Showing 9001 words to 12000 words out of 322641 words

Chapter 4 - DEEN Complete Hausa Novels By Arewa Novels.txt

27 Nov 2025

6126

6ulle, ko yayane ina ququtawa insamu average shiyasa ya tsiro Wannan muguntar" inji Zee cikin dacin rai

"wlh kam, ko shakka babu saboda ke yayi hakan don dama yana ciki dake na rashin attending din class dinshi da bakiyi" inji deeya

"plus idan Kin ganshi bakya gaidashi kuma ya tsani rashin respect, yaga yabi ta kowacce hanya yakasa cinma burinshi shiyasa yabi ta Wannan hanyar gashi muma ta shafemu" inji sumee

"Oh God! What am I gonna do? Banason carryover, I hate this school like mad! Na tsani school dinnan" tafada ashagwa6e tana yarfa hannu hawaye na taruwa a idanunta

Duk shiru sukayi suna kallonta ganin dagaske hawayen take

"Duk mummy tajamin Wannan abin, da yanzu inacan dasu Jidda muna karatunmu cikin kwanciyar hankali, Wannan ai immaturity ne, kawai don ya rasa yadda zaiyi sai yamin mugunta? Wlh nidai bazan yarda ba, gwarama asan abin yi don bazanyi wani carryover ba" tafada cikin 6acin rai still tana hawaye, dama haka take a zahiri kamar wata jan wuya saidai ruwa ruwa ce, abu kadan kuka

Saurin matsowa kusada ita sumee tayi tana sharemata hawaye tana rarrashinta yayinda rukky da deeya suka kalli juna suka dan ta6e baki

"haba dear, kibari mana don Allah, insha Allah bazamuyi carryover ba, back to sender, ki kwantar da hankalinki" inji Nurr itama tana matsowa kusada ita
"tayaya zan kwantar da hankalina Nurr? This man hates me, kullum cikin son ganin ya wulaqantani yake, me nayi mashi? Why cant haters just leave me alone!"

"Hmm ni aganina mafita yakamata mu nema ba Wannan ba let's just find solution to this" inji deeya

"wane solution? Inbadai zuwa zamuyi muyi begging dinshi ba ya taimaka ya janye qudurinshi" inji rukky

Dago watery eyes dinta da suka fara chanza launi tayi ta watsa mata kallo tace
"beg him? Wani abu muka masa ne? Kawai confronting dinshi zamuyi yagayamana inda aka ta6a yin haka, don Allah yadorashi a wani matsayi saiyayi zalunci? Wannan ai zalunci ne" tafada cikin 6acin rai

"Hmm ke kika san Wannan, kuma kinsan mr ibrahim baya tolerating din nonsense gwara ma mubishi ahankali don samun mafita wa kanmu" inji deeya tana dan ta6e baki

Zee bata qara cewa komaiba sai sake dafe kai datayi tana kallon qasa

Tana jinsu sunata shawarwarun yadda zasu 6illowa mr ibrahim, itadai kawai tana tareda sune amma hankalinta yayi wani wajen.

Yanzu ya zatayi idan ta fadi? Kenan carryover din zatayi? Tasake maimaita year dinnan? Kai bazai yiwuba, over her dead body! Insha Allah hakan bazata faruba

Sosai takejin zuciyarta na zafi don 6acin rai, jitayi zaman wurin ma ya isheta hakan yasata jan tsaki ta miqe tsaye tana duba time a tsaddadiyar wristwatch din hannunta

Duk kallonta suke basuce komaiba, zaro wayarta tayi ta lallubo number bala ta danna mashi kira

Ringing biyu tayi aka daga
"kazo muwuce" tafada ataqaice ta yanke kiran batareda ta jira jin me zaice ba

"badai tafiya zakiyi ba" inji nurr

"mezan jira?" zee tafada batareda ta kalleta ba

"kamata yayi mu zauna mu sama ma kanmu mafita" ta bata amsa

"kudai sama ma kanku mafita, ni na riga na yanke on monday zanje insameshi duk yadda ta fanjama fanjam" tafada tana niyyar barin wajen

Duk tashi suma sukayi suka maramata baya

Tafiya suke saidai ita tana gabansu don yau ba irin tafiyarnan bace ta yanga, yau ranta a 6ace yake shiyasa bata tsaya Wannan catwalk din nata ba

Tana cikin tafiya tana saqe saqen yadda zata 6illoma Wannan al'amarin, tasan dai ko ana manna mata garwashi a ido ne bazata iya yiwa mr ibrahim rashin kunya ba, yanada kwarjinin da bazata iya hada ido dashi na tsawon lokaci bare akai ga rashin kunya

