Showing 51001 words to 54000 words out of 322641 words

Chapter 18 - DEEN Complete Hausa Novels By Arewa Novels.txt

27 Nov 2025

4301

be ambata masu ba ta ambata wanda Hakan ba qaramin faranta mashi yayi ba don shima kamar kowanne teacher yana bala'in son student mai sharp brain

"a round of applause for her" yafada bayan tagama zayyano amsoshin


Class dinne ya kaure da tafi wanda Hakan yasata jinta on top of the world

Umarni yabata akan ta zauna takoma ta zauna haryanzu tana jin yadda zuciyarta ke tsalle

Har aka qarashe lecture din bata qara gigin daga hannu domin amsa wata tambayar ba don harga lokaci takasa komawa normal


Bayan lecture din daje tasamu Deen ta karanta mashi komai daya faru a ajin cikin tsananin murna, tana ta nannata wai yau ita mr ibrahim yacema ayiwa tafi


Deen dai Dariya yayita mata yana cemata ba sabon ba yayinda take cewa eh babu komai


Tofa tun daga ranar zee tafara zama active student a class din mr ibrahim

Yanzu koda cikin mutane dayawa ta daga hannu yakan cankota jefi2, hakan kuma ba qaramin qara mata popularity yayi ba a class don a hasashen kowa yanzu kamar duk acikin class din ita ke topping din class din a subject din don wani sa'in ita kadai ke iya amsa wata tambayar

Hakan yafara jamata farinjini a class din (kundai san yadda akema maqwara a fanni maths kallon manyan qwari😜)


Sai yazamana tana qara burge yan class din, tana ba kowanne sha'awa donma sanin halinta na wulaqanci yasa duk ake shayin zuwa wajenta amma yadda tayi sunan nan da lafiya lafiya da taga yadda ake tururuwar zuwa koyon karatu awajenta.


Su sumee kau a bangaren su wannan sabon cigaban na zee ba qaramin qara masu kiyyayarta yayi ba, sosai hassadarsu da baqinciki akanta yaqara farashi don sun lura akoda yaushe cigaba take samu ba ci bayaba

Hakan ba qaramin rura wutar abinda suke shiryamata yayi ba azuciyarsu


Saidai dayake munafukaine masu 2face ko kadan basu ta6a nunamata komai ba a fuska saima qara jawota jiki dasuke kuma koda wasa babu wanda ya tadamata maganar Deen acikin su saima yi dasukayi ma kamar ma sun manta dawani hallita Deen bayan a badini koda yaushe suna nan suna yimasu la6el either a library ko a sabon wurin zamansu, koda yaushe saisun je sunganosu wanda yanayin da suke tardasu yake qara hura wutar kishin nurr tarasa meke mata dadi a duniya.



A bangaren zee da Deen kau wani sabon fejin shaquwa ne ya bude a tsakaninsu, ada akwai ranakun da basada lecture wanda hakan kesa basa zuwa ranar, amma a yanzu basa fashin ko wace rana, kullum sai sunzo kuma inhar ba lecture suke ba to suna tare

Suna dan zuwa school din ranar saturday don yin karatu duba da yadda exams keta qarasowa, hakan yasa suka dage kowannensu ya maida hankali fiyeda da a karatu


Abin mammaki yanzu idan ba tare suke karatu ba basa jin dadin karatun, kuma be cika zama ba ma

Sau da dama idan suna gida suka dauki Littafi da niyyar karatu sai suji abin dai gashi nan, karatun duk bawani dadi

Amma idan suna tare koda kuwa kowa da littafinshi a hannu yana karatunshi shikadai sai suji sunfi jindadi kuma yafi zama, wannan abin ba qaramin mammaki yake basu ba hakan kuma yaqara donqon shaquwarsu, yaqarawa Abin armahi👌




Yau ma kamar koda yaushe suna zaune a sabon wajen zamansu, kowannensu riqeda Littafi a hannu sun juyawa kansu bawa kowa na abinda ke gabanshi


Jin kanta na neman fashewa don nauyin dayayi mata yasata maida littafin ta rufe tana dafe kan tana matse idanu


Duk abinda take Deen besan tanayiba don sosai yayi nisa a duniyar karatu

Juyowa tayi taga kanshi na kan Littafi bema san abinda ke faruwa ba hakan yasata dan 6ata rai tasa hannu ta fizge littafin hannunshi


Firgigit yayi ya waigo don abin yazomashi a bazata, Ganin tayi saurin maida littafin bayanta yasashi shima 6ata rai

"O'O! Give me my book"

Maqe kafada tayi tace
"anqi din, kai baka gajiya? Ni yanzu haka jin kaina nake kamar zai dare gida biyu"

Daga kafadu yayi yace
"then? Aike keji ba niba ko? Bani littafina" yafada yana neman amsa

Maida littafin tayi bayanta tana Dariya

Duk yadda yaso ya amsa qi tayi hakan yasashi hqr ba don yaso ba yace
"now tell me, me zamuyi bayan karatun?"

