Showing 42001 words to 45000 words out of 322641 words
Chapter 15 - DEEN Complete Hausa Novels By Arewa Novels.txt
tsintar kanta a Wannan halin
"so the solution shine, bayan sanin formula ki kuma san yadda zakiyi amfani daita ta kowacce siga, ya kasance ko tawane siga qyestion yazo miki zaki iya tackling dinshi, kuma wajen yin haka sai ansa nutsuwa sosai an fara sanin what the question is all about yadda xakisan yadda zaki 6ullomata, yanzu saboda qarancin lokaci bari mudauki wani topic din yadda kafin mutafi munqara two more" yafada yana bude note book din saikuma yabata yace ta bude wadanda sukafi bata wuya
Babu musu ta amsa ta budomashi wadanda ke mugun bata wuya nan suka shiga yi
Sai gashi maganar Deen ta tabbata don tuni kai yafara daukan chaji suka fara hada gumi.
Sai gashi kafin 4pm sunyi covering abubbuwa da dama don Deen is slow amma a bangaren karatu he's so fast and talented don yasan yadda zai fayyacema mutum abu nan da nan ya dauke gashi kuma anci sa'a kan mutumiyar taku naja sosai
Alarm din wayarta ya katsesu hakan yasasu Dagowa tare
"what's that?" inji Deen
Fuska a tur6une don bataso su tsaya yanzu ba tace
"Alarm nasa don karmu wuce lokaci mummy tayi farfesu na, mtcheew I swear I don't want to go now" tafada tana qara 6ata fuska
Murmushi Deen dake kallonta yayi yace
"but you have to, worry not ai zaki ida a gida, tomorrow ma saikiyi trying wasu abubbuwan idan muka hade monday sai inyi checking"
Shiru tayi cikin zuciyarta tana cewa kokuma ta amshi phone number dinshi idan tasamu matsala ta kirashi? Saikuma wata zuciyar tace no, ba ajinta bane ta tambayi number shi ba shi be tambaya ba, Wannan zubar da class ne
Hakan yasata miqewa tsaye tana cewa
"ok, thanks so much, ya na iya?"
Shima miqewa yayi yana kallon yadda take tattara stuffs dinta
Tattaro wasu yayi yabata hakan yasa ta dago ta kalleshi, Murmushi yayi mata itama ta maida mashi martani sannan ta amsa ta cusa a jakka cikin zuciyarta tana gulmar yadda Murmushi keyi mashi kyau
Saida tagama tsaf ta rataye jakkar ta dago ta kalleshi taga yana maida mask dinshi.
Tare suka fito yana qara gayamata logics da dabarun mathematics
Awaje ma students keta tafiya da alamu Suma sun gama, duk yadda zee taso yabisu qi yayi, ganin yanata kawo mata excuses duk na zamewa ga binsu yasata kyaleshi don dama bata wani qware wajen naci ba, haka tashiga motar da bala ya budemata ta zauna tana kallonshi ta window
Tsaye yayi shima yana kallonta hannunshi rungume aqirjinshi fuskarshi dauke da guntun Murmushi
Saida bala ya tada motar sannan ya shiga daga mata hannu yana Murmushi
Ganin haka yasa ta dagamashi yatsu itama tana Murmushi har suka fice
Bin motar yayi da kallo har saida ta fice daga school din sannan ya sauke ajiyar zuciya ya maida hannayenshi cikin aljihunan rigar yana sake qanqame jiki shima yanufi hanyar fita
Yau yafi jiya shan wahala kafin yasamu abin hawa suka shilla suma.
***
Koda zee ta isa gida saida tafara biyawa dakin mummy ta gwadamata takardar practical din, dama tun kafin ta fita ta zari wata takarda wanda sukayi practical aciki saita rubuta date din ranar asama yadda abin zai qara armashi shiyasa mummy na dubawa ta yarda ta maida mata abinta ta sallameta.
Shikau a bangaren Deen yana komawa gida ya duqunqune cikin bargo yana makarkatar sanyi, dama qaqa lfyar giwa?
