Showing 30001 words to 33000 words out of 322641 words

Chapter 11 - DEEN Complete Hausa Novels By Arewa Novels.txt

27 Nov 2025

6224

dinta banda rukky da itama tanacan tana faffutukar ganin ta kammala nata.

Hira sukeyi sama2 rabin hankalinta akan yan class din, tana kallon yadda duk suka bi suka tada hankalinsu

Tsaki taja arai, ina amfanin mugunta? Gashi don ita yayi amma gatanan zaune hankali kwance su students din nashi ke shan wuya

Tasan itama ba lallai bane taci abin kirki ba amma tana kyautata zaton duk lallacewa dai ta tsira da rabin marks din Wato 10 saidai tanada tabbaci cikin so called students dinsu dawuya quatern cikinsu yakai goman nan, yanzu wa gari ya waya? Garin yiwa wasu mugunta ka afka naka aciki, kodayake yasan abinda ya taka don duk qumu duk yadda students din nashi zasu fadi a Wannan assignment din sunada 30marks dama so haka baxaiyi affecting dinsu ba sosai, dan sakin Murmushin takaici tayi tana Girgiza kai.

Agogonta ta duba taga qarfe nawa don hayaniyar ajin ya isheta, gwara yazo ta miqamashi tsiyarshi ta fice

Ganin tara saura mintuna sha biyar yasata jan karamin tsaki, tajawo jakkarta da niyyar ciro assignment din tayi going through abubbuwan datayi kafin yashigo.

Saidai me? Takardar assignment din tace daukarni inda kika ajiye

Tun bata dauki abin serious ba har abin yafara bata tsoro hakan yasata miqewa tareda zazzage dukan abinda ke cikin jakkar bisa desk dinta Batareda ta saurari su deeya dake ta tambayarta lfy?

Da guda2 tafara daukar littatafan tana warwarewa tana zazzagewa ko zata ganta ta fado saidai harta gama babu ita ba alamun ta.

Tashin hankali da ba'a samaka rana! Komawa tayi jagwab a kujera tana dafe saitin zuciyarta

"wai zee lfy? Meke faruwa ne?" inji nurr suma duk hankalinsu ya tashi

"innallilahi waina ilaihi rajiun! Nashiga uku ni zainab" tafada cikin Tashin hankali

"wai menene zee? Kinafa tadamana hankali" inji sumee Itama cikin Tashin hankali

"Assignment dina... Ban ganshiba"tafada cikin yanayin fitar hayyaci

Galala sukayi suna kallonta speechless

Can deeya tasamu fizgo maganar tace
"kamar ya zee? Ina kika ajiye?"

Kama kanta tayi da hannu bibbiyu tana nanata innallilahi


"dan Allah zee kiyimana magana, ina kika saka assignment din?" inji nurr cikin rawar murya

Nuna masu jakkarta tayi don tama kasa magana, bata fatan abinda ke shirin faruwa ya tabbata

Dukkansu rufarma jakkar sukayi suka hau bincikata yayinda itakuma tayi suman zaune tana binsu da ido

Saida suka bincika suna sakewa kusan sau uku sannan suma suka yarda bata cikin jakkar

"ya sallam! Zee wa kika ba?" inji sumee kamar zatayi kuka

Qara riqe kanta tayi cikin rudani da Tashin hankali Batareda ta iya furta komaiba


"zee kiyi magana mana" inji deeya

"wa zanba deeya? Wa zanba? Da hannuna fa na sakata a jakkarnan kuma ban qara budeta ba sai yanzu" zee tafada cikin rudani

"To gaskiya da takardarnan na acikin jakkarnan da anganta, gaskiya bata nan, kidai qara tunawa ko kin mantata gida?" inji nurr

Dafe kanta tayi da hannuwa biyu tareda lumshe idanu tana fitar da numfashi ahankali

Rukky ta qaraso wajen cikin sauri, tana zuwa ta zauna jagwab tana maida numfashi
"wai! Allah yayi" tafada tana maida numfashi

Ganin dukkansu a moody state yasata dan shan jinin jikinta

"yadai?" tafada tana binsu da kallo

Duk shiru sukayi an rasa mai iya magana

"wai lafiya? Meke faruwa ne?" tQara tambaya tana dan Wara idanu

Deeya ta sauke ajiyar zuciya sannan tace
"rukky assignment din zee ne ya 6ata"

Kwalalo idanu rukky tayi cikin firgici tace
"wane assignment?!"