"komai ma Amma banda karatun, nagaji" tafada tana yatsine fuska

"komai kamar me?"

"komai dai, kamar labari da dai sauransu"

"Ni ai ban iya labari ba"

"wa din?" tafada tana eyeing dinshi

"Ni din" yafada shima yana Dariya

"hmm, gwara dakaba kanka Dariya" tafada tana harararshi

"nidai ai gaskiya nafadi" yafada yana cigaba da Dariya

Harararshi tayi kawai can kuma tace
"ka Bani lbr, na komai ma, ko naka, kona family dinka, komai ma, qila inji sauqin nauyin kwalwa ta"


Murmushi yadanyi sannan ya gyara zama yace
"to bari nabaki na Ni da family dina"

Itama gyara zama tayi cikin jindadi tace
"yauwa, to inaji" tafada tana buga tagumi da hannu daya


Murmushi yayi ganin yadda tawani nutsu ita dadi labari sai yace

"Nidai sunana Deen kamar yadda mutane including you ke kirana, Amma my real name is _*KAMALDEEN MUHAMMAD*_ Amma kakata nace min _Kyakyawa na_🙈" ya qarashe yana rufe fuska alamun jin kunya

Dariya zee tayi wanda hakan yasashi leqota ta tsakankanin yatsun dake fuskarshi


"waye Kyakyawan? Cemaka akayi kanada kyau ne? Ca6! Tana fada ne kawai don kaji dadi Amma dont let that get into your skull ok?"

Cire hannunshi yayi daga fuska yana kumburi

"cigaba"

Maqe kafada yayi alamun beyi

"meye kuma?"

"kin Cemin am ugly" yafada yana hade gira

Wara idanu tayi tace
"yaushe nace hakan? Kaji tsoron allah"

"ba yanzu kikace ba?"

"nace you're ugly? Cewa nayi bakada kyau"

"what's the difference?"

"difference din shine, ugly yana nufin mummuna, marar kyau kuma yana nufin marar kyau"

Yamutse fuska yayi yace
"me I see no difference in these"

"ni naga difference din, so cigaba"

Qara Maqe kafada yayi

Bata fuska tayi tace
"why na?"

"sai kince inada kyau" yafada yana turo baki

Dan Wara ido tayi sannan tace
"to shikenan kanada d'an kyau"

Juya idanu yayi yace
"eh babu komai, aidai inada shi ko? Keda bakidashi kwata2 fa"

Harara ta gallamashi
"me din?"

"kyau din" ya amsa yana mata gwalo

Yitayi kamar zata makamashi Littafi yayi saurin jada baya yana Dariya


Kwafa tayi tana jinjina kai

"in cigaba?" ya tambaya yana dan leqota

Hararshi tayi tace
"cigaba ba don halinka ba amma"


Dariya sukayi gabadaya sannan Deen yacigaba dacewa

"yauwa as I was saying, kakata na kirana kyakyawarta nikuma ina kiranta kakata.. Kakata itace komai na, my life, my happiness, my komai

Tana sona sosai, komai nata is kyakyawarta, haka nima komai nawa itace

Tana yin komai don ganin ta faranta mani, tana yin komai don taga ta inganta rayuwata mudin hakan be sa6awa shari'a ba

We are not rich but alhamdullilah bamu rasa komai ba.

