Showing 15001 words to 18000 words out of 322641 words
Chapter 6 - DEEN Complete Hausa Novels By Arewa Novels.txt
da cikawa ai ire irensu sunfi jaraba alqur'an" inji dayan
"au haba?" na farkon yafada yana bashi hannu
Kashewa sukayi dayan na Cewa "am telling you"
Shidai Deen kallonsu yake yakasa pointing finger akan abinda suke nufi
"to na kaka, zamuyi sama" inji nafarkon
"me zakuyi sama?" inji Deen
Dariya suka qara kecewa daita dayan yace
"kamo tattabaru, kaidai naga sadda zaka waye, muntafi da alamu dai bakada lecture ko? "
Kada kai yayi yace" sai 1:00pm"
"toko zaka rakamu kallon kwallo" inji na farkon cikin neman magana
Girgiza kai yayi yace "A'a kakata tace..."
"Allah sarki, Allah sarki, basai ka qarasa ba, nagane ai. Kai majeed mutafi" yafada yana kamo hannun wanda yakira majeed din suka wuce suna dariya
Binsu da kallo yayi har suka 6acemashi sannan ya maida hankalinshi kan littafin hannunshi yashiga budewa
A bangaren su zee kau kuka taita musu acikin mota dukda kau yadda suke bata hqr suna rarrashinta, jin zuciyarta take kamar a oven don zafi
Abin yaxame mata biyu, ga cin mutuncin mr ibrahim ga na Wannan mutumin da batama san sunanshi ba
Wai waye mutumin nan? Ranan ya fizge mata gyale ya yaga yau kuma ya jefata a ta6o
"wlh Allah bazan yarda ba, wlh saiya gane ya ta6ani, sai yasan kowa ya wulaqanta daga shi har wancan immature ibrahim din, wlh saina koyamasu darasin lifetime!" saikuma taqara Fashewa da wani kukan
Dukkansu qoqarin kumshe dariyarsu suke hakan yasa kowa kauda kai don idan ka ganta dole tabaka dariya tayi gaja2 kamar ba classic zee ba
Rukky ce tayi qarfin halin cewa
"Haba zee? Don Allah kibar kukannan hakanan kar yaja miki ciwon kai, kuma batun koya hankali ai dole ne don wlh saiya san ya ta6a classic girl kamarki" ta qarashe a siffar gaya magana
Itadai bata ce komaiba saima cigaba da kukanta datake don data tuna taqara tunzura
Babu abinda yafi 6ata mata rai kamar kalmarshi ta *faduwa kikayi?* idan ta tuni sai taji wani qululun takaici yasake danne zuciyarta
Suma kingin haqurin suka shiga bata suna qara tirata akan karta kyaleshi wlh, ta banbance mashi tsakanin aya da tsakuwa
Itadai kawai jinsu take saidai bata tanka masu ba sai kukanta data cigaba dayi
Saida suka biya ta wani mall daya ta fita tasiyo after dress sannan suka dauki hanyar gida
Koda suka isa budemasu gate akayi, ganin sune yasa hantar cikin bala kadawa don beyi tynanin ganin ta ba yanzu don tace dai da asr zaizo daukarta, To ko takirashi be saniba ne?
Saurin bin bayan Motar yayi don karya qara laifi
Rukky ce tafara fitowa hakan yasa ta sallameshi akan yatafi kawai babu komai
Saida tazura after din acikin Motar sannan ta fito
Bata qara kallonsu ba ta wuce ba gode bare nagode ta shigewarta ciki wanda zata tashi sama
Ta6e baki sukayi suma suka koma cikin Motar nurr ta tada suka fice
Sai anan suka samu damar amayar da dariyar dake cinsu tundazu, aikau sukaitayi kamar sabbin kamu.
Tafiya yake cikin nutsuwa hannayenshi riqeda littatafai, komai nashi cikin sanyi yakeyinshi saidai akwai karsashi
Idan ba sani kayi ba saikayi tunanin tafiyar qasaita yakeyi nan kau haka yake Tafiya naturally
Wata mota tazo dagudu taja burki agabanshi wanda hakan yasashi dakatawa yana jan baya
Sauke glass din Motar akayi wata kyakyawar budurwa ta bayyana
"barka!" tafada tana daga mashi hannu fuskarta dauke da Murmushi
Shima murmushin yasaki yana rungume littatafan a qirjinshi yace
"barka dai ramla"
"ina zakane?"
Dan Wara idanu yayi sannan yace
"gida" agajarce
"ok shigo mutafi" tafada tana budemashi kofa
Kallon inda ta bude yayi sannan ya girgiza kai yana Murmushi
Dan hade rai tayi tace "meye hakan? Bazaka shigoba kake nufi?"