Haka kaka taita mita akan ai dama ta hanashi fita ya nace ai ga irinta nan, shidai jinta kawai yake amma ko uffan bece ba
Hura wuta kaka tayi tasamu garwashi sosai tasa cikin wani abu kamar irin borner dinnan na qasa saidai Wannan yafi shi girma ta cikoshi takawoshi dakin sannan ta tado din dakyar yazo ya tsaya kusada garwashin don dumama jiki, be tashi daga gaban garwashin ba saida aka fara kiraye2n magrib sannan ya tashi yayi alwalla da ruwan dumi da kaka ta dumama mashi sannan yayi sallarshi agida don ga yadda yake ji dinnan bazai iya fita yashawo iskar waje ba
Yana zaune har akayi isha'i itama ya tashi ya miqata sannan yasha shayin da kaka tayimashi yadanci tuwo sannan ya kwanta, yau saidai kaka tayi aikin tatarta ita kadai.
Zee kau kusan raba dare tayi tana karatu, saida taga idanunta sun fara yimata yaji sannan ta hqr ta kwanta
Washegari ma yini tayi garden dinsu tana karatu, sallah kawai ke tadata, akwai wurare dayawa da duk bata fahimta ba hakan yasa take ticking βοΈ wajen akan idan sun hade dashi gobe saiya gwadamata
Abinci ma sai mummy ta mata magana take tunawa dashi, yau ma saida taji kanta na neman darewa gida biyu sannan ta shafawa kanta lfy ta hqr ta kwanta
*MONDAY*... βοΈ
Ummin fasihu π§π»ββοΈ?
8/2/21, 9:33 PM - Buhainatπ: *ππ»ββοΈDEEN ππ»ββοΈ?*
*017*
*MONDAY*
Kasancewar jiya bada wuri ta kwanta ba yasata makara wajen tashi don tunda ta tashi dakyar tayi sallar asuba takoma bata tashi ba sai 8 da mintuna
A gaggauce tayi shirinta sannan ta sauko ta cuccusa breakfast don tasan halin mummy bazata barta ta tafi ba idan bataci ba
Saida tagama komai tsaf sannan tayiwa mummy bankwana, daddy dama tun shekaran jiya yayi tafiya.
Babu 6ata lokaci ta isa parking space inda bala yake yana jiranta, suka shishige motar yabata wuta suka fice daga gidan.
*UMYAU*
Direct library ta nufa tanayi tana duba wristwatch dinta, 9 harta gota hakan yasata qara pace dinta.
Wata ajiyar zuciya ta sauke data shiga library din saboda hangoshi datayi can qarshen library din
Dukda Kanshi a kife yake kan desk hakan be hanata ganeshi ba, hakan yasata nufar seat dinshi direct.
Saida taja kujera ta zauna sannan tadan bubbuga desk din ganin ko motsawa beyi ba.
Ganin yadda yadanyi kyarma lokacin da take bugun desk din yasata sanin be san da ita dinba, wataqila ma barci yake
Dagowa yayi daga kwancen dayayi ya sauke idanunshi dasuka danyi surkin ja akanta
Dan Wara idanu tayi tace
"subhanallilah! Baka lfy ne?"
Dan Murmushi yayi sannan ya zauna sosai ya bude baki yace
"you're late"
Jin muryarshi tadan dashe yasata cewa
"yakuma naji muryarka haka? Are you ok?"
Ganin damuwa a fuskarta yasashi jin dadi, koba komai ta damu dashi kuma ta gano he's not ok
Gyaran murya yadanyi don maqogwaronshi yayi clearing yace
"am ok, kawai slight mura ne"
Maida fuskarta tayi kalar tausayi tace
"ayyah, hope kasha magani"
Daga mata kai yayi kawai yana Murmushi
"Allah ya sawwaqe" tafada tana kallonshi cike da tausayawa don yanzu mugun tausayi yake bata
Da amin ya amsa, ganin irin kallon datake mashi yasashi cewa
"ya weekend? Hope anyi abin kirki" yafada yana kallonta a dage
Hakan yasa ta watsamashi harara tace
"cemaka akayi ni lazy ce kamar kai?"
Bata fuska yayi
"O'O! Ni ba lazy bane"
"O'O! Kai lazy ne" ta kwakwayeshi
Dariya sukayi gaba daya sannan yace
"how's the weekend? Hope kidanyi wani abu"
"yeah, bari kagani" tafada tana doro jakkarta saman desk
"saidai fa there are lot da bangane ba amma nayi musu alama so that I'll show it to you" tasake fada tana fiffido littatafan
Bude mashi tayi ta tura gabanshi shikuma ya dauka yana Dubawa
Saida yagama duba duka sannan ya dago ya kalleta yaga itama shi take kallo
Dagamashi gira daya tayi alamun ya?
