Showing 63001 words to 66000 words out of 322641 words

Chapter 22 - DEEN Complete Hausa Novels By Arewa Novels.txt

27 Nov 2025

4315

saida kati suka nufa don sayen kati

Koda aka buqaci sunan majinyacin zee ce tabada full name din Deen.

Haka sukaita zirga2 har suka samu aka bude mashi file

Daga nan kuma suka wuce blood bank don siyan jini Saidai an duba kaf babu irin nashi kasancewar 'O' group yake mai wuyar samu

Dawowa sukayi wajen Dr din suka gayamata

Cemasu tayi to agwada acikinsu agani ko akwai meshi idan kuma babu su nemo ko cikin yan uwa, yanzu zata faramashi qarin ruwa, takuma gargadesu akan suyi sauri don jininshi yayi qasa sosai idan ba so suke ya sheqa ba


Haka suka fito kuma suka wuce lab inda ake gwajin jini dukda dukkansu sunsan ba 'O' group ne jininsu ba Saidai kowanne na fatan ace dayan na cikin group din


Sosai zee ke qarfin hali wajen zirga2 nan, don ita kanta da za'a aunata da anbata gado

Saida aka aunasu akaga duk jininsu beyi sannan suka fito jiki a mace

Juyowa mai adaidaitan yayi ya kalli zee dake dauke hawayenta da gefen hijabinta, fuskarta tayi fayau daka ganta saita baka tausayi

Shiru yadanyi sannan yace
"yanzu ya xa'ayi?"

Shiru tayi cikin rashin sanin abin yi don kwalwarta ta toshe

"ko kinada number wani daga cikin yan gidanku sai a kira"


Dagowa tayi ta kalleshi, ita sai yanzu ma ta tuna da kira tsabar yadda kanta yahau chaji

"eh amma banida waya ta fadi" tafada cikin sauri

Zura hannu yayi cikin aljihu ya Fiddo tashi

"ga wannan ki kira daita" yafada yana miqamata

Saurin amsa tayi hannu na rawa tashiga loda number daddy kaida gani tana cikin zaquwa


Dialing din number tayi ta kara a kunne idanunta na durar ruwa

_line busy_ akace mata Hakan yasa tayi Dialing din number mummy


Bugu biyu aka daga mummy tayi sallama cikin nutsuwa


Jin muryar mummy yasata fadawa cikin shauqi kukan datake dannewa Tundazu yafito

"subhanallilah! Zainab? Zainab kece? Hello?" inji mummy a rude

Duk yadda taso tsaida kukan saita kasa sai shesheqa take takasa magana

Can taji muryar daddy qasa qasa da alamu da mummy yake magana can kuma taji muryarshi yana kiran sunanta shima da alamu amsar wayar yayi

"daughter? Please talk to me, is that you?" yafada cikin tsananin damuwa

Dakyar ta tsaida kukan tasamu ta bude baki
"Daddy na.." saikuma ta fashe da kuka

Mai adaidaita yana gefe sai kallonta yake cikeda tausayawa

"ya ilahi! Daughter ina kika shiga? Gamunan hankalinmu duk ya tashi babu inda bamu jeba amma babu ke? Ina kike? Why are you crying?" yafada kamar shima zaiyi kukan

Jan majina tayi sannan tace
"Daddy muna asibiti, zai mutu. Haryanzu ban ganshi ba, be tashi ba" tafada cikin kuka sosai

"subhanallilah! Hospital? Meya sameki? Wazai mutu? Wane asibiti kuke?" ya jero mata tambayoyin lokaci guda

Kukan datake yasa takasa amsawa Hakan yasa mai adaidaitan amsar wayar hannunta ya kara a kunne yayi sallama

"wslm, bawan allah meke faruwa dan allah? Meya samu daughter? Wane asibiti kuke?" inji daddy hankali tashe

"amm.. Asibitin qwararu (medical centre) kuma jiki da sauqi amma so samu kuzo" yafada calmly

"to.. To.. Gamunan, Gamunan yanzu yanzunan, Gamunan..."