Girgiza kai yayi yace "A'a ngd yanzu zan samu abin hawa"
"nawa abin sauka ne halan?" tafada still bata saki fuska ba
Murmushin nan mai qara qawata qawattaciyar fuskarshi yayi yace
"A'a ina nufin adaidita"
"itama Wannan tana daidaitawa ai, wai deen meyasa kake min haka? Bafa sayar dakai zanyi ba" tafada cikin sigar tsokana
Qara fadada murmushin shi yayi yace
"ai bakiyi kalarsu ma ba"
"To kagani? Shigo mutafi kasa na tsaya kan hanya ko kaka ta hanaka shiga Motar mutane ne?" tafada cikin sigar tsokana tana Dariya
Dagowa yayi ya watsa mata hararar wasa yana dan turo baki sannan ka shiga tareda maido kofar ya rufe
"ato ai nasan halinka ne, komai kaka tace, kaka's boy" tafada cikin Dariya tana jan Motar
Bece mata komaiba sai murmushin daya sakeyi don dama shi murmushin shi yafi maganarshi yawa dukda wani sa'in idan yafara magana sai kasamashi full stop don besan ya taqaita bayani ba, taqarqarewa yake tsakaninshi da Allah yayi qoqarin fahimtar dakai
"ina ne unguwar tamu?" tafada tana dan satar kallonshi
Juyowa yayi ya kalleta yace
"unguwarku kuma? Ni tayaya za'ayi insani?" yafada yana dan Wara eyes
Lumshe idanu tayi ta bude acikin nashi, tana bala'in son innocent look dinshi
"To unguwarku nake nufi" tafada tana maida hankalinta kan kwalta
Daga gira daya yayi alamun aiyo? Sannan yace
"ke ina kika nufa?"
Juyowa tayi tadan saci kallonshi tace
"ina na nufa kuma? Kaike jana koni ke janka? Abeg mallam ina zan kaika don insan ko nawa zan chaza"
Kallonta yayi a mammakince yace
"dama kudi zaki amsa?"
Dariya tafashe daita har tana dukan sterring tace
"sannu dan son banza, nufinka kyauta zankaika? Ca6! Ai gwamnati ta hana aikin banza"
Murmushi shima yayi kawai bece komaiba
"inane?" tasake tambaya
"kofar kwaya wajen A.T.C" ya bata amsa
"wow hanyarmu daya Ni kofar saurii nike wajajen gidan sarki" ta amsa tana shan kwana
Bece komaiba sai Murmushin dayayi, satar kallonshi tayi itama tana murmushin tana ayyana da Allah zai mallaka mata deen da yagama mata komai, komai nashi burgeta yake.
Sanyi shi, muryarshi, murmushin shi, innocence dinshi, kai komai ma
Motar ce ta dauki shiru na wani lokaci kafin tayi breaking silent din da
"gaskiya fa dazu ka bada show, abinda kayi ya farantawa kowa"
Juyowa yayi ya kalleta itama ta juyo ta kalleshi tana Murmushi tareda daga mashi gira daya
Murmushi yayi shima sannan ya dauke kai cikin zuciyarshi yana mammakin yadda kowa kejin dadin abinda yafaru, dama haka kowa ya tsaneta? Sai jiyayi tabashi tausayi
"gwara da ka jefar da hegiya ta6o, ai ta raina uban kowa, ba students ba ba lecturers ba, kamin daidai wlh"
Shikau da be gajuya da kare Kanshi yace
"O'O! Nifa ba jefata nayiba" yafada cikin Jin haushin yadda kowa ke tuhumarshi akan fadawarta ta6on, mutanen dasuka tareshi da Wannan maganar yau basuda iyaka don har abin yafara isarshi
Ganin kamar ranshi ya 6aci yasata cewa "O'O! Nifa bacewa nayi kayi laifi ba ai hskanma dakayi daidai ne" itama tafada cikin salon maganarshi
"ba daidai bane, Ni ban jefata ba, itace tayimin tsawa shine na saketa Batareda na sani ba saboda na tsorata kuma wanda ya tsorata adrenaline hormones dinshi ke hawa yayi abu cikin fitar hayyaci ko abinda ya girmi hankali shiyasa nima bansan na saketa ba" yafada cikin son kare kanshi, yagaji da yadda suke fassara abin, shi harga Allah bakin gaskiyarshi yake fadi don a duniyar nan ya tsani tsawa fiyeda yadda kuke zato don da anyimashi firgicewa yake ya rude
"To ai shikenan tunda ba da gangan kayi ba, bakada laifi ai, Allah ya tsare gaba" tafada ganin fuskarshi ta nuna alamun rashin Jin dadi
Da amin ya amsa ahankali daga nan kuma babu wanda yaqara cewa komai
Cikin dan qanqanin lokaci suka isa unguwar tasu
Daidai makarantar A.T.C din ya sauka, yana shirin fiddo kudin taja motarta tafece tabarshi sagale da baki
Girgiza kai yayi yana wani slight Murmushi sannan yanufi wani mai saida yalo abakin titi ya sayi na hamsin sai agwalumar hamsin sanin kaka na sonta sosai ya bada kudin ya amsa bayan ansaka a leda sannan yayi hanyar gida cikeda doqin ganin kaka... âœï¸
Ummin fasihu 🧚ðŸ»â€â™€ï¸?