Sai yayi mata Murmushi yana hade yatsu babba da manuniya π yace
"fabulous! Gaskiya kinyi qoqari sosai, banyi tunanin zakiyi covering duk wadannan ba"
Murmushi kawai tayi
"To yanzu lets go straight to the lesson you see yanzu to 10 gashi inada lecture at 10:30 and I guess kuma kunada na safe ko?"yafada yana wasu yan rubuce2
"yeah, amma mu sai 11"
Kada kai yayi kawai yana cigaba da rubutun saida yagama sannan suka shiga karatun gadan2.
Kamar yadda yace 10:30 nayi suka dakata bawai don sun gamaba saidai ba laifi sunyi abin kirki sosai.
Barinta yayi anan yawuce class itakuma ta cigaba har saida taga 11am takusa sannan itama ta tashi tanufi class
Koda tashiga class har anfara taruwa, can ta hangi su sumee wurin zamansu suma duk sun zubamata ido hakan yasata qarasawa wajensu fuska ba yabo ba fallasa
Matsa mata sukayi ta zauna tana cewa
"hello babes"
Duk amsawa sukayi da "hyy dear!!"
Sai deeya ta dora da
"yar halak, yanzu muka gama maganar ki"
Daga gira daya tayi tace
"really?"
Sumee ta amsa da
"yes, tundazu muketa zuba ido muga ta ina zaki 6illo amma shiru kakeji wai mallam yaci shurwa"
Murmushi tadanyi tace
"am late ne yau, ban fito da wuri ba"
"ayyah, harmun fara zullumi don kinga ranar friday ma saidai muka nemeki muka rasa, bala ma yazo mukaita nemanki dashi, qarshe dai muka hqr muka barshi, wai ina kika shiga ranar?"
Zee da tunda rukky ke magana hankalinta ke kan memo din hannunta tace
"gida na wuce, banajin dadin jikina ne lokacin"
"ayyah, To how are you feeling now?" inji nurr
"am feeling better" kafin ma ta ida rufe baki lecturer din lecturen dasuka dashi ya shigo hakan yasa duk aka nutsu
40mins suka dauka a lecture din sannan suka fito
Direct usual wajen zamansu suka nufa badon ran zee yasoba don ita wurin Deen taso wucewa saidai tasan wadannan pest din bazasu bari ba, kafarta kafarsu.
Ita yanzu da sunsani da sundan ja baya da ita don yanzu bata cika son hulda dasuba ba, She really want a space from them amma basa ganewa don kullum qara likemata suke kamar snail and it shell
Suna zaune su sumee nata hirrarakinsu suna Dariya itakau zee jinsu kawai take saidai hankalinta ba anan yakeba, duk ya karkata yakoma ga aikin dazatayi a office din mr ibrahim, hakanan take jinta so nervous tana addu'ar Allah yasa karya 6ullomata ta hanyar da bazata iya sha ba.
Sosai takeson taqara nazari akan wasu abubbuwa kafin lokacin yayi saidai surutunsu ya hana, abin ban haushin ma surutan duk marar Ma'ana sukeyi don ba qaruwa ko kadan aciki
Haka dai taita hqr har 12 saura mintuna 10
Ganin ta tashi tsaye tana rataye jakka yasa duk suka dago suna kallonta
"ya dai?" inji rukky
"daidai" zee ta amsa a gajarce
"wani wuri zaki ne?" inji rukky again
"eh zani office din mr ibrahim ne" tafada absentmindly
Duk Wara idanu sukayi
"mr ibrahim? Hope komai dai lafiya"
"lfy, kawai chanza Wannan assignment din zanyi"
Duk sai yanayin fuskarsu ta chanza na yan seconds snn sukayi Saurin daidaita fuskarsu
"To? Kice Allah ya doraki akanshi kenan, lallai yau sai anyi ruwa harda qanqara, wai yau mr ibrahim keyin alfarma kuma wa ke" inji deeya in mixed feeling