Kitt... Aka yanke kiran

Juyawa yayi wurin zee data sulale ta zauna kan wata kujera sannan ya qaraso shima ya zauna daga dan nesa da ita

Kallonta yasake yi yana neman kalmar da zaiyi amfani daita wurin rarrashinta

"dan allah kibar kukan nan haka, insha allah allah zai tashi kafadunshi, a halin yanzu yafi buqatar addu'armu fiyeda komai, kiyi hqr allah baya dorawa bawa abinda bazai iyaba" yafada cikin rarrashi

Hakan ya dan taimaka don ta rage kukan sai shesheqa datakeyi akai2 jin kanta take kamar ba nata ba, kamar ta cire ta jefar ko zata huta


Shiru wajen ya dauka kowa da saqe saqen dayake duk suna jiran tsanmmani yayinda hankalin mai adaidaita duk yayi gida yasan matarshi nacan hankalinta atashe, sake duba agogon wayarshi yayi yaga 11 takusa gashi batada waya bare ya kirata ya gayamata halin da ake ciki

Gashi ita kadai ke gidan kasancewar duka2 watansu bakwai da aure yanzu haka ciki gareta na wata biyar Hakan yasa yaji duk hankalinshi yayi gida don yasan duk inda take hankalinta a tashe yake shi gudu ma yake kar tace zata fita cikin daren nan don yasan halinta qaramin aikinta ne tace zata tafi nemanshi gidansu, gashi Tundazu yake neman wayar qannenshi bata shiga

Komawa yayi ya jingina da kujerar ya harde hannayenshi a qirji yana karkada kafaffu, allah allah kawai yake mutumin dasukayi waya dashi yanzu din ya qaraso ko zai samu shima yatafi don bazai iya barinsu ba a wannan halin... ✍️


Manage👏



Ummin fasihu 🧚🏻‍♀?
8/2/21, 9:34 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?*





*024*




Zaune suke Shiru na wani lokaci, can ringing wayar mutumin ta dawo da kowanne daga duniyar tunaninshi

Duba wayar yayi yaga daddy ne

Dagowa yayi ya kalli zee dake kallonshi itama

"shine, qila sun qaraso" yafada yana dan yimata murmushi sannan ya daga

"assalamu alaikum"


"wslm, d'ana gamunan mun qaraso kuna ina ne?"

"ok bari nazo reception sai nataho daku" inji mai adaidaitan sannan ya katse kiran

Kallon zee dake suraronsu Tundazu yayi

"bari naje na taho dasu"

Kada mashi kai kawai tayi ya tashi ya tafi

Lumshe idanu tayi tana jin yadda kanta ke sara haryanzu



Koda mai adaidaitan yaje reception waige2 yashigayi don ganin inda zai hango mutumin


Yana cikin haka yaji an dafashi saurin juyowa yayi saiyaci karo da wasu yan sanda biyu, daya hannunshi riqe da waya yana kira yayinda daidai lokacin wayar mai adaidaitan tafara ringing


"shine" inji mai kiran yana sauke wayar daga kunne

Binsu da kallo mai adawo keyi gabanshi na faduwa, shine wa? Meye kuma nashi da yan sanda?


Kamar sun karanci tsoronshi don haka daya yace
"karka damu abokina, ni sunana A.s.p Jamal Qaseem, muna tareda mahaifin wannan yarinyar, fatan kaine mukayi waya dashi dazu"


Kada masu kai kawai yayi don shi bega abin tattago yan sanda ba a wannan case din

"ok muje, gasucan ku gana" inji dayan yana gwadamashi hanya

Ba musu yawuce suka takemashi baya har suka isa parking space daga gefe inda wata dalleliyar mota ke a parke securities takoina

Qarasowarsu wajen yasa A.s.p Jamal yawuce wajen motar ya kwankwasa

Mai adaidaitan besan ko me yace ba sai gani yayi an bybbude back seat din an fito


Wani mutum yagani wanda kallo daya zaka mashi ka gane ba qaramin mutum bane saboda cikar haiba da qwarjini irinna masu arziqi sai macen da kallo daya zaka mata kasan jinin zee ce saboda matsananciyar kama dasukeyi

Cikin nutsuwa suka qaraso wajensu mai adaidaitan, daddy na kafeshi da kallo

Sauke kanshi yayi cikin jin nauyin daddyn ya shiga gaidasu yana dan russunawa cikin zuciyarshi yana gulmar wai ashe masu kudine wadanda ya taimaka?

Amsawa sukayi atare sannan daddy yace
"bawan Allah kaine mukayi waya dakai yanzu?"