Duk fadin school din shine tafi shakka kuma tafi tsana don gwani ne wajen duzga mutum da kunyatashi

Tun farkon zuwanta school din suke takun saqa dashi, be qaunarta kwata kwata saboda rawar kanta da rashin kunya, duk sadda yashigo class dinsu beda wanda ya tsone mashi ido kamar ita

Duk tambayar dazai jefo to ita yake jefamawa, idan kuma bata amsa daidai ba yaimata tass a class din

Yasha embarassing dinta a class hakan yasa tabar shiga class dinshi sai taga dama, wani sa'in ma idan tayi attending din class dinshi taga damar ya jefo mata tambaya tayi kunnen uwar shegu dashi, qarshe dai saidai ya korata waje

Subject din da mr ibrahim ke koyawa yana daya daga cikin favourite Subjects dinta saidai kasancewar tasu batazo daya da mutumin ba yasa subject din siremata, taji yafita ranta, Tun tana jurewa tana zama Koda zai dizgata ne har tajima bata iya zaman lecture dinshi kwata kwata don Koda tana class yashigo tashi take tazo ta gifta ta gabanshi ta wuce, Wannan abin ba qaramin 6ata mashi rai yake ba shiyasa yaquduri anniyar koyamata hankali

Saidai duk yadda yaso kadata bata faduwa don duk qumu saita ci average, hakan na bashi mammaki sosai kuma hakan na nunamashi tanada qwalwa kuma da zata zauna ayi lecturen tareda ita da taci fin haka kuma da tazamo daya daga cikin masu topping class din a subject din

Amma girman kanta bazai barta ba, ita gani take tafi kowa kuma zata iya taka kowa, shikuma ya tsani mutum mai irin Wannan halin shiyasa basa ga maciji


MR IBRAHIM ADAM magidancine kuma lecturer a jami'ar umaru musa yar adu'a

Mutum ne na mutane wanda yayi suna kaff makarantar saboda dadewarshi acikinta dakuma kasancewar shike koyarda duka makarantar subject din mathematics

Mutum ne adali kuma mai tsayin daka akan gaskiya shiyasa ko ana bribing din lecturers don samun marks to babu mai iya tunkararshi da hakan, shi mutum ne mai aiki da gaskiya abinda kaci shi zaibaka ba don haka ba yadda ya tsani zee da tuni ya kadata

Mutum ne mai wasa da dariya amma fa da yazo bada darasi dinke fuskar yake dib donma kar akawo mashi wasa

Yanada experience sosai na koyarwa yadda mutum zai fahimta duk daqiqancinshi saidai idan dama baka shirya koya bane

Saidai kuma aduniya ya tsani raini da rashin kunya, duk yadda kuke dashi ka nemi kawomashi raini saiya nunamaka other side dinshi

Asalin gabarsu da zee yafara ne lokacin farko farkon zuwanta makarantar

Ranar tayi late kuma shi a dokarshi ba'a shiga aji idan yariga yashiga

Itakau tana zuwa tashige sundum2 kamar sa ko gaisuwa

Juyowa yayi daga rubutun dayake yana kallonta, ganin tana niyyar zama yasashi dakamata tsawa wanda ba qaramin kada hanjinta yayi ba don dama aduniya ta tsani tsawa

"ke wacce daqiqiyace zaki shigoma mutane class babu neman permission?!"

Bata amsaba sai yamutse fuskar datayi tana qoqarin daidaita nutsuwarta don ba kadan ba tsawarshi ta tsoratata

"bakijina ne! Ko bakisan kinyi late ba kuma a dokana babu mai shigo min class idan narigashi shiga?!"

Ga mammakin kowa sai gani sukayi ta gyara zaman handbag dinta tazo ta gifta ta gabanshi tawuce tana qass qass da chewing gum da taunarshi yariga yaxame mata jiki

Duk binta sukayi da kallo baki sake har mr ibrahim, fadin 6acin ran da mr ibrahim ya tsinci kanshi aciki 6ata baki ne, jiyayi zuciyarshi na tafarfasa kamar zata faso qirjinshi

Tunda yake ba'a ta6a wulaqantashi ba a bainar jama'ar dake ganin girmanshi ba irin na ranar, hakan yasa shima ya tattara takardunshi yafice don bejin zai iya cigaba da abinda yake.