Kakata na sana'ar koko da qosai da safe nikuma ina zuwa wani workshop anytime am free, ina koyon aikin furnitures a qasan layinmu. With that muke living happily the way We can" ya qarashe yana murmushi


Itama murmushi tayi cikin sha'awar simple life dinshi

"mama da baba fa? Tunda muke dakai ban ta6ajin ka ambacesu ba" tafada tana kallonshi

Dan jimm yayi, sai kuma yayi murmushi mai ciwo yace
"basa nan, tunda na bude idanuna duniya kaka nasani, itace mamata itace babana itace komai na, amma ga yadda kaka tace accident sukayi suka rasu kuma dama nikadai suka haifa shiyasa banida siblings, kaka kuma babana ne kadai danta shiyasa we're all alone, daga ni sai ita"

Tunda yafara take kallonshi cikin tausayawa, ashe maraya ne gaba da baya? Allah sarki


"am.. So sorry, ban sani bane, Allah yajiqansu yayi musu gafara" tafada asanyaye

Murmushi yayi mata cikin jindadin addu'ar tata yace
"amin ya rabb"

Shiru ya ratsa wajen inda zee tashiga saqe2, to ina dangin mamanshi? Ina dangin kaka? Yakamata ace basu kadai bane kamar yadda yace, koba komai Yakamata yayi maganar dangin mamanshi

"kefa? Saura ke kibani lbrin ki" yafada shima yana buga tagumi yadda tayi dazu

Dariya tadanyi tace
"nawa tarihin is not as special as yours"

"eh dukda haka abani" yafada yana kada kai

Slight murmushi tayi tace
"ni sunana zainab.. Zainab Farouq" ta tsinci kanta da kasa qarasa sunan

"Dan faranshi?" inji Deen yana daga mata gira

Kallonshi tayi da dan mammaki
"how did you know?"

Qara dage gira daya yayi yace
"the paper, ko har kin manta"

Dariya tayi tace
"to haka yake, nima ni kadai ce ga iyayena, babana bahaushe ne, mamata kuma barumiya"

"menene barumiya?" yafada cikin rashin fahimta

Yar Dariya tayi
"tribe ne, kai bakasan Rumawa ba? Masu tsagu biyu2 a gefen kunne?"

Girgiza kai yayi alamun a'a yace
"no, ban ta6a jiba"

"ai dama ya za'ayi ka sani? Kai dama kifin cikin rigiya ne" tafada tana Dariya ahankali

Ta6e baki yayi yace
"eh babu komai, yanzu ita mum dinki ce rome din?"

Dariya tayi tace
"ba rome ba, Rumawa nace"

"to Rumawa, amma itama tanada marks din?"

"yes, kuma yana Masu kyau sosai don yawancinsu farare ne kuma kyawawa sai kuma tsagar taqara fiddosu"

"wow! Kema Rumawa ce ko? Tunda Kema fara ce" yafada yana mata murmushi still be janye tagumin ba

Harararshi tayi tace
"barumiya zakace, mutane dayawa ne Rumawa, dummy!"

Daga kafadu yayi yace
"whatever"

"nima barumiya ce Tunda mamata barumiya ce hakama bahaushiya ce Tunda dad dina bahaushe ne, ruwa biyu kenan" tafada tana kashe mashi ido daya


Murmushi yayi yace
"bawani, ke ba barumiya bace Tunda bakida marks"

Xaro ido tayi tace
"marks? Ca6 allah ya sawwaqe, ni dama banaso a jikina nafi sonshi a na wasu shiyasa ma naji dadi da ba'ayimin ba"

"nikuma Inaso, i wish muma tribe dinmu anayi da kinga yanga" yafada yana juya eyes

Dariya tayi tace
"sai kuma gashi ba'ayi taar🤪"

"eh babu komai" yafada yana Hade gira

"to ku wadanne tribe ne?"

"hausa mana"

"hausa kuma? Kana nufin kai bahaushe ne" tafada tana mashi kallon uku saura kwabo

"yes, dafa?"

"and you want me to believe?" tafada cikin rashin yarda

"allah dagaske fa nake"

Harararshi tayi bata ce komai ba

"allah, wlh kinjima na rantse" yafada cikin son gamsar daita

"to amma babu either of your parent ko mama ko baba dasuka hada jini da Arab?"

Girgiza kai yayi alamun babu

"shuwa Arab?"