Itadai zee batace komai ba sai gyara rolling din gyalenta datayi tace
"bari natafi, 12 zamu fara, see yah" ta qarashe tana dagamusu yatsu
"see you!!" suma suka amsa suna daga mata yatsu suma
Duk rakata sukayi da ido harta 6acewa ganinsu
"kutt.. Wai kunji abinda naji kuwa koko ni ke ciwon kunne?" inji rukky
"nima that's what am doubting, mr ibrahim da yimata alfarma? Ko zaiwa kowa alfarma ai sai inga banda ita yadda ya tsaneta dinnan" inji deeya
"lallai kam, kodayake qila kuka tayita mashi tana gamashi da Allah da annabi akan ya taimaka ta chanza wani wancan ba ita tayiba, kinsan class din datake taqama dashi duk rubace, bakuga yadda muka isketa ba sadda muka taddata chan ba?" inji nurr
"ba shakka! Qila kukan tayita yimashi tunda ai shi muka tadda tanayi amma girma ya fadi wlh" inji sumee
"hmm Allah yasa ga kukan kawai aka tsaya, kinsan mutum idan yanason abu yana iya komai don samun biyan buqatarshi" inji rukky
"kamar ya fa?" inji nurr
"She can give what She have to get what She want" inji rukky
"kai, nanfa daya, kinsan zee kema saidai idan fadin son ranki zakiyi amma kinsan bazata iya Wannan ba" inji sumee
"ko zata iya mr ibrahim bazai bata hadin kai ba, kinsanshi ai" inji nurr
Ta6e baki deeya tayi tace
"kudai ba'a shaidar dan adam"
Rukky ma ta kyabe baki tace
"ato"
Haka dai suka cigaba da hirarta don kowa Wannan abin beyi mashi dadi ba, so suke atafi ahakan a yimata amfani da mark din assignment din don sufa haryanzu basuga takardar ba, duk a tunaninsu zero din taci don harsun fara sata a list din yan carryover na bana (Allah ka rabamu da abokai masu fuska biyu π€²π»)
Saida tayi knocking sau uku sannan aka bata izinin shiga
Duba agogonta tayi taga 12 dot sannan ta tura kofar tashiga bakinta dauke da sallama
Dashi da wani saurayi tagani a office din don amsar saurayin taji yayinda mr ibrahim keta rubuce rubucenshi na fama
Qarasowa tayi cikin office din tana gyara zaman jakkarta
"good afternoon sir" tafada tana kallon wani wajen
Idan kun amsa to shima ya amsa, hakan kuma ba qaramin 6ata mata rai yayiba amma saita fuske tacigaba da tsayuwarta
Saida ya mula yasha iska sannan ya dago ya kalli saurayin dake zaune can gefe sannan ya kalleta
Kauda kai yayi sannan ya miqe tsaye riqeda wata takarda yana cewa
"are you guys ready?"
Hakan dataji yasa tasan da ita da wannan saurayin zasuyi tare, To shikuma meye tashi matsalar? Oho
Saurayin kadai ya amsa da "yes sir"
Kada kai yayi sannan ya wuce wajen wani chalk board dake daga gefen office dinshi yana cewa
"kowanne ya zauna bisa different chair"
Jin haka yasata Juyowa ta kalli saurayin taga shima ita ya kalla saita Kauda kai ta wuce wurin wata kujera nesa dashi ta zauna
"drop your bag on my desk" ta sake tsinkayar muryarshi yana fadin haka Batareda ya juyoba
Ba musu ta tashi tawuce desk dinshi ta dora jakkar akai tadawo ta zauna daga ita sai pen sai calculator
Shiru office din ya dauka bakajin komai sai motsin chalk akan board din
Kasancewar ya tare board din yasa bata ganin komai sai motsin da bayanshi keyi sanadin rubutun dayake.
Shiru sukayi suna jiran yagama kowanne da saqe saqen dayake.
