Showing 141001 words to 144000 words out of 322641 words
Chapter 48 - DEEN Complete Hausa Novels By Arewa Novels.txt
wai duk inda zataje yana maqale daita har hotunansu ma Saida ya daukomin don su zama evidence.
Gabadaya ya shiga rayuwarta kullum da irin zugar da yake mata yana huremata kunne yana nuna mata wai sonta yake itakuma dayake she's dull takasa ganewa, mataki zan dauka akai tsatsaura kau, lokaci kawai nake jira" yafada cikin 6acin rai
Kan mummy ya kulle
"ni sai inga kamar wannan duk misunderstanding ne, yaron is very calm and quiet, kamar bazai iya Hakan ba"
"hmm wai ke kenan da kike babba bare ita da take qarama, kice inbar ganin laifinta don bata gane abinda nake nusar daita ba tunda kema gaki kin gaza ganewa"
"ba Haka bane Alhaji, Zainab ta sameni tagayamin komai kuma da gamsu dasu, wlh daddy a kallo daya idan kayima yaron zakasan yanada nutsuwa sosai, bakaga Zainab ta chanza ba taqara hankali a yan kwanakinnan? Tafada min duk shine sila bayan Hakan ga siyarda rayuwarshi dayayi wajen cetonta a wannan incident din nasu a school, da ba don shi ba da wani labarin mukeyi daban yanzu"
Daddy dayayi sakato Tundazu yana jinta ya girgiza kai cikin takaici
"ansha fadamin mata basuda hankali amma ban ida yarda ba sai yanzu.
Wato ta nan kuma ya 6illo? Dama ai shi tallaka be ta6a taimako don Allah ba, dole don ribar kanshi yakeyi Yayinda mu kuma sukeso mu kyautata masu don Allah
To idan maganar taimakon ta dayayi ne yazo yayi naming price dinshi ko nawa yakeso zan bashi, ladar taimakonta dayayi, ba shikenan ba?
Yazo ya fadamin ko nawa yakeso zan bashi amma wlh diyata tafi qarfinshi, diyata matar manya ce!
Kuma shiriya ta allah ce idan baki sani ba, dama can nasha gayamiki yarinta ke damun ta zata bari kece baki yarda ba shine kuma yanzu da shiriryar tazo zaki alaqanta ta da wani can, dama mutum ke shirya mutum ba allah ba?"
Mummy da duk ranta ya jagule akan magangganun da daddy ke fadi tace
"Alhaji ba Haka bane..."
"to yaya ne? Yaro yabi ya kallalameku da qarya da komai kun yarda dashi?
Nifa matafiyine mai shiga jama'a daban daban mai kuma hulda da juma'a masu mabanbantan hallaya.
Na fiku sanin me duniya take ciki.
Ke kanki kinsan case din Alhaji Hassan da surukinshi wanda haryanzu abu yaqi ci yaqi cinyewa
Shima ba ta wannan sigar yazo ba ya kwantar dakai ya ruda diyar mutane aka bashi ita
Yanzu kullum gasucan hanyar court suna sintiri ya danne duka dukiyarta yasa ta chanza komai nata da sunanshi ya handame komai, ko zakice baki san da Hakan ba?" yafada cikin hayayyakowa
Shiru mummy tayi takasa cewa komai
"shifa tallaka a duniya bayada babban maqiyi kamar mai arziqi don gani yake be kamata shi a hanashi ba wasu kuma abashi besan komai ikon allah ne ba muma bamu mukayi wa kanmu ba.
Kullum burinshi tayaya zai ra6emu ya kwashi na kwasa ya gudu
Babu wata soyayya a tsakanin tallaka da mai kudi duk qarya ce don kowacce qwarya da abokin ragayarta.
Idan har kikaga Hakan to akwai cuta aciki musanmman irin wannan case din da ita macen itace mai kudin, dama ace namijin shine mai kudin da da sauki don ana saran zai iya controlling dinta amma a wannan case din fa? Ita kanta kacokam a qarqashinshi take inaga maganar dukiyarta?
Saboda haka na riga na ajiye magana kuma ta ajiyu
Tunda kika ga nayi burus daita dukda nasan halin datake aciki Hakan ya isa ya nuna miki babu gudu babu jada baya a wannan maganar don bazan ta6a barin inzama silar cutar da diyata daya da allah yabani ba.
Don haka taje taita nema, ni ba matsa mata zanyi ta kawo miji dawuri ba, she should take her time wajen Fiddo wani responsible one bazan damu da tsawo lokacin dazai dauka ba Amma batun wannan yaron abu ne da bazai yiwuba wlh.