"wane bayan Wannan na mr ibrahim?" inji sumee

"innalillahi waina ilaihi rajiun! Garin yaya? Ina kikasashi zee?" tafada tana maida akalar tambayar ga zee

Kasa magana zee tayi sai qara tamke kanta datayi tana lumshe idanu

"cewa tayi a jakka amma babu neman da bamuyiba amma babu shi" inji nurr

Tashi itama rukky tayi ta zazzage komai na jakkar ta watsasu amma babu shi ba alamun shi

Duk abinda sukeyi babu wanda ya lura dasu don kan kowa ya dau zafi kowa takanshi yake

"innalillahi, zee wa kika ba? Ki tuna please" inji rukky cikin damuwa

Watsa hannunta zee tayi alamun batasaniba don magana ma wuya take mata, ita kadai tasan yadda takeji

"kiyi tunani sosai zee, ko kin barta agida ko wani wajen, kiyi tunani sosai" inji rukky

Riqe kai tayi tana dan yamutsawa alamun tana son tunanowa

"yauwa zee ki tunano tabbas ko tana gida ko kin ba wani" inji nurr

Cigaba da yamutsa kanta tayi idanunta lumshe, can saita tsaya cak da abinda take ta bude idanunta da sauri

"yaya???" suka hada baki suka tambaya cikin sauri

"Oh my Goodness!!!" tafada tana komawa jikin kujera yaraf

"menene? Halan gidan kika barota din" inji sumee

Dagowa tayi da idanuwanta dasuka duri ruwa tace
"da agida ne bada yafi sauqi ba atleast nasan kiran waya kawai zai biyamin buqatata amma Wannan banidama tabbacin yanzu akwaita" ta qarashe tana dafe kai

"me kike nufi da hakan?" inji deeya

"ya zanyi? Tana wajen wancan gayen" tafada cikin rawar murya alamun kukan na kusa

"wane gaye?" suka hada baki wajen tambaya

"Deen mana!" tafada tana bubbuga goshinta

"DEEN!!!" suka hada baki a mugun mammakince

Hawayen datake riqewa tundazu suka xubomata tace
"takardar nacikin littafin dana bashi jiya yayimin note, am doomed!" tafada tana Hawaye sosai

Galala sukayi suna kallonta sun kasa cewa komai

"yanzu ya zanyi? Am perfect sure ya jefar daita cikin haukanshi ko ya yagata, Oh my God why am I so unlucky?" taqarashe tana Fashewa da kuka

Hakan yaqara sanyaya jikinsu saidai kowanne yarasa me xaiyi ko zaice don tabbas idan har takardar nan na wurin Deen to tazama sheqaqa tuni

"zee kibar kukannan haka nan please" inji nurr cikin sanyin murya

"inbarfa kuka kikace, kinsan me hakan ke nufi? Hakan na nufi i've lost the 20% for good!" tafada cikin kuka

"kar kice haka zee, tayiwu tana nan, kawai abinda yakamata shine muje mu sameshi da muzauna muna qara wasting time, kinga 9 saura minti 10 yanzu munada minti 10 left" inji nurr

Kamar wadda aka tsikara tayi zumbur ta tashi tana cewa
"muje please"

Suma tashi sukayi suka maramata baya suka bar sumee na tattara abubuwan cikin jakkar zee dasuka watsar tana maidawa


Direct wajen zamanshi sukayiwa tsinke amma babu ko alamun shi, class dinsu suka wuce kasancewar su deeya sunsan class dinsu saidai mutanen da suka iske a class din basufi goma ba, da suka tambaya sukace basu ganshi ba dakyar ma idan ya iso don yau lecture din 12pm garesu.

Tashin sense! Yawo iya yawo sunyi, babu inda basu zagayaba a school din amma babu mai ko Kama dashi, zee banda dauke Hawaye babu abinda take, danasanin bashi aikin rubutun take sosai tanaji kamar ta maido hannun agogo baya saida suka gaji sosai sannan suka ja gefen wani class suka tsaya suna maida numfashi

Kallon agogo deeya tayi
"guys saura minti 4 fa"

"yanzu ya za'ayi? Deen dai baya makarantar nan wlh" inji nurr

"kawai mukoma class karya shigo bamunan" inji rukky

"zee kiyi hqr kizo mutafi" inji sumee

Share hawayen fuskarta tayi tace
"inje ina? Idan naje me zanyi? Kawai ku tafi"

"haba zee? Kitaho please, idan mukaje saikiyi mashi explaining" inji deeya

Murmushin takaici tayi taqara share hawayenta tace
"bazaku ganeba, ku tafi kawai"

