Duk sadda zasuzo gidan nan sai hassadarta cikin ransu taqara farashi don ba qarya zee tayi dace, tanada komai da mutum zai buqata arayuwarnan shiyasa wani sa'in basa blaming dinta idan tana wani abin don yes ta isa tayi ne

Haka suka baje dakin suka shiga koromata bayyanan abubbuwan daya faru a school da batazo ba harda qarin gishiri da maggi don abin yabada taste.

Sosai abin yaqara bata haushi nan ta dauki alwashin saita basu mammaki, zata gwadamasu cewa kunya gaba tabata ba bayaba.

Haka taita banbami suna tirata yayinda naciki ke cikinsu, basu sukabar gidan ba sai can goshin magrib, mummy ta hadasu da turraruka masu kyau da tsada ita kuma zee ta hadasu da kayan kwalama dake tile a dakinta suka jide suka tafi akan sai ran monday idan sun hadu a school.

Bayan tafiyarsu zainab taita saqa da warwara akan yadda zata 6ullowa yan school din, sotake ta gwadamasu cewa tawuce duk inda suke tunaninta

Haka ta qarar da weekend dinta wurin tsara yadda zata 6illowa kowanne dan air dayayi qoqarin kawomata wargi a school din.


*MONDAY*..... ✍️


NO EDITING🙏🏻


ummin fasihu 🧚🏻‍♀?
8/2/21, 9:31 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN*



*008*




*MONDAY*


Zaune suke suna labarin duniya kamar yadda suka saba, saidai bala nayi yana duba agogon hannunshi jefi2, ganin abin yayi yawa yasa security din cewa
"yadai mallam bala? Naga sai wani duba agogo kake tundazu"

Tsaki bala yaja yace
"kaidai bari, wlh tundazu madam takirani akan infito tunda wuri zamu fita amma kalla yanzu kusan awata biyu da zuwa amma babu ita ba alamunta" ya qarashe maganar yana jan tsaki

Dan guntun Murmushi security yayi yace
"indai madam ce kaga fin haka, yanzu haka idan ance bata tashi daga barci ba ba'a gardama, kaidai kawai Allah ya cigaba da bamu haqurin zama da wadannan mutanen"
Tsaki bala yasake ja yace
"amin ai ina ganin rayuwa, wlh da badon ina samu sosai da sana'arnan ba wlh da tuni nabar dan iskan aikin, wlh nikadai nasan wulaqancin danake fuskanta a aikinnan"

"Sai muyita haquri ai tunda Allah yariga ya qaddarta tanan zamu samu abinci kuma inda suke burgeni akwai fita haqqin ma'aikata don wlh nasan kafin kasamu inda ake biyan ma'aikata kamar mu sai kaci kwakwa, ga ci da sha mai kyau, kawai dai matsalar itace madam don Hajiya gaskiya babu ruwanta shima Alhaji sai an ta6amashi madam yake rashin mutunci"

"kumafa da gaskiyarka don wlh suna biyanmu fiyeda yadda yakamata, shiyasa na liqe na nace nake shanye duk wulaqancin da akemin amma wlh wani sa'in yadda kasan mammaketa haka nakeji" inji bala

Dariya sukasa security yace
"ai ina ganin qoqarinka wani sa'in har tausayi kake bani idan naga ka rude kana rawar kafa wajen yimata abu"

Dariya suka sake yi, bala yace
"ba dole ba? Ai nikadai nasan tsiwarta da rashin mutuncinta, duk wanda yasani saidai yabiyo bayana"

Kafin su sake wata maganar suka hango fitowarta, hakan yasa bala saurin miqewa yana cewa
"To lambata ta fito"

Dariya security yayi yace
"aikaudai lambarka ta fito"

Be qara sauraronshi ba yawuce wurin Motar dazai kaita da ita ya bude mata kofar baya tun kafin ma ta qaraso.


Tafe take cikin tafiyar ta ta yanga tana taku daddaya

Sanye take cikin baqar after mai igiyoyi a gaba duk ta daddauresu, kaffafuwanta Sanye da black hills masu tsinin gaske, kanta yafe da siririn veil baqi shima wanda tayi simple yafi dashi

Sai black shade data toshe idanunta dashi, ta saqalo black handbag mai masiffafiyar kyau a hannu dayan kuma riqe da faskekiyar wayarta.

Fadin haduwar datayi acikin Wannan shigar 6ata baki ne don baqi ne ya hadu da farar fata hakan yasata fitowa acikin shigar sosai.

Kamar kullum, yau ma heavy makeup ne a fuskarta saidai glass din idanunta ya rufe kusan rabin fuskar baka hangen komai sai jan qaramin bakinta mai daukeda qananun soft lips wadanda suka qara jaa saboda janbakin dasuka sha.

Zee is the real definition of beauty, tanada duk abinda mace ke muradin mallaka a bangaren hallita.

Zee farace irin tass dinnan wanda harda gudunmawar hutu na irinna masu kudi wajen sa fatar yin tass da sheki

Tanada round shaped face mai daukeda dara daran idanu dasuke farare tass sai dan madaidaicin hanci wanda yayi daidai da fuskarta.

Bakinta yafi komai qanqanta a fuskarta wanda yake dauke da two little lips masu tafiya da mutane


Bakinta da idanunta sunfi komai daukar hankali a fuskarta.