Yakusan 15mins sannan ya gama ya ba kowanne plain paper yana umartarsu akan answer kawai yake buqata a takardar
Duk amsa sukayi kowanne da addu'ar dayakeyi a ranshi sannan mr ibrahim ya koma mazauninshi ya zauna yana lura dasu
Da daddaya tafara bin questions din da kallo har takai qarshe
Wani slight Murmushi yayi forming a gefen bakinta don rabi da kwatan questions din shine karatun dasukayi da Deen ranar saturday
Babu 6ata lokaci ta zaro bironta ta budeshi ta dorashi a takarda tana basmallah
Aikin ya daukesu 40mins sannan saurayin yafara zuwa yayi submitting, yana ajiyewa mr ibrahim yayimashi izinin tafiya
Tafiyarshi da minti goma itama ta gama ta tashi itama takaimashi
Amsa yayi itama tareda bata izinin tafiyar, bata qara 6ata lokaci ba a office din tafice tanajin kamar taita tsallen murna
Da farko library tanufa saikuma ta duba agogo taga 1 tadan gota hakan yasata fasawa don tasan yanzu haka yana class don sunada lecturen qarfe daya
Wucewa tayi wajen da suke zama ta tarda wajen wayam babu su sumee
Hakan yayi mata dadi sosai don haka tayi zamanta tana ciro wata takarda tashiga rubuta questions din datake iya riqewa acikin wadanda sukayi yanzu don ba Deen yayi solving taga ko tayi daidai
1:30pm nayi ta rufe littafin ta tashi tanufi masjid din school din don yin sallah
Koda tafito wucewa class tayi a gaggauce saboda lecture dasuke dashi hakan yasa sukayi sa6ani da Deen don shikuma a daidai lokacin suka fito lecture
Shima masjid ya wuce ya gabatar da sallar zuhr sannan ya wuce gida don sosai murar ke nuqurqusarshi
Basu zee suka fito ba sai wajajen 3pm
Library tayi ko zata ganshi amma baya nan hakan yasa tanufi department dinshi taga duk sai tsiraru hakan data gani ne yasata tabbatar da yatafi gida, dawowa tayi class dinsu ta kira bala awaya akan yataho kawai don dama ita tace mashi yau sai 4 zaizo daukarta don da nufinta suyi karatun 1hr da Deen kafin sutafi gida.
Babu 6ata lokaci sai ga bala ya qaraso ya kirata ta fito suka wuce.
*WASHEGARI*
Kasancewar duk sunada morning lesson yasa basu hadu ba sai wajajen 11:30am
Zaune suke a wani silent cool wuri inda mutane basu fiye zurga2 awajen ba
Zee keta zuba yayinda Deen ya maidata t.v sai zabga Murmushi yake
"... Bakaji yadda naji haushi ba wlh, na tsani na gaida mutum yaqi amsawa, at that instant zan fara regretting gaisuwar, wai sai can ya tashi yana tafiya with that double crooked yams he called legs ya wuce gaban board yana muzurai kamar wanda ya hadiye gari, sannan cikin frog-like voice dinshi yace 'kowanne ya zauna bisa different chair' I was like 'dakace hakan, da bisa cinyarshi nace zan zauna?'"
Dariyar Deen data fito fili ya dakatar da ita
"haka kikace mashi?" inji Deen cikin Dariya
Harararshi tayi tace
"ya za'ayi incemishi haka? Cikin zuciyata nace hakan, all thanks to Allah dayasa ba'a gane abinda mutum ke fadi a zuciya da duniyar nan takoma war ground" tafada tana sipping juice din hannunta
Dariyar da Deen keyi yadan tsagaita yace
"but sai inga kamar zaifi idan ana hangen komai dake zuciyar mutum, kinga ko qarya mutum yayimaka zaka iya hangowa directly from the heart"
Dan Wara idanu zee tayi tace
"no, gwara dai da ba'a gani don some people dole saidai a zuciya zaka maida masu martani kamar dai Wannan mr frog din"
Murmushi yayi yace
"hmm but still gwara adinga gani, saboda wasu a waje they'll smile to you amma aciki they hate you kuma Kana tareda su always bazaka ta6a sanin whats on their mind ba amma idan ana gani kinga no more pretending"
Daga kafadu tayi tace
"that's their problem, so far hateness dinsu bazai yi affecting dina ba, To can su gane, ni bazan iya pretending inason mutum ba bayan ba haka bane har cikin zuciya, if I don't like you, To I don't like you ne and I don't care what people think about me, I just dont care"
Murmushi Deen yayi yace
"that's why mutane dayawa don't like you"
Dagowa tayi ta kalleshi tace
"mene?"
Shima kallonta yayi yana dan qara wara idanu yace
"yes, your I don't care manner yasa mutane dayawa basa sonki a school dinnan"
"harda kai ko?"
Dan zaro ido yayi yace
"ni?"
"yes, sau nawa kake cemun you dont like me? You hate me" tafada tana fuming
Qara wara idanu yayi yace
"O'O! Ni bance I hate you ba, kawai