Kuma shima zan sameshi, zan bashi damar rabuwa daita ta lallama idan kuma yaqi zan gwadamashi true colour dina, zai gane ba kowanne mai kudi ake jadashi a wanye lfy ba"
Yana kaiwa nan ya juya ya gyara kwanciyarshi ya rufe jikinshi har kai ranshi na qara 6aci yana kuma qara jin tsanar Deen a zuciyarshi
Shiru mummy tayi takasa cewa komai, sosai ranta ya jagule taji komai ya sake kwa6e mata, batasan daddy yayi nisa har haka ba, nisan da bazai ta6a jin kiraba inba wani iko daga allah ba.
Gyara kwanciyarta itama tayi ta lumshe idanunta batareda ta qara cewa komai ba ta cigaba da saqa da warwarar wannan rikittacen al'amarin a zuciyarta... ✍️
Ummin fasihu 🧚🏻♀?
8/2/21, 9:38 PM - Buhainat😝: *🙍🏻♂️DEEN 🙍🏻♂?*
*047*
*THE PROMISE*
Washegari Zee tayi ta jiran feedback daga wajen mummy amma shiru don ko makamanciyar maganar mummy bata tadomata ba
Haka ta haqura ta wuce school ranar tana tunanin qila bata kaida yimashi maganar ba, haka ta haqura a zuciyarta tana fatan koma da yaushe zata mashi maganar allah ya dorasu a kanshi.
A school ma ranar tare suka wuni da Deen wanda bayada lecture ma kwata2 a ranar kawai zuwa yayi don ita.
Sunyi karatu sosai don yanzu sun koma kamar da karatu suke babu kama hannun yaro don exam is at the corner dukda da dan saura ga lokacin.
Sai bayan zuhr sukayo gida inda su zee ne suka fara tafiya sannan shima daga baya yafito yasamu abin hawa shima ya wuce unguwarsu.
Deen hankalinshi Kwance yake gudanar da al'amuranshi don ko kadan besan abinda ke faruwa ba a 6angarensu zee ba.
He never saw anything like that coming shiyasa yake gudanar da al'amuranshi hankali Kwance.
Ya dade yana daily addu'o'in shi daya saba duk bayan kowacce sallah sannan ya shafa.
Saida ya dan qara yin Jimm a masallacin kafin daga baya ya tashi ya fito.
Babu mutane sosai a wajen masallacin Hakan yasa ya zura takalminshi kawai ya fito daga masallacin don komawa gida don dama shi daga masallaci sai gida, salmanu yasha tsokanarshi wai kamar mace ko irin fitowa wajen mai shayi beyi yadan rage dare yafison daya gama sallar isha'i yakoma ya qunqume gida kamar matar kulle
Shidai be ta6a tanka mashi ba Saidai yayi Dariya kawai a wuce wajen don shi bejin zai iya wannan zaman na majallisar mai shayi duba da yadda kodayaushe wurin ke cike da matasa anata hayaniyar cafta irin nasu na maza, shi idan yaje ma ai ciwon kai zai jama kanshi a banza saboda hayaniyar wajen, gwara shi salmanun dayaga zai iya yayi.
Tun daga nesa ya hangi wata mota parke a daga dayan gefen santarsu daidai gaban gidan Mallam Nasiru
Be kawo ma ranshi komai ba ya cigaba da tahowa kai a qasa yanata lissafe lissafe a zuciyarshi
Daidai yayi hanyar shiga gidansu yaga an dallareshi da hasken motar
Dan juyowa yayi yana kallon motar yana dan kare fuskarshi saboda yadda hasken yayi reflecting din fuskarshi
Kamar kau mai motar ya sani sai gani yayi an kashe hasken
Sake Juyawa yayi zai wuce aka qara dallaro hasken wannan karon harda dan horn Hakan yasa ya qara tsayawa ya juyo yana kallon motar.
Gani yayi an bude murfin mazaunin driver wani ya fito.
Tsayawa yayi yana kallonshi har ya tsallako 6angarenshi ya qaraso wajenshi sai a sannan ya lura da fuskar mutumin, bala ne drivern zee.