A 6angaren structure kuma doguwace amma ba can ba

Tanada diri mai tafiya da hankalin abokan hallitanmu

Tanada madaidaicin boobs cikkaku kuma tsayayyu sai flat tommy dinta mai Kama da wanda ba'a zubama abinci wanda yaqara taimakawa wajen fiddo shape dinta sosai.

Tanada hips sosai don yafi komai girma a jikinta.

Daga wajen cikinta zuwa waist dinta a tsuke yake sai daga waist din zuwa cinyoyi daya bude yabada curve mai tada hankalin mai kallo.

Tanada hips sosai wanda duk a jikinta yafi tafiya sa hankalin mutane, gashi ta iya sarrafashi yadda yakamata don idan tana tafiya ke dake mace saikin bita da kallo bare akaiga namiji.

A taqaice dai Allah yayi mata baiwar kyau da diri da duk wata mace zatayi alfahari da samun irinshi.



Koda ta qarasa ko kallon bala batayi ba bare ta amsa gaisuwarshi saima shigewa datayi cikin Motar a yangace tareda qamewa a bayan motar.


Rufe kofar yayi yayi saurin zagayawa ya shige mazauninshi shima yarufe nashi kofar ya tada motar tareda janta

Zuwa sukayi suka wuce security da tuni ya wangale musu gate suka fice daga gidan gabadaya.



*UMYU*


kasancewar safiya ce kuma safiyar ma ta monday hakan yasa dalibbai harma da mallaman school din kai kawo a harabar school din kowa na abinda yake gabanshi.

Shigowa motarsu zee tayi cikin harabar school din.

Babu wanda ya lura da ita don kowa harkar gabanshi yake kuma babu wanda yakawoma ranshi ita don tuni sunyi concluding tabar makarantar kunya bazai bari tazoba duba da duk kingin rannakun wancan week din batazo ba.

"Bala... Kayi abinda zaijawo hankalin jama'a akanmu" tafada hankalinta na kan wayar hannunta datake daddanawa

Satar kallonta yayi ta mirror kafin yace
"angama madam"


Kamar kau yadda ta buqata hakan yayi, da wani irin gudu mai tada qura ya qarasa parking space din wanda hakan yaja hankalin mafi akasarin mutanen dake harabar school din.

Kowannensu dakatawa yayi da abinda yakeyi ya maido hankalinshi kacokam akan motar kowanne da tunanin dake mashi kai kawo a zuciya


Murmushi tayi ganin duk taja ra'ayin mutane, hakan yasata ba bala umarnin yafita ya bude mata kofa

Babu musu yafita acikin zuciyarshi yana nema mata shiriyar Allah

Cire shade din fuskarta tayi tareda after dress din jikinta sannan ta ciro bubble gum ta jefa a baki.

Tun fitowar bala mutane suka shiga tsantsar mammaki don sunganeshi sosai, shine drivern zee. Wow! Tagama 6oye 6oyen kenan? Tambayoyin da mutanen harabar sukayi kenan a zuciyoyinsu yayinda duk aka kafe motar da ido anason ganin fitowarta.


Kamar kau tasan cike suke da doqin ganinta don saita ta mula tasha iska sannan ta zuro kafar dama mai dauke da hill mai shegen tsini sannan tabiyota abaya cikin wani irin slow motion

Duk sakin baki sukayi suna kallonta dumpfounded

Sanye take cikin royal blue t-shirt mai guntun hannu sai baqin straight skirt mai tsaga a baya wanda ya taimaka wajen bayyana fararan kaffafunta

Agaban rigar daidai gefen saman boobs dinta na haggu akayi wani logo mai kyau da daukar ido mai daukeda zanen crown 👑, zagaye da logo din kuma aka rubuta *BORN TO RULE*

A bayan rigar kuma aka rubuta *THE MUD QUEEN*

Bude shade dinta tayi sannan ta qwamama fuska tana taunar chewing gum din bakinta ahankali sannan ta amshi handbag dinta daga hannun bala daya fitomata da ita ta sagala a hannu sannan tafara tafiya cikin takunta na sabon salo don Wannan salon yafi wanda tasaba zuwa dashi.

Duk binta da kallo akayi baki sake ganin salon datazo dashi school din yau, babu wanda ya ta6a tunanin haka daga gareta don duk a tunaninsu bazata iya hada ido da kowaba don kunya amma saigashi ta shayar dasu ruwan mammaki ganin iskancinta ma gaba yaci ga sunan datayi printing a rigarta wanda yakamata su dinga amfani dashi wajen tsokanarta, alamun sunan yayi mata kuma bazai 6ata mata raiba.


Babu wanda yayi yunqurin tankamata sai rakata da kallon dasukayi kowannensu dauke da yanayi mabanbanta.

A class suka hade dasu rukky wadanda basu san ta iso bama.

Wara idanu sukayi suna ganinta duk sukaje suka rungumeta cikeda murna inda suka zamo yan kallo ga mutanen class din.

Nan suka fara tambayarta ya tabaro spain din? Kamar yadda suka tsara zasuyi ranar dasuka je gidansu

Cikin shan qamshi take amsawa da alhamdullilah sun dawo Suma kuma gifts dinsu na can na jiransu.

Shigowar lecturer class din yasa duk aka nutsu kowanne yanemi mazauni ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login