8/2/21, 9:31 PM - BuhainatðŸ˜: *ðŸ™ðŸ»â€â™‚ï¸DEEN ðŸ™ðŸ»â€â™‚ï¸?*
*007*
Saboda 6acin rai ko knocking batayi ba bare ayi batun sallama ta murda handle din ta tura qofar tashiga
Bata wani lura da mutum falo din ba tanufi stairs
"ke!" maganar datasata Tsayawa cak kenan daga yunqurin hawan stairs din datayi
Juyowa tayi tana kallon mummy dake bisa daya daga cikin kujerun falon, remote a hannunta
Ajiyar zuciya ta sauke cikin ranta tana addu'ar Allah yasa karta qaramata wani zafin
"mummy? Barka da gida" tafada still tana inda take
Bata amsa gaisuwarta ba sai cewa tayi
"ke yaushe zakiyi hankali zainab? Ki wani fadoma mutum daki ba knocking bare sallama? Which type of manner is this?"
Zuciyarta taqara dagulewa hakan yasa tafara hawaye kamar an bude fanfo
Sakin baki mummy tayi tana kallonta ganin tama zame qasa ta hada kai da gwiwa tana shesheka
Tafa hannu mummy tashiga yi sannan ta riqe ha6a
"zainab lfy qalau kuwa? Abin naki har yakai daga magana sai kuka?"
Bata amsa mata ba kuma bata dagoba sai sheshekar data qarawa volume
"wai badake nakeba!" inji mummy atsawace har saida zee ta zabura
Fashewa da kuka taqarayi ta miqe tahaye sama dagudu cikin kuka
Binta da kallo mummy tayi harta haye sannan ta girgiza kai tanama diyar tata fatan shiriya
Koda tashiga dakin gado tanufa direct tafada akai tana cigaba da kukanta
Jitake komai na duniyarnan beyimata dadi, Gani take babu mai sonta a duniyarnan, kowa burinshi ya cuzguna mata idan ka cire daddy mai son farincikinta
Saida tayi mai isarta sannan ta tashi ta cire kayan jikinta cikeda kyankyami ta jefa a basket sannan tafada toilet ta sakarma kanta shower.
***
Da sallama yashiga cikin soron gidansu, kasancewar akwai wani dan soro(zaure) saikabi taciki sannan kashiga ainahin cikin gidan
Gida ne mai dauke da dakuna biyu sai kitchen dake daga bangaren dama sai kewaye dake daga can qarshen gidan sai tsakar gida mai dan yalwa, gidan dai kallo daya zakamashi kasan na masu rufin asiri ne
Qara wata sallamar yayi bayan ya shigo cikin tsakar gidan don da alama ba'aji na farkon ba, kodayake ya za'ayi aji bayan yana magana ne kamar da Kanshi yake? Ko kadan be iya daga murya ba gashi muryar tanada taushi ba irin husky voice dinnan bane na maza
Jin haryanzu shiru ba'a amsa ba yasashi nufar dan kitchen dinsu ganin hayaqi na fitowa daga ciki da alamu girki ake ciki
A bakin kofa ya tsaya yana kallon wata tsohuwa dake duqe gaban murhu tana hura wutar da iskar bakinta don wutar tamutu sai uban hayaqin daya turnuke kitchen din
6ata fuska yayi yace "O'O!"
Sai alokacin tsohuwar tasan da tsayuwarshi a wajen
"A'a Kamal? Ashe ka dawo?" inji dattijuwar tana miqewa tsaye baki washe
"O'O! Kaka ba nace kibar hura wuta da baki ba?" yafada yana 6ata fuska
Dariya tayi tace
"To Kamal taqi huruwa, ya zanyi?"