Ranar rumours yaita zagaye school don hakan na daya daga cikin abubbuwan dayasa aka santa

Mr ibrahim bece komai ba don gani yake qaranta mane biyewa Wannan jaririyar yarinyar saidai labari na kaiwa ga kunnen school authority suka kirata

Dukda sundan ji shayi dasukaji waye babbanta saidai hakan be hana sukai mata fadaba suka tisata gaba har office din mr ibrahim tabashi haquri

Dukda yanuna ya haqura kuma dama shi abin be dameshi ba amma deep down yayi vowing saiya koyamata hankali shiyasa ya tsiro da salo salo na cin mutuncinta a class wanda hakan yaqara hura wutar gabarsu har zuwa Wannan ga6ar




Fitt.... Taji an figemata dan yalolon gyalenta daga kanta wanda hakan yasata dawowa daga duniyar tunani data lula

Waigawa tayi da sauri ganin wane dan iskan ne yayimata haka

Turus tayi tana kallonshi dama su sumee dake bayanta

Kanshi a sadde yake yana kiciniyar cire gyallen daya sarqaho mashi bracelet din hannunshi

Tsayawa tayi tana kallonshi cikin rashin sanin abin yi

Sumar Kanshi kawai take gani wanda yake rough ba gyara sai tip din hancinshi dakeda tsini sosai har kana hangenshi dukda kan a sadde yake

Binshi da kallo take up & down

Sanye yake cikin pure white jallabiya, it's so pure babu digon datti ko daya, kaffafuwanshi Sanye da baqin half cover shoes suma suna shinning da alamu sunsha polish sai hannunshi na dama dake sanye da agogo baqi mai matsakaicin kudi sai na haggun dake sanye da bracelet wanda shi gyallen zee ya tsarqaho

Duk yadda yaso yacire kasawa yayi hakan yasashi sa baki yana amfani da haqoranshi wajen ganin ya cire amma still yakasa hakan yasashi jan gyallen afusace sai ji kake kyattttttt! Ya keceshi

Zee da ta tsaya kallon ikon Allah tundazu ta wara manyan idanunta cikin tsakanin mammakin abinda yayi hakama su rukky

Jefar da gyallen yayi qasa yana zare zarruruwan gyallen da suka maqale a bracelet din haryanzu yajuya batareda yanuna yamasan da tsayuwar wasu akanshi ba koko bema san dasuba oho? Ya cigaba da tafiyarshi yana cigaba da zare zarruruwan

Ran zainab yaqara 6aci, dama yaya lfyar giwa? Hakan yasata saurin binshi tasha gabanshi

Da sauri ya dago kamar ma atsorace jin kawai mutum a gabanshi

Sauke hazal oily eyes dinshi yayi acikin nata large sexy eyes suka kafe juna dasu..... ✍️


Ummin fasihu🧚🏻‍♀?
8/2/21, 9:31 PM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN 🙍🏻‍♂?*



*005*



Wani irin abu taji ya tsirgamata daga tafin kafa har tsakar kanta

Cigaba da kallon kwayar idanuwan nashi tayi wadanda suke farare tass sai wani maiko2 sukeyi

Kasa janye idanuwanta tayi daga cikin nashi yadda kasan anyi magnetting dinsu

Shima kallonta yake ta siraran gashin Kanshi dasuka biyo ta idonshi kasancewar sumar ganshi is rough amma kuma hakan ba qaramin style yabada ba.

Kallonta yake cikeda nazari, ganin batada niyyar magana ko ta matsa mashi yawuce ya sashi ra6ata zai wuce

Hakan yasata dawowa daga duniyar kallonshi tayi saurin qara tare gabanshi

Jin ya sake zubamata wadannan idanun nashi yasata kawar dakai tace
"what did you think you did?"

Yamutsa fuska yayi yana mata kallon rashin fahimta hakan yasata nuna gyalenta dake yashe qasa abayansu tace
"look at what you did to my veil!"