Qarasowa bala yayi wajenshi cikin fara'a ya miqa mashi hannu shima Deen ya miqa mashi hannu yana murmushi suka gaisa
"Tundazu muke nan muna jiranka, wani yaro yace mana kana masallaci"
Murmushi kawai Deen yayi tareda Kada kai alamun haka ne
"lafiya dai ko?" inji Deen yana kallon motar dake can gefen titin parke
"lfy qalau wlh, kawai Alhaji ne keson ganinka, mu qarasa idan babu damuwa yana ciki" yafada yana nuni da motar
Qara bin motar Deen yayi da kallo sannan ya kalli bala yayi mashi dan murmushi yace
"ba damuwa, muje"
Atare suka sake tsallakawa dayan barin da motar take suka nufi inda motar ke a parke
Saida suka qaraso sannan bala yayi saurin Qarasowa ya bude back seat saiga daddy ya bayyana a zaune takardar jarida a hannunshi yana dubawa
Jin an bude kofar yasashi Dagowa daga kallon jaridar dayake ya kallesu.
"Gashi nan Alhaji" inji bala yana komawa daga baya yadda Deen zai bayyana ga Alhajin
Ganin daddy yasa Deen jin kunya don be ta6a tunanin shine ba
Fuska dauke da murmushi Deen ya zame qasa ya tsugunna yana gaida daddy cikin girmamawa.
Sai ji daddy yayi wani iri don rabon da ayimashi irin wannan gaisuwar harya mance
Sai kuma yayi saurin kawar da zancen a kanshi yana tuna tattaunawar da sukayi da Alhaji Abubakar dazu har yana cemashi talaka babu abinda bazaiyi ba na kwantar da kai duk don yasamu shiga domin suna iyayin komai don cikar burinsu.
Kawar da wannan tunanin yayi yashiga amsa ma Deen cikin fara'a yana cemashi ya tashi.
Tashin Deen yayi cikin sunkuyar dakai don shi harga allah kunyar daddy yakeji sosai
"zagayo abokina, zuwa nayi mu tattauna" inji daddy cikin fara'a
Gaban Deen yadan fadi da jin Hakan, badai yasan komai ba? Wayyo ya zaiyi da kunya?
Haka dai ya zagayo din kamar yadda ya buqata, ya bude kofar dayan gefen ya shigo ya zauna a darare yana dan wasa da band din hannunshi kamar irin amaryar nan idan ana siyan baki duk yabi ya takura.
Ajiye jaridar hannunshi daddy yayi ya gyara zama ya juyo yana kallonshi yana kallon yadda yakasa sakewa kwata2, sai yadanyi murmushi
"Kamal ko?" inji daddy yana kafeshi da idanu
Dagowa Deen yayi ya dan kalleshi sai kuma yayi murmushin tabbatar da Hakan
"Ina wuni Alhaji" yasake gaidashi a karo na biyu
Dan murmushi daddy yayi yace
"lfy lau, ya mutanen gida?"
"Duk suna lfy lau
"ya school? Ana dai maida hankali sosai ko?"
Murmushi Deen yayi yace
"insha allah daddy"
Shima daddyn murmushin yayi yana Kada kai
"to allah ya taimaka"
Da amin Deen ya amsa trying so hard wajen controlling nervousness dinshi
"dama wata yar magana ce takawoni wajen ka ko ince alfarma"
Dagowa Deen yayi ya kalleshi in surprise sai kuma ya maida kanshi qasa bece komai ba
"naji ance kai abokin yarinyata ne sosai kodayaushe ma kuna tare ko?"
Sake Dagowa yayi ya kalleshi again sai kuma ya sake sauke idanunshi
"eh daddy"
"dakyau, dama wata alfarma nazo nema awajenka akanta nasan kai kadai zaka iya yimin Hakan"
Shiru Deen yayi be kuma dagoba saima jin maganar daddy dayake wani banbarakwai, wai alfarma, ina shi ina yiwa mutum irin wannan alfarma?
"Dama akan Zainab ne, kwanan nan narasa gane kanta gabadaya, ta tsiro wasu hallaye da ba nata ba, bansan inda matsalar take ba ko itace ta chanza ko chanzata akayi oho?"
Qara Dagowa Deen yayi ya kalli daddy saikuma ya sauke idanunshi
"Wani abu takeyi ne?"
"Abubbuwa ma kai, lokaci daya yarinya ta chanza? babu irin wannan biyayyar ta da da jin magana ta, tabar saurarona ma bare tabi abinda nake nunamata"
Hankalin Deen ne yafara tashi kuma Hakan ya nuna a fuskarshi
"ya sallam! To meyasa?"
"nima shine ban sani ba Amma nafi kyautata zaton huremata kunne akeyi don ada ba Haka take ba.