Shiru sukayi kuma suka kasa tafiya

"kutafi karku 6ata lokacin ku a banza ayi biyu babu" tafada tana jin zuciyarta na suya sosai


Badon ransu yasoba kodayake idan yaso ma ba ganewa za'ayi ba suka juya suka tafi jiki a sa6ule

Zamewa tayi wajen ta tsugunna ta rungumo qaffafunta sannan ta cusa kanta a tsakankanin cinyoyinta tana kuka marar sauti... âœï¸


Ummin fasihu 🧚ðŸ»â€â™€ï¸?
8/2/21, 9:32 PM - BuhainatðŸ˜: *ðŸ™ðŸ»â€â™‚ï¸DEEN ðŸ™ðŸ»â€â™‚ï¸?*





*012*


_hhhh mutane nata complain wai sanyin Deen yayi yawa, To ni bansan ya zanmaku ba, Wannan labarin na riga na tsarashi tun kafin nafara rubutashi, yadda tsarin yake haka nake bi dashi kuma karku manta akwai ire iren Deen a real life wadanda keda irin Wannan halayyar kuma suna fuskantar wulaqancin mutane babu yadda suka iya, so kuyi hqr afterall duka duka yaushe aka fara novel din? Wannan farko farko ne kuma bamuda tabbacin haka za'aita tafiya, so please exercise patience, I don't like the way you guys are complaining, idan kuma kunaso muyi rushing abinne, fine🤷ðŸ»â€â™€ï¸_







Yanzu shikenan tayi loosing din 20% dinnan kenan? Dukda tasan ba duka zataciba amma tasan ko yayane dan mark din dazata samu zai dan taimaketa ko yayane, loosing dinshi is like a bad starting, alamu ne na faduwarta.

"Deen where are you? Please show yourself" tafada under her breath tana sake cusa kanta a cinyoyinta


"Mud queen!" taji anfada kamar daga sama

Cak kukan datake marar sauti ya tsaya tana bude idonta dake cikin cinyoyinta

"Mud queen!"

Taqara jin anfada akaro na biyu

Saurin dago kanta tayi idanunta suka sauka a nashi hakan yasata tashi azabure

Yadda ta tashin ne yasashi dan ja baya yana kallonta

Wani Murmushi yatahomata tareda hawaye

"OMG Deen, ina ka shiga ka kusan sani hawan jini?!" tafada cikin yanayin fitar hayyaci


Bece komaiba sai kallon daya kafeta dashi ganin hawaye a fuskarta, abinda be ta6a gani ba tunda yasanta

"ina littatafaina?" tafada tana wartar littatafan hannunshi Batareda ta tsaya jiran amsarshi ba

Cikin sa'a kau nata ke asama, jiki na rawa tashiga bubbude page pages din da sauri sauri jikinta sai 6ari yake kamar wacce ke a fridge, hakan yasa ta tsallake inda takardar take Batareda ta lura ba

Koda tagama bubbudewa taga babu ta dauki handout din shima tashiga bubbudewa saidai shima babu takardar


"as I feared!" tafada tana dafe kai wasu hawayen na zubomata

"why are you crying?" taji yafada calmly yana kallonta da pure white eyes dinshi

Dagowa tayi ta kalleshi da rinnanun idanunshi, jitake kamar taita kwala ihu

Dakyar ta saita muryarta tace
"ina ka yardamin takarda?"

"wacce?" yafada yana Wara mata oily idanunshi

"the damn paper I put here!" tafada cikin qaraji tana nuna littatafan ta

Bata rai yayi yana kallonta Batareda yace komaiba

"dakai fa nake!" tafada a qule

"O'O! Must you shout?" yafada yana kumburi

"me kake son nayi To?! Gabadaya ka lallatamin komai..."

Ganin yabude littafin ya zaro wata paper a tsakiyar littafin yasa kingin maganar maqalewa

"This?" ya tambaya yana miqamata

Kwacewa tayi da sauri tareda warwarewa

Sama sama tayi going through dinta taga itace hakan yasata gasping in excitement
"OMG! Itace!"

Saurin duba wristwatch dinta tayi, 1min to go

Bata bi takan Deen ba kuma ta rataye jakkarta ta nufi class dinsu cikin sassarfa gabanta na dukan uku uku.


Cikin sa'a kau bekai da zuwa ba hakan yasata saurin shiga tana saukar da ajiyar zuciya

Su sumee sunyi mammakin ganin shigowarta saidai kafin suyi wani yunquri har mr ibrahim ya shigo

Hakan yasa zee neman wuri ta zauna gaba gaba Batareda ta qarasa wajensu sumee ba


Duk tashi akayi ana gaidashi including zee saidai ita tashin kawai tayi amma bakin ko motsi beyi ba.