Qara dan duqar dakai yayi yace
"eh alhaji nine"

Ajiyar zuciya daddy ya sauke na jindadi yace
"to ina take? Ina daughter? Hope babu abinda ya sameta" yafada cikin damuwa


Kada kai mai adaidaitan yayi yace
"babu abinda ya sameta insha Allah, muje ku ganta" yafada yana basu hanya

"yauwa muje"

Nan suka shiga asibitin bisa jagorancin mai adaidaitan



Zee dake zaune haryanzu Saidai yanzu ta hada kai da gwiwa tayi shiru taji alamun tafiyar mutane na kusantota Hakan yasata dagowa da jajjayen idanun ta

Su daddy da mummy ta hango tafe da wasu mutane da bata wani tsaya tantancesu ba

Tashi tayi azabure ta nufi daddy da gudu

Fadawa jikinshi tayi ta kankameshi tana sake Fashewa da kukan da yanzu yabar zuwa da hawaye don suma idanun izuwa yanzu sun gaji da zubda kwalar

Maida hannuwa shima daddy yayi a bayanta ya rungumeta yana sauke ajiyar zuciya


Dagota yayi yayi cupping fuskarta a taffukan hannunshi yana bin fuskarta da kallo

"are you ok daughter? What happened? Meya samu fuskarki?" yafada yana bin fuskarta da duk sahun yatsun marukan datasha suka fito sukayi jajur abinka da farar fata kuma ta hutu

Batace komai ba sai qara komawa jikinshi datayi tana cigaba da kukan

Janta yayi wajen kujerar data taso ya zaunar daita shima ya zauna ya cigaba da rarrashinta


A dayan bangaren kuma mai adaidaita wanda yace sunanshi Ahmad yake bawa yan sandan bayyanin yadda suka hadu dasu dakuma inda yagansu

Saida suka gama sauraron dukkan bayaninshi sannan ya nemi su barshi yatafi gida don yabaro iyalinshi ga kuma halin datake aciki

Basu qi ba Saidai sun amshi number wayarshi sannan mummy tayita mashi godiya da fatan gamawa da duniya lafiya

Saida zai tafi sannan daddy shima yataso daga wajen zee dake narke jikinshi yana ta rarrashi Tundazu yazo shima yaita yimashi godiya yakuma debo kudade masu yawa yabashi, dafarko yaqi amsa amma ganin ya nace yasa ya amsa ba don yasoba ya tafi da alqawarin zai shigo gobe insha allah yaga mai jiki


Daga nan office din Dr Basira suka nufa don zee ta nace akan itadai Deen, karya mutu

Sosai Dr tayi mammakin ganin babban mutum kamar Alhaji Farouq a office dinta

Tarba tayi masu na mutunci sannan sukayi mata bayyani
Tayi mammaki sosai ganin cewa ashe diyar dan faranshi tayima haka, Hakan yasa ta tashi tafara rawar jiki wajen ganin an kula da Deen yadda ya kamata sannan ta qara gayamasu ana buqatar jini cikin gaggawa don nashi yayi qasa kuma gashi babu irin nashi a hospital din

Abunka da manya waya kawai Alhaji yayi wa family doctor dinsu ya fadamashi buqatar shi, cikin qanqanin lokaci saigashi a hospital din da jinin nan aka shiga qaramashi ana bashi taimakon gaggawa wanda za'a samu adan shawo kanshi kafin gobe da safe da za'a basu transfer sukoma wata asibitin


Zee ma daga baya kwantar daita akayi saboda wani zazzafan zazza6ine ya lullu6eta itama, Hakan yasa aka bata gado itama aka duqufa akan su biyun don ganin an shawo kan matsalarsu.



*KAKA*


Tunda aka fara iska iskar hadari hankalin kaka yaqi kwanciya

Sai duban hanya take taga ta inda Deen zai 6ullo amma Shiru kakeji

Hankalinta ne ya ida tashi lokacin da aka kece da ruwa, idan ta tuna da kayan daya fita dasu sai hankalinta yaqara tashi

Haka ta zauna bakin kofar dakinta ta buga tagumi tana hango qofar shigowa cikin jiran tsanmmani amma Shiru kakeji wai mallam yaci shurwa

Tun tana daukar abin wasa har abin yafara bata tsoro, tun tana jiran agama ruwan har taji bata iya wannan haqurin.