Cikin tura baki yazo yawuce ta ya nufi murhun wutar ya ajiye littatafan shi gefe wanda yayi Daidai da daukesu da kakar tayi, ya dauki makwashin shara(parker) ya shiga fifita wutar, saida shima tabashi wahala sannan takama sai a sannan yatashi yabiyo kakar wanda tuni ta fita ya tarda tana ajiye mashi ruwan sanyi data debo daga tulu acikin wani kofin silba akan tabarmar data shimfida mashi
Qarasowa yayi ya zauna still bakinshi a tunzure
Kaka itama zama tayi kusadashi tasa hannu ta shafa tulin sumar Kanshi tana Murmushi sannan tace
"waya ta6amin kyakyawa na?"
Sake kumbura fuska yayi yace
"O'O! Nidai A'a"
Dariya tayi sannan tace
"haba kyakyawa na? Idan kana fushi rage kyau kakeyi, ko kanaso ka koma mummuna kamar ni?"
Saurin kallonta yayi sannan yasake 6ata fuska yace
"O'O! Allah kinada kyau"
Dariya maganar shi tabata tashiga yi tana cewa
"A'a wlh, kaima kasani banida wani kyau, bakaga ni baqa bace?"
Zamewa yayi ya dora Kanshi bisa cinyarta yana jujjuya kai bisa cinyarta cikin shagwaba wanda tayi bala'in yimashi kyau
Itakau Dariya take mashi tana bashi hqr inda kamar qara tunzurashi take don sai qara shagwa6e mata yake
"kai ka tashi kaji, yau abinda kafiso nayi maka" tafada tana Dariya
Saurin miqewa zaune yayi yana dan Wara oily eyes dinshi
"dagaske kaka?" ya tambaya cikin doqi
"bari kagani" tafada tana yunqurawa ta miqe tawuce daya daga cikin dakunan gidan, can kuma tafito riqeda kwano mai murfi tareda plate din roba tazo gabanshi ta dire
Saurin jawowa gabanshi yayi ya bude
Lumshe idanu yayi cikin jindadi ya bude akan alalar dake ta tururi tayi jajur alamun taji taruggu kamar yadda yake sonta.
Washe baki yayi wanda yaba jerrarun fararen haqoranshi damar fitowa yana nuna alamun jingina ga kaka
Tallabe mashi keya kaka tayi tana cewa
"ja'iri kawai, meye anan?" tafada tana daukar ledar gabanshi
Be bata amsa ba sai 6are alalar dayake yi daga cikin leda
Budewa tayi tana leqa ciki, Murmushi tayi tana qara Jin soyayyar jikan nata acikin ranta
Tashi tayi taje ta daurayosu tadawo kusada Deen daya fara aika alalar shi
Haka suka zauna sunaci suna fira cikeda nishadi da annushuwa, kallo daya zakamasu ka hango tsantsar shaquwar dake tsakaninsu
Sai a lokacin nasamu damar qarewa kaka kallo
Baqace kamar dai yadda tafada, don bazaka ida tantance baqa bace sai idan kaga sun jera da Deen da fatarshi ke tass irin wanda ake cewa saika wanke hannu kafin ka ta6a
Batada muni hakama Batada kyau, kawai dai tanada dai tsaka tsaki wataqila harda tsufan datayi yasa baza'a iya tantancewa ba
Kaka a qiyasce takai shekaru sittin da wani abu amma tanada qarfinta don tanayin komai datakeso da kanta, haka zalika akwai zuciyar nema don kullum sai tayi koko da qosai na siyarwa dasafe
Da Wannan sana'ar take daukema kanta da dan jikanta nauyi dukda shima ba azaune yake ba, duk lokacin da babu school ko kuma beda lecture yana zuwa wajen wani carpentary shop dake qasan layinsu inda ake hada kayan furnitures Kama daga kujeru zuwa gadaje na amare.
Ko kadan babu wata Kama tsakanin Deen da kaka don idan bawai sani kayi ba sai kayi mashi daukar balarabe
Yana da kyau, irin kyawun nan mai tafiya da zuciya, komai nashi Daidai kamar shi ya hallici Kanshi, yanada cikar zati da qirar mazantaka don a kallon farko sai kayi tunanin wani jan wuya ne ko daya daga cikin ire iren jaruman nan na littatafan yaqi saidai a zahiri ba haka bane don wani irin mutum ne mai sanyin hali da mu'amala
Beda hayaniya ko kadan, komai nashi yana yinshi ne asanyaye, ma'abocin Murmushi, gwanin ban Dariya uwa uba he's so innocent, beda matsala ko kadan. Ataqaice dai Deen is a cool handsome guy da kowacce mace ke muradin samu a matsayin abokin rayuwa na har abada
Kaka... kaka ce komai na Deen don ko yanzu kuka fara haduwa dashi inhar zaka zauna na 10mins dashi saika fahimci kaka nada mutuqar muhinmmanci agareshi, beda wanda zai maye mashi gurbin kaka yayinda itakuma kaka ta maye mashi gurbin kowa.