Munyi maganar wani yaro daita, ita tama kawoshi da kanta tace tana so nakuma aminta da Hakan saboda yaron nagarttace ne sosai, yanada kyawawan hallaye ga tarbiya, yana sonta sosai itama tana qaunarshi
Lafiya lau muka tsaida magana da manyanshi akan idan tagama school za'a aura mashi ita
Amma kwatsam lokaci daya Abubbuwa suka fara chanzawa, bata saurararshi yanzu, bata bashi damar ganinta ko yin waya daita.
Tabi ta chanza a yan kwanakinnan duk mun rasa gane kanta, bata sauraron maganarmu sam bare tayi amfani daita kuma da ba Haka take ba, Zainab yarinya ce mai sauraron maganar iyayenta most especially ni amma yanzu ta chanza tayi fatali da duk tarbiyar da muka bata.
Mun rasa yadda zamuyi mata don sosai yaron yake cikin damuwa saboda yana sonta sosai amma duk yadda mukaso ta fahimcemu ko ta fahimtar damu meye matsalar taqiya.
Shiyasa danaji ance kai abokinta ne sosai kusan ma kullum tare kuke yasa na yanke shawarar zuwa wajenka wataqila ka iya abinda ke neman gagararmu"
Tunda Daddy yafara magana wutar Deen ta dauke diff, kanshi yafara jujjuya mashi ahankali, fadin tashin hankalin da zuciyarshi ta fada 6ata baki ne, jin magangganun daddyn yakeji kamar a mafarki
"shiyasa nazo wajen ka, please ka jawo ra'ayinta akan Hakan tunda naji ance kai abokinta ne, kana iya yin abinda mu muka gagara yi, ka kuma samata ido kaga ko wani ke zugata don ni nafi tunanin Hakan, ta yiwu wani ko wata ke zugata yana dorata a keken 6era da nufin kaita yabaro.
Please do this for me, kaji d'ana?" yafada yana kafeshi da idanu cikin son karanto yanayin dake fuskarshi kuma yasamu abinda yake nema don tsagwaron tashin hankaline rubuce all over fuskarshi
"bakace komai ba kamal" inji daddyn still yana kafeshi da idanu
Sai a lokacin Deen yadan qaqaro murmushin yaqe yahau yi
"insha allah daddy.. I'll try my best"
Murmushi sosai daddy yayi cikin nuna farinciki sosai
"yauwa d'ana, naji dadi sosai, allah yayi maka albarka, don Allah ka kulamin daita sosai, ka nusar daita sosai idan ma kaga alamun zugata akeyi to let me know, sai na tabbatar na koyawa munafukin hankali don na tsani munafurci kana gani na nan, duk yadda muke da mutum daya munafurceni to wlh nagama dashi kuma zamu sanya kafar wando daya ne dani dashi"
Kasa dago kai Deen yayi don jiyayi kamar ma dashi yake, gudu sosai zuciyarshi take acikin zuciyarshi yana lissafa cewa kenan shine mai huremata kunnen, da daddy yasan da Hakan da da wane ido kuma zai kalleshi?
Hakan yasashi jin duk ya takura, a zahiri sauraronshi yake amma a badini duk bayama gane abinda yake cewa.
Dakyar dai yasamu yagama magangganun shi yana kuma qara jaddada mashi ya taimaka mashi wajen ganin sun shawo kan matsalar.
Da insha allah kawai Deen ke amsawa batareda ya iya hada idanu dashi ba
Godiya sosai daddy yayi mashi yana Tambayar kaka shikuma yana amsa mashi da tana cikin gida
"to my regards to her"
Sai kuma ya karkata gefe ya shiga lalubar aljihunshi
Shidai Deen besan yana yi ba don kanshi na qasa haryanzu yana sake jujjuya magangganun daddy a ranshi
"ga wannan babu yawa" yaji daddy na fada
Dan Dagowa yayi sai yaga ashe kudi yake miqomashi
Dan murmushi yayi sannan ya girgiza kai ahankali
"A'a daddy, ngd qwarai"
"haba ka amsa mana" inji daddy
"don Allah daddy kabarsu"
"meyasa? Ko sun maka kadan ne?"