Hakan yasa tafito cikin ruwan tareda yar lemar ta (umbrella) ta nufi gidan maqofcinsu wanda ya samomashi form din company dinnan

Ta dade tana bubbugawa sannan aka bude gidan

Sosai maqofcin wato mallam Nasiru yayi mammakin ganin kaka cikin wannan ruwan da ake tsugawa

Iso yayi mata ta shigo ciki nan tashiga gayamashi abinda ke faruwa cikin matsar qwalla

Kwantar mata da hankali mallam Nasiru da matarshi suka yi da cewa wataqila fakewa yayi har ruwan ya dan tsagaita sannan yataho tunda shima yasan da lalurarshi bazai yarda yashiga ruwan ba

Da wannan hankalin kaka ya dan kwanta Saidai still takasa komawa daidai, bini bini ta kalli agogo zuciyarta na qara tsunduma cikin fargaba

Haka dai matar mallam Nasiru ta zauna da ita suna jiran tsanmmani

Ganin har magrib ta gabato babu Deen ba alamunshi yasa hankalinta ida dugunzuma

Kuka kawai takeyi tana cewa itadai makarantar nan zata tafi, tana ji aranta duk inda Kamal yake ba lafiya ba

Tun Mallam Nasiru na rarrashinta akan tabari ruwan ya tsagaita har ya haqura yaje yasamo mai adaidaita na cikin unguwa suka shiga dashi da kakar mai adaidaitan yajasu zuwa makarantar

Kafin su isa makarantar ruwa ya tsagaita sosai don harya koma yayyafi

A bakin gate din makarantar suka sauka sukaje nufi wajen mai gadi

Sosai mai gadin yayi mammaki jin wai wani suka zo nema nan yace musu gaskiya baya tunanin akwai sauran student ko daya a school din don tun hadarin nafara taruwa suka fito dama ba yawa garesu ba yan qallilan ne dake qarasa Jarabawarsu yau kuma suna fitowa motar school ta kwashesu ta tafi dasu don kosun tsaya ba samun abin hawa zasuyi ba

Dukda haka kaka tayi insisting akan itadai a duba wataqila shi be fitoba

Babu yadda suka iya haka suka shiga makarantar aka fara nemanshi


Every nook and cranny saida suka duba babu Deen babu alamunshi, kuka kau kaka ta shashi harta godewa allah

Dakyar aka rarrasheta akan su koma gida sugani qila yakoma, wataqila harda shi aka shiga bus din saiya fake cikin unguwa kafin ruwan ya tsagaita

Haka suka fita suka shiga napep din kaka nata kuka suka nufi gida kowa na addu'ar allah yasa su taddashi gidan


Fitarsu kaka daga school din keda wuya motarsu daddy ma tashigo

Suma the same story ne da kaka don ruwan saman ya hana bala zuwa daukanta sai yanzu suka samu yadan tsagaita suka taho Saidai suma the same amsa mai gadin yafada masu

Suma basu yarda ba suka shiga school din suka duba koina babu ita ba alamunta Saidai duk nemansu babu wanda ranshi yabashi su duba can bayan school din don basu ta6a kawoma ransu ba don school din nada girma da fadi kuma can bayan school din duk jejine bazasu ta6a kawo ma ransu zasu nufi wajen ba

Suma haka suka haqura suka tafi

Wasa wasa abu qarami yazama babba don koda su kaka suka dawo gida babu Deen Hakan yasa hankalin kaka yayi qololuwar tashi, kuka take tana fadin dan allah a nemomata dan marayanta, bashi da kowa sai ita itama batada kowa sai shi

Cikin qanqanin lokaci labari ya kewaye unguwa, Deen din kaka ya 6ata

Saigashi cikin daren nan gungun mazan unguwar, matasa da dattijawa suka bazama neman Deen yayinda mata sukaita shigowa gidan kaka suka zauna daita anata rarrashi da jaje


A bangaren su daddy kau koda labari ya riskeshi akan ba'a ganta a school ba hankalin shi ne ya tashi, gashi anata neman number ta bata shiga Hakan yasa shima fitowa aka shiga neman dashi

Dafarko police station suka nufa inda daga nan aka qara komawa school din don qara bincikawa Agefe kuma aka kira school authority din aka gayamashi abinda ke faruwa

Hankali tashe shima yakira wasu manyan school din suka dunguma sukayi school din

Sosai aka shiga nema again ana chaje koina na school din Saidai babu ita.