Uwa, uba, aboki duk kaka ce. Yana qaunarta fiyeda tunanin mai karatu hakan ma kaka bata da kowa bayan shi kuma batada wanda yafiyemata shi, Ataqaice dai kaka ce duniyar Deen itama shine duniyar ta
Koda yagama harta sauke ruwan data dora a murhu ta sirka mashi takaimashi a bayi.
Saida ya kauda kwanikan sannan yashiga dayan dakin da nake kyautata zaton nashi ne ya rage kayan jikinshi yafito daga shi sai vest da nicker
Wow! Gaskiya Deen ya hadu takoina, ashe dazu kallon tsoro nayimashi?
Sosai mazantakarshi taqara fitowa acikin Wannan shigar, ata cikin vest din kana iya hango broad kirjinshi da flat tommy dinshi mai dauke da packs
Deen irin mutanen nanne masu gargasa wato masu gashi ajiki, hatta hannayenshi da kaffafu gashi ne kwanttace qawace dasu.
Zura slippers yayi ya dauki kwandon wanka yawuce makewayin dake can daga qarshen gidan
Makewayin ba rufi asama irin buddaden nan ne, shiga yayi bayan yayi addu'ar shiga toilet da kaka ta koyamashi ya rufo qofar.
Kaka kau gyara inda sukaci abincin tayi sannan ta zubo ruwa abuta tayi alwallar sallar asr wanda aketa kira, koda tagama saita qara zuba ruwa aciki ta ajiye tashigewarta dakinta
Kaka bata jima da shigewa ba yafito daga bayin riqeda bokitin qarfen wanka da kwandon soson sai qanqame jiki yake, saurin ajiyewa yayi yanufi dakinshi da sauri.
Ba'ayi minti 3 ba yasake fitowa Sanye da jallabiya baqa, yanufi ruwan da kaka ta ajiye ya tsuggunna yashiga daura alwalla.
Tashi yayi bayan yagama yaqara komawa dakinshi befi seconds goma ba yafito Kanshi Sanye da hular tashi da kwakwa fara sai counter dayake qoqarin sanyama yatsarshi
Kaka ce tafito Sanye da hijabi ta kalleshi
"kafayi sauri karka rasa sallar gashi can an kabbara" tafada tana miqamashi kudi
Da to ya amsa sannan ya amshi kudin hannunta yafice bayan yayi mata saiya dawo, da addu'ar dawowa lfy tabishi sannan takoma daki itama
Massalacin beda nisa da gidan su, koda ya isa har anyi ruqu'i hakan besashi zuwa aguje don karya rasa raka'arba, shiga yayi ya Daidaita sahu da wani sannan yatada kabbara lokacin har sun dago, haka yabisu har suka idar da sallar shikuma ya tashi ya kawo daya rasa
Koda yagama komawa yayi ya zauna yana danna counter din hannunshi, saida yaqara mintuna kusan talatin ahaka sannan yayi daily du'a dinshi yashafa.
Saida ya gaggaisa da yan tsirarun da suke cikin Massalacin sannan yafito, nan ma wasu ya iske waje suma saida ya gaida nasama dashi ta hanyar russunawa Daidai shi kuma ta hanyar musabaha, har rige rigen amsamshi dattijen keyi kowa na binshi da kallon sha'awa suma tsararrakinshi har rige rigen bashi hannu suke don su gaisa, saida suka gama gaisawa yajuya yanufi hanyar da zata sadashi da kasuwa don yiwa kaka siyayyar geron kokon jibi da waken qosan gobe idan Allah yakaisu
A bangaren zee kau tunda tashige daki bata qara saukowa ba, ko abinci bata nemaba, dama can batada yawan ci sai gashi abin ya hade da rannan she's in a bad mood hakan yasata loosing apettite dinta taji bata marmarin cin komai.
Zaune take kan gado jingine da kan gadon tana danne dannen waya saidai kallo daya zakamata kasan she's moody
Kwankwasa kofar da'akayi yasata dan dakatawa daga abinda takeyi ta kalli kofar Batareda tace komaiba
Sake Kwankwasa kofar akayi hakan yasata dan yamutsa fuska kafin tace
"waye?"
Ba'a amsa ba sai turo kofar da akayi aka shigo da sallama
Ganin mummy ce yasata sakin fuskarta data daure tamm tana jiran ganin