Cikin takun izza yafara takowa tsakiyar class din yanabin kowanne student da kallo, dayake yau da biyu ba lecture kawai za'ayi ba, class din yacika maqil

Jin kamar ana kallonta yasata dagowa idanunta suka fada a nashi

Saurin fizge nata idanun tayi ta saukesu qasa gabanta na tsinkewa haka kawai zuciyarta ta bata Wannan kallon ba normal kallo bane na tsana daya saba yimata, abayan Wannan ta hango wani wanda yayi kamada ta manufa

"sit..." yafada cikin bada umarni

Hakan yasa duk suka zazzauna, class din yasake daukan deadly silent


"yeah... Today I noticed class dinmu yaqara cika, guess akwai reason behind this" yafada yana Murmushi

Class din ya dauki qananun qananun surutai wanda baka iya sanin abinda ake cewa

"silent!!" yafada authoratively don kawo shiru a class din, aikau nan da nan class din yadauki shiru

Itadai zee batayi kwakwarar motsi ba tundazu burinta kawai ya buqaci takardar shi tabashi taqara gaba

"well koma menene, we shall see" yafada yana zama kan desk din gaba yana facing dinsu

"hope kowa na riqeda assignment dinshi?" yafada yana Bin kowa da kallo

Wani mumuring din yasake tashi kamar dazu. Yanzu ma saida yakira order sannan akayi shiru

"well, koma baku riqe ba ba tawa matsalar bace, just know that 20% of your exams marks ne sukabi iska"

Nanma surutanne suka qara tashi saidai kafin yayi nisa yaqara takamusu burki sukayi tsit

"is better you keep quiet and listen, meye na hayaniya, if you pass you pass hakan if you fail you fail, simple! You cant plant pepper and harvest onions, you reap what you sow, so kowa ya fiddo assignment nashi"

Dumm.. Gaban zee yafadi daidai kalmar qarshe na mr ibrahim.


Wani abu yashiga dawowa zee a kwalwa yana mata gizo.

The handwriting... Yes! Tabbas taga handwriting din... Amma a ina?

Lumshe idanunta tayi ta bude su cikin son tunano abinda ketayimata guje guje a kwalwa

Handwriting din... The unique handwriting... Taganshi a wani wuri... Ina?

Sake lumshe idanunta tayi

_*ZAINAB FAROUQ DAN FARANSHI*_

cak! Brain dinta ya tsaya daga aiki na wucen gadi

Yes, haka tagani anrubuta da unique handwriting din, sunanta aka rubuta

_a ina?_ tambayar datayiwa kanta kenan

Gabanta ne yasake yankewa ya fadi har saida tadan dafa chest dinta

_No.. No.. No! It cant.. be_ abinda tafada a ranta kenan

Saurin bude jakkarta tayi tareda zaro takardar da ta amso hannun Deen yanzu hannu na 6ari tashiga warwarewa tama manta a class suke


Turus.. Tayi ganin abinda zuciyarta ke fargabar gani

Handwriting dinshi ne, ba nata ba! Ya chanza mata rubutu, ya chanza!


Going through din content din paper takeyi hankali tashe, komai ya chanza, kwata2 Wannan ba aikinta bane ba calculations dinta bane

"now start submitting!" taji muryar mr ibrahim na cewa haka

Dagowa tayi taga yana row din farko yana amsar takardun da guda guda

Saramata kanta yashiga yi tanajin kamar roof din classroom din na jujjuya mata

Fasalta maku halin data shiga a Wannan lokacin ba mai yiwuwa bane , ita kanta bazata iya misalta halin data tsinci kanta aciki ba Kawai dai azahiri zaune take kamar kowa paper a hannu amma ita kadai tasan abinda zuciyarta ke going through.

Batasan tsawon lokacin data dauka ahaka ba sai jitayi daga sama ana cewa
"yes? Your assignment miss"

Dagowa tayi ta ganshi akanta fuskarnan murtuk

Kallon gabanta tayi taga duk babu students din gabanta alamun duk sun bada sun fice Sai wadanda ke bayanta da ba'a kai wajensu

"mallama you're wasting my time!!" inji mr ibrahim atsawace hakan yasa tayi Saurin jerking back to life

Hannu na dan kyarma ta bashi takardar ya amsa yana jan guntun tsaki tareda yin gaba

Jitayi classroom din na cigaba da juyamata hakan yasata Saurin miqewa ta jawo jakkarta ta nufi hanyar waje tana hada hanya.