Hankalin daddy yatashi sosai Hakan yasa ya baza jami'an tsaro akoina don nemo mashi tilon diyarshi

Itama mummy hankalinta ya tashi sosai, tsakanin uwa da 'ya sai allah saigashi sai dauke hawaye take akai2, addu'arta kawai allah ya karemata diyarta a duk inda take

Sai wajajen shadaya ne kira yashigo wayar mummy, tana ganin kiran taji ajikinta cewa kiran nada alaqa da Zainab Hakan yasa tayi saurin dagawa

Jin kukan Zainab yasata yin sallalami takira sunanta wanda Hakan yaja hankalin daddy dake gefe baya zaune baya tsaye yana amsar kira takoina

To shine fa yazo ya amshe wayar hannun mummy inda anan sukaji ainahin inda zee din take.


A bangaren kaka kau kwanan zaune tayi akan sallaya don wajajen shabiyu tawagar neman Deen suka dawo basu ganshi ba amma sun aje akan gobe da angama sallar asuba zasu qara bazama nemanshi dukda sunkai rahoto a station din unguwar

Abinda zai burgeka shine yadda kowa ke jajjantawa al'amarin dakuma yadda kowa ya damu don masha allah Deen mutumin mutane ne bayada matsala ko kadan

Duk wanda ya budi bakinshi a wajen sai kaji yanata kwararo yabone akanshi


Dakyar dai matan suka samu suka lalla6a kaka tabar kuka sannan dayawa suka koma gida suna fatan allah ya bayyanashi inda wasu kamar su matar mallam Nasiru da wata dattijuwa tsarar kaka wanda suke amintaka sosai da ita suka tayata kwana

Yadda kaka taga rana haka taga dare don kwana tayi zaune akan sallaya tana kwararo ma Deen addu'o'in tsari a duk inda yake




*WASHEGARI*


Alhamdulillah zee taji sauqi sosai don yanzu babu wani zazza6i a jikinta sai murar datake dakuma yan ciwukkan dataji da akayi treating dinsu

Da safen akayiwa Deen da har yanzu bai farkaba transfer daga wannan asibitin zuwa asibitin kudi inda family doctor dinsu yake

Duk yadda akaso zee tabi mummy su koma gida don itama ta huta qi tayi da taga za'a matsamata ma saita sa kuka Hakan yasa daddy yace abarta don idan akwai abinda ya tsana to kukan shalelenshi ne


Acan private hospital din yan sandan jiya wato su A.s.p Jamal suka iskesu, lokacin har anyi admitting din Deen likitoci sun duqufa akanshi suna baje kolin basirarsu ta wannan fannin


Zee suka samu suka nemi ta gayamasu duk abinda yafaru

Bata 6oyemusu komai ba ta warware masu duk abinda yafaru tana kuka


Ran Alhaji farouq ya 6aci sosai yabada umarnin aje akamo masu sa hannu a wannan abin duk inda suke sannan a dayan 6angaren kuma a nemo dangin Deen don yasan suma sunacan cikin tashin hankali

Amsawa sukayi da angama suna bashi tabbacin cika aikinsu yadda ya kamata





*UMYAU*


School ne ya rikice lokacin da labarin abinda yafaru jiya ya riski yan tsirarun mutanen dasuka zo school din

Abin be ida rikicewa ba saida yan sanda suka dira school din

Can bayan school din kamar yadda zee tayimasu bayani suka nufa inda anan suka tsinci littatafan Deen dasuka jiqe suka 6aci da cha6i sai jakkar zee da gyallenta sai agogon daya daga cikinsu master


Sosai hankalin mallaman makarantar yatashi jin abinda yafaru a bakin polisawan

Nan da nan aka fifiddo files dinsu master dasu sumee na makarantar don bincike


Babu 6ata lokaci aka watsa yan sanda don kamo mutanen da ake zargi

Cikin sauqi aka ritsa dasu sumee kowacce a gidansu

Zokaga tashin hankali wajen wadannan ahali dasu kansu su sumee

Abin yazo masu mugun bazata don ko kusa basu ta6a tunanin abin zai juye masu haka ba tunda su aganinsu an riga an gama daita babu yadda za'ayi a zargesu

Duk hada kansu akayi akayi station dasu aka garqame


A bangaren su master kau, anyi neman duniyan nan ba'a gansu ba don kowannensu babu wanda iyayensu ko danginsu suka san inda suke, wasu ma rabon da susasu dansu a idanu mantuwar harta manta musanmman ma iyayen master wadanda sun tsufa ga talauci daya qarawa tsufan tsanani

Abin tausayi haka aka kama uban kowanne aka riqe akan idan aka ganosu za'a sakesu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login