Nan ma Girgiza kai yayi

"allah mai iko, buzaye fa ko fulani dukda bakayi kalarsu ba"

Qara Girgiza kai yayi snn yace
"I told you ni bahaushe ne, mutane dayawa na tambayar kaka kuma haka take cewa, both mum da dad dina duk hausawa ne" yafada innocently


Kada kai tayi tana kallonshi bawai don ta gamsu ba tace
"kuma fa, amma nayi mammaki amma kuma ba abin mammaki bane, ikon allah kenan"

Murmushi yayi kawai suka cigaba da firarsu cikin jindadi wanda sosai yadan ragemasu nauyin da kansu yayi


Saida lokacin tafiya gida yayi suka rabu, ita zee tahau motarsu shikuma ya tari adaidaita



_guys are you ready for the next chapter?_

_to ku tanadi hanki 🤧 domin zaiyi yaji 🌶? irin sosai dinnan_




Ummin fasihu 🧚🏻‍♀?
8/2/21, 9:33 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?*






*021*


😆😆😆 jiya nace ku tanadi hanki mutane sun gigice, O'O!🙍🏻‍♀️Kudai bakusan wasaba, to wasa nake muku 🤗

Ku kwantar da hankalinku kamar kunyi baqo ya sheqa🙄






Haka lokaci yayi ta wucewa, exams nata qaratowa

Kan kowa ya dauki chaji da masu qoqarin da mashiriritan duk aka komawa allah aka rungumi Littafi


Alokacin library yakoma kamar bashi ba saboda cika, duk wanda ya rungumo guntun littafinshi to library yanufa

Hakan yasa su Deen chanza wurin zama suka dawo silent place dinnan bakidaya

Izuwa yanzu bama ce su mr ibrahim da zee sun shirya ba Saidai babu wannan yar tsamar dake tsakaninsu ada, yanzu lafiya lau suke mu'amallantan juna irin mu'amalar tsakanin malami da dalibi, abin nasu safa safa ba yabo ba fallasa


Da farko zee taso tabashi hqr a lokacin sai kuma taga zaifi tabari sugama exam don karma yayi tunanin taimakonta takeson yayi a exam din😏

Hakan yasa ta qudurta cewa dasun gama exams zata bashi hqr komai ya wuce a tsakaninsu


Tsakaninta dasu sumee babu yabo ba fallasa don tunda exams ya qarato kai yadau chaji haduwarsu tayi wuya, dama haka yake yawan faruwa don tun kafin ma zee tasan Deen da exams ya gabato take ajiye shiririta ciki hardasu tayi facing karatun ta don tasan idan ta biye musu ita hau zai hau don kwata2 babu ruwansu da karatu koda kuwa irin wannan lokacin ne na gabatowar exam don sunfi damqa imaninsu ga expo(satar amsa)

Ita kuma dayake bata iyaba yasa duk lokacin gabatowar exam haduwarsu ke dan wuya don lokacin busy take karatu sukuma busy suke da shashanci dayaimasu yawa a brain shiyasa irin wannan lokacin basu cika hadewa ba sai ta waya ko idan an Hade a makarantar a gaisa tsaitsaye awuce


To Hakan ta kasance yanzu ma, basa yawan hadewa saita waya wanda mafi yawanci su ke kiranta su gaisa, wannan kulawar dataga suna bata yasata qara jin sonsu don ita tana masu so na tsakani da allah kuma kamar yadda tace ita bata iya pretending ba, idan tanason abu to tanasonshi idan kuma beyi mata ba to 6aro2 zata nuna beyi matan ba bata tsoron bayyana Hakan


Tun suna lissafin exams saura sattitika harya koma saura kwanaki har yazo ma gabadaya

Sosai school din yaqara daukar serious atmosphere don wannan exam din na chanza aji ne babu mai fatan yayi repeating Hakan yasa kowa ke iya bakin qoqarinshi don ganin ya tsallake

Su zee sun riga su Deen fara exam kasancewar daman ba course daya suke karanta ba kuma dama yafita da shekara daya, ita tana level 200 zata shiga 300 shikuma yana level 300 zai shiga 400 level


Sosai zee ta baje kwalwarta sosai wajen jarabawar sai gashi wannan karin maganar ta turawa na _how you spread your bed that's how you lay on it_ wato _yadda kayi shinfidarka haka zaka kwanta akai_

Sosai exams din sukazo mata da sauqi fiyeda kowane semester don tafi shirya mashi a wannan semester din fiyeda kowane


Har yanzu tare suke karatu da Deen, duk wanda lokacin shiga ajinshi yayi saiya tashi yabar dayan yaje ya zana ya dawo

A bangaren su sumee kau bana kasuwa batayimusu dadi ba don bana an tsamar tsaro sosai dakyar suke samu sudanyi satar amsa wanda ahakan ne aka kama rukky har Sau biyu inda duk inda aka kamata tofa tayi loosing din jarabawar don yake papern akeyi kuma bazata sake wata ba, daga baya ma sai aka wareta daga cikin students aka kawo mata kujera da desk gaban class inda ba damar satar amsa, wurin yazama wurin zamanta duk in zasuyi exam, Hakan yasa komai yaqara dagule mata don kwalwar fankoce babu komai a ciki sai dusa