Suma su sumee saida sukayi submitting sannan duk suka fito waje.

Waige2 suka shiga yi na neman inda zasu hangota, ganin basuga ko 6il6ishinta a wajen ba yasasu nufar usual mazauninsu dake bayan classes.


Tun daga nesa suka hangota zaune kai hade da gwiwa, basu kawo komai aransu ba suka ida qarasowa wajen.

Zazzaunawa sukayi nurr tace
"ya dai? Kin samu Deen dinne halan?"

Ko motsawa batayi ba bare ta dago

"zee?"

Nanma shiru

"zee wai lfy?" inji sumee tana dago kanta

Kwacewa tayi tasake maida kan akan gwiwowinta

"she's crying fa" inji sumee tana kallon sauran

Dawowa kusada ita duk sukayi suka sata tsakiya

"zee wai lfy? Bakiga Deen dinbane?" inji deeya

"To amma ai tayi submitting" inji rukky

"da wannan yar iskar takardar danayi submitting ba gwara banyi exam dinba gabadaya ba?!" inji zee data dago afusace fuska jage2 da hawaye

Duk Tsayawa sukayi suna kallonta sannan nurr tace
"bamu ganeba"

"dama tayaya za'ayi ku gane?! Wancan lunatic fring din ya chanzamin takarda ya jefar da wancan ya chanzamin da nashi dake cikeda hauka!" saikuma ta dafe kanta hawayenta na qara gudu

"mene? Kiyimana gwari2 yadda zamu fahimta" inji rukky

"bayan kun tafi na ganshi kuma na amshi takarda only to realised that he changed my paper at the deadly time! Nace mashi ya ta6amin takarda ne? Ko na bashi ajiya ne dazaiyimin tempering da ita, duk ya sauya calculations dina ya sanya nashi na hauka!" tafada cikin tsananin bakinciki

"kutt! Kina nufin aikin Deen kikayi submitting?" inji rukky sai kuma tafashe da dariyar da bata shiryaba don can ta hango Deen ya zauna ya daddage yana mata lissafin hauka a paper

Sosai dariyarta taqara tunzurata hakan yasata miqewa a fusace tace
"yes, Dole kiyi Dariya mana tunda ba akanki abin yafaru ba, I won't blame you, am to be blamed most!" tafigi jakkarta tayi gaba fuuu

Kallon rukky da tabar Dariya duk sukayi sannan suka ta6e baki suka marama zee baya leaving rukky behind, daga kafadu rukky tayi ta koma ta zauna saikuma tasa Dariya tana imagining face din mr ibrahim idan yana marking, he'll be like anya script dinnan bana psycho nake marking ba, hakan data hasaso yasata qara Fashewa da wata dariyar.


Zee kau tafiya take amma kallo daya zakamata kasan cewa a mugun fusace take kuma bala'i na cin zuciyarta don fuskarnan dinke take d'ab, su sumee kau na bayanta suna binta amma sun kasa taddota kasancewar tafiyar tata ta fusattatu ne ba yanga aciki

Tun a nesa suka hangoshi zaune a inda yasaba zama shikadai riqeda littafi yana dubawa sai lemun coke na can dayake dan korawa akai2

Bata ja burki a koina ba sai agabanshi, kafin ya dago ta fizge littafin hannunshi tayi flinging dinshi.


Saurin miqewa tsaye yayi yana kallonta

"kai wane irin daqiqi ne?! Nace kai wane irin daqiqi ne!!"


Bata jira amsarshi ba ta fizgo can din coke dinshi, beyi auneba sai jin sanyi yayi ya ratsashi a qirji dama duk gaban jikinshi


Jan wani irin wawan numfashi yayi Kanshi na saramashi a lokaci daya

"zee!!!" nurr tayi exclaiming

Bata saurareta sai cigaba da cewa
"how dare you temper with my work? How dare you!!"

Kanshi ne yaqara sarawa sosai, dagowa yayi ahankali ya sauke fararen idanunshi da izuwa yanzu sunyi jajur akanta

"I said how dare you!" tafada tana daga hannu da niyyar marinshi


Carraff taji an cha6e hannu ya maqale akan iska

Kafin ta tantance komai taji an dauketa da wani bahaggon mari... âœï¸



Ummin fasihu 🧚ðŸ»â€â™€ï¸?
8/2/21, 9:32 PM - BuhainatðŸ˜: *ðŸ™ðŸ»â€â™‚ï¸DEENðŸ™ðŸ»â€â™‚ï¸?*





*013*



Wani irin spark kanta yayi taga wuta ta gilma mata a idanu, baya baya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login