Juyawa yayi yana kallon inda take nunawa nan yaga gyallen inda yake yashe

Izuwa yanzu su sumee sun matso kusa suna kallonsu donma inda suke babu mutane da yanzu anfara taruwa don ganin kwam

Dan wara oily eyes dinshi yayi alamun aiyo? Sannan maida kallonshi kan zee dake cike famm

"ya.. Maqalomin bracelet ne" yafada cikin very cool voice mai gardi da jawo hankalin mai sauraro Izuwa ga mammalakiyarta

Sosai muryar tashi tasake dulmiyar da Ita Izuwa duniyar kallonshi, she don't know what came over her kawai tsintar kanta tayi da sake kafeshi da large eyes dinta

Ganin tayi shiru kamar dazu yasashi sake yunqurin wucewa

Hakan kuma yaqara fargar daita tasake tareshi cikin fushin ganin yadda take wani shagala da kallonshi kamar yau tafara ganin namiji

"Don ya maqaloma bracelet saika yagamin kaya ka jefar?!" tafada atsakankanin haqoranta

Ganin ya tsaya yana kallonta beda niyyar cewa komai yasata qara fusata tace
"ko bakaji ba!" atsawace

Ga dinbim mammakinsu sai gani sukayi yayi saurin jada baya yana toshe kunnuwa da hannayenshi yana 6ata fuska

"ouch! That's so scary" yafada cikin cool voice dinshi yana qara yamutse fuska still hannunshi dafe da kunnuwa

Kallon juna zee dasu sumee sukayi sannan suka sake maida kallonsu Kanshi

"babu kyau shouting, zai iya affecting kunnuwan mutane" yafada yana kallonta innocently

"babu kyau me? Kayimin laifi kuma kanada gut din fadamin magana? Kasan koni wacece?!" tafada afusace

"O'O! Kinji haushi ne?" yafada yana sakin hannayenshi daga dafe kunnuwan dayayi

Kasa cemashi komai tayi tacigaba da kallonshi ganin yadda yayi maganar anarke

Suma su deeya sakin baki da hanci sukayi suna kallon abu mafi al'ajabi a rayuwarsu

"Don't worry, kakata tace idan mutum yaji haushi ya ja nannauyan numfashi ya fesar... duk numfashin dazaija yayi tasbihi idan zai fesar kuma yayi tahlil... idan kayi haka sau goma zaka nemi fushin ka rasa

Kuma tace bakyau reacting nan take idan kana fushi, hakan zai iya zama cutuwa gareka, misali yanzu ke kinyi reacting cikin fushi ta hanyar yin tsawa, kinga zai iya zamo cutuwa gareki. nafarko maqogaronki yana iya yimiki ciwo nabiyu muryarki na iya shaqewa, kuma yana iya zama cutuwa ga mai sauraronki, nafarko yana iya affecting din kunnenshi na biyu yana iya tsorata kamar yadda nayi kuma ga duk lokacin da mutum ya tsorata hakan na affecting adrenaline hormones dinshi wanda zaiyi jerking dinshi yasashi yin abinda ya dara qarfinshi ko iyawarshi kinga idan mutum yacika tsorata To zai fada risk din yin abinda ya girmi hankalinshi har takai watarana yayi abinda zaizama cutuwa agareshi

Kuma duk Wannan zai farune sanadin fushinki, kinga gwara first option din, inhale tasbih, exhale tahlil and stay safe"


Baki, ido, hanci, kunnuwa suka saki suna kallonshi tunda yafara magana kamar sun samu majigi

Ganin ba wanda ya motsa acikinsu kuma babu mai niyyar motsawa yasashi cewa
"zan tafi, kakata nacan tana jirana" yafada cikin cool voice dinshi sannan ya ra6a yawuce suka bishi da kallo batareda wani daga cikinsu yayi yunqurin sake dakatar dashi ba

Rakashi da kallo duk sukayi suna kallon yadda yake tafiyar tashi cikin sanyi da nutsuwa babu alamun sauri ko kadan aciki don tafiyar tafi Kama da ta qasaita ko sarauta

Saida ya 6acemasu sannan suka maido kallonshi ga juna

Fashewa da wata iriyar dariya deeya tayi harda dan duqewa yayunda kingin suka shiga tayata idan ka cire zee da tasake bin inda yabi da kallo

"OMG! Kunkau ji abinda naji? Ko ni kadai naji?" tafada cikin dariya

Rukky dake dariyar itama tace
"like seriously anya kanshi daya kuwa?"

Sumee tace "adai kammani he's ok amma a kwalwa ina tantanmar hakan"

Dariya suka sake Fashewa dashi hakan yaqara qule zee

"Wai meye abin Dariya anan? Ku bama ta matsalar damuka shiga ba kuke kun tsaya kula matsalar wasu, mtcheew this is immaturity kuna wani kware baki a tsakar santa and you still call yourselves classic girls, mtcheew"

Hakan yasasu yin shiru amma ba qaramin zafi maganar ta tayimusu ba

Guntun tsaki tasake ja sannan tawuce rai a matuqar 6ace, abubbuwa sun hademata goma da ashirin

Binta da kallo sukayi ransu ba dadi, suna niyyar maramata baya sukaga Rukky tajuya zata tafi

"ina zaki?" inji nurr

Bata ko kalleta ba kuma bata tsayaba tace
"class, ku kuma da bakuda zuciya saiku rakatan" tawuce tabarsu nan tsaye

Jiki asanyaye suka juya sukabi bayan zee saidai suna zuwa sukaga har motarta tafice daga school din

Suma rai a6ace suka watse kowa ya Kama hanyarshi.