Suma su sumee ba'a barsu abaya ba don duk watsasu akayi a class din, kowanne da mazauninshi gashi ba damar satar amsa saboda idon da aka samasu Hakan yasa basa ta6uka komai a duk jarabawar dazasu zana, wata jarabawar ma Saidai su rubuta sunayensu su sake copying din questions din aciki suje suyi submitting hakanan


Sosai suka shiga damuwa da baqinciki don fa bana ba sauqi sai wajen allah, qarin baqincikin su shine idan suka hango zee ta sadda kai tanata rubutu ko dagowa batasonyi sai suji wani qululun baqinciki ya tokaremasu maqwalato suji kamar suyi tsuntsuwa sugansu gabanta su fizge shegiyar takardar su yayyaga, oho batasan sunayi ba don abinda ke gabanta takeyi su tabari da harara cikin duhu😡



Jarabawar mr ibrahim itace kusan ta tsakiya, duk cikin Jarabawar babu wanda akafi zullumi kamar ita, wadanda basuyi barci ba ranar daren Jarabawar sunfi yawa


Ciki harda mutumiyar taku wanda a lokacin Saidai Deen ya ajiye nashi karatun sukayi nata tare

Kuma Hakan ba qaramin taimaka mata yayi ba don sosai sukayi covering abubbuwa da dama

Dayake Jarabawar monday ce sai suka hadu ranar saturday a school inda ranar ma wata Jarabawa sukayi on their own don ranar tambayoyi Deen yayta rubuta mata tana amsasu kuma tayi qoqari sosai don ta ciye rabi da kwata, kingin kuma suka farmasu harta fahimta

Ranar sunday kuma kwana ta kusan yi zaune saboda karatu Hakan yasa ta tashi washegari da ciwon kai Saidai cikin amincin allah tana shan magani taji dama2


Kamar yadda kowa ya chanfa Jarabawar mr ibrahim da mugun wuya a kowanne semester haka kuma yafaru a wannan ma don wasu suna tozali da question paper din zufa yafara ketomusu

Kunsan *goyon goyo?* to haka questions din suke, kowanne tambaya da goyon datayi itama goyon da nata goyon shima goyon da nashi don a question daya kana iya bata long sheet gaba da baya kodayake ga yan wahala yake Hakan don su yan baiwa (su nurr) ko gaban long sheet daya basu cika ba ga dukkan questions din tsabar gwanancewa 😆 (ouch! Waya jefeni 🥺)

An saba duk wuyan exam iyakar gudun tsiya kayi 1hr kana yi amma wannan saida akafi awa biyu kafin afara fita

Qarin gishiri cikin ciwo kuma harda mr ibrahim cikin invigilators din Hakan yasa abin yafi daukan


Zokaga rikicewar students ranar

Mafi yawa a cikin students din kuka sukaitayi wasu na jama mr ibrahim allah ya isa kamar yadda suka saba duk Jarabawa

Sukau mutanenku sai suka zama yan kallo don su aganinsu ma kuka ai rahamane, tunda har suka samu sukayi kukan to matsalar tasu bata kai matsala ba


A bangaren zee ma sosai Jarabawar ta jigatar da ita dukda dai tana saka ran samun abin kirki don ita kanta tasan tayi qoqari

Haka tadawo wajen Deen gajiye ti6is Deen sai Dariya yake mata


Kingin exams din ma sukazo suka wuce, inda students sukayisu cikin jindadi don dama zaffafan su suka fara zuwa Kingin kau duk yan tagajan2 ne


Su zee sun riga su Deen gama Exam don dama sun rigasu farawa

Lokacin da su zee suka gama su Deen saura paper uku sugama Hakan yasa take ta shan hutunta tabarshi da wahala

Acikin haka ta yanke shawarar bama mr ibrahim haquri Saidai ta rasa ta wace hanya

Itadai tasan bazata iya samunshi face 2 face ba hakan yasata yanke shawarar yin haka a rubuce

Wata zungureriyar takarda tasamu fara tass ta zauna tafara tsara kalaman ban haquri

Saida ta cika gaba da baya sannan ta linke neatly

Sai a sannan kuma tafara tunanin ya za'ayi takardar takai mashi don gaskiya tana tsoron taje da kanta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login