Sake Dagowa yayi ya dan kalleshi sai kuma ya sauke idanunshi
"ba Haka bane daddy, kaka batason haka, zatayi fada kayi hqr"
Dan ta6e baki daddy yayi ya maida kudin a aljihunshi
"to shikenan ai, babu damuwa, ngd kaji, please kayimin qoqari akan Hakan"
"insha allah daddy"
"bari mu wuce, dare sai qara yi yake"
"to" inji Deen yana fitowa daga motar dama bai rufe kofar ba
Maido mashi kofar yayi ahankali ya rufe yana mashi sallama da fatan isa gida lfy shikuma daddy ya daga mashi hannu kawai yana murmushi bala yaja motar sukayi gaba
Bïñ motar yayi da kallo harta fice daga layin nasu
Lumshe idanu yayi ahankali ya bude yana jin kanshi na wani irin saramashi.
Meke shirin faruwa ne?
Wanene Zainab keso har aka tsaida maganarsu?
Wake huremata kunne?
Bayada wanda zai bashi duk wadannan amsoshin Hakan yasashi Juyawa jiki a sanyaye yashige cikin gida.
Koda ya shiga Saida kaka ta tambayeshi dalilin dadewarshi awaje yau sai cemata yayi suna dan fira ne da salmanu.
Duk yadda yaso 6oye yanayinshi ga kaka Saida ta gano sauyin yanayinshi
Hakan yasata Tambayar shi meke damunshi, babu komai yace mata ganin zata matsa mashi yasashi cewa barci yakeji sosai jikinshi duk ciwo yake mashi.
Jin Hakan yasata gabatar mashi da abinci da sashi yadanci ba laifi sannan ta rakashi har daki ya kwanta bisa katifarshi tana jera mashi sannu.
Saida taga barci ya daukeshi sannan ta taso ta fito daga dakin ta cigaba da yan qananun aikace aikacenta don Allah ya taimaketa tunda marece sukayi tatar qullin kokonsu.
Saida tagama duk diminiyarta sannan ta daura alwalla tashige nata dakin itama ta rufo kyaure.
A bangaren Deen kau barci qauracewa idanunshi yayi, dama pretending yayi kamar yayi barcin don kaka ta kyaleshi tana fita ya bude idanu ahankali ya tsurama saman rufin dakin ido.
Ya rasa meke mashi dadi a zuciyarshi, ya kuma rasa yadda zai fassara magangganun daddy.
Dama zee tanada wanda takeso aka har aka tsaida magana dashi kafin yashigo da tashi manufar akanta?
Koko dai za6amata akayi daga baya?
Zainab na son mutumin dagaske kamar yadda daddy yace?
Koko shi take so?
Meyasa bata ta6a yimashi magana makamanciyar wannan ba?
Meyasa bata ta6a cemashi an tsaida maganar ta da wani ba?
Daren ranar Deen kasa rintsawa yayi saboda damuwa
Yarasa me keyimashi dadi, ya kasa Kamo bakin xaren al'amarin, yadda yaga rana haka yaga dare.
*WASHEGARI*
Still haryanzu mummy bata yimata maganarsu ba dukda kau kasa kunnen datake tayi tun jiya, abinda bata saniba shine bata kaiga gayamashi bane koko ta gayamashin Itadai ce bata bata feedback ba?
Tana son Tambayarta kuma tanajin tsoro Hakan yasata haqura ta cigaba da kasa kunne da jiran tsanmmani.
Shirin school tayi a gagauce don yau tanada morning lecture
Koda ta sauko breakfast tayi sama sama ta tashi tayi sallama da mummy tafito, babu 6ata lokaci suka shige mota ita da bala suka fice daga gidan.
*UMYU*
Koda ta isa school saura minti biyar su shiga aji Hakan yasa tayi ma ajin tsinke Direct
Mintuna 40 lecture din ya daukesu sannan suka fito daga class din
Rataya jakkarta tayi itama ta biyo ayarin masu fita daga class din itama tafito.
Direct wajen zamansu tanufa tana tafiya a gajiye tana tare goshinta da wani littafin saboda hasken rana dake reflecting goshin nata.
Tun daga nesa ta hangeshi zaune ya juya mata baya
Ahankali ta qaraso wajen tana kallon bayanshi tana jin soyayyar shi a kowane magudanar jininta
Ganin kamar besan da isowarta ba yasa ta qarasa bayanshi cikin sand'a ta dan duqa saitin kunnenshi tayi tafi da qarfi
Aikau firgigit yayi yayi saurin waigowa Hakan yasa tashiga yimashi Dariya tana toshe bakinta
Dan murmushi yayi sai kuma ya juya ya cigaba da kallon inda yake kallo
Qarasowa tayi ta zauna itama tana dan basu space