Yinin ranar qarasheshi tayi rai ajagule, abin duniya sun taru sunmata yawa ta rasa meke mata dadi hakan yasa takoma sukuku komai yinshi take kamar marar lakka

Tsabar yadda tasa abin aranta saigashi itace harda su mafarkai wai a qarshen semester dinsu tasamu carryover din, mr ibrahim ya fiddota gaban jama'a yana dizgata itakau sai kuka take

Da Wannan mummunar mafarkin ta tashi

Addu'a tayi ta tofa a gefen haggunta sannan takoma ta jingina da kan gado tana qara tariyo mafarkin nata

Tana ahaka taji bubbugar qofa, tasan mummy ce, dama tasaba duk asuba saita tadata tayi sallar

Kauda kai tayi daga kallon qofar tana zu6ura baki, jitayi tana jin haushin mummyn don kome yafaru duk itace sila da tana uk da ba haka ba

Jin still tana bugun kofar kuma ba barin bugun kofar zatayi ba saita tashi yasata janye bargon jikinta a fusace ta sauko sannan ta nufi kofar tana yan gunaguninta wanda ita kadai tasan abinda take cewa

Saida tasaki fuska ta maida ta kalar wanda ya tashi daga barci be isheshi ba sannan ta bude kofar

Mummy ta watsa mata harara tace
"ke shikenan idan kin kwanta kamar mai barcin mutuwa baki ko motsawa"

Dan turo baki tayi tace
"mummy Allah banfa jiba"

Tsaki mummy taja tace
"dama yaza'ayi kiji kina Wannan barcin asarar, kiwuce kije kiyi alwalla gashican sai assalatu akeyi"

Da To ta amsa sannan tajuya tawuce itama mummy tarufe kofar tawuce

Alwalla ta dauro ta chanza zuwa wata brown jallabiya da dama ta wareta mainly for sallah sannan tazura hijab ta shimfida sallaya tahau kai tashiga gabatar da sallar

Koda tagama komawa tayi ta jingina da gado sa6anin da da datagama take hayewa gado takoma barci

Tunanin mafita take ga matsalar mr ibrahim, Allah yasani abin na ranta sosai kuma yana damunta, tasan kome zatayi bazata iya cinye kingin 50% dinba kuma samun qasa da 50% din yana daidai da faduwa koda 49% ne kuwa, gashi dama yaya lafiyar giwa? Daman cikin 100% take takarkarewa tasamu 60 ko 62% Shima saita hada da sleepless nights ta hana kanta barci tana karatu sannan zata take samu, gashi fa tana ganin tayi iya qoqarinta na karanta duk abinda aka koyar a class amma be zama kamar yadda zata dauka a class din idan anyi lecturen daita kuma dama abinda zaka dauka idan aka koyar dashi cikin aji yafi wanda zaka dauka idan ka ware kanka kai kadai da niyyar koyawa kanka

Maida kanta tayi ta jingina da gadon tareda maida lower red lip dinta cikin baki tana tsotsa

Yanzu meye mafita? Taje ta roqeshin kamar yadda taji su rukky nacewa? Idan ta roqeshi zai saurareta? Koko ma qara samun kafar wulaqantata zaiyi? To idan ma taje ya xatace? Bata ta6a roqon alfarma ba kuma batasan yadda akeyi ba, kuma batajin tana iya strooping so low ta roqi alfarma, rashin roqon kuma na iya chazamata wulaqanta ta qarshe amma kuma ai batada tabbacin roqon zaisa ya saurareta

Cije lip din tayi tana lumshe ido cikin rashin samun mafita

Fuskarshi yayimata gizo a idanunta hakan yasata bude idanun

_inhale tasbih, exhale tahlil and stay safe_ maganar shi ta dawomata


Tsaki taja tana cewa "phsyco kawai" under her breath

Miqewa tayi daga kan sallayar ta ninke ta ajiye ta cire hijab dinta sannan takoma kan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login